Author : Binta Umar Category : Complete Novels
Omar na da masifar son 'yaya a rayuwarsa sai ya fara adduar Allah yasa itama ta dinga haihuwar 'yan biyu.
Wannan labarin da ya samu daga gurin mahaifiyarsa shine ya kwad'ai ta masa shiga sashen Nanne domin tin zaman sa gaban mahaifiyar tasa take shaida masa da cewar Safa kullum na sashen suna tare da Aysha yaji ransa ya 'baci sam! wannan amintar tasu da kuma kusancinsu baya kaunarsa saboda shi suke cuta dama kuma yana cike da Aysha da takaicin da take 'kunsa masa ya sani sarai ita ke sanya safarau wataran nayi masa rashin kunya shiyasa itama ya tattara ta ya watsar don ya gaji da wulakancin da take masa....
*"Tofa! idan Aysha na takama da jinin sarauta! To shima fa Yana takama da nashi sarauta* Zamu ga wanda zai riga karaya a tsakaninsu.
Aysha na kuryar dakinta suna cin abinci wanda Ayshan ta girka musu da kanta Aysha yanzu a fagen girki babu abunda za'a nuna mata sai abunda ba a rasa ba zamanta na wannan lokacin gurin mahaifiyarta yasa ta iya abubuwa da dama idan tayi abinci Safarau ta dinga santi kenan abunka da me yaron ciki, Nanne tana masifar jin dadin yanda Aysharta ta koma ta nutsu tayi hankali sosai yanzu tana alfahari da aysha a ko wane irin yanayi ne shiyasa kwata kwata yanzu bata takura mata kuma ta kudiri aniyar cewar baza ta tursasa ta ta koma hannun Omar ba tinda shi baiji kunyar sakinta a gabansu to suma baza suji kunyarsa ba.
Nanne ta kar'be shi hannu biyu suka gaisa hankalinsa nakan baby Safa dake gefanta a kwance tana tsotsar hannu yace."Nanne haka yaran nan suka girma ashe."?
Tace."Aikam gasu nan sunyi wayo ai kasan dama irinsu basu iya girma ba tubarkallah." Sai ya mike ya isa inda yarinyar take ya dauketa fuska a sake ya kai bakinsa kan nata ya sumbuta, aikam sai yarinyar ta fara 'bangala dariya shima yasa dariyar yana kallon Nanne yace."Yarinyar nan fara'a gareta Nanne." Tace"Haka take ai ko motsa guri akayi sai ta hau dariya ta dauka wasa ake mata ta gaji mai sunan nata safarau."
Sai ya sake rungumeta a jikinsa yace."Har Halin ma Allah yasa ta gaji irin nata."
Nanne tace"To ameen ya rabbi." Dakin Ayshan ya nufa da yarinyar a sa'be a kafadarsa Nanne ta bishi da kallo sai taga kamar ya rame ba kamar sanda ya tafi ba.
Aysha na cikin wasu ingilish wear riga da siket irin na jins siket din ya dan kama mata 'kugu sosai rigar ma haka ita rigar irin mai yankakken hannu ce mai kamar vest gaban rigar da adon stons a jiki ta tattare gashin kanta ta daure da katon ribbon duk da ba wata shahararriyar kwalliya tayi ba idan ka ganta a lokacin sai kaji kamar ka sace ta ka gudu Aysha shigar kananun kaya nayi mata masifar kyau!!! Hira suke da safarau ya bude dakin ya shigo bakinsa dauke da 'yar 'karamar sallama.
Dukaninsu suka jiyo suna kallon bakin kofar 'kamshin turaransa ya gauraye d'akin......Idanunsa tsaye kansu ya 'karasa tsakiyar dakin ya nemi guri ya zauna kan Sofa.
Safa tace"Yayana sannu da hanya ashe kana tafe jiya baka fad'a min ba." Murmushi yayi mai kyayartawa yace."A kan me zan fad'a miki zan dawo Safa nasan idan na sanar dake dawowata zaki fad'awa wanda bana so su sani shiyasa kawai na baki mamaki."!
Tayi dariya ha'koranta duk suka bayyana tace"Sannu da zuwa to bari in had'a maka abinci kaci kasha lemo duk dai nasan kaci abinci gurin mama nasan ba zaka ki cin wannan ba na mussaman ne."
