Advertisements
Chapter 13 Reading Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar

Author :  Binta Umar Category :  Complete Novels

Chapter   13 / 29

36K to 39K   out of 86.8K words

kammala cin abincin Galadima ya gyara zamansa a nutse yace."Kazo kaji in da aka kwana akan magabar ko."!?


Omar ya risinar da kansa 'kasa.

Galadima yace."Hakikanin gaskiya iya bunkince munyi kan yarinyar nan da kake nema kuma mun tabbatar da abunda ke da akwai Omar wannan yarinya bata dace da ta zama matarka ba kuma uwar 'yayanka saboda hujjojin da muka samu masu karfi ne a kanta kaga na farko dai yarinya mutane da dama suna zarginta da cewar ba cikakkiyar macece ba, wato tana yawo 'kasa-'kasa da sunan sana'a tana zubda mutuncinta kaga kuwa wannan bata cancani da ta zama d'aya daga cikin alhalin wannan gidan ba duk da mun shaida da cewar mahaifinta mutumin kirki ne amma wannan ba zai sanya mu muna ganin kashi da rana mu taka ba."


Omar ya dinga goge gumin dake tsatstsafo masa a gushi ya dago yana kallon Galadima da jan ido wato idan ya kasance Azima 'batacciya ce to babu shakka 'Yarka ma 'batacciya ce."!!!! Abunda zuciyarsa take ta ingiza shi ya fad'a kenan!!!! Da kyar yace."Ranka ya da'de ni ina ganin wannan ba zai hana aure ba Wallahi duk sharri ne irin na mutane tabbas Tana kasuwanci amma ni a yanda na yarda da tarbiyarta ba zata ta'ba zubar da 'kimarta ba na yarda da yarinyar sosai ranka shi dade wannan duk sharri ne na mutane ina so a bani dama na aureta domin ina ganin kamar idan nayi hakan nayi jihadi ne."


Galadima yayi shiru yana nazarin maganar kafin yace."To shikkenan Omar mun amince maka da auran wannan yarinyar domim ba musan abunda yake lullu'be ba Allah ya sanya alkairi cikin lamarin yanzu sai ka fad'i a dadin lokacin da kake so a daura auran insha Allahu ni zan nemi waliyin yarinyar domin mu tsai da magana."


Wani irin farin ciki da annushuwa ya sauka a zuciyarsa godiya ya shiga yi yana fad'in"Za'ayi komai a gama cikin sati uku ko biyu nagode Allah ya kara girma."


Galadima yayi murmushi tare da fad'in "Babu kalmar godiya a tsakanina dakai Omar hakkinmu ne mu tsaya kai da fata kan lamuranku gabakid'aya Ubangiji Allah ya sanya alkairi a ciki Allah ya tayaka ri'ko."


Omar yayi masa sallama ya futa zuciyarsa wasai da farin ciki.


Sashensa ya nufa palon shiru babu kowa sai ya dinga mamakin suna ina yau babu hira kenan! ba tare da wata damuwa ba ya zauna cikin kujera wayarsa ya dauko yana sakin wani murmushi na jin dadi Test ya turawa Azima cewar komai ya kammala auransu nan da sati biyu uku don haka ta fara shiri."


Kiranta ne ya shigo wayar tashi bai san sanda ya dauka ba....Azima ta dinga murna tana dariyar farin ciki Shima taya ta murnar yake yana wani 'kan'kantar da murya tare da lafewa jikin kujera yana lumshe ido sosai yake sauraran sambatun Azima da take masa...."Nayi maka tanade-tanade masu kyau baby na shirya maka kaina! zan kula da kai zan jiyar da kai dad'in da baka ta'ba jin irinsa ba a rayuwa zan kula da kai domin ina mutukar sonka fiye da kaina!!!! Cikin wata iriyar murya take masa wannan maganar Omar ya shagala da inda yake kawai ya dinga biye mata.....Cikin wannan yanayi Aysha ta fito palon ta same shi...Sai ta zauna kan kujerar dake fuskantarsa tana kallonsa sai wani walwala yake kamar wanda akayiwa albishiri da gidan aljanna....Ganin ayshan yasa ya tsahirta da abunda yakeyi ya dai dai ta zamansa tare da cire wayar a kunnensa yace."Okey zan 'karasa jin tanade-tanaden da kikayi min anjima! bye." Ya kashe wayar yana fuskantar aysha da fuska a sake.


