Author : Binta Umar Category : Complete Novels
Allah me yasa kake min haka? Azima fa kawata ce to mai zai sanya don ta ziyarce ni ka dinga jin haushi laifin me tayi maka da har zaka rufe mata kofa? ta tafi wata 'yar unguwa yanzu zata dawo.!
Yace."Ta tafi dai gantalin ta ni dai na fad'a miki." ya kama hanya zai futa sai tabi shi ta rike masa riga ya juyo yana kallonta,
"Don Allah kar ka rufe kofar nan ba'a haka don Allah ka kyaleta ta shigo."
Ido ya tsira mata yana kallo sai marairace fuska take.
Yace."Saboda Azima kike hadani da Allah ko? yanzu idan da laifi kikayi min ban isa ki bani hakuri ba amma saboda kawarki kina bani hakuri ta fini mahimanci a gurinki kenan."!?
"Ni fa ba haka naje nufi ba kawai kaine baka gane ba Babu dadi mutum yazo gurinka ka wulakanta shi idan ka kwantar da hankalinka ma ba dadewa zatayi ba."
Yace."To na hakura muje na duba babyna."
Zumburo baki tayi ya rike le'banta na 'kasa yana murzawa a hankali idanunsa har sunyi jaa!!
Ture hannunsa tayi ya rike duka hannunwan nata ya bankare mata kirji.
'Yar kara tasa tana kallonsa ya dora kansa saman kirjinta yana gogo fuskarsa.
Tsigar jikinta ta mi'ke hannunsa ya zira ya ri'ko kungunta ya hadeta da bango bakinsa ya had'a da nata ya shiga kissing dinta babu ji babu gani
Aysha ganin yana nema ya wuce gona da iri ne yasa ta tureshi ya dago shanyayyun idanunsa yana kallonta.
To itama kallonsa take tana sake jin felling na taso mata.
Yun'kurin riketa yake tace"Wai meye hakane ? kana shiga hakkin me hakki kaje gurin matarka kayi babu ruwan aysha." ta wuce ta bar masa gurin.
Kamar wani mara hankali yake binta da kallo yanzu dai ita kad'ai yake muradi amma babu hali saboda yana dakin Safarau.
Ya dade ya a tsaye a gurun kafin ya dawo nutsuwarsa ya bude kofa zai futa kenan Azima ta kawo kai.....Sai yayi sauri janyewa ya bita da kallo har ta shigo tana 'yar dariya da fad'in"Afuwa ranka shi dade ashe kana ciki sannu."!
Ko kallonta Baiyi ba ya fuce daga dakin da sauri.
Aysha ta tare da sauri tace"Sannu kawata amma kinsha hanya ina fatan dai an samu abunda ake bukata.
Azima ta cire gyalanta ta aje ta fara kokarin bude jakarta wani karamin kwali ta d'auko guda biyu (misco clear) misco prostol) tace"Wannan k zaki shanye a yanzu da asubah kuma sai ki shanye wannan kafin safiya aikin gama ya gama insha Allah."
Aysha tace"Nagode sosai kawata bari ma ki gani na shanye yanzu." Aysha ta mike da sauri zata dauko ruwa....da sauri Aziman ta rike hannunta tace"Ina fatan dai kinci abinci." Ajiyar zuciya ta sauke tace"Allah banci ba ke nifa babu abunda ke damuna yanzu sai cikin nan burina kawai inga ya futa daga jikina.
Azima tace"Tom dole dai sai kinci abinci kar ya galabaitar dake." Aysha tace "Tashi muje palo Ikilima ta had'o mana.
Tare suka fita palo aysha ta bawa ikilima umarnin kan ta fito musu da abinci.
Suna cin abinci Azima na danne-danne a wayarta sai da ta tura masa test din sannan ta mayar da hankalinta gurin cin abincin.
Tana kallonsa ya fito daga dakin Safa daga shi sai vest da karamin wando short nickhar ya nufi dakinta sam bata kawo komai ba a ranta ta cigaba da cin abincin....Dake kofar dakin a bude ya barta yasa taji yo sautin miryarsa da karfi yana kiran sunanta.
Da sauri ta mike ta shiga d'akin.
Yana tsaye tsakiyar dakin da kwalayen magani a hannunsa,Ba tare da wata fargaba ko faduwar gaba ba tace" Gani." Kwalayen maganin yake nuna mata rai a mutukar bace yace."Wane irin magani ne wannan."? ta karba tana dubawa kamar bata sanshi ba.
