Advertisements
Chapter 11 Reading Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar

Author :  Binta Umar Category :  Complete Novels

Chapter   11 / 29

30K to 33K   out of 86.8K words

iya sadaukar da rayuwata kanka kar ka manta kai namiji ne na mace hudu zan zauna da matanka lafiya."


"Wallahi kin bani mamaki Azima yanzu dama haka kike? na amince miki kin ha'ince ni ashe dama mijina kike so shiyasa kike bibiyata nagode Azima bani da abinda zance miki." Kashe wayar tayi hawayen bakin ciki na zubo mata

Azima tayi sakare da waya a hannu lallai ma ashe yana tare da aysha ya kirata har yake ikirarin ya fasa auranta wato ya fada mata ta nuna rashin yardar ta, tabdijam aikam ba zata ga samu taga rashi ba, hannu na kyarma ta nemi numbar Hasina.


Sun jima cikin dakin yana rarrashinta kafin ya shawo kanta suka koma sashen su hankalinta ya dan kwanta kad'an jin cewar ya janye kudirinsa na auran Azima tana adduar Allah yasa da gaske yake har zuciyarsa.


Ranar Dashi da Safarau haka suka yini suna hidima da ita a palo shi kansa yaji dadin yanda ta sake take magana dasu ya zauna tsakiyar iyalinsa suna hira cike da walwala da farin ciki.

Ko da suka shiga daki haka ya dinga lallabata da kalamai masu dadi har ya samu ta sakar masa jikinta suka kwana suna soyayyar su washe gari suka tashi cikin walwala da farin ciki.

To Aysha ta soma sakewa tana sanya ido kan shige da ficen mijinta sosai take kula dashi da bashi kalamai masu dad'i kullum ya dawo daga aiki suna tare a palo sai kusan goma suke tashi Safarau taji dadin sauyin da aka samu ta bangaran aysha yanzu ta lura dama kwanciyar hankalinta shine zaman lafiyarsu a gidan."


*Tsugune bata 'kare ba*


Azima da Hasina ne gaban wani mutum bakikirin mai siffar samudawa yana zaune da wasu tarkace a gabanta wanda kana ganinsa kasan cikakken d'an tsubbu ne na gani kasheni.

Ko da ya gama jin abunda yake tafe dasu sai ya sanya dariya yace "Wannan abun ba wata matsala bace babba duk yanda za'ayi zai taimaka mata zaiyi mata aikin da zai sake karkato mata da hankalinsa kanta amma dole akwai sharadi idan ta amince shikkenan.

A take tace" Ta amince ya fadi ko wane sharadi ne yace."Zata aje sallahr guda daya cikin salloli biyar tsawon sati guda wacce sallah ce take gani zata aje.

A take tace"Ta aje sallahr asubahi boka yace"To bukata ta biya wani koka ya mika mata mai kurzunu-kurzunu ya bata wani bakin ruwa cikin robar faro yace kije ki daureye gabanki ciki da bai duk ki kwakule ko ina ki kawo min.

Azima ta fita waje wani karamin daki ta shiga taje tayi yanda yace mata ta dawo da ruwan daurayar a cikin koka ya karba ya sansana yana murmushi ya dauko wani bakin abu ya barbada a ciki yace."Ki tafi da wannan gida kina zuwa kiyi wanka da ruwan kina ambatar sunansa da fad'in "Kin cinye zuciyarsa da izinin aljanar arzikila hankalinsa zai dawo gareki domin da ita na had'a aikinki zata taimaka miki sosai, itace zata dinga hura masa wutar sonki a cikin zuciyarsa.

Azima tayi godiya tare da zube masa makudan kudi suka dauko hanya tana zuwa gida ta shiga toilet ta kwabe kayan jikinta tas ta wanke jikinta tana ambatar sunan Omar da fad'in" Omar na cinye zuciyarka sai na mallake ka da izinin aljana Arzikila." Tas ta wanke jikinta ta fito a take ta soma jin jikinta yayi nauyi sai ta kwanta bacci mai nauyi ya kwashe ta.