Yace."Safa ba wannan ne a gabana ba kece a gabana Mama tayi min albishir mai dadi mai yasa duk wayar da mukeyi dake baki fad'a min ba ko an hanaki sanar min ne."!? Yana sane ya fad'i maganar yasan aysha zata tsargu aikuwa ta tsargu din sosai kuma taji haushin shariyar da yayi mata sai ta fara tunanin abunda zatayi masa ta huce!
Safa ta dinga mirmushi tana fad'in"Haba Yayana ba haka bane wallahi ni babu wanda ya hana ni na fada maka kawai dai ina jin kunya ne."
Yace."Kunya ta 'kare tunda nasani kuma cikina ne nasan sanda nayi abuna to meye abun kunya don kin fada min." Shiru tayi tana murmushi yace."Tashi muje in duba babyna mu gaisa dashi.".
Sai ta kalli Aysha da sauri!! Yace."Meye kika yi saurin kallonta ko sai ta baki umarni ne."!? Safarau tace"Kai Yayana ni ba haka nake nufi ba yanzu dai kaci abinci tukkuna."
Yace."Ai komai kikace yanzu dai-dai ne zuba min amma bada yawa ba."
Ta bude abinci ta zuba mishi shinkafa ce da miyar kifi irin manya manyan nan sai kamshi miyar takeyi tace "To ka sakko 'kasa mana." Hannu ya mika ya dauki plate din yana da kan kujerar ya fara cin abincin......Duk da ba wani abinci ne na 'kakale ba yayi masa dadi sosai babu karnin kifi ko kadan sai kamshi da miyar takeyi ya cinye tas! ta mika masa lemo yasha tace"Ko in 'karo maka abincin." ? Yace."Ya isa haka da dai banci wani sasashen mama ba da naci da yawa domin miyar tayi min dadi sosai." Tace"Aunty Aysha ce tayi nima naji dadin abincin sosai wallahi.
Ya kalli Aysha da gefan ido ya lura kamar hankalinta ma baya kansu abincinta kawai take ci sai kawai ya zage ya dinga kallonta yana 'karewa jikinta kallo kafin kice kwabo sha'awa ta kamashi komai na Aysha na mussaman ne Aysha ta zama tamkar wata balarabiya waye zai ce ita ke shayar da 'yab tagwaye nonowanta ko na wata budurwar albarka ko ina a jikinta a cike dam babu rama ya tsurawa shara'bar ta ido dake siket din ya d'an tattare daga 'kasa dan in ka sanya ido ma har cinyar ta zaka gani sai ya shagala da kallonta yana sauke ajiyar zuciya.....Jikinta ya bata da sauri ta dago kai suka had'a ido yayi saurin kauda kansa yana shafa sajensa ta'be baki tayi ta yagi tissue ta goge bakinta ta kalli Safa tace"Ya kamata kiyi gaba da mijinki Lada ya isa zan sa a gyara min daki in samu in kwanta in huta kafin waccan 'yar rigimar ta dawo ta hanani bacci." Safarau tasa dariya ''Kai aunt Aysha yau korata kikeyi kenan aikuwa zan sa gwaggo ta dawo miki da ita ta hanaki ki huta." Tace"To Safa me zakiyi kuma bayan mijikin ya dawo kije ki kula dashi." Safarau ta mike tana fad'in"Aunty Aysha kenan." Hanyar fita ta nufa so take ta basu guri su gana da juna su dai-dai ta tsakaninsu shiyasa duk abunda aysha zatayi mata take kokarin biye mata duk dan ta dawo dakinta.
Safa na futa ta mi'ke ta nufi bakin window tana wata iriyar tafiya tana sane take motsa mazaunanta kuma babu abunda zatayi bakin window din kawai don ta d'aga masa hankali ta mike domin ya ganta cikin kayan da yake mayatar son yaga tasa irinsu.
Aikuwa gumi ya dinga yi yana binta da kallo kamar yaje ya rungumeta haka yake ji da kyar ya mike ya fita daga dakin ransa idan yayi dubu ya 'baci! wannan girman kan na Aysha na masifar 'kona masa rai!
****
Bayan Sallahar isha'i ya sake zuwa sashen wannan karon gurin Galadima yaje Nanne ta shiga ta sanar da zuwansa ta fito tace masa ya shiga.
