Author : Binta Umar Category : Complete Novels
gwara in tafi kawai."
"Mtsssw! Wai Azima me yasa kike hakane? na fad'a miki babu abunda zai faru wallahi ku sunanki ya fito cikin lamarin zanyi kokarin kareki tunda ai kema ba laifinki bane nice na tilas taki kwana daya kacal sai kice zaki tafi."
"Ki bari zan dawo bayan ankwana biyu amma yanzu dai hankalina yayi gida wallahi."
Aysha tace"Ai sai kiyi ta tafiya mtssw kin san ma abunda ya faru d'azu."!?
Azima tace"Menene."!?
"Shashashar yarinyar mana Safarau ita ta shigi min daki wai tana so muyi magana ta fahimta da ita shegiya da taga babu fuska sai ta 'kulle gulma da munafurcinta ta futa."
Azima tayi shiru tana naxarin maganar tabbas ta lura da yarinyar 'yar bin 'kwakkwafi ce kuma ta gama fahintar tafi Aysha wayo ta ko wanne fanni d'azu a gabanta suka fita ita da Omar din dole zata zargi wani abun to tunda hakane kuwa zata fara ta kanta tunda ta fara janyo hankalin Omar kanta abunda yayi saura a tsakaninsu shine aure.
Tace"Me yasa baki mari shegiya ba tana yawo kamar ka busheta ai idan nice tana fara magana zan tsinka mata mari nace ta fuce min daga daki bana son gulma."
Aysha tasa dariya tana fad'in"Kawai sai ta mareta babu dalili ai shiru ma magana ce wallahi sam bana son take shiga sabgata shegiya bini bini zakiji tana ma'kale murya aunt gimbiya ina kwana Yayana Anyi kaza da abu kaza. mtssw!
Azima ta 'kunduma mata ashar tana fad'in "Shegiya jikar mayu 'yar gidan makafi kawai." Aysha ta kalleta da mamaki zagin da takewa Safaraun yaso yayi yawa tom wai me yayi zafi ne."!?
Gyalanta ta d'auka ta yafa tace"Nifa ko don wannan figaggiyar yarinyar ta gidan naki zan iya tafiya Allah aysha bana so in hude idona in ganta."
Aysha ta mi'ke tana fad'in"Lallai 'kawata ke har kin so ki fini kishi ma irin wannan zagi haka gaskiya kina kishina da yawa nagode."
Tare suka fita Aysha na fad'in"Sai kace wacce ake kora kin wani rataya jaka zaki tafi ko karyawa bakiyi ba."
Azima ta kalli gefan da Safarau take zaune tace"'Kawata dole ce ta sani tafiya wallahi domin ji nayi kamar zan mutu jiya da daddare ana kokarin lashe ni to ni duk maitar mutum dole ya gaji ya hakura don Wallahi kurwata kurr! tafi karfin sarkin mayu ma ba irin wasu ba."
Aysha tayi sakare tana kallonta sai ta nuna mata inda Safarau ke zaune ta sunkuyar da kanta kasa tana danne hawayen daje zubo mata.
Aysha murmushi kawai tayi don bata da bakin magana.
Azima ta cigaba da cewa"Ai da gaskiya ta kawata kema kiyi taka tsantsan dake da yaronki da kuma abunda ke cikinki don wallahi wannan mayar da kike tare da ita da d'ai-d'ai da d'ai-d'ai sai ta cinye ku mayu fa basa tsoron Allah hummm! in banda abu ma irin na mutanan da kawai sai su d'auko wanda bai da asili wanda ba'a san daga inda ya fito ba su rike daga baya ya zama makashinsu Allah dai ya kyau......"Keeee!! mahaukaciya ya isheki haka."!
Muryar Safarau ta karad'e palon. sai suka jiyo suna kallonta cike da mamaki.
Ta nuna Azima da hannunta tana wani irin huci tace"Ki shiga hankakinki dani wallahi ko kin dauka ban gane inda kika dosa bane? shin wacece mayyar ? wallahi zaki min komai na hakura amma ba zaki min kazafin maita ba na zuba miki ido aikin banza kawai jahila mara kamun kai mace mara daraja da bin mazajen mutane!! duk wani abu da kikeyi wallahi tar! nake ganinki sai dai na kalleki kawai ke har kina da bakin da zaki ciwa wani mutumcin ci to ki sani ina raga miki ne saboda abu d'aya amma wallahi da ba don shi ba sai nayi miki wankin babban bargo banza kawai jahila mai bibibbiyar mazan mutane......"Karaf! a kunnen Omar da ya shigo palon....Azima na ganinsa sai ta fasa abunda tayi niyya ta fashe da wani irin kuka tana nuna kirjinta "Safarau ni kikewa wannan cin mutuncin kike zagina kamar baki sanni ba, da gyara sai cin mutunci da zagi."!!