Itama kallonsa take babu yabo babu fallasa yace."Gimbiyata ya akayi ina abokiyar taki take ne."!?

Shiru tayi masa tana kallonsa yace."Kin san abunda ke faruwa kuwa."? Girgiza kai tayi alamun bata sani ba." Yace."My second wife tace tana mi'ko gaisuwarta gurinku, mussaman keee."!

Murmushi tayi tace"Shiyasa naganka cikin walwala da farin ciki ko? komai ya kammala yanzu an daina jin haushinmu ana ganin kamar mune muka hana aure hummm! Allah ya sanya alkairi."

Ya amsa da ''ameen." Gimbiya Aysha." Share shi tayi ta tsirawa tv ido ba tare da tana fahimtar abunda ake a tv ba lallai duniya budurwar wawa wai yau itace Omar ke fad'awa baki da baki zaiyi aure lallai idan baka mutu ba kana da shauran kallo.

Haka dai ya 'karaci surutan sa ya mi'ke ya fita cike da walwala da farin ciki ya kusa mallakar Azima sarauniyar zuciyarsa.


*****

'Bangaran Azima kuwa shiri takeyi sosai Hasina na tayata A tarihin Azima kaf bata ta'ba aikata zina ba sai mad'igo take d'an ta'bawa shima ba sosai ba wani sa'in ne idan sha'awa ta kamata take biyawa kanta bukata da d'an ya tsanta! *Wa'iya zubillahi!* To wannan ne ya sanya suka shirya ita da Hasina takanas ta kano suka nufi garin Sakwato domin ta samu maganin da zai dawo mata da budurcinta domin ya kankaro mata martaba da daraja a gurin Omar.

Sun samu magunguna masu kyau da tsada Azima ta saki kudi sosai suka dauko hanyar gida inda suna sauka Azima ta fara amfani da tarin magangunan matan da ta siyo garin sakwato na matsi dana ni'ima......Kullum sai ya kasance duk sanda suka gama waya da Omar din saboda tsabar bukatuwa da yanayin yanda magungunan ke tasiri a jikinta yasa bayan sun gama waya babu dare babu rana sai ta tusa d'an ya tsanta a cikin headquarter d'in ta sosai ta kwakule tas! har sai ta samu ta kawo sannan take hakura, *Ubangiji Allah ka kiyashe mu da ta'bewa*


'Bangaran Gidan Sarki kam shiri suke sosai dangane da auran dalili bikin auran ya kasance guda biyu dana Faisal da 'yar gidan Waziri shiyasa komai ya dagule.

Saura sati daya d'aurin aure Ashiru da Yunusa suka dinga shiga da wasu manya manyan jakuna na fata sai da suka shida da guda ashirin da hudu suka jere a palo kana gogon naku ya shigo ya tadda su Aysha na bin jakunkunan da kallo, Kishi a ma'kare a zuciyar Safarau wato har gida ya kawo musu kayan lefan sa to meye amfanin abunda yayi.


Ya tsaya kansu hannunwasa duka cikin aljihu yace."Iyayen gida gashi ku duba ku gani ko akwai abunda ake bukata sai na sanya a siyo."


Safarau ta kalleshi da jan ido tace"Haba Yayana wannan ai rainin hankali ne kayan ma sai ka kawo mana mungani ba zaka barmu muji da abunda ke damun mu ba ka duba fa kaga halin da aunyna ke ciki haihuwa ko yau ko gobe."


Yace."Daga abun arziki sai fad'a Safa Allah ya huci zuciyarku wannan akwatinan ba na kowa bane naki ne ke da Aysha ko wacce ta dauki set d'aya."


Aysha tace"Babu albarkacin wata 'yar iska da zanci kai kasan ba rashin suttura nake ba ka kwashe kayanka bana so."

Safarau tace"Ni haka wallahi bana bukata."

Ransa a 'bace yace."Meye amfanin wannan abun da kukeyi? ke Safa na lura yanzu zaman Aysha kikeyi a cikin gidan nan duk umarin da ta baki shi kikeyi to billahillazi ki kiyayeni ki shiga hankalinki dani! kema duk kin bi kin zama wata shashasha Shin kishi hauka ne? ko kuma akanku ka fara aure."!!!Fad'a sosai yake zazzaga musu aysha ta zabga masa wani matsiyacin tsaki ta mi'ke zata bar gurin Wuf!! ya ri'ke hannunta yana huci! suka had'a ido da ita....Sai ya sassauta ri'kon da yayi mata ganin yanayin da take ciki ya ta'bashi Ayshansa duk ta koma wata iri cikin jikinta ya kalla sai ya sakar mata hannu ta kama hanyar dakinta.