Da wata iriyar azalzalar zuciya ya tashi wanda da kyar ya samu yayi wanka yana tsaka da shiryawa aysha ta shigo tinkis tinkis domin cikinta ya soma girma ganin yanayin sa yasa ta gane yana da damuwa sai ta cigaba da tayashi sanya kaya tana tambayarsa abunda ke damunsa yace.""Babu komai ya tashi da nauyin jiki ne da kyar ya karya yayi musu sallama ya fita......To ko da ya zauna a ofis ma kasa kata'bus yayi kawai sai ya tsinci kansa da d'aukar wayarsa ya fara neman numbar Azima.
[6/2, 9:42 AM] Bintu Novel: 69



Azima na tsaka da bacci taji ringing din wayarta ta lalubi wayar ta kara a kunne jin muryar Omar ya sanya ta mikewa da sauri tana mutsika ido wayar ta sake rikewa tana wata iriyar shashsheka dace"My Man yau ka tuna dani ko ina kwanace ciwon sonka zai kasheni ina fatan zanji magana mai dadi daga gareka.


Omar ya murza fatar goshinsa yana jin yanda sautun muryarta ke kashe masa jikinsa yace."Na kasa hakura dake Azima ya za'ayi ne ina bukatarki a tare dani ba tare da anja dogon lokaci ba."

Tayi wata siririyar dariya tare da fad'in"Wallahi ko yanzu a daura mana aure da kai a shirye nake." Yace."Ki bari zanzo yau da daddare zamuyi magana insha Allahu." Sallama sukayi ya aje wayar sai yanzu ya samu sassauci a cikin zuciyarsa ya fara aikin dake gabansa.


Aysha da Safarau ne zaune a palo suna cin abinci Safarau tace."aunty Aysha ni kuwa kin fahimci yanayin Yanda Yayana ya fita dashi kuwa kamar bashi da lafiya."


Aysha tace"Nagani Safa na tambayeshi yace."Wai ya tashi da nauyin jiki amma kirashi a waya muji lafiyarsa."


Safarau ta dauki wayarta dake gefe a aje ta fara neman numbar Omar din Suna tare da Sulaiman a ofis ya ga kiran a 'ka'idar sa baya daukar wayar iyalinsa gaban kowa da yaga numbar Safarau ce sai ya share har ta katse ta sake kira nan ma bai dauka ba.


Jiki a sanyaye tace"Aunt kina dai ji ko."!? Aysha tace"Bari in kirashi da waya mu gani." Sai ta fara yunkurin tashi Safarau tace"Bari in dauko miki wayar aunt"

Aysha ta koma ta zauna tana cije baki wannan cikin na jikinta yazo mata da sauyi kala-kala komai take karfin hali kurrum take.


Safarau ta karaso hannunta rike da wayar Aysha ta karba ta fara kiransa.

Lokacin suna sallama da Sulaiman har wayar ta shigo ta katse bai dauka ba ta kara kira nan ma ta katse bai daga ba, kufula tayi ta aje wayar tana jan tsaki tace"Ke nifa jikina na bani babu wani abunda ke damunsa kawai tsabar wulakancin sa ne ya tashi kar ki 'kara kiransa a waya mu zuba masa ido muga inda ya dosa."

Safarau tayi shiru tana nazarin maganar ayshan.

Bayan Sulaiman din ya fita ya koma ya zauna a nutse ya dauki wayar tashi ya fara kiran numbar aysha......Koda ta duba taga shine sai taki dauka ya kira sau kusan uku ta share sai ya koma kiran ta safarau Aysha ta hanata dauka itama ya kira kusan sau biyu sai ya hakura ya aje wayar ya cigaba da aikinsa zuciyarsa na azalzala masa ya tashi kawai ya tafi gidansu azima ita kawai yake so ya bude ido ya gani.



Karfe biyar ya shigo gidan Aysha ce kawai a palo safarau na kicin tana hidimar abincinsu na dare....yayi sallama ta amsa masa a ciki...Mikewa tayi da kyar ta karasa ta kar'bi abubuwan dake hannunsa har da wayoyinsa tayi gaba saboda yanayin tafiyar tata yasa yazo ya shige ya bude dakin ya shiga itama ta shiga ya dinga bin fuskarta da kallo ganin yanda take cin kunu ne yasa yace."Me akayi kuma naga sai faman shan 'kamshi kike ko nayi wani laifin ne gimbiya."!?

Tace."Haba ba dole in 'bata rai ba, ka fita ka barmu cikin fargaba mun kiraka a waya ka'ki d'aukar wayar kana tunanin ranmu zaiyi dadi."