Safarau da Aysha suka dinga kallon Azima cikin mamaki gani irin gurshe'ken kukan da take Aysha guri ta nema ta zauna domin ba zata ta iya jurar tsayuwa ba saboda jirin dake kwasarta.
Omar ya tsirawa Safarau ido ransa idan yayi dubu ya 'baci Yace." Safa yaushe ne kika zama mara kunya haka? Ko banza Azima ta girmeki nesa ba kusa ba ai kyayi kokarin ganin kin bata girma shin menene tayi miki kike nuna ta da hannu kina zaginta."
Hawaye ta goge tana sha'kar hanci tace"Zagina tayi tana kirana da mayya ni kuma bazan iya jura ba."!
Azima tace"Gaskiya Safarau kin ciki mace mai sharri yaushe na zageki na kiraki da mayya daga cewa Ki bani Abdul mu gaisa zan tafi shine na zageki to ai babu komai ga Aysha a zaune itace shaida."
Omar ya kalli Aysha dake faman cin kunnu sai ya mutsa fuska take kowa da abunda ya dameshi ita babban burinta taga cikin jikinta ya 'bare.
Dauke kansa yayi daga kanta yana jan tsaki! Sam yanzu baya marmarin ganinta ballanta magana mai tsayi ta had'ashi da ita, ya fahimci Safa ce bata da gaskiya tunda dai lokacin da ya shigo bai ji muryar Aziman ba kuma yana da ya'kinin Azimar ba zata kira ta da mayya ba, kawai dai ya lura Safaraun akwai abunda ke damunta na "bacin rai a cikin 'yan kwanakin nan shiyasa har shi bata bari ba gashi nan sai taga dama take girki ko kuma yayi ta mata magana tana shareshi.
Fuskarsa a had'e ya kalleta yace." Ki bata hakuri kafin ta tafi kuma wallahi duk sanda na sake ganin kinyi mata figala da rashin kunya ranki sai ya 'baci Safa wannan itace tarbiyar da aka baki kema ina yabon ki sallah zaki kasa alwala to karki sake mu sanya 'kafar wando guda dake."! Fad'a sosai yake mata ta dinga share hawaye murya na rawa ta bawa Azima hakuri ta shige dakinta a guje tana wani irin kuka.
Omar ya kalli Azimar a nutse yace."Muje in saukeki a gida ko." Aysha tayi saurin d'ago kanta tana kallonsu Yayi wani irin shan mur!!! ko kallon inda take Baiyi ba ya sa kai ya fuce daga palon
Azima tace"Kawata ya kikaga wannan aikin nawa." ta mike da kyar tana kallonta tace"Ai ni na rasa ma abun cewa Azima sharrinki yafi na shaid'an duba don Allah kinyi abu kuma kin juyar dashi kanta."
Azima tasa dariya ta bata hannu suka tafa Aysha ya'ke kawai takeyi amma al'amarin ya d'aga mata hankali shin me zai sanya Azima ta tsananta kishinta kan Safarau bayan ba miji suka had'a ba, babban abunda ya sake d'aga mata hankali shine kalmar Omar ta karshe kafin ya fita, Wato dai yana nufin shine zai kaita gidansu anya kuwa wannan al'amarin ba abun dubawa bane.?
Ta jima a zaune a palo tana nazarin al'amarin kafin ta mike ta shiga daki kwanciya tayi kan be bacci mai nauyi ya dauketa.
To haka dai gidan suka yini cikin bakin ciki da bacin rai ba kamar Safarau da take jin kamar zuciyarta zata fashe saboda kunci da halin damuwa da yake ciki.
Shima da ya shigo bai nemi kowacce ba yayi zaman shi a palo yana kallace kallacen sa dama ya riga ya gama ciko cikinsa sashen mamansa, karfe goma sha biyu da rabi na dare ya kashe tv yana kokarin shiga dakinsa ne ya jiyo kukan Abdul dake dakin aysha.