Sai da suka ci abinci tukkuna suka nutsu ya fada masa abunda yake tafe dashi.
Galadima yace."Idan dai ka tabbatar da haka d'in ne to meye amfanin zaman aysha a tare damu kayi saki kuma ka janye a lokacin ta tabbata matarka insha Allah,saboda haka ka kwantar da hankalinka insha Allahu zaka cigaba da zama da matarka."
Godiya yayi sosai yayi masa sallama ya tafi.
Koda Nanne ta shiga dakin bayan tafiyarsa ya sanar mata da abunda ke da akwai sai ta nuna rashin amincewar ta kan lamarin tace"Sam! bata yarda ba kawai tana ganin ya fad'i hakane saboda babu yanda zaiyi ai a gabanta komai ya faru me yasa bata ji lokacin da yace ya mai da ita ba karya kawai yakeyi." Wannan kace nacen sai ya jawo musu 'bacin rai! a tsakaninsu abunda bai ta'ba faruwa ba suka rabu ran kowa babu d'adi!
Washe gari da safe kafin ya futa fada ya sanya aka kira masa ayshan dama tunda ta ji kiran tasan maganar ce......"Aysha Omar yazo min da wata magana mai muhimanci kuma na zauna nayiwa maganar kyakykyawar fahimta tabbas abunda Omar ya fad'a gaskiya ne saboda tun yana yaro na san halinsa nasan abunda zaiyi da wanda ba zaiyi ba Omar ba zai yarda kuyi zaman zina ba lokacin da na umarce shi kan ya sake ki nayi miki hakane domin kiji d'acin da mace takeji lokacin da aka saketa sannan nayi hakane domin ya zama gargadi a gareki hakika lokacin kin bani haushi mutuka aysha shiyasa na yanke wannan hukuncin a kanki sanin kanki ne babu uban da zai so a saki 'yarsa, wannan dalilan dana fada miki sune suka sanya ni na umarce shi da aikata haka, To dake Ubangiji nasan auranki dashi a take bayan yayi sakin Allah ya nufe shi da janyewa ma'ana ya mai dake saboda haka ina so ki nutsu ki maida komai ba komai ki koma dakinki ko rungumi 'yayanki, Duk wata mujadalah ta 'kare a tsakaninki da mijinki saboda yarinyar da ta asassa tashin hankalin a tsakaninku Allah ya saukar da ikonsa a kanta yau tsawon sati biyu kenan da rabuwarsu da Omar din yanzu haka tana kwance a asibiti cikin halin taimako to kinga kenan duk abinda aka barwa Allah komai yakan zo cikin sauki."
Aysha ta dinga mamakin maganar mahaifin nata Omar ya rabu da Azima tun ba'aje ko ina ba! shin me hakan yake nufi? dama da wace niyya Azima ta shigo rayuwarta me ya had'asu da juna har ya saketa? bata da me bata wannan amsa dole sai shi mai gayya mai aiki.
A hankali tace"Baba ba wai na'ki jin maganar ku bane A'a ba haka bane wallahi ina so ku 'kara bunkice sosai kan maganar da ya kawo muku a kai Kuma ina so a kira Safarau ta zama shaida a gabanta komai ya faru kuma nima ina da sauran hankalina banji sanda ya furta da bakinsa cewar ya mayar dani ba har sai da na haihu tukkuna sannan yazo asibiti yana cewa ya mai dani dakina, idan hakane kuwa kaga na riga na haramata a gareshi tunda na haihu ina da ikon in za'bi abinda nake so a rayuwata."
Baba galadima jikinsa yayi sanyi da jin maganar 'yar tashi hakika maganar ta abar dubawa ce sosai yana da kyau su tabbatar da gaskiyar al'amari kafin su yanke hukunci dole zasu yi zama a dakin taro dukaninsu wanda abun ya shafa domin a warware matsalar.....Yace."Ki tashi kije babu komai zan duba maganarki."
Mikewa tayi ta futa ranta fari tas ta rantse kafin ta koma hannunsa sai ta bashi wahala duk taurin kansa sai yayi mata kuka ta tabbatar da nadamarsa sannan zata koma hannunsa.