Sai ya karasa inda take ya rugumeta a jikinsa yana d'an shafa bayanta yace."Aysha sarkin fushi ayi hakuri naga kiranki lokaciin ina tare da ba'kone okey shiyasa nima dana kira aka rama kenan." !? Fari tayi da ido tace"Eh mana kai ma kaji inda dad'i." Sai yasa dariya yace."Ai ni duk abunda zakuyi min baya bani haushi sai dai ya bani dariya." Tace."Ai dama baka da zuciya." Wani sihirtaccan kallo yayi mata yace."Kin manta tuntuni kin cinye min zuciyata aysha."!? ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya kiss ya manna mata a kumatu yace."Bari nayi wanka na fito na duba babyna kwana biyu ana shiga hakkina da yawa in nayi magana ayi min wayo da dubara yau ba zan yarda ba."

Tana dariya tace"Wallahi baka isa ba ai nace na yafe maka kaje gurin 'yar uwata ka sauke bukatunka haka kawai ka kasheni da raina kai fa kanka ka sani ta ko wane fanni baka da sauki."

Murmushi kawai yayi ya nufi toilet sai tabi bayansa tana fad'in"Bari na had'a maka ruwan wanka ko."!? Yace."Aysha bari kawai jeki huta zan had'a da kaina nagode miki."

'Ki tayi sai da ta had'a masa ruwan wanka yana tsaye yana kallonta fuskarsa dauke da 'kyataccan murmushi yana mamakin wai yau shine tare da ayshan sa suke zama irin na ma'aurata tabbas addua ba 'karamar garkuwa bace a gurin ko wane muslumi

Tace."Ko nayi maka wankan ne."? Girgiza kansa yayi yana lumshe ido yace."Bari kawai aysha kan ki tsokano ni kije ki huta kinji ko Allah yayi miki albarka ya barni dake."

Tace."Ameen Annuri." Fita tayi daga toilet din ya bita da kallon so da sha'awa a halin yanzu duk abunda aysha tayi a gurinsa dai-dai sunfi karfin sati hudu rabon da su hada shimfida da ita yana cike da tsananin sha'awanta amma saboda ta nuna masa sadaukarwa ya sanya ya daure ya hakura, yake sauke dukanin lalororinsa gurin Safarau to dake hausawa sunce rai dangin goro ne sai yaji yana marmari aysha bawai don ya gundura da safarau ba ko d'aya kawai saboda ya saba shiga raga biyu ne shine dalili amma ta ko wane fanni safarau bata da makusa yana masifar jin dadinta kuma duk jarabarsa tana gamsar dashi gata da wata iryar baiwa wacce shi kadai ne ya santa.

Aysha kam wardorbe dinsa ta bude ta dauko masa jallabiyar sa da gajeran wando ta dauko manshi da yake shafawa coco butter ta zauna gefan gado tana jira ya fito.

Daya daga cikin wayoyinsa taji alamar sa'ko ya shigo sai ta sanya hannu ta dauka tana dubawa.

Sabuwar number ce inda Allah ya rufa asiri kenan.


_"Da fatan ka tashi aiki lafiya to Ubangiji Allah ya kara maka d'aukaka gami da nasara a rayuwarka, Ina so in san da kamar 'karfe nawa zaka zo domun in shirya maka kaina."_

Wani irin gumi ya tsinkewa aysha ta dinga duba sa'kon hannunta na kyarma!! "Yaushe zaka zo domin in shirya maka kaina." duk cikin wasi'kar wannan kalmar itace tafi daukar hankalinta shin Omar neman mata yake ko meye? hannu na kyarma tayi yunkurin kiran numbar sai kuma zuciyarta tace"Idan kin kirata kice mata me? jikinta a sanyaye ta aje wayar tana jin wani irin juyi a cikinta.


Ya fito daure da towel a daure a 'kugunsa, sai tayi ta 'kokarin danne damuwarta tana so tayi amfani da shawarwarin da Nanne ke bata kan ta dinga tsayawa tana bukince kafin ta yanke hukunci.


Da kyar ta danne damuwarta ya zauna yana goga mata danshin ruwan jikinsa a jikinta murmushi kawai take ta dauki mai tana shafa masa shi kuma sai sun'kulinta yake ya ta'ba nan ya ta'ba can har sai da yasa ta dariya.....Wayarshi ce tayi 'kara dake tana gefanta sai ta d'auka kallo daya tayiwa numbar tagane sai ta share mika masa tayi ya karba yana duba fuskar wayar, ta gefan ido ya saci kallonta aysha na kallonsa sai tayi kamar ma bata ganshi ba ta tsalleke can kan bed din tana shafa masa mai a bayansa.

