Author : Binta Umar Category : Complete Novels
biyu da suka wuce.
Tiryan tiryan Buba ya zayyanawa Alhaji Lado abunda ya faru shekaru a shirin da suka wuce da zuwan Abdu makaho garin Kano da yanda aka wayi gari aka ga sun makance shi da matarsa. karshe ya fad'a masa yanda ajali ya sauka a kansa ranar juma'a bayan yayi sallahar juma'a ya shaida masa tabbas maganar wannan bawa gaskiya ce Abdu yana da budurwa 'yarinya a lokacin da mutu Sarki ya rike ta ya aura mata d'ansa na cikinsa.....Hawaye Alhaji Lado kawai yake sharewa hakika Abdullahi yaga ibtila'in rayuwa da 'kiyayya irin ta 'yan uwa Abdu shine babba shi yake binsa su kad'ai mahaifiyarsu ta haifa ta koma ga mahallincin ta suka cigaba da zama cikin gidan Ubansu tare da matan mahaifinsu wanda basa kaunarsu ko kadai saboda baiwar da Allah yayi musu.
*To Asalin Safara'u Wacece ne."?*
*Shin wane bawa ne yaje can garin bauchi domin ne man abinyi ta dalilinsa Asalin Safara'u ya bayyana?*
Wannan amsar bata da wahala 😃
Don Allah ku sanya ni a cikin adduarku a cikin wannan goma ta karshe 😭 Wallahi ina bukatar addua a cikin irin wannan lokacin Ubangiji Allah yayi maganin abunda ya dameni da sauran al'umar musulumi bakid'aya👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
[6/13, 8:19 AM] Bintu Novel: 80
Malam Haruna mai dala'ilu mutum ne salihi wanda bashi da wani buri a duniya face ya bautawa Allah mutum ne mai tsoron Allah da bin dokokinsa a wancan lokacin cewa akayi saboda tsabar tsoron Allah da yake yi baya iya zama sai dai tsuguno duk abunda xaiyi a tsugune yake ko da zai bada karatu ne idan kaga ya zaune to yana sallah ne ko kuma yana cin abinci sannan ance bai ta'ba kwana kan katifa ba sai dai ta barmar karauni ko kuma ya kwanta kan buzunsa har garin Allah ya waye.
Kullum bashi da magana sai dai kaji yana cewa Allah kasa muyi mu gama lafiya mu koma gareka lafiya motsi kadan zaiyi kalmar shahada.
To sai kuma Allah ya jarabce shi da shaidanun mata Kullum gidan babu zamn lafiya sun raba masa kan 'yayansa gaba suke da junansu ya zaunar dasu yayi musu fada amma babu wanda ya dauki nasiharsa suka cigaba da abunda sukeyi.
Kwatsam! Jibo Dan fulani wanda ya kasance babban abokinsa Allah yayi masa rasuwa Malam Jibo 'Yarsa d'ays tal Wanda itama kafin ya haifeta sai da ya share shekaru talatin da biyu sannan ya haifeta don har girma ya baibaye shi sannan.
Kafin Jibo ya rasu yace duk rintsi kada Asabe ta auri wani bayan abokinsa Malam Haruna shi ya aminta dashi shine zai rike masa yarsa da amana
Wannan dalilin ya sanya ana share makoki Aka daura auran Malam Haruna da Asabe wacce a lokacin take da shekaru goma sha uku a duniya.
Tofa sai rigima da tashin hankali na gidan Malam Haruna ya dawo kan Asabe suka hura mata wuta su da 'yayansu ta kurawa babu irin wacce basa yi mata suyi girki su hanata su sanya yaransu su jefeta suyi mata rashin kunya.
Malam Haruna bakin ciki da damuwar abunda iyalinsa suke wa Asabe ya sanya hawan jini ya kamashi babu wanda ya sani shi dai sai da yayi ciwonsa ya warke.....Cikin wannan hali Asabe ta haifi Abdullahi kamarsu daya da babbansa Malam yayi ta murna da farin ciki ya dauki son duniya ya dora kan yaron tofa wannan sai ya kara janyo tsana daga gurin iyalinsa duk sanda malam ya futa zaure su kuma sun samu damar azabtar da abdullahi Asabe da kyar ta cetonsa tana kuka tana nadamar rayuwar da takeyi a gidan sam basu da imani iyalin malam Haruna.