Misalin karfe goma na safe Fulani ta shigo sashen suka gaisa cikin girmawa da Nanne Aysha ta fito daga kicin cikin girmamawa ta tsunguna har kasa ta gaida Fulani kana ta mi'ke ta cigaba da aikinta.
Fulani tace"Nanne magana mai muhimanci ce take tafe dani tsakanin yaron nan Omar da Aysha.
Nanne ta fahimci inda maganar take sai ta gyara zama a nutse tace"To ina sauraron ki Mai babban d'aki.
Fulani tace"Ashe mune muke ta abunmu tuntuni Omar ya janye sakin da ya ratsa tsakinsa da Aysha kafin ta haihuwa sai jiya da ya dawo yake shaida min da haka shiyasa nace zan shigo da kaina muyi maganar na kuma rarrashi aysha don Allah ayi hakuri a yafi juna Aysha ta koma dakinta ta rungumi 'yayanta."
Nanne tace"Ban tari numfashinki ba mai babban d'aki! Fulani tace'Ina sauraronki.'' Nanne tace"Omar zai iya zuwa ya fad'a miki magana ki yarda da ita saboda yana so ya kare kansa kuma yans bukatar aysha ta koma dakinsa, to zancan gaskiya maganar da yake fada muku ba gaskiya bace A gabana ya saki Aysha kuma banji lokacin da yayi wannan furucin ba har na bar dakin.....Bai furta irin wannan al'amari anayin sa ne a gaban shaida idan kuma yana da shaida to sai ya fad'a wallahi Aysha zata koma dakinsa mutukar an tabbatar da shaidar sa gaskiya ce."
[6/11, 9:36 AM] Bintu Novel: 78
Fulani tayi shiru tana sauraron jawabin Nanne cikin nutsuwa tace"Hakane kuma maganarki a gaskiya tunda babu wanda yaji ko ya gani a lokacin da yace ya mayar da matarsa to dole ne a tsaurara bunkice akai duk da dai a jikina ina ji Jarumi ba zai fad'i son ransa ba kawai don biyan bukatarsa dai-dai gwargwado yana da ilimin addini ina ganin ba zai aikata abunda zai je ya dawo ba, amma dai d'an yanzu ba'a shaidarsa mussaman kan batu na aure tabbas zamu zauna dashi akan maganar insha Allah ya tabbatar min da waye shaidarsa kuma waye ya ji ko ya gani lokacin da ya furta ya mayar da ita."
Nanne tace"Wannan shine gaskiyar magana dama ba wai ina adawa da komar aysha dakinta ba A'a ni nafi son ta koma dakinta domin shine suturarta ina dai so a tabbatar da gaskiyar magana ne."
Fulani tace"Duk na gane abunda kike nufi Nanne kuma kina da gaskiya ai babu komai insha Allahu komai zaizo cikin sau'ki."!
Hira suka cigaba dayi suna jajantawa juna abunda ya faru dangane da auran Omar din da Azima nan Aysha ta sake tabbatar da gaskiyar lamarin taji dadi sosai da Allah ya tona asirin Azima da wurwuri wani gefan kuma na zuciyarta taji tana tausayawa Azima rayuwa kenan idan kasan farkon ka baka san karshen ka ba yanzu Azima sai dai ta dinga yawo a keken guragu Allah yasa mufi karfin zukatanmu ameen.
Omar kam ganin Fulani bata sashen sai ya matsawa Safa kan dole sai tayi masa matsar kafafu a cewarsa wai duk jikinsa ciwo yakeyi sai yayi d'ai-d'ai a palon Abdul na saman sa suna wasa.
Ita kam Safarau tsoron kusantarsa take saboda tasan halin jarabarsa yasa ta dinga baya baya dashi.....Wani Shu'umin kallo yake mata yana bin kyakykyawar fatarta da kallo goshinta sai she'ki yake yayin da idanunta suka kara haske ya kai idonsa kirjinta yaga sun cika sosai tsigar jikinsa ta fara tashi Safa duk tana lura da irin kallon da yake mata kuma ta gane a cikin sha'awa yake ita tun da ta samu ciki ta daina kaunar al'amarin nan bata so, tace"Tunda bacci zakayi kawo Abdul din a mika shi gurin Mai kula dashi."
murya a harde yace."Tashi muje in fada miki wata magana."Shiru tayi masa.
