Advertisements
Chapter 21 Reading Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar

Author :  Binta Umar Category :  Complete Novels

Chapter   21 / 29

60K to 63K   out of 86.8K words

da ita!! Can gefen hanya ta gangara jikinta jina jina da jini kafafunta sun karye 'baras sunyi wani daga-daga tamkar ba jikin mutum suke ba....Ita kuwa dama tuni ta suma.....Wasu mutane dake gefan titi masu siyar da fetur dake sunga daga inda ta fito da gudu daya ya tsallaka titin ya nufi cikun hotel din kafin ya karasa sun buga karo da Omar a rikice yace."Yallabai wata yarinya yanzu ta fito daga nan gata can mota ta take ta."

Ba tare da ya tsaya sauraransa ba ya nufi cab tsallaken titin inda ya hango cincirindon mutane tabbas itace abunda zuciyarsa take ta ayyana masa kenan aikuwa yana zuwa ya ganta kwance tamkar matacciya ga kafafu a kwankwatse! sau kawai ya kama kukan zuci ido jawur yake kallon Azima wannan wace iriyar kaddara ce ta afko masa innalilhi wa ina ilahi raji'un! Ai kafin kice kwabo tuno police sun iso gurin nan ka samu aka tattara Azima aka wuce da ita babban asibiti domin dai al'amarin nata yayi masifar tsananta......Omar bai bisu asibitin ba domin nunawa ma yayi bashi da wata ala'ka da Azimar yana kallo jama'a sukayi dafifi suka bi bayan police din, shi kuma ya koma cikin hotel din hankali a tashe.



Omar ya sanya aka bashi numbar wayar mamalakin hotel din ya kirashi yace."Babban case ne a faru a hotel dinsa yazo yanzu......Aikuwa mintina ashirin ne ya kawo mutumin inyamuri ne dan kimanin shekaru ar'bain da biyar zuwa hamsin kana ganinsa zaka gane mugun cristar ne saboda yanayin shigarsa.....Wani guri suka zauna Omar ya fada masa abunda ke faruwa! Wani irin gumi ya shiga ketowa mutumin ba tun yau ba mutane suke kawo masa magana kan Emeka suna fad'in Ya sanya ido sosai a kansa lalatacce ne yana bin mata karuwai harda ma matan aure tabbas yau ya gazgata maganar domin ya san Omar ba zaiyi masa karya ba tare suka nufi room din Omar din Nan Baba Tinde yaga Emeka kwance yana wani irin nishi na wahala....Ko da ya d'ago kansa yaga shugabansu Baba Tinde sai ya fara kuka murya na rawa yace."Sorry sir tsautsayi ne sir......! please ban nemeta ba itace ta neme ni sir......Wani wawan duka Baba Tinde ya kir'ba masa a baki sai ga bakin ya karkace yana zubar da jini!!! Ya dinga zaginsa yana cin mutuncinsa tare da fad'in "Bai isa ya tozarta shi ba ko kuma ya 'bata masa suna ya 'bata masa sana'arsa ba sai ya d'auki tsautsaran mataki a kansa.......Emeka ya dinga wani irin marayan kuka yana tausayawa kansa...Omar kam kama hanya yayi ya fice daga dakin can 'kasa ya sauka ya fara neman numbar Sulaiman ya shaida masa abunda ke faruwa....Hankali a tashe Sulaiman da Akande suka nufi hotel din, sai da suka tausayawa Omar ganin yanda duk ya zabge lokaci kankani nan suka zauna suna rarrashinsa da bashi baki suna nuna masa ko wane mutum akwai irin kaddararsa ya dauki al'amarin a matsayin 'kaddara wacce ta riga fata....Omar dai jinsu kawai yake sai tsane gumi yake yana tunano irin artabun da suka buga da Aysha kan auran Azima ashe aysha tasan babu alkairi shiyasa tace bata so shi kuma son zuciyarsa ya rinjaye shi gashi Azima ta shigo cikin famly dinsu mai tsabta gami da kyakykyawar nasaba zata 'bata tabbas a auran Azima da yayi tsawon sati uku babu abunda zai d'orar na farin ciki sai dai bakin ciki!!! Tuntuni ya kudirta a cikin ransa ya saketa saki biyu amma ba zai furta mata yanzu ba sai taji sauki tukkuna. Kukan zuciya ya cigaba dayi yana kuma nanata kalmar Innalilihi wa'ina ilahi raji'un!


