Author : Binta Umar Category : Complete Novels
ni amma nima nasan aunty gimbiya bata ta'ba yi min wani abuba don ta muzguna min."
Aysha taja wani matsiyacin tsaki ta bude kofar dakin ta futa.....Ajiyar zuciya ya sauke yace."Banji dadin abunda kikayi ba Safa me yasa kika raba min hankali kan maganar da farko na tambayeki kinyi shiru hakan shine yasa na gazgata al'amarin saboda sanin halin aysha zata iya komai kuma yanzu kince babu komai kar ki 'kara min irin wannan." Cike da 'bacin rai yake maganar.
"Kayi hakuri Yayana." tafad'i maganar hawaye na kwaranyo mata.
Tausayi ta bashi sosai ya rungumeta yana rarrashinta tayi shiru yace."Idan na shigo anjima zaki sanar min da abunda ke damunki."
Sakinta yaya ya futa daga dakin.
Ya fito ya tarar da ita zaune a palon suna hira da Ikilima, hanyar futa ya nufa Ikilima tayi masa barka da fitowa ya amsa yana kallon ayshan da gefan ido ita kam kallo ma bai isheta ba domin wani irin haushinsa takeji.
Sai bayan isha'i Safarau ta fito daga dakinta ta shirya daining ta zauna palon da su aysha ke zaune.
Aysha kam ganin ta zauna sai ta mike ta bar gurin Ikilima ma ta tafi dauko Abdul dafa sashen Fulani.
Tana shiga d'aki ta nufi toilet tana tsaka da d'aura alwala zuciyarta ta dinga tashi sai ta fara kakarin amai yi take yaki fitowa, ta fito wurjajan daga toilet din miyau duk ya cika mata baki zama tayi kasan kafet tana mai da numfashi.
Ikilima ta shigo dakin da abdul wanda yana ganinta ya fara zillo yana miko hannu ta d'auke shi.....Ganin yanayin da take ciki ya sanya Ikilima tambayar ta abunda ke damunta.
"Ikilima bana jin dad'i bakina babu dad'i kije gurin gwaggo kice ta bani goro yanzu."
IKilima ta juya zata futa Abdul ya saka kuka yana turjewa shi sai yace gurin mamansa.
"Ikilima jeki dashi kawai yanzu idan na kar'beshi shikkenan zai dameni da tsotsar nono."
Ikilima ta futa daga d'akin da sauri karo suka ci da Omar yace."Ina zaki dashi yana kuka."!?
Kai a kasa tace"Sashen gwaggo zani." Hannu ya mi'ka ya 'kar'bi yaron ya nufi dakinta dashi Ikilima ta bar gurin da sauri.
Tana toilet tana kakarin amai ya shiga dakin dake kofae toilet din a bude take yana hangota ciki ya karasa da sauri....
Ganin abunda takeyi ne ya sanya shi ya aje abdul din da sauri ya rirriketa suka fito.
"Aysha wane irin amai ne wannan me kika ci? baki da lafiya baki fad'a min ba."?
Hannunta ta cire daga nasa ta koma ta zauna tana yatsine fuska shi kansa bata son jin 'kamshin jikinsa ya karaso gurin dai-dai lokacin da Abdul ya rarrafo ya riketa ya mike yana kuka nono yake sonsha.
Daukarsa tayi ta d'ora a cinyarta tana kokarin ciro nono ya zauna kusa da ita yana tayata cirowa kanzil bata ce masa ba ya tsira mata ido yana kallo har ta gama shayar da yaron ya kar'beshi cikin sassauta murya yace." Ayshata."! kallonsa tayi da wani irin yanayi ya marairace fuska "Baki da lafiya ko."?
" Umm bana jin dad'i." tafad'a tana kokarin kwanciya yace."Allah yasa abunda nake zargi ne."
Ido a lumshe tace"Menene kake zargi."!?
Kusa da ita ya kwanta yace."Allah yasa ciki ne dake." mi'kewa tayi zaune tana shima ya mike yana kallonta....."Allah ya kiyaye nayi ciki yanzu waye yace da kai zan kara haihuwa dakai cikin wannan halin."!
Fuska ya 'bata yace."Wannan wace irin magana kikeyi aysha."!? Sai ta fusata tace"Eh na fad'i abunda ke raina ne kasan ni bana magana biyu kuma bana munafurci Kana maganar ciki da haihuwa bana fatan ta kaje ka haihuwa da wata dama tuntuni ni na fad'a maka ba zan kara haihuwa da kai ba."