Ya mike tare da Abdul din dake son yin bacci a jikinsa....Dakin da yake a madadin nata ya nufa sai ta bishi da kallo cike da mamaki shikkenan ya dawo yanzu zai fara takura mata.
Ta jima kafin ta mike tabi bayansa sai ta tarar dashi har ya cire kayan jikinsa daga shi sai gajeran wando Abdul yayi bacce ya kwantar dashi kan kujera.
Tana shiga ya ware mata hannuwansa duka biyun wai tazo.
Tace"Yayana meye haka don Allah duba fa kar ka manta fa a sashen Mama kake don Allah kasa kayanka."
Yace."Safa bani da kuzarin saka kaya yanzu bacci ma nake ji ga gajiya data dame ni nace kiyi min tausa kin'ki ko"
Tace"Ba wai na'ki bane Yayana nima bani da wani kuzarin kirki shiyasa.
Ta karaso a hankali ta zauna a kusa da kafafunsa ta fara matsa masa jiki sama-sama....Ido yake lumshewa yana cije lips dinsa ya bude jajayen idanunsa da suka rine da sha"awa ya kalleta a hankali yace."Safa baki tambayeni amaryata ba.".
Zumbura baki tayi tace"Allah Yayana idan kana so muyi hirar arziki ka daina min maganar wannan maci amanar meye ruwana da ita."
Murmushi yayi ya shafa hannunta dake cinyarsa yace."Bana so muyi fad'a safa yanzu lalla'ba ku nake saboda na gane kune mataye nagari dama duk abunda ya faru a baya tsautsayi ne insha Allahu mun daina fad'a."
Ta'be baki tayi ta cigaba da matsa masa jiki shi kuma yana shafa hannunta yace."Kin san menene."!? Tace."A'a." Ina tsananin 'kaunarku dake da Aysha Ko da nayi tafiyar nan ma hankalina na kanku burina kawai na dawo na same ku amma me yasa yanzu bakya bani kulawa ko kuma aysha ke zugaki a kaina uhmm!."
"Babu ruwan Aysha ina ganin kaine duk ka jawo komai daka dinga nuna rashin adalci sannan kaje ka auri kawarta ai wallahi ina ganin duk abunda tayi maka bata yi laifi ba don kaine ka jawowa kanka."
Yace."Okey kina so ki fada min cewa itake dora ki hanyar da zaki 'kin bin umarina ko? ai ba haka na aure ki ba ada duk abunda nace miki kiyi kinayi babu musu, yanzu kuwa kin mai dani wawa duk abunda kike so shi kikeyi kina so ki koyi d'abi'u irin na Aysha ko.
Rai a 'bace tace"Yayana ka daina ganin laifin aysha da kokarin d'ora mata laifi wallahi aysha mutuniyar kirki ce sai wanda ya zauna da ita ne zai gane halinta duk abunda ya dinga faruwa da kai da ita a baya dana zauna nayi tunani sai na gane cewa duk laifin kane kuma Aysha tunda muke da ita wallahi bata ta'ba shirya min magana ba akanka ko tace nayi maka rashin kunya da sauransu kullum idan nayi ba dai-dai ba sai ta gyara min Aysha bata kishina yanzu a baya ma rashin fahimta ne yasa ta dinga kishina amma yanzu ni na tabbatar da cewar tana kaunata tsakani da Allah."
Shiru yayi kawai yana jinta sai da ta gama sannan yace."Tana baki shawara ki kula dani ki bani hakkina me yasa ita bata kula dani umm? kina kallo daga tafiya na dawo ko kallo ban isheta ba Aysha baza ta ta'ba canzawa ba."
"Yayana dole fa sai kayiwa aunty aysha uziri a irin wannan lokacin domin ka 'bata mata rai ka 'kunsa mata bacin rai da ba'kin ciki kawai kaje ka cigaba da rarrashinta fushi ba naka bane a halin yanzu."!
Yace." Duk wata magana dai ta 'kare wacce akeyi domin ita bama tare a halin yanzu to sai me kuma? Sai ku zauna ku biyu kamar yanda kuke bukata."
Ta kalleshi cike da mamaki tace"Bangane maganar ba.
Murmushi yayi me ciwo yace."Safa na saki Azima tsawon sati biyu da suka wuce."
Safarau taji gabanta ya fad'i! duk 'kin da takewa Azima sai da taji