Abdullahi na da shekara biyu Asabe ta sake haihuwa da namiji aikuwa bakin ciki tamkar ya kashe su kan me Asabe zata zo tana haihuwa kuma duk maza ai wallahi baza su yarda ba,
Sai tashin hankalin ya koma kam mijin nasu wai dole sai ya saketa domin ba sa'ar auransa bace
Malam yace basu isa su sanya ya saki matarsa ba.
Su kuma sai suce shikkenan su zuba su gani dashi dasu suka cigaba da muzguna masa shi da Asabe da Abdullahi rayuwa tayi musu xafi sosai.
Akwar watarana da babban yaron malam mai suna Tanimu suka hada baki da mahaifiyarsa ya dauki abdullahi a boye ya fita dashi can bakin wata tsohowar rijiya ya nufa dashi rijiyar mugun zurfi ne da ita yana zuwa bai wani tunani komai ba ya jefa shi ciki ya bar gurun da sauri
Cikin ikon Allah Allah ya kawo wani magini da kurar ruwa da diro a kai da alams ruwa zai diba sai ya dinga jin kuka yana le'kawa ya hango yaro saman ruwa yana kuka.
Dake magini ne kuma har hakar rijiya yana yi kawai sai ya tattare wandonsa yayi shahada ya shiga rijiyar cikon ikon Allah ya fito dashi sa'be a kafadarsa Abdullahi na cikin kariyar ubangiji.
Take gurin ya dinke da jama'a kowa na fadin albarkacin bakinsa......Wani dattijo da ya kasance almajirin Malam Haruna ya kar'bi Abdullahi ya rike shine yaja su har kofar gidan malam din wanda shi kuma jin labarin abunda ya faru ya yanke jiki ya fadi ko ina nasa ya daina motsi sai dai ido kawai.
Tashin hankali sosai jama'ar unguwar suka shiga tare da tur da iyalin malam din domin kowa ya gane sune silar komai.
Asabe ta kar'bi yaronta tana kuka tayi masa wanka ta gyarashi ta nufu gidansu tana kuka mahaifiyar ta itace ta rarrasheta ta dawo dakinta da zama ta cigaba da kaf-kaf da yayanta.
Magani akewa malam al'marin na kara rikicewa a takaice dai malam Haruna sai da yayi shekaru uku a kwance yana jinya Allah ya dauki rayuwarsa....Wannan mutuwa Asabe akayi wa ita domin da aka share makoki korarta sukayi daga gidan ta koma gaban mahaifiyarta wacce ita kuma girma ya kamata hade da rashi lafiya wadatacciya haka ta nufu gurin maigari domin akwatar mata hakkinta maigari yaki sauraranta saboda dama tuntuni iyalin malam Haruna sun bashi cin hanci dama dashi aka raba gado sai ya koreta ta nufi gida tana kukan bakin ciki.
Asabe ke sirfau tayi dakai tayi kuli-kuli ta ciyar da kanta da mahaifiyarta da kuma yaranta.....Tsawon shekaru goma sha biyu Abdullahi ya girma sosai sai ya fara neman na kansa to tindaga lokacin ta soma samun hutu Abdullahi zaiyi wanki da guga zai zuba shara a kura zai tura kurarar ruwa kai duk dai abunda yasan zaiyi asirinsa ya rufu zaiyi ya kawo gida a ci
Lokaci kuma yayyunsa maza su sanya shi a gaba domin dai dukaninsu basu iya sana'a ba don gadon da suka raba tuni ya kare da kyar ake ci a gidan sai suka fara jifan Abdullahi wai dole shima sai ya lalace kamarsu.......Amma da yake Allah baya basu sa'a asirinsu baya kamashi.
Uwani mahaifiya ga Asabe Allah yayi mata rasuwa mace ma kishin kanta da kaunar iyalinta hakika Uwani ta taka muhimiyar rawa a rayuwar su shiyasa data mutu sukayi kuka sosai.
Abdullahi da dan uwansa Lado suka cigaba da neman kudi babu ganda da son jiki kafib kice kwabo sai aka fara kawo musu tallan 'yan mata ko suna so a garin abun burgewa ne ka aurawa yarka namiji manemi mai sana'a.........Abdullahi ya amince da zai auri wata yarinya domin ya yaba da tarbiyarta da kuma gidan da ta fito a take ya kai kudi aka sanya rana mahaifiyarsa tasa albarka sosai cikin lamarin.