Yace."Yanzu ke ko kunyae fad'ar wannan magana baki ji ba Aysha."?
Harara ta watsa masa tace"Zancan kake so Ni dai don Allah ka tashi kayi tafiyarka kar ka had'a min zafi biyu kaje ka huta kawai."
Yace."Tashi muje gurin Dr Rakiya."
"Ba yau nayi niyyar zuwa ba kuma idan zani ba da kai zanje ba." tafada ba tare da ta kalleshi ba.
Ya mike tare da fad'in "Zan ga ta yanda zaki futa daga gidanan ba tare da sani na ba." Futa yayi daga d'akin, Safa na palo a zaune ya fito ranta duk ya 'baci ta jima zaune a palon ashe yana cikin dakin aysha ita kam bata so yana shiga dakin aysha ranar kwananta
Suna cin abinci suna hira sama-sama don gabaki daya hankalinsa da nutsuwarsa yana gurin aysha akwai rigima kenan idan ta tabbata aysha nada ciki a gidan.
To bayan sun gama rayuwar auransu ne tana kwance a kirjinsa har ya soma bacci ma yaji muryarta tana magana.
Bude idonsa yayi yace."Menene kike cewa ne."?
"Yayana cewa nayi Allah ya bani ciki na haihu nima."
Ya shafa gashin kanta cikin kulawa yace."Ki kwantar da hankalinki Safa zaki haihu da ikon Allah."
Rungumeshi tayi tace"Ina addua sosai Yayana kai ma ka tayani da ita." Yace."Ko da ma abunda ke damunki kenan kike shiga yanayi na damuwa."
Hawayenta yaji a kirjinsa tace"Nakasa daurewa ne yayana Allah nima ina so na haihu."
Yace."To ki kwantar da hankalinki komai na Allah ne zaki haihu insha Allah."
Rungumeshi tayi tana kuka shi kuma yana shafa bayanta haka bacci ya dauke su.
Omar sam baiyi wani baccin kirki ba asubar fari ya tashi ya dauke safa dake kwance a jikinsa toliet dinta ya shiga yayi wanka ya dauro alwala kana ya nufi dakinsa.
Tsaf ya fito ya nufi masalaci domin gabatar da sallah asubahi a gurguje suka gaisa da Maimartaba ko sashen fulani bai tunkara ba ya nufi sashensa.
Kai tsaye dakin aysha ya nufa lokacin tayi sallah ta koma bacci ya shigo yana jan bargon da ta rufe jikinta dashi yana kiran sunanta.
Ta bude ido tana kallonsa yace."Ki tashi muje asibitin." Mai da idanunta tayi ta rufe ita ta manta ma da zuwa asibitin.
Zama yayi gefanta yana sake janye bargon....."Ki tashi muje asibitin mana.
"Kyaleni ba yau zanje ba"
"Kamar yaya ba yau zakije ba? ki tashi mana jiya banyi wani baccin arziki ba saboda ke."
"Humm! abunda tace kenan ta juya masa baya.
Gashin kanta yake shafawa a hankali yake kiran sunanta " Don Allah ka rabu dani." Tafada tana cire hannunsa daga jikinta.
Kwanciya yayi gefanta ta mike zaune tana masa wani irin kallo, shima ita yake kallo "Wannan wane irin abu ne ka shigo ka hanani bacci na."
"Ba hanaki bacci nayi ba Aysha so nake ki tashi muje asibiti idan kin dawo sai kiyi baccin.
Mikewa tayi ta nufi toilet tayi wanka ta fito ya dinga binta da kallo yana sauke ajiyar zuciyar zucia addua yake Allah yasa ciki ne da ita.
Sai da ya tabbatar ta shirya sannan ya futa daga dakin nasa ya nufa ya shirya cikin yadi mai ruwan kasa ya fito yana kamshin turare a palo ya tarar da ita tana karyawa Da kunun gyada wanda tasa Ikilima ta dama mata.
Sai ya nufi dakin Safarau tana zaune ta ma kasa tashi ballanta ta shirya musu break tsabar bakin ciki da takaicin dake damunta.
A cunkushe suka gaisa yace." Zamuje asibiti da Aysha yanzu."
Ta kalleshi idanunta na kawo ruwa "Sai kun dawo." tafada tana dauke kanta.
Fita yayi daga d'akin Aysha ta mike suka futa Safarau kam bakin ciki ya sakata kwantawa kasan kafet tana kuka.