"Ba magana nake dake ba."!?
Yafada a tunxure.
"Ire-iren maganin da Dr Rakiya take bani ne fa." Yace."Karya kike aysha kina so ki raina min hankali ko."!? Wane irin rainin hankali wai kai don Allah me yasa kake da zargi ne."? tafada a fusace!
Mari ya kai mata ta goce da sauri tana kallonsa cike da mamaki! tace"Kina so ki zubar min da ciki ko Aysha."! gabanta ya tsanatsa fad'uwa sai ta fara hawaye Wane irin na zubar maka da ciki kai ka yarda cikin gareni toni wallahi ban yarda ma ina da ciki ba idan kana mafarki to ka farka."
Gumi! ya shiga zubo masa wai shin aysha na da lafiyar kwakwalwa kuwa?? Girgiza kansa yayi ya kama hanya zai futa hannunsa rike da kwalayen maganin ta bishi tana kuka rike hannunsa fuzgewa yayi tace"Ka bani magani to." A fusace ya juyo ya wanke mata fuska da mari!
"Ki shiga hankalinki dani wallahi duk wani abu da kikeyi kamar a gabana kikeyi gurin da kika aika a kar'bo miki magani domin ki zubar min da ciki sune suka sanar dani to naga wannan gobe ma sai ki sake aikawa a kar'bo miki wani maganin."
Ture ta yayi ya futa daga dakin a fusace!! Azima na ganin fitowarsa ta mike da azamah ta shiga dakin.
Aysha na durkushe kasa tana kuka ta dagota "Aysha wai meke faruwa ne? na jiyo hayaniyarku.
" Azima yaga maganin nan fa."! tafada tana sha'kar hanci
Azima ta dafe kirjinta "Innalilihi wa'ina ilahi raji'un garin yaya haka ta faru."!?
" Kan drowar fa na aje magani shaf na manta kuma banyi tsammanin zai shigo ya gani ba."
Azima taja ta suka zauna kan bed tace"Lallai akwai matsala tunda ya riga ya gani ni tsoro nake ji ma kar sunana ya fito kar ya zargi ko da sa hannuna."
"Kar ki damu Kawata nasan halin Omar da bin'kwakwkwafi watakila lokacin da kika fita yasa an bi bayanki ne don yace min wai gurin da kika amso maganin sune suka sanar dashi."
Azima tace"Kin gani ko ai shikkenan nasan zaiyi tunanin nice na saki ki zubar da ciki."
"Kar ki damu Azima duk yanda zanyi zanyi na kareki ki kwamtar da hankalinki."
Azima tace" To shikkenan 'Kawata amma dai gaskiya ina jin tsoron masifar mijinki gobe zan tafi don ban san da wani ido zan kalleshi ba."
Tsaki taja tace"Don Allah ki daina damun kanki kan wannamn abun tunani na ya zanyi wace hanyar zan sake bi gurin ganin na zubda cikin nan.
Azima tace" Ki kwantar da hankalin ki zanyi tunanin mafita nima bana so ki haihu yanzu wallahi. Aysha ta kwanta tana tunanin yanda zatayi da cikin jikinta sam bata damu da cin mutuncin da yayi mata ba tasan shike da gaskiya ita kuma kome zaiyi sai da yayi amma tana nan kan kudirinta.
Kwata kwata Safa kasa gane kansa tayi sai tayi zugum! kawai tana kallonsa ya d'auki pilo ya fita palo kallo ta bishi dashi ta mike tabi bayansa.
"Yayana wai lafiya don Allah tashi mu koma daki kaji.!
Ya kalleta da jajayen idonsa " Jeki kwanta kiyi bacci Safa zan shigo idan anjima."
Ta zauna kusa dashi tana shafa kirjinsa wanda yake cike da gargasa....cikin wata siririyar murya take lallashinsa kan ya taso suje daki.
Ya mike zaune ransa a bace Yace."Wai ke dole ne sai na shiga dakin ne? Malama tashi ki bani guri haka."!!!! Safa ta mike tsaye jikinta yayi sanyi tunda suke bai ta'ba yi mata tsawa ba irin yau salau-salau! ta shige daki ta zube kan gado tana kuka taso yau yayi sex da ita ko zata samu ciki ya shiga yanzu sai nan da kwana biyu zai dawo dakinta gashi ya kwana a palo ranar kwananta wannan takaici dame yayi magana.