Fushinsa ya huce kan Safarau ya dinga zabga mata rashin mutunci...Ta mike a guje tana gurshe'ken kuka ta shige d'akinta Hijab dinta ta zaro ta fito a gigice ta kama hanyar fita kafin ma ya ankara tuni ta bude kofa a gaggauce ta fice! ya mike da azama ya bi bayanta Sashen Fulani ta nufa sai ya rufa mata baya.
[6/4, 10:35 AM] Bintu Novel: 71


Inda Allah yasa harabar gidan babu jama'a sosai da a yanda safarau ke sauri tana goge hawaye tilas wasu su fahimci abunda yake faruwa.... to sai Allah ya rufa asiri jama'ar da suke kai kawo a harabar gidan basu da yawa kuma hankalinsu duk ya dauke gurin ayyukansu hakan ya bata damar isa sashen Fulani cikin wani irin yanayi na damuwa da tashin hankali.


Cikin damuwa Fulani ta gyara zamanta tana kallon Safaraun dake wani irin kuka gwanin ban tausayi tace"Safarau kiyi shiru ki fad'a min abunda ke faruwa kin tayar min da hankali wallahi bana kaunar wannan hawayen naki idan wani abu mijinki yayu miki ki fad'a min ni a matsayin uwa nake a gurinki zan magance miki matsalarki."


Ta d'ago kanta tana kallon Fulani tana kara jin kaunar matar a cikin zuciyarta hakika bata da abunda zata saka mata dashi komai na rayuwa ta yi mata tunda tazo gidan bata barta tayi kukan rashin iyaye ba sai ta dinga tunanin me yasa ma tazo zata d'aga mata hankali yana da kyau duk wani abu da Omar din zai mata ta hakura ta khaleshi don darajar mahaifiyarsa......Tana tsaka da wannan tunanin ya shigo da sallama Fulani ta amsa masa babu yabo babu fallasa jikinsa a d'an sanyaye ya zauna yana mika gaisuwarsa ba tare da ta amsa ba tace"Me yake faruwa ne ? Safarau ta shigo tana kuka ina fatan ba kaine kayi mata wani abun ba."


Shiru yayi domin bashi da tacewa.

Tace"Shirun ka ya nuna min cewar kaina silar zubar hawayen marainiyar Allah, to kafin na yanke hukunci ina so in san abunda tayi maka ka sanya ta cikin damuwa."

Sai ya sake yin kasa da kansa cikin jin kunya sai dai yayiwa safarau karya amma shi tunda suke bata ta'ba yi masa laifi ba.

Cikin 'bacin rai Fulani tace"Kai nake saurare Omar."

Yace."Mama girki takeyi ta hanani don nayi magana shine laifi."

Fulani tayi jim! tana nazarin maganar ta kalli Safarau tace"Hakane kina girki kina hana mijinki."?

Safarau tace"Eh hakane Mama." cike da mamaki Fulani tace"To kan wane dalili kike aikata haka."

Sai wasu zafafan hawaye suka shiga zubo mata tace"Mama yau kusan wata biyu da kwanaki kenan idan mukayi abinci baya ci kullum zan aje masa haka zan dauke ya lalace bai ci ba, to shine na daina a je masa abinci saboda lalacewa yake.

Fulani tace"Omar kaine baka da gaskiya saboda 'barna sai ayi abinci da kai a ajiye maka ka'ki ci kuma saboda isa kayi fad'a wannan ba dai-dai bane to tukkuna ma ina kake cin abinci kai da kake da iyali sai ka bar nasu kaje kaci a waje."!?


Sai ya fara kame-kame Fulani tace"To kar in 'kara jin wata 'baraka ta fito daga cikin iyalinka shin kai ba abun alfaharinka bane kawunan matanka sun had'u mai zan sanya kai ka dunga cusguna musu shin ko don za kayi aure shine kake kokarin sauya d'abi'a."?

Omar yayi shiru da kai 'kasa bashi da bakin magana.

Fulani tayi masa fad'a sosai da sosai bai ta'ba ganin 'bacin ran mahaifiyarsa ba sai yau akan kuma safarau dole ya kiyaye domin idan akwai abunda ya tsana a duniya bai wuce ganin 'bacin rai a fuskar mahaifiyar tashi ba.


