Author : Binta Umar Category : Complete Novels
kwakwalrsa.
Duk da haka sai da ta fahimci sauyi daga gurinsa tun bayan fitowar ayshan hankalinsa ya koma kofar kicin bini-bini sai ya kalli kofar.....Jikinta duk yayi wani irin sanyi wanda a take taji wata iriyar tsanar aysha gami da wani azababban kishinta.
Mi'kewa take niyyar yi wata zuciyar tace"Ki daure kar ki nuna musu gazawarki sai ta koma ta zauna tana sakar masa murmushi cikin kissa ta fara 'kir'kirar labarai masu dad'i tana bashi aikuwa hankalinsa ya koma kanta suka dunga kyalkyala dariya tare.
Aysha ta fito daga kicin din hannunta rike da plate cike da soyayyan dankali da 'kwai idanunta suka nuna mata abunda ke faruwa.
Dauke kanta tayi taja wani matsiyacin tsaki ranta yayi masifar 'baci mutuka wato ya zauna ya tasa ta a gaba yana cin abincinta alhalin ranar girkinta ne sam baza ta yarda da wannan tsarin ba.
Safarau na ganin fitowar aysha sai ta sake sakin jikinta sosai ta dinga dariya tana fad'in"Allah Yayana da gaske nakeyi a lokacin naji zafi sosai kai gaskiya ranar nasha wahala." shi kuma yace."Yau ma idan kika yi min gardama haka zanyi miki." dariya tasa tana fad'in"Yayana kenan."!
Suka had'a ido Safa ta d'auke kanta ta mai da 'kasa a sake tace"Aunty gimbiya sannu kin tashi lafiya."!?
Ya juyo cikin wani irin yanayi yana kallonta sam baiyi tsammanin ta fito ba, ko kallonta batayi ba ballanta ta amsa gaisuwar ta, ta bude kofar dakinta ta shige hade da bugo kofar da karfi.
Duk suka bi kofar da kallo Omar baya jin dadi abunda aysha takewa safarau ba sam baya son irin wannan zaman na rashin fahimtar juna dole ne yayiwa tufkar hanci.
Ya kalli Safarau dake rungume da Abdu girgiza kansa yayi cikin ransa yake fadin"Kullum yarinya na d'awainiya da d'anki amma baki da abokiyar gaba sama da ita aysha abunda takeyi bata kyautawa gaskiya.
"Safa." Ta dago kanta tana kallonsa yace."Please kiyi hakuri kinji ko ki cigaba da abunda kikeyi ni ina gani kuma ina yaba miki kar don aysha ta'ki amsa gaisawarki kema kice zaki tsiri gaba da ita karkiyi itama zata daina insha Allah."
''Haba Yayana kar ka damu wallahi dama ai tun farko na shaida maka ni ta bangarena babu wata matsala insha Allahu zanyi kokarin ganin na kawo zaman lafiya a gidanka ka kwantar da hankalinka."
Yace."Alhamdullihi Nagode kwarai Safa Allah yayi miki albarka."
Cike da annushuwa ta amasa da "ameeen" zuciyarta wasai ga yanayin yanda taga fuskar ayshan tasan taji haushi tayi mirmishi cikin ranta tace"aunty gimbiya kenan nima ina da tawa kissar mu zuba ni dake.
Bayan ya kammala sai ya kar'bi Abdul din ya nufi dakinta dashi,
Tunda ta kalleshi sau daya bata sake kallonsa ba tana zaune kasan kafet tana shan tea....Ya zauna kan Sofa yana fuskantarta
Dago kai tayi ta kalleshi shima ita yake kallo ta mai da kanta kasa a hankali tace"Ina kwana." Ya amsa babu yabo babu fallasa ya kira sunanta.
Fuska a had'e ta kalleshi yace."Me yasa duk lokacin da safa zata gaisheki bakya amsawa ne."!?
Shiru tayi masa....Yace."Ina magana kinyi shiru...A fusace! tace"Meye ala'kata da ita da zan amsa gaisuwarta ta rike bana so."
Cike da mamaki yake kallonta yace."Wannan ba magana bace aysha kina musuluma kina kokarin kafurtar da kanki Safa 'yar uwarki kice laifi ne don ta gaisheki meyasa wai kullum kike so kiga raina na 'baci ne."!?
Banza tayi masa ta cigaba da kur'bar tea dinta.
