Advertisements
Chapter 9 Reading Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar

Author :  Binta Umar Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 29

24K to 27K   out of 86.8K words

kanku ne ? kan inje in auri wacce baku sani ba ai gwara in auri Azima ta da'de tana nuna min so da kulawa ina tunanin yanda take sona ke da aysha bakwa sona haka a kwanakin baya kinyi min korafi kan messages din da ake yawan turo min nace miki ban san wacece ba to Azima ce shin cikin ku ke da aysha wacece don na tafi aiki ta zauna ta shirya min kalaman soyayya irin wannan? har gwara ke kan aysha idan na dawo gida kina bani kulawa, Ni ina so inga ana kula dani sannan ana nuna min so da tattali babu laifi don na aureta saboda haka ki kwantar da hankalinki Auran Azima ba zai sanya ni na juya miki baya ke kanki shaida ce kan irin son dana ke miki."


Safarau taji kamar ta fad'i a gurin saboda tsanin damuwa da tashin hankali aure wata biyar har an daina yayinta za'ayi mata kishiya duk yanda taso da ta hana hawayenta zubowa sai da suka zubo ta....Omar ya rungumeta kam a jikinsa yana rarrashinta da mayaudaran kalamansa sai da ya kashe mata jiki da kalamai sannan ya dagota suka fuskanci juna rintse idonta tayi tace"Nasan kana jin yunwa ko in kawo maka abinci nan." ? Ya daga mata kansa kamar wani karamin yaro.


Sauka tayi daga jikinsa ta fita daga dakin tana nanata kalmar innalilihi wa'ina ilaihi raji"un!

Tana futa ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya nufi toilet wanka yayi ya fito kugunsa daure da towel da karami a wuyansa ya sanya gajeran wando da vest kana ya nemi kasan kafet ya zaune yana duba wayarshi test messages din Azima sun kai guda goma tun safe take turo masa har yanzu bai duba d'aya ba,


Yana kokarin dubawa Safa ta shigo sai ya aje wayar da sauri ya tare da abunda yake hannunta, ta zauna tana fuskantarsa tsaf ta hada masa abincin ya tubure wai sai ta bashi a baki haka ta dinga d'iba da hannunta tana bashi yana ci yana mata wani munafikin kallo ita kuma sai dariya take masa.


Bayan ya kammala sai ta mike ta gyara gurin ta dawo dakin toilet ta nufa tayi wanka ta fito daure da towel yau mijinta kawai take muradi domin an dade ba'a had'u ba...To shi kuma Omar burinsa kawai ya samu sakewa ya duba sa'konnin Azima ta kirashi ya kai sau biyar yaki dauka saboda gudun fushin Safarau.


Ganin Safa ta fito cinyoyinta duk a waje ya sanya shi sauke ajiyar zuciya sha'awarsa ta motsa shima dama a cikin yan kwanakin hakuri kawai yake yana dannewa amma a tsananin bukace yake gashi Azima na sake kunnashi da kalamanta wanda suke kashe masa jiki.


Hannu ya bude mata wai tazo aikam Safa babu kunya taje ya rungumeta kam! yana sansana jikinta suka dinga sauke ajiyar zuciya a tare a take al'amarin ya sauya.


Kimanin awa daya da rabi sukayi suka samu gamsuwa Safarau addua take Allah yasa ciki ya shiga ta samu kafin Azimar ta shigo itama ta fara tara 'yayanta.


Tare sukayi wanka ya daukota suka fito kana kallonsu kaga masoya na gaskiya sai farin ciki suke kamar basu taba samun sa'bani ba kan kirjinsa ya dorata yana shafa dogon gashinta haka bacci mai nauyi ya dauketa.


A hankali ya sauketa daga jikinsa ya gyara mata kwanciya ya mike tare da daukar wayarsa ya fita daga d'akin.


Kwanciya tayi kan kujera ya fara duba sa'konnin Azima yana murmushi kafin ya gama jikinsa ya mutu murus ya dinga tunano siffofin jikinta muryar ta yake son yaji don haka sai ya fara kirab wayarta.