Haka sai ya bashi damar daga wayar da sauri yace."Zan kira ka anjima kad'an." Kashe wayar yayi ya aje ya juyo yana mata shu'umin kallo tace"Wannan kallon fa habibi." Ajiyar zuciya ya sauke yace."Aysha kin riga kin gama kashe min jiki gashi yamma tayi ya za'ayi ne."! Tace."Komai kake so zanyi maka ka bari sai anjima ko." Sai ya saki fuskarsa yana dariya "Alhamdullhi. Yau kince in shirya zan gwangwanje zan barje gumina." Yanda yake fad'in maganar ne yasa ta dinga kyalkyala masa dariya shi kuma ya dinga kallonta da jan ido yana girgiza kai yace."Dariya kike min ko."? Hannu ta d'a masa tana girgiza kai sai ya shammace ta da sauri ya riko hannuwanta duka biyun da hannunsa daya ya tallafo kanta bakinta ya hada da nasa ta shiga kissing dinta a d'imauce.

Sai da ya tsotseta son ransa sannan ya saketa da jan ido yace."Kika sake min dariya yanzu zanyi me gabakid'aya."

Aysha ta sauka daga bed din tana zanga masa harara shi kuma sai dariya yake mata ya biyo ta a baya palo suka fita yana tsokanarta Safarau ta fito daga d'akinta cikin gawurtacciyar kwalliya safarau kusancin su da Aysha yasa ta soma ganewa yanzu kwalliya take sosai ta kananun kaya hakan na sake janyo hankalinsa gareta ..Yanzu ma kwaliyyar ta ta tafi dashi sosai ya dinga satar kallonta har suka zauna a daining domin cin abinci yana kallonta tare da jin sha'awarta yana ganin kaf duniya babu wanda ya kaishi sa'ar mata


Cike da walwala da farin ciki suke cin abincin ko kusa ko alama aysha bata nuna masa komai ba tana so taga abunda zai faru nan gaba aikuwa wayarshi ake ta kira ya'ki dauka ya kai sau biyar Safarau tace"Yayana kanaji fa ana kiranka." Yace."Safa kyale kawai kiran bashi da muhimanci ne." Sai suka share kawai suka cigaba da hira Ya dan kalli agogon hannunsa yace."Zan d'an fita yau amma ba wani dad'ewa zanyi a waje ba ina fatan babu matsala."

Aysha tace"Babu Allah ya dawo da kai lafiya."

Mikewa yayi ya nufi dakinsa cikinsu babu wacce tayi yunkurin binsa sai suka cigaba da hirarsu cikin fahintar juna.

Ya fito cikin wata rantsatstsiyar shadda wagambari ruwan kasa anyi masa din hannu tazarce ce sai yayi amfani da hula dara 'yar gaske kamshin turare kawai yake kafafunsa sanye da takalmi rufaffafe irin na gidan sarauta.

Dukaninsu suka bishi da kallon mamaki! irin wannan kwalliya haka kamar wanda zashi daurin aure Ya riga ya gama tona kansa a gurin aysha Safarau aka bari a ruwa.


Kallo guda tayi masa ta dauke kanta tana mamakin halin cin amana irin nasa....Yazo ya tsaya kansu yana gyara links din hannunsa Safarau tace"Yayana irin wannan ado haka! hummm! ko dai zance zakaje ne."!?

Harararta yayi yace."Ke wane irin zance kuma ana zaune lafiya yanzu yanzu zan dawo gurinki muyi zance mai dalili."

Sai ta sa dariya tana fad'in"Aunty gimbiya ki shiga cikin maganar nan fa ki duba ki ga irin kwalliyar da mijinki yayi gaskiya ni ba zan barshi ya fita da ita ba."


Murmushin karfin hali kawai tayi tana kallonsa yana kallonta ko kunya babu.....Safarau ta mike tsaye da gaske take wai sai yaje ya cire kwalliyar tayi yawa ai su yafi kamata yayiwa kwalliyar ba mutanan waje ba."