Yace."To daga yau sai yau kar in 'kara gani tayi miki magana kin share wannan ba d'abi'a bace me kya......! kafin ya karasa ta d'aga masa hannu "Don Allah kayi min shiru ka kyaleni mana."! ta fad'a tana kallonsa da tsayayyun idanunta.
Kallonta yayi ransa a 'bace!
Ta cigaba da cewa" Ni ba munafuka bace kuma bana shiri da munafikin mutum anamimi wato ta zaunar da kai ta shirya maka magana ko? hummm! to a shirye nake wallahi dana ci ubanta ni sa'arta ce da zata dinga kai 'karata gurinka to me take so kayi min ? wallahi kaja mata kunne ta futa sabgata tunda bana shiga tata nice nake da bakin magana amma saboda anfi ni iya munafurci an rigani....Don Uwarta huruminta ne ta baka abinci kaci a yau ai dai ban futa daga lokacina ba har yanzu ballanata tace kai kuma ka bud'e baki da ciki kana ci kana dariya ga sauna ka aje ad'aki to ba zan yarda da wannan tsarin ba."!!!!!
Hannun kujera ya daka da karfi! ya mi'ke tsaye cikin tsananin bacin rai yace."Aysha ki kiyayeni wallahi! ki shiga nutsuwarki Saboda rashin d'a'a da kirki ni kikewa tsawa! har kina nuna ni da hannu akan an fada miki gaskiya? Wallahi na daina saurara miki ranki sai yayi mugun 'baci duk ranar da safa ta gaisheki kika ki amsawa kuma kar in 'karajin kina zaginta wannan ai rashin hankalin ne Yarinya kullum na hidima dake da yaronki bakya gani wai shin ke wace irin macace."!?
Tana kuka take fad'in"Sai dai duk abunda zakayi kayi min wallahi amma abunda nasa kaina shi zanyi kuma wallahi duk sanda ta sake shiga gonata wallahi tallahi sai na an zane ta a gidanan."!
Yace."Kisa a daketa nima na dakeki wallahi"!
"To shikkenan Ubangiji Allah yasa ta sake kulani ko kuma in ga yarona a hannunta a ranar sai ta gwammace kid'a da karatu."!
" Aysha kiyi abunda kike so nima zanyi abunda raina yake so." Fuuuuuu! ya fuce daga dakin a fusace!!! arba sukayi da Safarau a zaune kan kujera ashe bata bar palon ba, duk yanda yaso da ya dai-dai ta kansa ya kasa sai da ta gane ba tare da yace mata komai ba ya bude dakinsa ya shiga.
Kwata-kwata bata wani damu da yanayi da ya fito ba tasan sunyi fad'an da suka saba ne ita tana mamakin me yasa yake kokarin boye mata halin da yake ciki da aysha bai san motsi d'aya yayi ba ta gane inda ya dosa saboda yanda take saka masa ido dangane da zamansa da aysha....
Kwanciyarta tayi kan Kujera ta kuna tv tana kallo abunta, sai taji duk damuwar da take ciki babu ita.
Aysha kam kuka taci ta 'koshi tabbas maganar hausawa ta fito inda suke cewa d'an hakin daka raina shike tsone maka ido hakika yarinyar tayi mata bazata da yawa ta lura tana mata kisan mummu'ke ne! wanda ita kuma a rayuwarta ta tsani haka gwara kawai a fito ayi wacce za'ayi....Duk sanda wara rigima zata 'bullo a tsakaninsu ta lura ita ke haddasa musu ita tabbas dole ta sanja taku. Ita babban takaicinta ma yanda ta saki jikinta ya kwana ya hantse yana sasakarta amma saboda shi din butulu ne ya manta yazo yana ci mata mutunci kan shegiyar yarina yar gidan makafi.
***
Wanka yayi ya fito yayi shirin zuwa Fada ko da ya fito sai ya tadda palon babu kowa Safaraun ma ta shige dakinta....Fucewarsa yayi ba tare da ya tunkari ko wacce ba.
****
"Wai ke Azima waye ya fad'a miki ana sanya ne? wallahi idan nice da tuni an wuce gurin kina da kyau da kudi kina da diri mai kyau wanda ko wane namiji ya gani zaiyi sha'awar ki amma kin tsaya kina fad'in wai ke kunyar Aysha kunyar taci uwarta kawai kiyi ta kanki 'yar gari idan kuma kika zauna kallon ruwa to billahillazi kwado ne zaiyi miki kafa."