Test ne ya shigo wayarsa dake gefansa.
Ya d'auka yana dubawa.
_Nasan zakayi mamakin abunda ya faru a yau to ina so ka bani dama in warware maka dukkanin abunda ya faru_
Ya karanta test din ya kai sau biyar yana mamakin daga ina ya fito....tsaki yaja ya aje wayar sai kuma ya dauka ya fara maida amsa.
_Da waye nake magana_
Abunda ya rubuta kenan ya tura, minti biyu ta bashi amsa.
_"Nice Azima mai kaunarka da bibiyar lamuranka da dukanin abunda ya shafe ka_
Da sauri ya Mi'ke zaune yana sake duba test din _Azima ce mai kaunarka da bibiyyar lamuranka_ Shin wace Azima ce wannan.?
Bashi da me bashi amsa dole yasa ya mayar mata da magana.
_Ina so in san da wace Azima nake magana_
Ta mike zaune da sauri tana murmushin samun nasara gefan da Ayshan ke kwance ta kalla sai bacci take abinta sai ta mike ta koma kan Sofa ta xauna.
_"Azima dai wacce ka sani Aminiyar matarka Aysha_
ta mayar masa da amsa.
Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama karantawa.....Tabbas wannan numbar ita numbar da aka dauki tsawon watanni takwas ana turo masa sa'konnin soyayya da kalamai masu dadi da ita wato dama itace ke masa test irin wannan? tabbae biri yayi kama da mutum.
Azima tayi ta sauraron taji abunda zaice taji shiru tafi karfin awa guda a zaune tana jiran amsarsa shiru....Wanda a lokacin shi kuma bacci mai nauyi ya d'auke shi.......Karfe hud'u da rabi Safarau ta fito daga dakinta salau-salau ta isa inda yake kwance yana bacci tukuru....Hankalinta ya koma kan wayarsa dake haske da kiran sallah da alama alarm ne ya saita saboda sallahr asubah...ta dauka domin ta kashe wayar taga test sai ta bud'e tana karantawa.
_"Nayi ta tsammanin jiran amsar ka naji shiru to mu kwana lafiya farin cikina."_
Gabanta ya shiga dukan uku-uku sai ta fara bunkice a wayar hannunta sai kyarma yake.
Tun daga farkon maganar su har ya zuwa 'karshe sai da ta karanta tsaf_tsaf ta fahimci abunda ke faruwa....Azima ce aminyar matarka Aysha!
Innalilihi wa'ina ilahi raji'un!! abunda take iya fad'a kenan ta aje wayar ta mike ta bar gurin....motsin bude kofar tane ya tashe shi ya mike da sauri ya nufi dakinsa.
A gurguje yayi wanka ya fito ya shirya zuwa massalaci.
Bai shigo gidan ba sai karfe tara da rabi da yaje sashen mamanshi suka gaisa ya shigo da Abdu sa'be a kafad'arsa.....kai tsaye idanunsa suka sauka kan daining wayam! babu komai a kai!
Ya nufi dakin nata, tana zaune ta had'a tagumi! hannu biyu ya shigo ta kalleshi tare da dauke kanta tsayuwa yayi kanta yana fad'in"Kina jina ina sallama baki amsa ba Safa ko kina fushi dani ne."!?
Idonta ta tsira masa tana kallo yace."Ga Abbanki ku gaisa yau naga ko abun kari babu Allah yasa na tsaya na d'an ci wani abu sashen mama."
Ba tace masa komai ba ta 'kar'bi Abdul din ta futa ta barshi a d'akin....Kallo ya bita dashi yana girgiza kansa a fili yace."Mata lamarin ku sai ku....Wayarsa ya dauka ya turawa Azima test.
_Ki same ni can harabar gida Zamuyi magana_
Yana tura mata ya mike ya fita.....Safarau ta bishi da kallo Azima ta fito cikin uwar kwalliya ta kece raini ta bi bayansa.