Jin Abdullahi zaiyi aure ya zauna a gidan kansa yasa 'yan uwansa kowa ya fito da abunda yake boyewa domin su sabauta masa rayuwa kowa da irin asirin da yake masa saboda kawai tsabar kiyayya gami da kin gaskiya.
Ranar da aka daura aure aranar abdullahi yaji kwata-kwata baya sha'awar zama a cikin garin dare nayi bayan 'yan kai amarya sun watse ya rike hannunta kamar wanda ake ruruwa wuta a jiki suka nufi tasha ba tare da yasan ina zashi ba kawai suka shiga motar da ake lodi zuwa kano.....Wannan shine dalilin da ya kawo Abdullahi makaho garin kano da zama
*******
Tunda aka wayi gari aka ga babu Abdullahi cikin gari da matarsa sai hankalin mahaifiyarsa dana dan uwansa ya tashi sosai suka shiga nema dangin Rahamu amarya ma suka shiga tashin hankali gari ya dauka an nemi Abdullahi da amaryarsa an rasa a gari.
Labari ya samu su Tanimu dadi kamar su zuba ruwa a kasa su sha dama sunyi masa kurciya ne ya bar garin gabadaya kuma baza su daina jifansa ba har sai sunga ya daina motsi a duniya.
Har cikin garin kano sai da Asabe da Lado suka zo su gama bunkicen su basu labarin wanda ya ga su Abdullahi ba haka suka koma garinsu cikin damuwa da tashin hankali wannan shine mafarin kwanciyar asabe ta dinga ciwo aka rasa meke damunta ta rame ta lalace kullum cikin kuka da kiran sunan danta Abdullahi damuwa tayiwa Lado yawa shima sai ya koma kamar wani zautacce.....Bangaran su Tanimu farin ciki suke sosai da faruwan al'amarin sunyuwa Abdu kurciya sannan kuma lado ya samu ta'bi kwakwalwa burinsu ya cika.
Ranar Asabar Lado yaje gurin sana'ar sa ya dawo yana shiga gida ya tadda gawar mahaifiyarsa Asabe rai yayi halinsa.....Ya dinga fadin kalmar innalilhi wa'ina ilahi raji'un!
Jama'ar unguwa da 'yan uwanta suka sallaci gawar aka kaita gidanta na gaskiya sati biyu da rasuwarta Lado ya tattara koma ya bar garin shi kuma sai ya nufi jahar Bauchi ya cigaba da sana'oin sa.
***
To wannan al'amarin da ya faru yayiwa su Tanimu dadi kawai sai suka kira dilallai suka sanya su siyar gidan da Asabe ta gada daga gurin mahaifinta wanda gidan kuma ya kasance gadon su Abdullahi ne a maimakon maigari ya tsawatar harda shi a cikin masu kasafin kudin gidan 'Yan uwan Uwani da suka rage a unguwar sukayi shiru domin suna jin tsoro suyi magana maigari ya koresu daga garin....Haka Tanimu da maigari suka kasafta gudin gida kowanne ya tashi da kaso me tsoka.
****
To sai bayan haihuwar Safarau ne wannan ibitlain ya sauka a gidan Abdullahi ta dalilin wata guguwa da akayi lokacin damuna a lokacin kowa na kokarin 'buya saboda kar wani abu ya same shi domin wannan guguwa ta tawo da abubuwa da dama a wannan lokacin Rahamtu ta fito daga daki a gaggauce take kwashe kaya wai kada ruwan sama ya jika su sai kawai taji kamar kwaro ya fada mata ido tayi ta mutsika ido yana mata yaji da kyar ta lalubi dakinta ta shige ciki.
Shi kuwa Abdullahi yana kan hanya ya dawo daga nema guguwar ta fara a maimakon ya 'boya kamar yanda yaga mutane nayi sai kawai ya cigaba da tafiya yana sauri ya isa gida.....To shima irin abunda ya fada idon Asabe shine ya fada a idonsa sai kawo shi gida akayi baya gani.....Wannan shine mafarin makancewar iyayen Safarau wanda tun daga lokacin ta zama 'yar jagora.
*Wannan shine Tarihin iyayen Safara'u*
Washe gari Alhaji Lado da Yaransa Hanif da Mubarak suka shirya tsaf suka nufi unguwar kurawa gurin Malam Buba shine zai yi musu jagora fadar Sarkin kano domin su samu ganawa da Safarau wacce suka d'okantu da ganinta.