Kwata kwata baiyi niyyar shiga dakinta ba duk kuwa da cewar ranar kwananta ne yana so ya nuna mata kuskuranta to amma kukan da Abdul keyi ya daga masa hankali ya riga ya san muguntar aysha zata iya hanashi nono yasha.
Ya tura kofar dakin ya shiga hannunwansa goye a bayansa.
Tana kwance rigingine Abdul din na saman ruwan cikinta tana lallabashi bacci takeji sosai amma yaron ya hanata sai kalatar nono yakeyi shiyasa in dai yana gurin Fulani take jin dadi.
Tana jin sanda ya shigo dakin sai tayi luf ta dauka ai ba zai shigo ba ya kunna fitila haske ya gauraye dakin murya a cunkushe yace."Me akayi masa yake kuka ne."!?
"Banza tayi masa ta dauke kanta.
Ya sake maimata maganarsa.
Da kyar tace" Shi wannan sai anyi masa wani abu zaiyi kuka rigima ce kawai."
Ya rankwafa kanta yana kokarin daukar yaron nuffashinsu ne ya had'u guri guda ita dashi suka sauke ajiyar zuciya a tare Abdul din ya dora a kafadarsa yana rarrashinsa yaron ya sake rikicewa da kuka....Sai ya zauna yana duba jikinsa yaji zafi da akwai alamun zazzabi a jikinsa.
"Ina magungunansa suke? akwai alamun zazzabi a jikinsa." ta jiyo muryarsa cikin baccin dake fizgarta.
Shiru tayi masa sai da ya sake magana sannan ta mike zaune tana mutsika idanu ta sauka daga bed din dauke kansa yayi yana jan karamin tsaki ta je ta dauko masa maganin kar'ba yayi ya mike ya fita, Aysha ko a jikinta ta koma tayi kwanciyarta dama so take ta samu ta sake tayi baccinta.
Palo ya zauna ya bawa yaron magana kana ya cire masa riga ya barshi daga shi sai pampas yana jijjigashi dayi masa addua cikin ikon Allah ya samu bacci ya dauke shi sai ya dora shi saman cikinsa ya dafe da hannunsa bacci yake so yayi amma kuma tunanin rayuwa ya hanashi yayi sai gefin asuba bacci mai nauyi ya dauke shi.
Karfe bakwai na safiya ya farka ya dauke Abdul din ya nufi dakinsa tunda yake sallahar asubah bata ta'ba wuce shi ba sai yau yau din ma ya tabbatar da cewa tashin hankalin da yake ciki ne ya jawo masa haka....Wanka yayi ya kimtsa jikinsa lokacin Abdul din ya tashi yana ta wasa da kafafunsa, sai ya gyara dadduma ya tada sallah.
Lokacin da ya fito palon shiru ko wacce na dakinta sai Ikilima dake ta faman aike-aike da goge goge ta zube har kasa tana gaishe shi ya amsa tare da mika mata Abdul ya fita daga palon ba tare da ya tunkari ko wacce ba.
Yana fita sai ya nufi sashen Nanne.
Cikin mutunci da mutuntawa suka gaisa tana tambayarsa iyali yace "Sunanan lafiya kalau."
Ganin yanayin sa ya sanya tasha jinin jikinta tace"Ina fatan dai lafiya Omar kwana biyu hankalina ya kwanta aysha ta soma samun nutsuwa ina fatan babu wata matsala ko."?
Ya sauke ajiyar zuciya tace"Omar Aysha ce ko."!? Ya dago kansa yana kallonta gaskiya yana tausayawa matar saboda itama bata da kwanciyar hankali a kullum zancan ta aysha aysha ha'kika Aysha bata yi musu adalci ba.
Omar yace."Nanne ina ganin Aysha zata dawo sashen nan da zama saboda wasu dalilai guda biyu."
Tace"Omar fad'a min abunda ke faruwa."!Nanne tafad'i maganar jikinta a sanyaye.
A hankali ya warware mata abunda ke faruwa da yanda take yunkurin zubar da cikin jikinta.
yace."Ni yanzu tsorona daya shine in fita aiki ta aikata abunda tayi niyya shine dalilin da ya sanya nazo na shaida miki halin da ake ciki.