Sunan Zaune Baba Tinde ya sauko yana goge gumin fuskarsa securities din dake gurib ya kira suka nufi dakin da Emeka yake.


Dauko shi sukayi kamar wani gawa suka sashi a mota ko ina zasu kaishi oho!

Baba Tinde yazo ya tsaya gurin su cikin turanci yake baiwa Omar hakuri yana fadin"Wai Ya fadi duk irin hukuncin da yake so ayiwa Emeka tunda ya shiga huruminsa Omar yace."Kawai ya kyaleshi dai ya barshi da Allah yasan kafin ya koma gareshi zai saka masa


Ranar suka sanja hotel domin Omar ji yayi sam ba zai iya sake zama a cikinsa ba.


To sai da Azima tayi kwana uku a sibiti sannan Sulaiman ya taushi zuciyar Omar sukaje dubata halin da take ciki yayi masifar girgiza su tabbas wannan duniya abar tsori ce shiyasa duk rintsi duk wahala mutum ya kiyaye sa'bawa dokokin ubangiji Azima ta aikata munanan laifuka na farko *Mad'ogo Zina da auran wani a kanta Shirka* ma'ana had'a Allah da waninsa sannan ta amince da maganar dan tsubbu ta daina yin sallahr asubahi sallah mai muhimanci da tarin lada abu na karshe data aikata shine cin amana ga 'kawarta data yarda da ita ta bata dukanin sirin ta Ubangiji yayi mata kwaf d'aya yanzu ya rage ya nata kuma Allah yasa abunda ya faru da ita ya zama izina ga dukanin masu irin halinta.


Duk yanda Omar ke 'kinta sai da ya tausaya mata don dukanin kafafunta a yanke su ga wasu irin d'inki a fuskarta duk tayi dameji don idonta guda daya ma baya budewa sosai sai wani irin ruwa yakeji da kyar take numfashi kallo guda yayi mata ya kama hanya ya futa daga dakin har su Sulaiman din suka fito kana su wuce gurin aikinsu suna jajanta al'amarin



To a tsakankanin kwanakin ne kuma fargaba da damuwa suka dabaibayi aysha haka kawai sai taji gabanta ya yanke ya fadi musamman idan ta tuno da Omar din sai gabanta ya tsanata faduwa Gashi dan kiran ma da yake musu a waya ya kwana biyu bai ba sai taji duk ta damu tana so taga yana kiran wayarta tana wulakanta shi abun nayi mata dadi.....Yau dai ta kudurta a ranta in Safa ta shigo zata bugi cikinta ko ita yana kiranta.

To Safa na shigowa ko zaman minti biyar batayi ba cikin dubara Aysha tace"Safa mijinki yayi zuciya ne kwana biyu baya kiran waya ko kinyi masa laifi ne."!?

Safa dake cikin damuwa ta laulayi tace"Wallahi aunty ni har mantawa ma nake dashi nifa laulayin nan ya sani a gaba aunty wayar ma sai ta kwana ta yini a kashe hummm! aunty kowa ka gani da d'ansa ka kalleshi ashe haka kuke shan wahala"!?


Aysha tasa dariya tana fad'in"Wato da ke kin dauka al'amarin na da sauki ko? sai ma kinzo haihuwa tukkuna."! Cikin sigar tsokana ta fadi maganar Safa tace"Don Allah aunty daina fad'ar min da gaba."!


Aysha dariya kawai take mata itama na taya ta dariyar.....Tace"Kin same za'ayi yanzu."? Girgiza kanta tayi tace"Ki dauko wayarki sai ki kirashi ko kiyi maaa test nasan i dan ya gani zai kira watakila zuciya yayi mana kwana biyu."

"Allah aunty da kin kyaleshi wallahi ni bana son damuwa yanzu kin san halinsa da ba'ka'ken maganganu yanzu zai 'bata mana rai kan jakar matarsa."


Aysha tace"Ke baki da wayo dallah kije ki dauko wayarki ai ba laifi bane don kin tura masa tes ko kinyi masa plashing idan ba kyaso ya san kin damu dashi zan kare ki."

Safa ta mike ta fita tana fadin "Autyna kenan.""""


Aysha nan zaune ta shigo da wayar tace"Kawai kiyi masa flashing yafi 'kona rai nasan zaiji haushi ya kira wayar.....Aikuwa sai Safa tayi masa flshig har sau biyu ta aje wayar suka zauna jiran tsammani.