Azima dake kokarin yin bacci ta duba taga numbarsa ce sai ta mike zaune da sauri ta kara wayar a kunnenta tare da narkar da murya...."Babyna me yasa ka'ki d'aukar wayata yau zuciya ta ta kusa ta buga saboda bataji muryar ka." Lumshe ido yayi ya sassauta muryarsa sosai yace."Aiki ne yayi min yawa amma naga test messages dinki duk na karanta naji dadin kalamanki kwarai." Tayi wata shashsheka tana sakin nishi na fitina tace"To ya iyalinka ina fatan suna lafiya? ina Abdul."!?

Yace."Kowa lafiya hope kema kina lafiya ya mutan gidan." ? tace."Duk kowa lafiya lau suna gaisheka."Yace."Inanan zuwa mu gaisa sosai zan shigar da maganata gurin manya bana jin za'a ja wani dogon lokaci."


Azima taji kamar ta fasa ihu saboda dad'i sai ta fara wata iriyar shagwaba tana narke murya wannan salon yayi masifar rikirkita shi kwanciya ya gyara yana sauraranta sai zuba masa kalamai take shi kuma yana lumshe ido.


Fitowar Aysha daga dakinta yayi dai-dai da lokacin da yake fad'in"Waye yace miki bana sonki? idan bana sonki ba zan tsaya na saurareki ba, maganar aysha kuma ki ajeta gefe guda Aysha bata isa ta haramta abunda Allah ya halasta ba aurane dake ba haramun bane saboda haka ni abunda na sanya kaina nakeyi wata mace bata isa ta sani abunda banyi niyya ba"

Sai da ta 'karaso tsakiyar palon sanna ya lura da ita dake akwai hasken fitula a palon suka had'a ido,Ya mike zaune da wayar a hannunsa idanunsa tsaye kan Ayshan yace."Zamuyi waya gobe in Allah ya kaimu kiyi bacci mai dad'i." Sai ya kashe wayar yana me tsira mata ido.

Kallonsa take ta rasa wane tunani zatayi a kansa ashe haka ya koma? cikin dare sun shanya baki suna bacci ya fito yana cin amanarsu wani irin takaici da bacin rai suka bijiro mata kai gaskiya namiji munafiki ne wallahi duk basa tsoron Allah. Tayi niyyar ta tanka masa sai kuma wata zuciyar ta hanata kawai ta kad'a kai ta wuce kicin yunwa ce ta tasheta dake ta kwanta da wuri bata ci abinci ba tace Ikilima ta bar komai a kicin in tayi bacci ta tashi ta dauko da kanta shine dalilin da ya sanya ta fito palon


Idanunsa tsaye kofar kicin din ta fito hannunta da plate a rufe dakinta ta nufa ba tare da ta kulashi ba....Itafa yanzu rayuwar kawai yin ta takeyi babu dadi ga wannan cikin na jikinta ya tsaya mata a ranta.......Tana shiga ta zauna ta fara cin jallop din taliya ce duk da a fulas take batayi mata yanda take so ba tafi son ana saukewa taci to amma bacci yaci karfinta, mikewa tayi domin ta dauko ruwa ya shigo dakin...Bakin frge ya karasa ya rankwafa har jikinsu na had'uwa hannunsa ya dora kan nata ta cire hannunta da sauri ta matsa daga gurin...Ruwa da lemo ya dauko mata ya mai da firge ya rufe.

Ko da wasa bata kalli inda yake ba cin abincin ta takeyi a nutse har taci iya inda take so ta mike ta nufi toilet wanko bakinta tayi ta dawo tayi kwanciyarta.

Ya mike ya isa bed din tsaye yayi a kanta yana kallonta tana lumshe ido wannan girman kan na Aysha na mugun 'bata masa rai!

A hankali ya zauna kusa da kafafunta ta janye da sauri tana jan tsaki, sai ya jawo kafarta guda d'aya yana kokarin d'aga mata rigar bacci.

Cikin jin haushi ta buge hannunsa tare da fad'in"Meye haka."!

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace."Na d'auka ai kurma ce."! Tsaki taja ta juya masa baya ba'kin ciki kamar ya kasheta.


Ransa a d'an bace yace."Kar ki kuskura ki 'karayi min tsaki kinji ko."!


Shiru tayi masa, sai ya fara surutai da neman magana duk don ta kulashi tana jinsa tayi masa banza haka ya gaji da maganarsa ya mi'ke ya fita.

Yana fita ta hau goge hawaye tana fad'in "Allah wadaran namiji munafiki Na tsanake Wallahi." Da kyar bacci ya d'auketa.