Nanne ta jima kanta a 'kasa wani irin bakin ciki da takaici na cinta ta dago kanta suka hada ido Omar yayi saurin yin kasa da kansa ganin ruwan hawaye a kwarmin idanunta hakika aysha tasa mahaifiyarta ta zubar da hawaye a kanta tabbas batayi mata adalci ba.
Tace"Kayi hakuri Omar a halin yanzu ni bani da abun cewa wallahi na rasa yanda zanyi da Aysha amma babu komai idan anjima zan shigo sashen naku insha Allahu.
Yace."Babu damuwa Nanne zan koma fada domin yau bamu da aiki."
Tace."Allah yayi maka albarka Omar ka dai cigaba da hakuri kaji ko insha Allah kai ke da riba.
Ya fita daga palon yana dan jin sassauci a cikin ransa.
Nanne ta sanya hannu ta goge kwallar dake idanunta wannan ba'kin ciki dame yayi kama? Wai Aysha me take so ta zama a rayuwarta daga wannan sai wannan a tsakanin kwanakin data koma dukaninsu sun kwantar da hankalinsu ganin ta samu tana zaune lafiya ashe tsugune bata 'kare ba, idan Aysha tayi kuskuran zubar da cikin jikinta to babu shakka zata futa daga cikin al'amuranta gabakidaya zata yafewa duniya ita.
Nanne ta kasa barin maganar cikin ranta sai da ta sanar da gwaggo ta dunga salati tana jajanta lamarin.....Tare suka nufi sashensu Ayshan.
Aysha murna tayi sosai da zuwansu sai dai yanda taga yanayin Nanne yasa tasha jinin jikinta sai ta rage zumudi da walwalar da take.
Fad'a sosai Nanne keyi mata ta inda ta shiga ba tanan take futa ba gwaggo dai tayi shiru sam bataga laifin Nanne ba domin itama lamarin ayshan ya soma furgitata
Cikin kuka tace"Nanne nifa bani da ciki kuma wallahi duk abunda yaje ya fada muku kar........! Ai bata karasa maganar tata ba Nanne ta mi'ke tsaye jikinta na kyarma ta zabga mata wani irin mari Aysha ta kwala 'kara zata mike Nanne ta sake kai mata wani marin "Dan Ubanki mijin naki ne makaryaci ashe dama baki da mutunci Aysha ashe baki nutsu kin shiga hankalinki ba ko! kina so kiyi sanadiyata ko Aysha kika kasheni Ban yafe miki ba."! Sai ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya zubewa tayi kasan kafet.!
Gwaggo tace" Haba ke kuma Nanne meye haka ? kar kiyi mata baki shi wannan kukan naki bashi da amfani a tare da ita."!
Ta kalli Aysha dake cikin tsananin tashin hankali da rud'ani tace"Kiyi maza ki nemi gafarata tun kafin kiga sauyi rayuwa hakika aysha baki kyautawa rayuwarki sannan baki kyauta mana meye ribar ki idan kin zubar da cikin sinna yanzu ba kyajin tsoron Sarki yaji labarin abunda kikayi kin san dai dole ransu ya baci saboda wannan abun da kike so ki aikta ba karamin abu bane gaskiya kin bani mamaki aysha."""" Da rarrafe ta karasa har inda Nanne take ta rirrike mata kafafu tana wani irin kuka tace"Nanne ki yafe min don Allah na hakura dama sharrin shaid'an ne ki daina zubar min da hawaye na hakura zan haihu na hakura na hakura."!! tana kuka take maganar.
Nanne ta mike tana gyara yafen ta tace"Gwaggo tashi mu tafi ke kuma Aysha ina nan ina zuba ido naji labarin zubewar ciki karki fasa abunda kikayi niyya."
Gwaggo ta mike suka fita rayukan su duk babu dadi....A falo suka tadda Safa ta gaisa dasu cikin mutumci sannan sukayi mata sallama suka fita.
'Karfe biyar da rabi ya shigo yaji kamshi girki tundaga shigowarsa yau Safa tayi niyyar shiga kicin kenan.
Zama yayi cikin kujera tare da kurawa kofar dakin Aysha ido......Ikilima ta fito daga dakin suka gaisa nan yake tambayarta Abdul tace"Yana can sashen Fulani."