Kusan mintina arba'in babu amsa sai duk jikinsu yayi sanyi Aysha tace"Babu shakka yayi fushi da yawa ki sake yi masa wani." Safa ta sake masa nan ma bai kira ba. takaici duk ya ishesu Safa tace"Dama na fada miki aunty yaushe zai kula da wani flashing yana tare da wannan banzar jakkar maciyar amana kawai ki kyaleshi aunty."


Aysha tace"Yo ni dama meye ya dame dashi kawai saboda ke yasa nace kiyi masa wannan dubarar tinda ya gani yaki biyowa shikkenan sai a rabu dashi."


Omar kam aiki ne yayi musu tsanani shiyasa sam bai mai da hankali ba koda ya duba yaga safa ki masa flashing sai ya aje wayar kawai ya cigaba da aikinsa yana so ya samu sarari sai ya kirata a nutse.


Sai bayan sallahar la'asar sannan ya kira wayar Aysha tace"Safa maza zi ki dauka." Hands free ta bude wayar tayi sallama ya amsa cikin wani yanayi da kasalalliyar murya duk wannan karsashin da karfin sautin muryarsa babu shi.


To su kansu sai da sukayi mamaki wannan wane irin yanayi ne ko dai bashi da lafiya ne? Yace."Safa sai yau kika tuna dani ko? a maimakon ki kira waya sai ki dinga flashing meye amfanin haka."!? Tace"Kayi hakuri ban san ma nayi ba."! "okey ya kuke ya jikin naki? Mama tace kina ta fama da zazza'bi ko."!? tace." Eh." yace."Ina tafan kina shan magani."! Eh naji sauki ma."! Yace."Tom Alhamdullhi." Shuru sukayi Aysha tayi sakare tana jin yanayin maganarsa tamkar ta wani majiyanci Anya kuwa!

Yace."Safa ina 'Yan biyu na ina fatan suna lafiya ina Abdul kina kulawa dasu ko."!? Tace"Eh sunan kalau sunyi wayo Abdul kuma kullum sai yayi rigima yana kiran dady dady!."!


Sai yasa dariya yace."Kice masa dady nan tafe insha Allahu." Tace"Aifa kamar kun 'kara kwanaki kan kwanakin da ka fad'a zakuyi." Yace."Eh wata 'yar matsala ce ta Same ni Safa kiyi min addua." ! Sai kawai taji idanunta na kawo ruwa! ta kalli Aysa da kanta yake a sunkuye bakin ciki duk ya isheta wato ita da bai damu da ita ba ba zai tambaye ta ba lallai Omar!

Tace"Yayana wace irin matsala ce nifa nace naji muryarka wani iri."! "Karki damu Safa ba wata matsala bace mai tsauri tuntuni ma na magance ta okey zan kashe wayar yanzu ina aiki zan kiraki idan anjima." Kashe wayar yayi.....Safa tayi sak! tana kallon Aysha tace"Aunty Aysha anya Yayana yana da lafiya kuwa."!? Ajiyar zuciya ta sauke tace"Nima naji yanayinsa Safa Allah ya sawa'ke mai."

Safarau ta amsa da "ameen" suka cigaba da hira sama-sama Aysha na danne abunda ke damunta a cikin zuciyarta.
[6/10, 9:32 AM] Bintu Novel: 77


To haka dama rayuwa ta gada yau da dadi gobe babu rayuwar da Omar keyi a yanzu sam baya jin dadinta yayi mutukar nadamar auran Azima a rayuwarsa yanzu tunanisa ya zaiyi gurun fadawa iyayensa abunda ya faru mussaman maihaifiyarsa fulani da babu yanda batayi dashi ba kan ya janye maganar auran Azima ya'ki yanzu wani irin kunyar Baba galadima yake ji saboda farkon al'amarin ya zaunar dashi ya fada masa wacece Azima duk iya bukicen da sukayi a kanta babu shaidar arziki amma duk ya biyewa son zuciyarsa ya watsawa masoyansa kasa a ido..duk sanda ya tuno da lokacin da galadima ya umarce shi ya saki aysha sai yaji wani irin bakin ciki da takaici na kama shi yana tunanin garin ya akayi har haka ta faru babu shakka ya cika butulu da ya iya sakin aysha a gabansa.....Yayi nadama sosai kullum cikun kukan zucci yake da neman yafiyar ubangiji tabbas yanzu ya fahimci cewar baya cikin hayyacinsa a lokacin da ya auri Azima kuma tabbas yasan bai kyauta mata ba.