Fulani ta kalli Safarau tace "Ki goge hawayen ki kinji ko In dai ina raye a duniya ba zakiyi kuka da takaici ba duk wani abu in da yayi miki idan bai gamsheki ba kiyi maza ki zo ki fada min insha Allahu zan magance miki matsalar ki."

Safarau ta goge fuskarta sai yanzu zuciyarta tayi sanyi tace"Nagode Mama Ubangiji Allah ya kara girma yaja kwana."

Sallama tayi mata ta futa shi kuma Omar din ya zauna gefanta yana sake rarrashinta baya so ta dalilinsa ta sanya bacin rai a ranta shiyasa sai da ya tabbatar da ta gamsu da rarrashinsa sannan ya yi mata sallama ya fita.


****

To a tsakankanin kwanaki biyun da suka gabata Omar ya dai-dai ta ya rage abunda yake musu yanzu hankalinsa ya dauke gurin sabgar bikinsa da ya kasance saura kwanaki hudu masu zuwa.


****

Yana tsaka da aiki Akande Ya shigo ofis din nasa suka gaisa yace."Ina fatan ka samu labarin abunda ke faruwa ."!?

Omar yace."Me yake faruwa ne." ? Akande yace."Ranar Monday me zuwa zamuje Togo bud'e sabon company mu na sarrafa Kayan abinci Kuma shugaba yace."Kaine zaka jagoranci tafiyar saboda idan da kai komai sai yafi tafiya dai-dai sannan baza mu dawo ba sai komai ya dai-dai ta company ya fara aiki tukkuna."

Omar yasha mur!! yana kallo Akande yace."Shin wai me yasa Yalla'bai yake yi min hakane? kana sane da cewar yau saura kwanaki uku daurin aurena kuma zai shirya tafiya dani duk yawan ma'aikatan dake company nan dole sai ni nifa nagaji wallahi ko wace irin tafiya sai ace dole sai dani gaskiya wannan karon dole ne in shigar da korafina kan wannan al'amarin zan iya aje aikin wallahi."


Akande yace."Haba Oga Omar ai saboda kwazonka da jajurcewarka ya sanya Yallabai ke son sanya ka cikin al'amari yasan idan ka sanya hannu kan al'amarin zai fi tafiya dai-dai nima na fahimci dalilin da ya sanya Yallabai din ya kasa fad'a maka maganar baki da baki saboda yana jin nauyin fad'a maka yasan cewa daf kake daka angwance amma ni ina ganin babu matsala ai idan an daura aure ranar juma'a ranar litinin sai kawai mu wuce tare da iyalinmu kai ka dauki amarya kawai mu wuce tare ko yaya kace."!?

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Zan duba maganar ka abokina."! Akande yace."Yawwa ko kaifa kasan Yallabai na mutukar sonka dalili kenan da ka taka wannan matsayin da kake kai a wannan company nasan kana sane da d'umbin jamar dake maka 'bakin ciki da hassada kan baiwar da Allah yayi maka da yanda yallabai ke karrama ka shine dalilin da ya sanya nake so ka basu kunya domin idan ka bujire to dama su haka suke so bukatar su ta biya."

Omar yace."Kar ka damu Akande duk nasan abunda ke faruwa a wannan masana'antar kawai nasa ido ne ina kallon kowa kuma magana ta wuce insha Allahu na amince da tafiyar." Akande ya mike tare da mika masa hannu yace."Ni zan koma ofis." Sallama sukayi ya fita shi kuma ya cigaba da aikin dake gabansa.


****

Sai yamma li'kis ya shiga masarautar domin sai da ya tsaya suka tattauna da Yallabai Aliko kan tafiyar sannan ya nufo gida cike da nasarori a rayuwarsa.


Kai tsaye d'akin Aysha ya nufa jikinsa duk a sanyaye kwana biyu kawai idan ya tuna da ita sai yaji gabansa ya fad'i sai ya fad'i kalmar innalilihi sannan yake samun sassaci......Tana zaune kan sofa da wata 'karamar loptop a cinyar ta kallo take na film din barkwanci na Marigayi Rabilu Musa Dan Ibro shi da Marigayiya Aisha d'an kano, Dariya take ti'kawa yanzu babu abunda ke d'ebe mata kewa sai irin wannan fina finan....Tana dariya ta amsa masa sallamarsa ya karaso inda take zaune yana le'ken abunda take kallo yace.''Wai ke bakya gajiya da kallon wannan haukan ki zauna kina ta dariya aysha kamar wata shashasha."