Gwajin farko Dr Rakiya ta tabbatar musu da ciki dan wata uku farin ciki gurin Omar ba'a magana inda Aysha kuma tayi kici kici da fuska ba tace komai ba dai tana jinsu suna ta maganarsu sai da zasu tafi ne tayi mata sallama Dr Rakiya sai shawarwari take bata.
jinta kawai takeyi amma ta kudiri aniyar zubar da wannan cikin nata kota halin yaya ne.
A mota sai lallabata yake yana rarrashinta da kalamai masu dadi shiru tayi masa in banda kukan zucci babu abunda take haka suka isa gida yana wani irin kula da ita da rarrashinta.
Aiki ya wuce yana cike da farin ciki mara misali.
Aysha kam zurfafa tayi cikin tunani da neman mafita hakikanin gaskiya bata kaunar sake haihuwa a halin yanzu don haka tun kafin cikin yayi kwari zata san abinyi.
Omar kam ya kira wayar ta ya kai sau goma taki d'agawa saboda tsananin haushinsa da takeji wanka tayi ta fito Palo da wayarta a hannunta.
Wayar Azima ta kira suka gaisa Azima tace"Yanzu nake shirin kiran ki wallahi, zan ce dake in Allah ya yarda ina kan hanya gobe ko jibi."
Aysha tace"Shikkenan ina sauraron zuwanki dama akwai shawarar da zamuyi."
Azima tace"To tunda hakane gobe zanzo insha Allah." sallama sukayi ta aje wayar.
****
Ko da ya dawo daga gurin aiki sai ya ga sauyi sosai daga gurin Safarau domin da kyar ma tayi masa barka da zuwa ya tambayeta abunda ke damunta tace ciwon kai ya jima yana nazarinta kafin ya fita daga dakin ya kalli daining yaga babu abinci batayi ba kenan tabbas akwai abunda ke damun safarau.....Sai bayan sallahr isha'i ya shigo gidan.
Aysha ce kawai ita da Ikilima suna palo suna kallon wata drama ta hausa film Aysha sai dariya takeyi ya tsaya kanta yana kallonta Ikilima ta mike ta bar gurin.
"Aysha kinsha maganin ki ko."!? Fuska a sake tace" Eh nasha."
"Okey zan futa me kike bukata."? yanda yake maganar yana karyar da kai sai ya bata tausayi tace" Komai in ka siyo min ina so."
"Tashi muje tare." Yafada cike da kulawa.
Girgiza kanta tayi tace"Kaje kawai na huta a gida."
Ya kad'a kai ya fita daga palon ajiyar zuciya ta sauke ta cigaba da kallonta.
***
To haka suka kwana ya kasa gane kan Safarau sai fushi takeyi taki sakin jikinta idan ya tsananta mata da tambaya sai ta fashe da kuka tilas ya nufi sashen mamanta ya sanar mata da halin da ake ciki.
Fulani da kanta ta shigo sashen Ikilima ta tura ta kira mata Safarau ta futo cikin hijab tana ganinta sai hawaye ya soma zuba a fuskaerta taje ta zauna kusa da kafafunta.
Aysha na ganin haka sai ta mi'ke zata bar gurin Fulani tace"Aysha dawo ki zauna."
Komawa tayi ta zauna Fulani tace"Safarau saboda ke nazo sashen ku.Shin wai menene yake faruwa ne? kwana biyu mijinki ya sanar dani cewar kina takure kanki cikin daki kina kuka da damuwa wani abun yake miki ko kuma baki da lafiya ne."?
Safarau ta sunkyar da kanta tana kokarin mayar da hawayenta
Fulani tace"Ba kuka zakiyi mun ba safarau ki fada min abunda akai miki kike wannan kukan."
"Mama babu komai wallahi haka kawai nake jin raina na 'baci."
Fulani tace"To duk lokacin da kikaji ranki ya 'baci ba kuka Zakiyi ba addua zakiyi sharrin shaid'ain ne wannan damuwar da kike da kuka n bashi da amfani mijinki yana damuwa da hakan."
Ta kalli Aysha dake gafanta a zaune tace"Aysha don Allah ku zauna lafiya kema naji yace bakyajin dadi ko? to Ubangiji Allah ya rabaku lafiya."
Ta amsa da "ameen Mama." Fulani tayi musu sallama ta tafi sosai al'amarin yake bata mamaki ta kasa gane waye mai laifi tsakanin aysha da Safaraun.