Azima ta sauke a jiyar zuciya mai zafi ta furzar da wani irin huci a bakinta ta kalli 'kawarta Hasina tace"Hasina maganarki gaskiya ce wallahi tallashi yanda nake son guy nan ina ji uwar data haifeshi ma bata sonsa. Tun yana a matsayin bawa nake sonshi kawai dai ina biyewa aysha ne muna tozarta sai kawai naga ta aureshi bayan tozarcin da take masa wai har tana jin haushi don nace masa bawa wanda ada ita ke kiransa da sunan.....Tabbas nasan yanayi mata yanda take so ne shiyasa ta iya zama dashi kuma na lura tana sonshi....Ni abunda ke daga min hankali shine guy baya sona baya son kallona ko da can ma ballanta na yanzu ko gaisheshi nayi baya amsawa ga wannan matsiyaciyar figaggiyar yarinyar da yake so Duk jarabar aysha sai da ta hakura domin ba karamin so yakewa yarinyar ba tunani nakeyi yaya za'ayi ni na kafa kaina nima na samu matsuguni cikin zuciyarsa.
Hasina ta sauke ajiyar zuciya tace"Gaskiya kinyi magana me kyau kuma abar dubawa amma ai baki san wani abu ba k'awata idan kina da kud'i kuma kina neman biyan bu'kata to magana ta 'kare wallahi na gazgata malamai da nake bi domin duk wani mataki da kikaga na taka to da taimakonsu kuma da gudumawarsu idan kin yarda zan raka ki gurin malamina da yake tsaye kan lamurana insha Allah zai taimakeki idan so kike ki mallaki zuciyar Omar a tafin hannunki na tabbata malam Iliya zai yi miki aiki yanda ya kamata."
Azima tace"Babu damuwa Hasina ko nawa ne zan iya kashewa kan Sadauki don gaskiya zuciyata tayi nisa a kan kaunarsa.
Hasina tace"Shikkenan sai mu bari sai wani satin sai muje amma zamu fita da wuri domin ana cika a gurin kin san duk malamin da ya iya aiki dole ki samu gurinsa cike da mutane.
Nan Azima da Hasina suka tsaida ranar zuwa gurin malam Iliya dake can garin bichi.
*Kika futar min da book Allah ya isa! Kika karanta baki biya ba kema Allah Ya isa!*
My numbers
*08089965176_07084653263*
Accont numbar
*0542382124.....Binta Umar gtbank*
_Ina mi'ko sakon godiya ta gareku 'yan uwa masoya na na kwarai nagode sosai da adduoin ku nagode Allah ya bada lada ha'kika ina mutukar alfahari daku kuma na jinjina kaunar da kuke min nagode muku A bisa ta'aziyyar da kukayi min na rashin da nayi na iyayena nagode_
[5/28, 9:42 AM] Bintu Novel: 64
Duk bayan kwana biyu limami da almajirai suke saukar al'kurani mai girma Omar idan yaje gurin yayi ta raba musu sadaka yana zaune cikin almajirai limami zai daga hannu yayi ta addua kan Allah ya biya bukatarsa to cikin ikon Allah sai ya soma ganin sau'ki cikin al'amarinsa a tsakankanin kwanakin aysha tayi sanyi albarkacin alkur'ani mai girma yanzu dukanin abunda ya umarce da tayi masa tanayi babu gardama in dai batayi masa abu to bata iya ba zaman lafiya sukeyi ita dashi.......Kullum Abdul na sashen Fulani idan baya gurinta to yana hannun Safarau.....Wani abu dake damun safarau shine ganin a tsakanin kwanakin da aysha tayi da dawowa ta fara laulayi yau da lafiya gobe babu sai ta d'aga hankalinta sosai ta sanya ido kan aysha tana zargin ko ciki ne da ita.
Duk sanda aysha zata gifta ta gabanta ta dinga kallonta kenan sama da kasa aysha ta sanja sosai tayi kyau da haske duk wani alamu ya bayyana na mace mai yaron ciki, shigewa take daki taci kukanta ta koshi don wani lokacin ma idan omar yazo ya tadda ta tana kuka sai dai ta 'kirkiri karya domin ta kare kanta.
Wannan 'Dabi'ar data tsiro da ita ta soma damunsa....ko yau ma da ya dawo daga aiki kai tsaye dakinta ya nufa domin ranar girkinta ne sai ya tarar da ita zaune a jikin gado ta takure jikinta cikin hijabi tana kuka don saboda tsananin kukan da takeyi ne ma ya sanya bataji shigowarsa ba.