Ya mike ya nufi dakin Tananan a kwance gurin da suka barta taci kuka ta koshi idanunta sunyi fulu-fulu har wani zazzabi zazzabi takeji....Tana jin muryarsa a kanta ta mike da sauri tana watsa masa matsiyacin kallo....''Hankalinka ya kwanta kuma bukatarka ta biya mahaifiyata ta zubda min da hawaye burinka ya cika ka hadani da iyayena kan biyan bukatarka wai shin haihuwa da kai dole ne? zakace lallai tilas sai na zauna da cikinka har da hadani da iyayena wallahi sai Allah ya saka mun." Tana kuka take maganar.
Yayi jim! yana kallonta Nanne tazo kenan ? yafada cikin ransa gyada kansa yayi ya juya baya hanyar futa ya kama ta bishi da kallon tsana tana ji kamar taje ta sha'ko wuyansa tayi ta dukansa ko ta huce takaici
To haka gidan suka kwana gabakidayansu cikin kunci da damuwa Omar yayi musu kaura baya shiga dakin ko wacce a cikinsu lura da yayi da yanda Safarau ta dauki fushi dashi tun ranar da ya sanya ta bawa Azima hakuri take fushi sai kawai ya watsar dasu idan ba kwakkwarar magana ce ta kama a tsakaninsu baya sauraransu abinci kam sai ya ga dama yake zama yaci idan baiyi ra'ayi ba sai kawai ya zauna sashen mamanshi ya cika cikinsa yayi hira da 'yan uwansa Faisal ma ya zo hutu tare suke cin abinci su sanya d'ansu Abdul a tsakiya suna masa wasa.
Baya shiga sashen sa sai kwanciyar bacci wannan lokacin ko wacce tayi bacci zai shiga ya bude dakinsa ya mayar ya kulle.... su raba dare dashi da Azima suna waya sosai take kashe shi da kalamai na soyayya shiyasa baya wani damuwa dasu Wannan sauyin da aka samu ta 'bangaransa yayi mutukar kashe musu jiki mussaman Aysha data bi ta zabge saboda laulayi da fargaba miji baya kula ka ita kuma girman kai ya hanata ta bashi Hakuri..... bangaran safarau kam al'amarin ya dameta don haka sai ta yanke shawarar tunkararsa domin ta bashi hakuri.
Karfe goma shaura na dare ya shigo gidan tana jin motsin bude kofarsa ta fito daga dakinta Salau-salau "Yayana barka da dawowa." Ya dan Juyo kad'an ya kalleta babu walwala a tare da ita yace."Sannunki da gida." Karamar jakar dake hannunsa ta kar'ba ya mi'ka mata wayoyinsa kana ya bud'e dakin tabi bayansa.
Ita ta taimaka masa ya cire kayan jikinsa ya dinga binta da kallo yana ayyana abubuwa da dama akanta ko da wasa bai ta'ba tsammanin Safa zatayi masa wannan shirmen ba, gyaran murya yayi ta kalleshi yace."Kin daina fushin da kike dani kenan."?
Tayi 'kasa da kanta ba tare da tace komai ba girgiza kansa yayi yace."Kin bani kunya Safa wato kema yanzu kin waye kina kokarin ganina cikin matsala shin idan ban samu nutsuwa dake ba da wa zan samu? kin fi kowa sanin irin zaman da muke da Aysha yau da dadi gobe babu dad'i wannan halaye da kuka tsiro min dashi ya sanya ni naji ina jin sha'awar kara aure." Da sauri ta kalleshi idanunta suka fara far-far! Girarsa guda ya daga mata yace."Kwarai kuwa aure zan kara tunda kun kasa bani kulawa ke da Aysha ban san abunda ke damunku ba....."Yayana don Allah kar ka aureta."! tafad'a tana kokarin danne bacin ran dake taso mata tasan tunda yace zai kara aure to babu shakka sai ya 'kara ita tsoronta daya kar ya auro musu wannan Azimar.
[5/31, 9:50 AM] Bintu Novel: 67
Fuskarta ya d'ago da hannunsa guda yana kallonta tana ta kokarin danne hawayen dake kokarin zubo mata yace."Safa me yasa bakya so na kara aure."?
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Ba wai bana so kayi aure bane ni itace bana so ka aura wallahi zata tayar mana da hankali kai kanka ba zaka samu nutsuwa da ita ba."
Yayi bala'in shan kunu yana kallonta "Waye yace miki bazan samu nutsuwa da Azima ba? wai mai yasa ku mata kuka fiye son