Sai wajan biyar da rabi na yamma Azima ta iso sai da taje can sashen su Nanne suka gaisa sa'anan d'aya daga cikin bayin dake sashen suka kaita sashen su Aysha.....Tana shiga ba da wacce ta fara cin karo da ita sai Safarau sukayi kalli juna ko wanne zuciyarsa babu dadi Safa ta dauke kanta ba tare da ta tanka wa Aziman ba ta wuce kicin.....Azima tayi gaba tana fad'in"Zaki ci uwarki ne 'yar iska.....Aysha ta fito daga daki suka rungume juna suna cike da farin cikin haduwa da junansu.
[5/29, 9:46 AM] Bintu Novel: 65
Tare suka zauna gefen bed Azima sai wani irin kallon kurrulla takewa aysha kafin tace"Mutuniyar irin wannan kyau haka! shin kin san yanda kika koma kuwa a gaskiya sadauki ya iya kiwo yana miki yanda kike so." Dariya aysha tasa tace"Ke kam 'yar sharri ce wallahi wane irin abunda nake so yana dai cunguna min da zaman hakuri."
Azima tace"Haba haba! kawata duk wanda ya kalleki yasan kina hutawa ta ko'ina kin ciko yanzu fa kin kusa kamo ni a jiki dubi fatarki fa."!
"Humm! Azima kenan bafa wani abu ne ya janyo min wannan sauyin ba sai d'an tayin dake ciki na."
"Bangane ba." Azima ta fad'a tana kallonta.
'Bata fuskarta tayi sosai tace"Azima ciki gareni dan wata uku."!
"Kan Uba! ya akayi haka ta faru? kina me har kika sake kika dauki ciki da 'karamin yaro."
"Tsautsayi ne kawai 'Kawata wallahi baki ga yanda na shiga damuwa ba saboda cikin nan sanin kanki ne ra'ayi na bana son wannan haife haifen shi ke jawowa mace ta tsufa da wuri sai kiga miji ya daina yayinta."
''Wallahi maganar ki haka take aysha,nima sam bana son haihuwa wallahi zan iya kare rayuwata ba tare da na damu ba don ban haihu ba, amma ke yanzu wace shawara kika yanke kinga dai idan kika bari ya kara wata daya kan ukun to gaskiya kina cikin hatsari don bai zama lallai ya zube ba gwara tun wuri ki san abunyi."
Ajiyar zuciya ta sauke cikin yanayi na damuwa tace"Kece kike da magana kawata shiyasa nayi murna da zuwanki nasan zaki sama min mafita kin san ni duk irin wannan harkar ban iya ba."
Azima tace"Ki kwantar da hankalin ki 'kawata ni zan fita in anjima insha Allah zan shigo miki da 'kwayoyin da zaki sha kafin safiya cikin zai fice ai duk abu mai sauki ne."
Aysha ta sauke ajiyar zuciya ta bata hannu suka tafa tana dariya tace"Na sani a gurinki mai sauki ne 'yar gari." mikewa tayi tace"Bari in sa Ikilima ta kawo miki abinci.
Azima ta bita da wani irin kallo tana girgiza kanta ta dinga bin dakin ayshan da kallo tana ta'be bakinta kishi ma'kare a zuciyarta.
Safarau na gama ayyukanta sai ta shige daki ta kulle kofarta zuwan Azima gidan ya daga mata hankali mussaman data jiyo dariyarsu cikin daki duk sai ta tsargi kanta da kanta, tayi alkawarin har ta gama zamanta a gidan ta tafi ba zata tanka musu ba.
Sai da yayi sallahr isha'i sannan ya shigo gidan....Ya fara Jiyo dariya da saurin maganganu a dakin aysha abun ya bashi mamaki yasan dai aysha ba zata zauna da Ikilima suna wannan hirar ba har da shewa kai tsaye dakin ya nufa cikin yanayi tafiyarsa ta kasaita.
Ya tura kofar ya shiga da sallama, sai ya toge a Bakin kofa tare da zura hannunsa guda a cikin aljuhu yana kallonsu.
Kafin aysha ma ta ankara dashi ita Azimar ta kula sai ta hau gyara fuska tana wani fari da ido tace"Barka da shigowa." Aysha ta kalli bakin kofa har yanzu fuskarta a sake take tace"Sannu ka dawo."!?
Idanunsa a tsaye a kanta ya amsa ba tare da ya kalli gefan da Azimar take ba yace."Aysha ina fatan yinin yau kin kula da kanki kuma kin sha magani kan 'ka'ida."