Kusan kullum da daddare suna tare da safarau ya waya hakan sai yake debe masa kewa ko da wasa bai ta'ba tambayarta ina aysha ba zasuyi hira dashi sosai yayi ta tambayarta yaransa wani lokacin ma yace ta bawa Abdul wayar yayi tai masa gwalatu yana dariya.....To 'bangaran Aysha duk sanda Safarau zata fad'a mata sunyi waya da Omar sai hankakinta ya tashi tayi ta tsammanin ko zai kirata a waya sai taji shiru lokaci 'kan'kani ta shiga damuwa wato dama duk abunda yake fad'a akanta 'karya yake to in dai hakane itama zata kama kanta sai ta fara adduar Allah ya cire mata sonshi da take ji cikin zuciyarta.


****

Yau Satin Azima biyu a asibiti alhamdullhi ta dan samu lafiya tunda tana gane mutane duk sanda ta kalli kafafunta sai ta fashe da wani razannan kuka tana nadamar abunda ta aikata, duk sanda Omar yazo asibitin ta dinga kuka kenan tana bashi hakuri da kanta ta fad'a masa aikin da tayi a kansa har ya aureta tana kuka tana komai take neman gafararsa.....Shi dai sai dai kawai ya kalleta baya iya cewa komai sai dai tu'ajibi da mamakin al'amarinta.


***
Alhamdullahi Company yayi kyau duk wani abunda suke bukata su gabatar a company sunyi shi tare da jagorancin Jarumi kan Komai wato sadauki duk da yana cikin tsananin damuwa da tashin hankali sam bai bari al'amarin ya shafi aikinsa ba Omar za'kwa'kuri ne kan komai....Company ya fara fitar da na'uin kayan abinci iri iri kayan masarufi masu kyau da inganci abun dai sai dai muce Allah ya inganta ya kuma sanya alkairi.........


****
Kwana biyu kacal suka 'kara yi bayan kammaluwar aikin nasu suka nufo gida, ko wannen su na murna da farin cikin ganin iyalinsa.


Dawowarshi tayi musu bazata mutu'ka.....Tun sanda labari ya riski Aysha sai gabanta ya tsananta fad'uwa sai ta fara tunanin irin artabun da zasu sha dashi....Safarau ta shigo cikin kyakykyawar shiga tayi wani masifar kyau! da kwarjini ta kara cikowa yayin da fatar jikinta ta sake gogewa sai sheki takeyi kana ganin ta kasan me yaron ciki ce tana cikin wani leshi brown wanda kudinsa ya tasamma dubu hamsin tayi ado da glod kirar dubai ta shigo dakin Aysha tana ya mutse fuska.

Koda Aysha taga uwar kwalliyar da taci sai taji wani abu ya dan soki zuciyarta da sauri ta kawar da abun ta saki fuska sosai tace"Eyee Wato kinji ya dawo har kinje kinyi wanka kin tsantsara kwalliya da kullum kina lafke ke baki da lafiya waye-waye!

"Allah aunt ba'a son raina ba nima mama ce ta matsa min tana jin labarin dawowarsa tace maza inyi kwalliya babu dadi yazo ya same ni kaca-kaca shine fa na shirya amma da dan ta nice sai dai ya same ni a haka."

Aysha tace"Hakan da kikayi shine dai-dai yana da kyau kema ki bashi mamaki."! Safa tayi shiru tana wani tunani tace"Aunty a cire fa maganar wasa cikin wannan maganar tawa Allah aunty mutukar ba zaki koma dakin ki ba to nima na bar auranshi don gaskiya ba zan iya zama da shaid'aniyar matar nan ba."

Kallonta tayi kawai tana mamaki tace"Aikuwa zakiyi kaffara Safarau zaki koma dakin mijin ki Azima kuma ina ruwanki da ita ba fa a gida daya zaku zauna ba."

"Eh duk da haka dai aunty aysha ba zan zauna a gidan ba mutukar babu ke." Aysha tace"Safarau kenan aini kuma na gama yayina na gama idan kuma kina so dole sai kin zauna da wata to zance ya sake wani auran." Safa bata san sanda ta harareta ba tana zumbura baki aysha dai dariya kawai takeyi.