Washe gari wasai ya tashi yanzu ya sauko ya daina fushi dasu ko da zai tafi aiki sai da ya shiga sashen kowacce ya dubata sannan ya wuce gurin aiki.


Safarau ta gama girkinta ya zagayo kan Aysha ta yini tana bakin ciki da rashin walwala tasan yanda taga yana rawar jiki tun safe to tasan zai dameta ne kwana biyu tana hutawa dama Abdul ya dad'e a hannun Fulani tun sanda yayi wani zazzabi tace ciki ne yaje ta'bashi shine dalilin da ya sanya ta kar'beshi ta cigaba da rainonsa,

Aikuwa da wuri ya dawo gida yau domin biyar ma ba tayi ba kuma bai zarce ko ina ba sai sashensa da idan ya dawo daga aiki da wuri yana shiga fada ko kuma yaje sashen mahaifiyarsa ya huta yau saboda d'okin Aysha babu inda yaje.

Ganinsa ya shigo da wuri sai abun ya basu mamaki mussaman Safarau Aysha kam ta riga ta gane abunda yakewa tun safe yake wani lalla'bata da rarrashinta abunda ya jima bai yi mata ba cikin zuciyarta ta kudiri aniyar muzguna masa tayi rantsuwar komai nacin sa ba zai samu abunda yake so ba kuma dama so take su 'keba sai ya fad'a mata wace tsinanniyar ce suke raba dare da ita suna waya.

Da yakan kai tara zuwa goma a waje yau kam ana idar da sallahar isha'i ya shigo gidan.....Ya shiga dakinsa ya cire jallabiyar jikinsa 3qutar ya sanya a jikinsa sai singilet fara tas ya fito palon.

Aysha na ganin fitowarsa sai ta mike ta bar gurin ya bita da kallo yana girgixa kansa, har tayi wanka ya shirya bai shigo ba sai tayi kwanciyarta tana tunane tunane na neman mafita.

Shi kam d'an zama yayi yana kallon tashar Sky movies wani indian film suke mai suna Darr! yana son film din sosai shine abunda ya dauke masa hankali sai kusan goma shaura film din ya kare ya kashe tv dakin Safa ya nufa yayi mata sallama ya fita....Binsa tayi da kallo ranta yayi ba'kikirin ganin yanda yake ta wani rawar jiki kamar bai ta'ba kwanciya da Ayshan ba.


Bargon da take rufe dashi ya shiga ya fara lalubenta yana mata magana 'kasa-'kasa, sunanta yake kira cikin wata iriyar siga yana zura hannunsa cikin rigarta.

"Ka tashi ka futar min daga d'aki."! Tafada ranta a 'bace!

Sake 'kam-'kame ta yayi yana sakin wani irin nishi!

Ta mike zaune da sauri tana tureshi yana sake rikota.

Kuka ta sanya masa a wahalace tace" Wannan bayi bane kuma zalinci ne kana gaba dani sama da kwana uku kazo kuma kana yi min wani abu sam bazata sa'buba kaje can inda aka saba baka kayi amma ni nan ba banzar macece bace da har zaka dinga yi min irin wannan rainin hankalin wallahi."


Rungume bayanta yayi yace."Aysha har abadah ke tawa ce kuma dukanin abunda yake faruwa a tsakanina dake kece sila gaba da kike magana akai har abadah banayi dake bana jin dadin irin irin zaman da muke dake shiyasa ma nazo neman alfarma a yafe min kinji."!!

Ta ture kirjinsa tana watsa masa harara"Eh dole kace haka mana saboda jarabar ka ta ciyo ka sai ka tuna da Aysha ko ga Aysha wawuya wacce batasan kanta ba kayi mata ciki ka watsar da ita kana shan shagalinka da 'yan iskan 'yan matanka ai wallahi ka bani mamaki mutuka"


"Ni bani da wasu 'yan mata sai ke da 'Yar uwarki Safa kuma ita tuntuni mu dai-daita tsakaninmu kece kikeyin abubuwan da basu dace ba aysha don Allah ki fuskance ni mu fahimci juna."


"Dakata wallahi baka isa ka yaudare ni da wad'anann kalaman naka ba tuntuni an riga an wuce gurin ni halinka sai dai in fad'awa wani shi yanzu dai ina so ka fad'a min wacece ne kuke waya da ita jiya."!?