****
Sarki yaji mutukar farin ciki bayyanuwar Asalin Safarau matar dansa a take ya sanya aka kaisu masauki mai kyau ya shiga gida da kansa ya sanarwa da Fulani abunda ke faruwa yace ta kira Safarau ta sanar mata da abunda ke faruwa Fulani ta aika wata baiwa can sashen su safarau tace tazo tana nemanta yanzu.
Safarau ta nufi sashen fulani gabanta na faduwa tana adduar Allah yasa ba wata matsalar bace tana isa taga fuskar Fulani tamkar gonar audiga sai ta saki ranta suka gaisa Fulani tace"Albishir ne mai dadi shiyasa na hana kowa ya fada miki sai ni."
Safa tace"Mama wane irin albishir ne wannan ko aunty Aysha ta amince zata koma dakinta."!? Fulani tayi murmushi tace"Allah Sarki Safarau ki kwantar da hankalin ki insha Allahu aysha zata dawo dakinta."
Tace"Allah yasa Mamana."
Fulani na dauke da murmushi a fuskarta ta sanar da ita zuwan kawunta da 'yan uwanta Safarau ta mike tsaye jikinta na kyarma tace"Mama ashe dama zanga wannan rana? ashe nima ina da 'yab uwa? sai hawaye shaaa! ya shiga zubo mata a fuska wanda yayi dai-dai da shigowar Omar palon.
Da gudu taje ta rungume shi tana kuka tana fada masa Omar ya nemi karin bayani gurin Fulani ta tabbatar masa da hakane tace yanzu haka ma suna can dakin baki.
Omar da kansa ya rike hannun Safarau suka nufi can sasashen bakin........Safarau nayin tozali da Alhaji Lado sai ta yanke jiki ta fadi suma tayi sai da ta farfado sannan taje ta rungumeshi tana kuka takw fad'in"Kuna kama da babana nayi farin cikin zuwanka a wannan lokacin ina cikin kunci da tashin hankali na rashin dangin uwa da uba ashe nima ina da asali." Alhaji Lado ya dinga rarrashinta yana share hawaye da hankici yace"Nine zanyi farim ciki da kasancewa dake Safarau nayi farin ciki da Allah ya sanya dan uwana ya haife ki kafin Allah ya dauki ransa ina sonki sosai tun kafin na ganki Wad'annan sune 'yan uwanki." Ya nuna mata Mubarak da Hanif da suke cike da farin cikin gamuwa da 'yar uwarsu tace''Nima ina kaunarku kuma ina alfahari da kasancewa ta a cikinku."
Omar kam na tsaye yana kallansu tausayi suke bashi sosai ashe akwai ranar da zata zo safarau ta hadu da danginta.
Alhaji Lado ya daga kai ya kalli Omar yace"Ba zan boye maka ba Omar hakika naji dadi mutuka da ka kasance miji ga d'iyata Safarau nayi farin ciki sosai kuma bazan daina mika godiyata a gareku ba kai da mahaifinka ni nasan bani da abunda zan baku ko inyu muku in biya ku dashi sai dai addua kawai hakika mahaifinka mutum ne shi mai adalci da iya mulki ina yi maka fatan samun nasara a rayuwaka tare da kwaikwayon hali irin na mahaifinka.
Omar yace"Babu godiya a tsakanimu Alhaji duk abunda mukayi hakkin mu dole muyi hakika nima nayi farin ciki da bayyanuwar ka a matsayinka na mahaifin matata Ubangiji Allah ya tattabar mana da alkairi."
Sai ya mika masa hannu sukayi musabah ya mikawa Hanif da Mubarak sukayi sallama ya kama hanya ya fita ya bar ta tagana da 'yan uwanta
[6/13, 8:19 AM] Bintu Novel: 81
Alhaji Lado ya dinga bawa Safara'u labarin danginsu da mahaifin su Malam Haruna Mai dala'ilu mahaifiyarsu Asabe da irin wahalhalun da suka sha da yanda 'yab uwa suka tsangwa me su har sai da sukayi nasarar barinsu mahaifar su.
Safa kuka take sosai tana tausayawa musu gaskiya idan hakane sun sha wahalar rayuwa ba kamar babanta tunda shi Alhaji Lado yana zuwa garin bauchi Allah ya hadashi da wani attajirin mutum mai kaunarsa shine ya dorashi kan harkoki na kasuwanci har ya tsaya da kafafunsa yazo yayi kudi na ban mamaki 'karshe Alhaji Kabir din ya aura masa 'yarsa Tun daga lokacin wahalarsa ta yanke sai ya shiga neman d'an uwansa Abdu babu dare babu rana sai yanzu Allah yayi ikonsa ya samu labarinsa ashe ma baza su gana da juna ba tunda tuntuni Allah ya dauki ran abunsa.