Omar ganin tana nema ta bata masa lokaci sai ya sha mur!! yace."Wai ke meye hakane? ni ina ruwana da 'yan mata kallo basu isheni ba mtsssw ke kin fiye kishi Safa." Kad'a kansa yayi zai fita. Aysha ta rike hannun Safarau murya a cushe tace"Kyaleshi safarau duk inda zaije yaje ke menene na tayar da hankalinki." Omar na jinta amma dake hankalinsa nacan wajan Azima bai sa ya tsaya ba yayi saurin fita domin yana jin tsoron su gano zance ya tafi.


Safarau ta zaune jikinta a sanyaye tace"Aunty anya kuwa yana da gaskiya wallahi jikina yayi sanyi anya kuwa aunt."?

Murmushi tayi me ciwo tace"Me kika fahimta dangane da kiran da ake masa a waya."

Safarau tayi shiru gabanta na fad'uwa tace"Na fahimta aunt na fahimta zance ya tafi wallahi ko kaffara ba zanyi ba."

Tace"To kingani shiyasa nace ki rabu dashi domin in kika tsananta masa ranki ne zai 'baci kin san dai halinsa."


Sai kwalla ta cika kwarmin idonta "Wallahi aunty ina jin tsoro kar yaje yayi aure tazo ta hana mu zaman lafiya muna zaune 'kalau nafi son mu zauna daga ni sai ke."!

Aysha tace" Yanzu ke a tunaninki kina ganin zai iya zama damu mu biyu mijinki fa sarkin zara ne da son mata Safarau duba da kyau ki kalli irin baiwa da kyau da hallitar da ubangiji yayi miki ni idan nice namiji Allah ba zan kalli wata macan ba."

.Safarau tace"Aunty kenan wai dani kike kwantance Allah bashi da godiyar Allah meye bakya masa menene baya samu a gurunmu shine yake faman kule-kulen mata mtswww!! sai hawaye shaaaaa!! aysha ta saki baki tana kallonta lallai ne safarau kukan dadi take.

Tace."In dai kai Omar ne to zaki karar da hawayenki wallahi gwara ma ki daina 'batawa kanki rai! idan aure zaiyi yaje yayi ni yanzu na daina damuwa Safarau na gane halayensa da d'abi'unsa to kinga dole muyi hakuri tunda haka Allah yayi shi ko wancan karon da kikaga hankalina ya tashi nasan kina da labarin inda yaje ya rakito auran Azima kawata yake son aura shine dalilina da ya sanya na tashi hankalina amma yanzu tunda ya janye auranta yaje ko wacce mace zai aura ya aura wallahi babu damuwata."


Safarau ta goge fuskarta tace"Aunty wannan 'kawar taki dama na tsaneta wallahi munafuka ce naji dadi da maganar auranta ya ruguje."

Aysha ta dinga bata labarin irin sha'kuwarsu da Azima da irin hallacin da tayi mata a rayuwa Safarau tayi ta mamaki tace"lallai aunty d'an adam abun gudu ne.


To har karfe goma da rabi gogon naku bai shigo gida ba yana can suna soyayya da Azima domin har ya samu ganawa da mahaifiyar ta dake mahaifinta ya rasu shekaru biyar da suka gabata sun riga sun gama magana da mahaifiyarta tace zata sanar da kawunan Azima insha Allahu su da kansu zasu zo gabanan Mai martaba a tsaida magana.


Azima tamkar ta zuba ruwa a 'kasa tasha saboda murna da farin ciki a gaskiya in dai da akwai bokaye irinsu wannan bokan da yayi mata aiki to gaskiya kukan su ya kare a duniya tunda bukata tana biya da gaggawa.

Hira suka sha cikin had'addan palon da aka had'a masa kayan alatu da cima iri-iri Omar yaga gata da tarairaiya gami da kwarkwasa gurin Azima gashi ta sanya wasu matsiyatan kaya da suka fito mata da shatin jikinta duk ta susuta shi yana dai daurewa ne kawai da yayi yunkurin tafiya sai ta sake dauke masa hankali da hira sai kusan Karfe goma sha daya sannan sukayi sallama da juna sai da taga tashin motarsa sannan ta juya ta koma gida cike da farin ciki da annushuwa bukatar ta ta kusa biya omar ya kusa zama mallakinta.


Aysha kam na gani sha d'aya tayi sai tace"Safa ya kamata muje mu kwanta wannan

11 / 29