"Wai shin meke faruwa ne? Anya aunt Aysha tasan abunda ke shirin faruwa dasu kuwa gaskiya da ta sani da tuni tayiwa tufkar hanci ashe dama Omar haka yake mayaudari mai son matan tsiya dama itafa sam bata yarda da wannan Azimar ba to yanzu ma ina suka tafi ne? bata da me bata wannan amsar jikin ta babu kwari ta mike ta nufi dakin ayshan gabanta na faduwa ta tura kofar ta shiga lokacin aysha ta fito daga wanka.....Dauke kanta tayi ta nufi wardrobe domin dauko kayanta.
Kan Sofa ta zauna tace" Aunt Aysha kin tashi lafiya."?
Ba tare da ta jiyo ba tace"Lafiya." ta cigaba da kintsa jikinta....Tace"Aunt ina da magana amma ina so kiyiwa maganata kyakykyawar fahimta."
Aysha tayi mata banza ta cigaba da shirye shiyenta.
Duk sai ta muzanta tana tunanin ma idan ta sanar da Ayshan abunda ke faruwa baza ta yarda ba domin taga alamar ta amince da kawar tata.
Mikewa tayi ta kama hanya zata fita, Aysha tace"Ashe gulma ce ta shigo dake ba maganae arziki ba ko."!? Safarau ta juyo ranta a d'an bace tace"Aunt Aysha wannan maganar da zamuyi dake me muhimanci ce amma ga yanayin yanda kika amsa min yasa na gane ba yarda zakiyi ba shiyasa kawai na yanke shawarar barin abata a ciki duk sanda tayi wari zakiji."
"Mtsssw!!! Aysha taja tsaki mai tsayi kana tace" Idan naji maganar bata gamshe ni ba ai kinga ba zan yarda ba saboda kin san ni bana shiri da munafikin mutum da munafurci ki bari kawai idan tayi wari naji kamar yanda kika fad'a."!!
Safarau ta bude kofa ta futa daga dakin ranta in yayi dubu ya 'baci!
Tana futa taja tsaki"Banza munafuka kawai ta 'kullu munafurcinta shashasha 'yar kauye."
Aysha ita kad'ai take surutanta har ta shirya ta fito palo lokacin ikilima har ta gama had'a musu break.
Wani ke'bantaccan guri suka zauna Omar ya gyara yanayin fuskarsa babu alamun wasa yace."Ke nake sauraro."
Azima ta gyara zama a nutse tace"To maganar gaskiya da gaskiya zamuyi da kai kuma kauna da so ne duka ya jawo hakan a tsakanina da kai shiyasa nake yin ruwa da tsaki a cikin al'amuranka Yau sati biyu kenan Aysha na damuna a waya kan inzo tana nema na to sai da nazo sannan ta warware min abunda ke faruwa kuma ta fad'a min nufinta nayi kokari sosai gurin bata shawara kan kan abunda take yun'kurin yi bai dace ba ta nuna min ita shine dacewa a gurinta bata son haihuwa saboda dalilanta kuma kai ma kasan dama tuntuni Aysha ba son haihuwa take ba tace dole sai na samo mata maganin zubda ciki idan ba haka ba zata je da kanta ta samo ganin yanda ta tayar da hankalinta yasa naje na na kar'bo mata maganin amma kuma ban bari ta sha ba saboda ina so ka sani wannan test din da aka tura maka da farko nice na tura maka shi da d'aya numbar ta nace ka shiga d'akin ka d'auke maganin a gaskiya dole ka tsaya tsayin daka kan lamarin Aysha domin batajin magana kuma bata daukar shawara ha'kika idan nice na samu damar data samu wallahi ba zanyi wasa ba zan zauna nayi ta haihuwa domin su 'yayan da take gudu rahama ne a garemu sai wanda Allah yaso bawa wannan shine dalilin da ya sanya nace ka bani lokaci domin mu tattauna maganar dani da kai." ta kare maganar tata kamar wata mutuniyar arziki.
[5/30, 10:24 AM] Bintu Novel: 66
Omar ya jima yana mamakin maganganun Azima tabbas dukanin abunda akace masa aysha ta aikata ko shakka ba zaiyi ba saboda ya san zata aikata abunda yafi haka, gumi duk ya jika masa jiki saboda tsabar fargaba da tashin hankali idan hakane gaskiya lamari to Azima na cikin masoyansa na gaskiya tunda har zata ga abunda ya shafeshi ta shiga cikin lamarin tana bada gudumarwar ta dole ya dan saurara mata tunda ya gane ita din mai kaunarsa ce.