Kimanin awarsa daya a cikin fada tare da iyayensa maza yana zayyane musu abunda ya faru tsakaninsa da Azima Omar bai rage musu komai ba dangane da al'amarin to dukaninsu babu wanda bai shiga rud'ani ba da jin abunda ya faru....Baba galadima yace."Yanzu ina ka baro Yarinyar."? Yace."Tana can asibiti nace a cigaba da kulawa da ita har lokacin da zata samu lafiya in yaso sai a daukota."


Galadima yace."Hakan shine dai-dai amma tilas iyayanta da 'yan uwanta su san abunda ke faruwa kana kuma su san halin da yarsu take ciki." Waziri yace."Wannan shine magana."

Maimartaba kam shiru yayi yana jajanta al'amarin addua kawai yayi cikin zuciyarsa da Allah ya tseratar masa da yaron sa.


To ko da ya fito daga fada kai tsaye sashen su ya nufa wasu bayi na biye dashi a baya suna rike da wayoyinsa da kuma karamar jakkarsa to da yake kullum sai bayi sun shiga sun gyara shiyasa ko ina tsaf ya bude dakinsa a nutse yana shiga ya zube wayoyinsa da karamar jakarsa ya xauna gefen bed tare da rintse idanunsa hannunsa yasa ya rufe fuskarsa ruf yana tunanin abubuwan da suka faru......Ya jima zaune kafin ya mike cikin sanyi jiki yayi wanka ya fito ya shirya jikinsa cikin wani Pakistan irin na maza wani rufaffan takalmi yasa kana ya nufi sasashen mahaifiyarsa domin su gaisa.


Sosai Fulani ta tar'be shi kana ganinta kasan tana cikin annushuwa da farin ciki yaronta ya dawo cikin aminci Omar ya dinga mamakin yanda Abdul ya girma yayi wayo sosai tamkar wanda yayi shekara bai ganshi ba haka ya daukeshi ya rungume a jikinsa wanda da kyar ya samu yaci kayan abincin dake gabansa hankalinsa ya dauke kan wasa da Abdul wanda dama sun saba kafin tafiyarsa shiyasa suka masifar shakuwa da dan nasa.

Da kyar ya samu yaci Abincin Abdul na taya shi duk yayi faca-faca da gurin ya zubar da lemo da sauransu Fulani ta kira wata baiwa dake aike aike a sashen tace"Ta dauke Abdul din taje ta gyara masa jiki aikuwa yaron sai yasa rigima wai bai yarda ba da kyar ta fita dashi yana kuka da kiran dady.......Sai da aka gyara gurin sannan ya nutsu ya samu damar sanar da ita al'amarin da ya faru sosai fulani tayi mamaki ita kanta sai da tayi nadama bai omar din ba tace"Kaga abunda akaita guje maka kenan amma dake Allah ya kaddara maka wannan kaddarar sai da haka ta faru naji dadi da auranku da yarinyar baiyi tsayi ba ballanta a samu zuria saboda haka yanzu abunda nake so da kai shine kaje ka sasanta tsakaninka da Aysha ta amince ta koma dakinta wannan kawai zakayi min ka burgeni."


Ya sauke ajiyar zuciya mai zafi yace."Mama tun ranar dana furta kalmar saki kan Aysha na janye na kudurta a raina kan cewar na mayar da ita itama Ayshar tasan da wannan saboda haka yanzu dakinta kawai zata koma."


Fulani tace"To Alhamdullahi ai duk mu yanzu mu dauka ai sai bayan ta haihu kayi wannan furucin shiyasa jikinmu duk yayi sanyi muna jiran dawowarka to tunda abun hakane ni da kaina zan iske Mahaifitar yarinyar in shaida mata abinda ke da akwai sannan ina fatan ka shaidawa iyayenka maza yanda abun yake."

Yace."Sai zuwa dari zan shiga sashen Baba galadima zan sanar dashi a nutse nasan mutum ne mai fahimta kuma a gabansa komai ya faru sai ince ma shine silar afkuwar lamarin.


Tace"To babu laifi Ubangiji Allah ya had'a kan iyalinka ya kuma dai-dai ta zaman su." Ya amsa da "ameen." Gaskiya duk wanda ya rasa uwa dole yayi kuka.

Cikin hirar ne take shaida masa cewar Safarau ciki gareta na kusan wata uku....Aikuwa ya dinga washe baki

21 / 29