" Ban gane maganar ki ba Aysha." Yafada cikin kasalalliyar murya


Daurewa tayi ta sake maimata masa maganar yace."Linda ce abokiyar aikina."

"Linda."!? tafada tana kallonsa ya d'aga mata girarasa guda.

Girgiza kanta tayi babu shakka Omar ya mai da ita hamaguwa Linda ce take yin hausa tar!! Murya da taji na bahaushiyar macace ne.


" Idan baki yarda ba yanzu sai na kira miki ita a waya ki tabbatar da ita d'ince aysha ni me zanyi da mace bayan ina dake aysha!!!!!! idan ina gurun aiki sha'awa ta kamani siffofinki kawai nake tunawa dasu nake jin relief."! ya karasa maganar yana goga mata gemunsa a wuyanta.

Tsigar jikinta ta soma tashi da sauri ta hankad'e shi tace"Okey Linda abokiyar aikinka ko? itace take hausa kamar bahaushiya sannan abokiyar aikinka Linda itace kakewa kalamai har da fad'in tayi bacci mai dad'i hummm! to sai kaje gurinta ta biya maka bukatunka."


Tana gama maganar ta mike ta bar masa gurin kan kujera ta zauna tare da rufe fuskarta da duka hannunwanta.


Ya tsaya kanta yana 'kare mata kallo tabbas bashi da tacewa aysha ta gane abunda yake 'boyewa.


Dago kanta tayi ta watsa masa wani kallo kana tace"Ka matsa daga kaina mayaudari ma'karyaci Allah ya isa tsakanina da kai."!!!!!


A fusace! yace.''Aysha ni kikewa Allah ya isa."!?

Sai ta mike itama jikinta ya soma tsuma da hannu ta nuna shi "Nayi maka Allah ya isa sai me? ai kaine ka janyowa kanka ni zaka rainawa hankali ka had'ani da mahaifiyata kaje ka ha'intata wallahi nayi nadamar auranka da haihuwa da kai don da ina da yanda zanyi da wannan cikin na jikina da tuni nayi wallahi sai dai duk abunda zai faru ya faru me za'ayi da Namiji irin......! Omar ya fusata iya fusata kafin ta karasa ya damtse mata baki da hannunsa yana murza le'bunanta cikin mugunta.

Ta dunga hawaye tana bugunsa yana rirriketa sai da ya galabaitar da ita sannan ya saketa yana huci! yace." Aysha zaki sha matukar wahala aikana wallahi duk irin son da nake miki ba zai hanani na hukuntaki ba Yanzu ma zan fad'a miki kome ke faruwa saboda 'boye miki sam bashi da amfani ina so ki sani ina daf da 'kara sabon aure."

"To sai me don ka 'kara aure? ko ka d'auka zan tashi hankalina ne kamar yanda na tayar da hankali lokacin auran waccan banzar yarinyar bari kaji idan duka matayen garin nan zaka aura ko a jikin aysha saboda sai kana son mutum kake kishinsa wallahi kaje kayi aure aysha bata damu ba domin ba kaina a gabanta ba.

Wannnan kalaman sunyi masifar ba'kanta masa rai sai ya dinga huci! yana zufa!!! aysha da bakinta take fad'in bata sonsa bata kishinsa yaje yayi auran bata damu ba, a take wani katoton abu yazo ya tokare masa a ma'koshi ya kai ya kawo a d'akin ita kuma tana watsa masa 'ba'kaken maganganu iya son ranta.

Juyowa yayi a fusace! ya ma'kureta a jikin kujera jikinta ya dinga kyarma! sai kuka take to shima kukan zucci yake domin idanunsa yayi wani irin ja le'bansa sai rawa yake yana wani irin cijewa gumi kam sai zuba yake a jikinsa kamar babu Ac a dakin.

Da kyar yace." Nine bakya so ko aysha."!??"Bana sonka wallahi saboda ka cika azalimi kuma kai kana da son kanka da yawa ni me zanyi da kai."!

Ya dafe kansa ya tsani yaji aysha tace bata sonsa.


"Menene nayi miki me zaifi wanda yasa kika tsaneni."!!?