"Eh nayi." tafada tana gyara fuskarta don taji haushin watsin da yayi da Azima.
Ya juya zai futa daga dakin tace"Kanaji Azima na gaisheka fa ka share."
Bud'e kofa yayi yayi fucewarsa ba tare da yace mata komai ba.
Azima taji wani bala'in haushi da takaici amma ko alama bata nuna a fuska ba Aysha tace"Rabu dashi 'kawata idan 'yan wulakancin nasa na kusa nima haka yake min."
Azima tace"Don ma ya samu ke d'in bata wasa bace da abunda zaiyi miki sai yafi haka." hannu ta bata suka tafa tace"Keee! Ai wallahi Omar da nayi masa lako lako da tuni na zama abunda na zama ai yana farawa nima nake hawa sam bana saurara masa."
"Yayi kyau kinga kina zaune lafiya ita kuma waccan figaggiyar fa shegiya da idanu kamar na tsaka wallahi na tsaneta."
Aysha tasa dariya tace"Rabu da ita Azima haukan banza takeyi wallahi sam bata gabana ni ban dauketa a matsayin mutum ba shegiyar yarinya sai kishin tsiya da kissa da munafurci hummm! ke ai da ba don sun same ni a tsaye ba daga ita har shi sai sun takani to don nima bana saurara musu shiyasa abun yazo da sauki."
Azima tace"Yayi kyau 'kawata bari in sallah in fita kar dare yayi." mikewa tayi ta nufi toilet din Ayshan ta dauro alwala ta fito tayi sallahr a gurguje ta idar ta dauki mayafinta suka fita tare.
Suna zaune tsakiyar kafet Safa na fuskantarshi Yau Omar sangarta yake a baki take bashi abinci sai dariya take kyalkyala masa shi kuma sai tsotse mata hannu yake.
Aysha tayi saurin dauke kanta gabanta na wani irin fad'uwa ji tayi kamar ta koma d'aki saboda takaici sai dai ta dake ta nufi kofar fita Azima kam idanunta na tsaye a kansu har sai da Omar din ya tsargu ya juyo suka had'a ido sai tayi saurin dauke kanta ranta idan yayi dubu ya 'baci da sauri tayi gaba Aysha na fad'in"Don Allah ki samo min masu kyau 'kawata sai kin dawo."
Azima bata samu damar amsa mata ba ta fuce cike da takaici da bacin rai.
A gaggauce ta juyo ba tare da ta kalli inda suke zaune ba ta shige dakinta, toilet ta nufa domin daura alwala.
A hankali ya tura kofar dakin ya shiga.
Tana zaune kan dadduma bayan ta idar da sallahr ta amsa ba tare da ta kalleshi ba.
Kan Sofa ya zauna yana kallonta ta mike tana nannade daddumar yace."Aysha wannan shashashar 'kawar taki me ya kawo ta ne."!?
''Kamar yaya."!? tafada tana kallonsa.
"Kin san dai sam yarinyar batayi min ba kuma bana son tarayyarku dake da ita."
"Azima bata da wata matsala gaskiya kaine dai kawai ka tsaneta."
"Dole in tsaneta aysha saboda ita ke sake tunzura min ke."
Shiru tayi masa kawai ta nufi toilet wanka tayi ta fito daure da towel har yanzu yana zaune a dakin.
Wardrobe ta nufa ta dauko kayan bacci ya bita da kallon sha'awa tsaf ta shirya jikinta ta fesa turere duk idanunsa na kanta, Yace."Ina Abdul ko yana sashen mama."
"Eh yana can." Okey kina nufin can zai kwana ko me."!?
"Eh ai mamance da tace haka bani bace."! tafada tana dan turo baki.
Shiru yayi yana kallonta yace." Kin san dai bana kaunar wannan kawar taki ko."!?
"Wai don Allah meye na damun kanka ne kan Azima wai me zata tare maka ne? shikkenan kawayena baza su kawo min ziyara ba sai kai ta damun kanka."
Hannu ya d'aga mata fuskarsa a hade yace."Bana son hauka da hayaniya ni ina miki maganar data dace ke kina d'aga min murya."
Ta zumbura baki tana dauke kanta
Tsaki yaja ya mike tsaye kana yace."Zan sanya a rufe sashesn nan sam bana bukatar sake ganinta a gurina.
Sai ta mike tsaye murya na rawa tace"Haba dai! wai don