Tace"Abbah ka gafarce ni a gaskiya wad'annan 'yan uwa naku basu da imani dasu da iyayensu sune sukayi sanadiyar mutuwar mahaifinku wanda naso in ganshi in rayu dashi, hakika wannan labari daka bani ya ta'ba min zuciya sosai ta yanda nake jin a yanzu bani da babban makiyi sama dasu Kawu Tanimu saboda duk sune suka zama silar faruwar komai."
Alhaji Lado yace."Ai tuntuni Sunyi nadama Safara'u suma kullum cikin neman inda zasu ga Abdu sukeyi kuma duk wata ina zuwa can garin namu muna gaisawa dasu karki damu komai ya wuce insha Allahu kema zan kaiki garin ki gaisa dasu zasuyi farin cikin ganinki a madadin d'an uwansu.
Safara'u ta goge hawaye a nutse tace"Shikkenan Abbana dukanin abunda kace haka za'ayi Allah ya kara tsarkake mana zuciyarmu.
Wayarsa tayi kara alamun kira Mubarak ya mika masa tare da fadin "Mama ce."
Alhaji Lado ya kar'bi wayar fuskarsa da yalwatacciyar fara'a ya amsa sallamar tace"Alhaji ina fatan dai wahala ta yanke."?
Yace."Alhamdullahi Hajiya Yau Allah ya yanke min wahala....Sai ya shiga warware mata abunda ke da akwai.
"Innalilihahi wa'ina ilaihi raji'un!" Allah yajikansa ya gafarta masa." Hajiya Abida ce ke wannan maganar cikin alhini tace"Bani mu gaisa da 'Yar tawa."
Alhaji Lado ya mikawa Safara'u wayar ta kar'ba a nutse suka fara gaisawa da Hjy Abida cikin nutsuwa Safarau taji matar ta kwanta mata a cikin zuciyarta kamar yanda itama Hjy Abida take jin kaunar safaraun cikin zuciyarta sai kawai suka zage suna hira tamkar wanda suka shekara da sanin juna.
Alhaji Lado ya dinga murmushi yana jin dadi yasan halin matarsa da kirki kamar mahaifinta ko shakka bayayi zata rike masa Safarau da amana.
Kayan abinci cima iri-iri bayi suka dinga shigowa dashi suka jere musu tsaf Safa tace"Abba ya kamata kuci abinci ku huta ko."
Mubarak Sarki barkwanci yace."Wane abinci kuma ai mu murnar ganinki ta kosar damu bama jin yunwa."
Dariya tayi tace"A'a idan kai a koshe kake shi Hanif din fa." Hanif yace."Rabu dashi Sistar shima sharri ne kawai yanzu bari ki gani sai yafi kowa cin abincin.
Tana 'yar dariya take zuba musu abincin sai bayan ta hada komai sannan tace"Abbah zan shiga cikin gida kafin ku kammala cin abincin sai na dawo ka cigaba da bani labarin d'an tsoho."
Alhaji Lado yayi murmushi yace."Safarau Allah yayi miki albarka ya rabaki da cikin jikin ki lafiya."
Cike da kunya ta amsa ta fita daga palon cikin nutsuwa su kuma suka sauko tare da zama kan dadduma domin cin abincin.
****
Kwanakin su Alhaji Lado Hud'u a masarautar kano suka gane lallai masarautar ta bambanta da sauran masarautu saboda karamcinta da yanda ake gudanar da mulki cikin tsari da adalci domin kullum a fada suke zama suna kallon yanda take tafiya sai dare suke shiga masaukinsu.......Da safe kafin su fita Safarau zata shiga su gaisa da juna suyi hira yan uwa a gaskiya sunga karamci da yanda ake tattalin ba'ko a masarautar sunga abubuwan tarihi sosai domin Omar da kansa ya dinga zagawa dasu kofofi da tsofaffin dakuna da suke da abubuwan tarihi a ciki suka dinga yin hotuna a gurin domin tarihi.......Tsaf suka shirya tafiya Safarau ta tubere wai sai sun kara kwana uku sun cike sati guda Alhaji Lado da baya son fushin Safarau sai ya amince suka cike kwana ukun ana ya gobe zasu tafi Safarau tana manne dasu taki sauraron Omar wanda