Tace."Don dai baka tsaya ka kalli film din ba wallahi kai ma sai kayi dariya yace."Yau dai zan tsaya na kalli film din nan inga abun da kikewa dariya a ciki."


Loptop din ta kashe ta mike tsaye da kyar! sai ya riketa yana d'an hararata yace."Ina zakije aysha ke bakya tausayawa kanki ko."!? tace"Nasan wanka zakayi shine zan had'a maka ruwa." Yace."Nagode Aysha kije ki huta zan had'a da kaina."

Sai ta koma ta zauna da kyar! tana ya mutse fuska yini guda haka take fama da ciwoka 'kafafu mara baya kwankwaso da dai sauransu....Ya fito daga toilet daure da babban towel dinta da karamin a hannunsa yana tsane jikinsa yace."Aysha lokacin haihuwar ki yayi har ya gota baki haihuwa ko dai zamu koma gurin Dr Rakiya ne."!?

Girgiza kanta tayi tace"Dama yana haka ai ko mutum ya 'kara lokaci ko kuma mutum ya rage lokaci babu gurin da zamuje insha Allahu zan haihu idan lokaci yayi.''


Yace."Bana son ganinki da wannan 'katon cikin wallahi.....Murmushi tayi tace"Duk abunka baka kaini ba domin ni ajikina yake cikin yau yini nayi da ciwon mara inaji ma haihuwa zanyi."Yace."Allah yasa Aysha Allah ya rabuku lafiya."ta amsa da "ameen."


Yace."Wai duk babu rigunana ne a dakinki aysha." ? Tace"Gaskiya babu domin idan an kawo wanki ina kai maka su dakinka bari in dauko maka."

Da sauri yace."Zauna bari na dauko da kaina." Sai ya fita daure da towel din a jikinsa....Itama mikewa tayi tabi bayansa, Safarau na tsaye a bakin daining tana gyarawa taga ya fito haka gashi dama tubarkallah ya kara 'kiba da girma sai wani motsi jikinsa yake dariya ce ta kusa kufce mata ta 'kunshe bakinta tana kallonsa ya kalleta tare da girgiza kansa ya shige dakinsa.
Sai suka fashe da dariya ita da Aysha dake kokarin zama kan kujera....Safarau tace"Wai!! tubarkallah mutum sai kace yana cin 'karfuna jiki duk a murd'e! humm! Aysha dai shiru tayi ita kad'ai tasan abunda ke damunta......To ko da ya fito ma bai tsaya ba sai kawai ya fita domin daf ake da a kira sallahr magariba.


*****

Washe gari ya kasance saura kwana biyu daurin aure gidan ya dan soma hargitsewa da jama'a sai hada hada ake da shirye shirye ranar kuma Aysha ta tashi da wani irin ciwon mara da ciwon baya ga kafafu sun ri'ke da kyar take tafiya shiru tayi bata fad'awa kowa ba ta dinga daurewa har sai da gwaggo ta shigo da yamma ta fahimci nakud'a takeyi a fakaice tace"To idan taji ciwon yayi tsanani tayi maza tayi musu magana tace"To zatayi." Omar kam ai hankalinsa ya dauke sai shige da fice yake sam bai gane halin da take ciki ba ya shigo dakinta yana neman a gogonsa neman duniya ba'a ganshi ba dakinsa ya nufa domin ya duba nan ma babu sai ya nufi dakin Safarau sai kace jaraba kamar shi kadai ne agogonsa....Tare suka dunga neman agogon da Safarau basu ganshi ba.

Aysha ma ta kokarta ta shiga dakinsa lokacin yana dakin Safarau ta fara bunkicen neman agogo wata loka ta bu'de tana dubawa a take ta ciro wasu katikan d'aurin aure da sukayi masifar daukar hankalinta ta kurawa katin ido tana kallo.


_Mai girma Sarkin Kano Sarki Salisu Abdullahi Na farin cikin gayyatar 'yan uwa da abokanan arziki daurin auran 'yayansa wanda za'ayi ranar Juma'a 5/7/2005 Za'ayi daurin auran cikin gidan Sarki da misalin karfe biyu da rabi bayan sallahr juma'a_

*UMARUL FARUK SARKI SALISA*

13 / 29