Ganin yayi shiru yana kallon guri daya ne ya sanya Azima sake sassauta murya tace"Naga kamar baka yarda da maganata ba idan kana shakku sai in kaika gurin dana amso mata maganin ka tambayesu yanda mukayi."
Ya kalleta a burkice yace."Bana shakka ko wasiwasi kan abunda kika fad'a Azima, dukanin abunda kika fad'a kan Aysha na gazgata domin aysha bata jin magana kuma zata aikata abunda yafi wannan kawai abun ke bani mamaki sosai wasu na can na nema ido rufe ita Allah ya bata tana kokarin butulce masa tabbas wannan al'amari ba zai tsaya a tsakanina dake ba dole zan nuna mata nasan komai sannan kuma dole ne magabatan mu suji abunda ke faruwa."
Azima ta langwa'bar da kanta tana wani firirita ido tace"Gaskiya kam ya kamata ka sanya ido kan iyalinka ka kuma dauki matakin gyara kan Aysha wallahi na rantse maka da Allah ganin kana nuna mata kauna da sone yasa take wani iskancin ka watsar da ita kawai sai ta shiga hankalinta.".
Mirmushi yayi mai ciwo ya shafa sajensa yace."Azima son Aysha a cikin jinina yake duk yanda naso da na cireta daga rayuwata na kasa ba zan ta'ba daina son Aysha ba har abadah Aysha jinina ce kuma uwar 'yayana ce ita wannan ba zai sanya in sanya mata ido tana aikata abu mara kyau ba dole sai na dauki matakin gyara a cikin gidana sannan zan samu nutsuwa da kwanciyar hankali."
"Gaskiya ne to Allah ya shiryeta da ita da masu hali irin nata."
Ya amsa da "Ameen." yana kokarin mikewa.
Sai ta sassauta mirya cikin kissa da sigar jan hankali tace"Don Allah ka zauna ina so muyi magana da akai ta fahimta."
Omar ya koma ya zauna yana duba agogon hannunsa duk da yau babu aiki amma yana so ya futa fada ya zauna
Yace."Ina sauraronki."
Azima ta fara wasa da awarwaron hannunta sai wani motsa baki take ta kasa magana.
Yace."Duk abunda ke cikin zuciyarki ki fada min kar kiji shakka Azima yanzu na lura kina da hankali kuma kin san abunda kikeyi."
Tayi 'Yar dariya mai daukar hankali kana tace"Na tabbata dai kana duba test messages dina na kwanakin da suka gabata yanzu ina so ka bani amsa shin kana sona ko baka sona ni dai har ga Allah tun kafin ka kai wannan matsayi nake sonka ko da can ma kawai ina biyewa aysha ne muna cin mutuncin ka amma cikin raina bana jin dadin abunda muke maka don Allah kayi hakuri kaji ko zaka iya aurana."!?
Omar ya tsira mata ido yana kallo babu yabo babu fallasa Azima ta kowane fanni ta cika cikakkiyar mace wanda duk wani namiji mai lafiya ya ganta sai yaji sha'awarta tayi masa kuma yana jin zai iya auranta tunda ba haramun bane hakan amma kuma dole ne ya tsaya yayi nazari kafin faruwan hakan kwata-kwata yanzu shi ba aure ne a gabanshi ba yaga Ayshansa ta dawo mai nutsuwa da hankali.
"Karki damu Azima zanyi tunani kan maganar ki Idan Allah ya 'kaddara aure a tsakanina dake zan aure ki insha Allah."
Ta sauke zazzafar ajiyar zuciya ta mike tsaye tana 'yar dariya ta murna tare suka jero suna hira sai da suka fito harabar gidan ne sannan kowa ya kama gabansa.
Omar fada ya nufa ita kuma ta koma sashen Aysha domin tayi shirin tafiya tunda dai bukatar ta ta farko ta cika.
Aysha ta d'aga kai ta kalleta cikin nazari tace"Wai ina kikeje ne da safiya na fito tun dazu ban ganki ba."?
Tana gyara zamanta a kusa da ita tace"Ina sashen Nanne muna gaisawa."
"Okey nima idan anjima da yamma zan shiga domin na kwana biyu rabona da sashen."
Azima tace"Aysha ina ganin fa yau din nan zan tafi wallahi har yanzu jikina a sanyaye yake bana so in shiga tsakaninki da mijinki na lura ganin wannan 'kwayoyin maganin ya d'aga masa hankali