Tureshi take yana sake makureta sai haki! suke tace" Kaje ka tambayi kanka abunda kayi min ni bani da lokacin tsayawa fad'a maka."

Ya girgiza kansa yana sakin ajiyar zuciya yace."Wato ke ba zaki ta'ba zama lafiya dani ba ko aysha a yayin da kike jin kin tsaneni baki sona ni kuma a lokacin sonki da kaunarki suke 'kara linkuwa a cikin raina Why! Aysha ya kike so nayi miki ne." Yana maganar muryarsa na rawa kamar zai kuka duk ya koma wani kalar tausayi.

Kai tsaye tace"Duk hanyar da zan amince maka in soka tsakani da Allah baka biyo ta ba a gurina kullum kai baka da gaskiya kullum cikin munafurtata kake zaka kara aure meye baka samu a gurinmu ? har wani sake fad'a kake zakayi aure to sai me??? nace"Sai me."!?? cikin hargowa take maganar


Sai ya hau d'aga hannu kamar wani zautacce! yace."Ya isa!! Ya isa!! nace miki."!! Inaa! Aysha bata san yana magana ba rashin kunya da rashin arziki kawai take masa duk maganar data zo bakinta ya'ba masa take.....Aikuwa ya fusata sosai ya wanke ta da lafiyayyan mari ta kurma! ihu!!! hanyar futa ta kama a guje ya bita ya ri'kota ta baya d'aga ta yayi cakkk!! ta dinga wuntsil-wuntsil tana zaginsa sai ya sauketa Omar yau yaga tashin hankali Yana dureta kan bed ta mike da sauri bakin mudubi ta nufa ta fasa kwalbar turere kansa tayi ido a rufe sai ya mike da azama! ya tare ta ya rirrike hannunta tana kuka tana fad'in"Sai na kasheka maci amana na tsaneka! mugu azalimi nayi nadamar auranka.""

Hannun dake rike da fashashshiyar kwalbar turaren yake kokarin murd'ewa ya kasa don ba karamin riko tayiwa kwalbar ba duk ta tsatstsaga mata hannu amma ko a jikinta burinta kawai tayi masa lahani.....Sai ya fara rawar murya "Aysha pls ki bari saki wannan kwalbar zaki jiwa kanki ciwo kar ki lahanta kanki aysha naji nayi laifi Allah ya baki hakuri ki bari nace! kinga baki da lafiya."" Ko kallonsa ba tayi ba kuka take tana fad'in"Ka isa kace zaka yaudareni ni zakacewa Linda ce ko baka fad'a min wacece ba jikina ya bani ko wacece gwara tun wuri ka fito ka fad'a min gaskiyar lamari idan ba hakaba wallahi tallahi sai na illata maka rayuwarka."

Yace."To naji na yaudareki Allah ya baki hakuri sakar min kwalbar ki zauna in fad'a miki komai idan kince ma bakya so sai na hakura aini kwanciyar hankalinki nake bukata Uwar 'yayana farin cikina Aysha gimbiyar mata Aysha jinin jikin Omar rayuwa ta kaf-kaf taki ce idan kika kasheni kiyi rayuwa da waye? humm! naji na amsa laifina zan fad'i komai."

Da kyar ya samu ta saki kwalbar turaran ya kama tafin hannunta yana dubawa ransa a bace yace."Duba ki ga irin lahanin da kikayiwa kanki aysha me yayi zafi."!?

Fizge hannunta tayi ta nemi guri ta zauna tana kallonsa ya zauna kusa da ita....Mintina goma suka dan samu nutsuwa tace" kai nake jira." !
A nutse yace."Kince bakya son rufi da 'boye-'boye ko? to dama duk wannan ba halina bane, Kan nace zanyi aure shine kike nema ki kasheni kiyiwa kanki rauni!! Aurena ba zai rageki da komai ba Aysha saboda nasan ko mata dubu zan tara a gabana kin zartasu a gurina So ki kwantar min da hankali........"Nifa ba wannan surutun nace kayi min ba cewa nayi ka fad'a min wacce zaka aura kuma a ina take."

Kai Tsaye yace."Azima ce 'kawarki ita nake son aure a matsayin matata ta uku." Aysha ta dinga binsa da kallo tana kallon abun kamar a cikin mafarki....."Azima Azima Azima sai mai ta fara tunanin wacece Azima

9 / 29