Ya aje jakarsa ta gun aiki ya tsuguna gabanta tare da kiran sunanta.
firgigi ta dago kanta tana ganinsa sai ta hau goge fuska tana ya'ke yace."Yau dai ba zaki min 'karya na yarda ba na gani da idona wato dama haka kike rufe kanki a daki kiyi ta kuka safa me akayi miki."!?
Wasu zafafan hawayen suka suke tsinke mata.
Sai ya janyo ta ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta da 'kyar tayi shiru sai ajiyar zuciya take saukewa .
"Kiyi hakuri ki fad'a min abunda akayi miki safa insha Allahu ni zan maganance miki matsalar ki bana so na ganki cikin damuwa."
Ta sauke ajiyar zuciya tare da riko hannunsa a hankali tace"Babu komai Yayana kawai na tuno iyayena ne shine dalili."
Yace."Ban yarda ba akwai dalili domin sau tari dani dake muke zama muna hirar iyayen naki bakya kuka da shiga yanayi irin wannan ki fad'a min ko aysha ce ke miki wani abu idan na futa."!?
Shiru tayi tana sinne kai a 'kirjinsa.
Sai ya sake tambayar ta d'ago kanta suna kallon juna
"Aysha ce ke miki wani abu idan bana nan ko."!? sai ta sakeyin shuru tana farfar da ido ya tsuruwa fuskarta ido yana mamakin sharri na aysha wato dai ba zata taya shi rike amanarsa ba kenan.
Sakinta yayi ya mike tsaye ta mike ita tana kallon yanayin fuskarsa data sauya da bacin rai!! tace" Yayana babu abunda aunty gimbiya take min wallahi ba ita bace."
Yace."Magana ai ta wuce safa kin fad'i hakane duk domin ki kareta duk abunda aysha tace zatayi nasan xatayi nafi ki sanin wacece ita."
"Allah da gaske babu abunda take min ka yarda da maganata Yayana." Yace."Me yasa dana tambayeki daga farko kikayi shiru."!? kasa tayi da kanta tana wasa da hannunta.
Yace."Hakan da kikayi ya nuna min cewar da akwai abunda ke faruwa aysha ta tsawalla miki a cikin gidanan ta hanaki sakewa kullum kina daki kina kuka ina dalili."!
"Kayi hakuri Yayana." Shiru yayi ya nufi kofar futa sai tabi bayansa da kallo yana futa ta zauna kan bed tana tunani sam bata so yaje yayi mata masifa data sani takeyi tun farko da ya tambaye ta ta fad'a masa dalili to tace masa me? zuciyarta tace"Kice masa kina son haihuwa kema. sai ta yanke shawarar tunda yau kwananta ne idan ya shigo zata fad'a masa ko zasuje asibiti a dubata.
Koda ya fito daga d'akin Safarau sai sukayi arba da juna ya kad'a kansa ya shige d'akinsa ba tare da yace mata uffan ba.
Al'amarin sai ya bata mamaki lafiya 'kalau suka rabu da safe lokacin da zai tafi gurin aiki amma ya dawo yana wani cin kunnu....Sai kawai itama ta had'e girar sama da ta kasa ta wuce kicin inda Ikilima ke hidimar dora mata abincin dare tace"Ikilima kiyi min towon semo da miyae busashiyar kubewa kisa min nama sannan miyar tayi yajin attaruhu."
Ikilima tace"To ranki shi dad'e anyi an gama insha Allah."
Fitowa tayi daga kicin din ta zauna a palo na farko tana kallon tv zuciyarta na wani irin tashi a cikin kwanakin nan tana yawon jin tashin zuciya da bushewar ma'kogwaro tana ganin gobe idan Allah ya kaimu zataje gurin Dr Rakiya ta dubata sam! bata kawo cewar ciki gareta ba.
Ya fito cikin jallabiya mai ruwan 'kasa da dogon wando a jikinsa fuskarsa tar!! daga ni wanka yayi don ga alamun ruwa nan a kanshi babu cikakkiyar walwala ya karaso inda take.
Remot dake hannun kujera ya d'auka ya sauya tasha kanzil bata ce masa ba, sai ma 'kokarin barin gurin da take yace."Ina Abdu yake."!?
Ba tare data kalleshi ba tace."Yana can sashen fulani."!
"Ki koma ki zauna zamuyi magana dake."
Sai ta koma ta zauna tana kallonsa tayi wani irin shan mur ta lura abunda suka kwana biyu basu yi ba yau shi zasuyi tace"Ina sauraronka.
Volom ya rage ya juyo yana kallonta itama shi take kallo.
"Aysha menene kikewa Safa wanda ke sanya ta rufe kanta a d'aki kullum tana kuka bana son hayaniya kiyi min magana a nutse."! yana kallonta yake maganar.
Tayi shiru tana nazarin maganarsa ta ma rasa yanda zata auna maganar.....Wai shin me yasa Omar ke mata hakane? me yasa yake zuwa yana titsiyeta kan matarsa in dai kaga bacin ransa to akan matarsa ne ? wai me zatayi mata ne? wallahi har mantawa take da ita a cikin gidan sai ta ganta take tunawa da ita amma kullum sai yace tayi mata abu kaza da abu kaza.!
" Dake nake magana kinyi shiru aysha yanzu abunda kikeyi dai-dai kenan? yarinyar nan fa marainiya ce gaba da baya gashi tana miki biyayya iya iyawarta amma ke kullum burinki kiga kin 'kuntat........Bai 'karasa maganarsa ba ta mi'ke kai tsaye d'akin Safa ta nufa tana wani irin nishi na 'bacin rai!
Ya mi'ke da sauri ya bi bayanta Safa na zaune kan kujerar mudubi tayi wanka ta shirya tsaf tana daura dankwali aysha ta fad'o d'akin, sai ta mi'ke da sauri tana rarraba ido "Aunt gimbiya sann....Omar ya shigo dakin da sauri ya tari gabanta " Kar kice zaki daketa ko ki mareta Allah kika aikata d'aya daga cikin biyu sai na rama mata."
Hannu ta d'aga masa tace"Babu abunda zan aikata a cikin abunda kake zargina dashi kawai zan tambayeta ne." Yace."Wace irin tambaya kuma ai dani dake muke magana.
Shareshi tayi ta tsaya gaban Safa suka kalli juna Safarau taji gwiwarta tayi sanyi sosai gaskiya aysha tayi mata kwarjina mutuka sai ta sunkuyar da kanta kasa.
"Wa kike da suna ki d'ago kanki ki kalleni Zamuyi magana dake."!
Safarau ta d'ago fuskarta ta kalleta tana kokarin aro jarumta tace" Ina jinki aunty.
"Ina so don Allah ki fad'a min abunda nake miki a cikin gidanan wanda yake sanyawa kina kulle kofarki shin dukan ki nake? ko kuma dariya nake miki? zagin ki nake ko kuma ina miki wani abu makamancin abunda na fada yanzu."?
Safarau taji duk gwiwoyinta sunyi sanyi gaskiya idan tace Aysha nayi mata wani abu to tayi mata sharri sai tace aysha ma ko kallon inda take batayi ballanta ta shiga sabgarta ko had'uwa sukayi a palo kowa harkar gabansa yake.
" Answer me." Aysha tafad'a tana me tsura mata idonta da suka kad'a Sukayi jawur.....Safa tace"Aunt kiyi hakuri don Allah idan wani abu ya had'aki da mijinki ki daina sanyo ni a ciki ni dai bance masa kina min wani abu ba."!
Aysha ta ri'ke 'kugu tana kallonta cike da mamaki ya tana mata magana ita kuma tana sako wata banzar magana wai idan wani abu ya had'ata da mijinta.mtessw!!
Omar d'in ta kalla shima ita yake kallo jikinsa ya soma yin sanyi tace"Kaji abunda tace ko wato da kai da ita dukanin ku baku da gaskiya kai kazo ka titsinye ni da tambaya ita kuma na had'a ta da girman Allah ta fad'i gaskiya tana sako min wata magana shin ni da kai akwai wani sa'bani da muka samu wanda ya sanya take wannan maganar."!?
Dakin yayi shiru Omar na nazarin maganar ta, Ya kalli Safarau dake jingine da jikin mudubi yace."Safa tsakaninki da Allah da Annabi me aysha ke miki kike shiga kunci da damuwa bana son tashin hankali kuma bana son na shiga hakkin ko wacce daga cikin ku."
"Yayana nifa dama bance maka aunt tayi min wani abu ba kaine ka ki tsayawa ka fahimce