Author : Binta Umar Category : Complete Novels
har ta katse wani kiran ya kara shigowa dui da ya fahimce ayshan ce bai yi yunkurin dauka ba saboda tunaninsa na bashi ba abin arziki zata fada masa ba.
Da tagaji da kiran wayar bai dauka ba sai ta jefar da ita ta kwanata tana kuka da neman mafita.
Sai bayan ya kammala abunda yake yi ne ya dauki wayar a nutse ya fara kiranta.
Tana ganin kiran ta dauka sosai yayi mamaki yau shine ya kira aysha sau daya ta dauka lallai akwai damuwa.
Shashshekar kukanta yaji ta cika masa kunne Innalilhi ya fara kira a zuciyarsa kafin yayi gyaran murya a bankali yace."Aysha menene wai kin kirani kina kuka ki fada min abunda ke faruwa waye babu lafiya ko mutuwa akayi ne ni ina gurin aiki."
"Burinka ya cika."!! Tafadi maganar a sha'ke! ta cigaba da cewa " Burinka ya cika kayi min ciki sai kazo ka san yanda zakayi da abunka kafin in tona maka asiri a idon duniya."
Zamansa ya gyara sosai babu alamun wata damuwa ko fargaba a tare dashi yace."Aysha babu wanda ya isa ya tona min asiri sai Allahn da ya hallice ni bani da wata damuwa akan cikin da kika samu dama burina kenen kamar yanda kika fada saboda haka yanzu ya rage naki ki koma d'akin ki ko kuma ki zauna a gida ni dai ki kula min da abuna ina sonshi.'"
."Wallahi baka isa ba sai an zubar da cikin nan tunda ba d'an sinna bane." Tafada tana shashsheka!
Kamar zaiyi kuka dan 'bakin ciki yace."Aysha d'an nawa kike aibatawa kina kira da ba dan sinna ba? Wallahi tallahi mutukar wani abu ya samu cikin nan sai na daureki."!
Sai kawai ya kashe wayar ya jefar da ita sai wani irin huci yake saboda tsabar bacin rai.....Sai da ya dan samu nutsuwa sannan ya mike da niyyar zuwa gidan ayi abunda za'ayi shi ya gaji da wannan al'amari yana son cikinsa sam ba zai lamunci wani mutum yayi sanadinsa ba.
Nanne kam da tagaji da zancan zucci kawai sai ta nufi sashen Fulani domin tana ganin wannan al'amari ba abu ne da ya kamata tayi shiru ba abune da ya kamata kowa da kowa ya sani domin ayiwa tufkar hanci.
Fulani tayi ta jajanta al'amarin tana mamakin ya akayi haka ta faru babu shakka Omar kunya tayi masa 'karanci to wai shin wannan cikin da wane irin suna zasu kira shi ne?
Haka suka gama jimamin su sannan nanne tayi mata sallama ta koma gurinta da tunanun neman mafita.
Aikuwa kafin dare Aysha ta galabaita domin yini tayi tana amai ga zazza'bi mai zafi Omar din da kansa ya sanya aka 'kara mata ruwa yana tsaye a kanta ko kunyar iyayen nasa baya ji wanda suke masa wani irin kallo na mamaki........Sai bayan sallahar isha'i ne Maimartaba ya kira taro kamar yanda suka saba idan wani abu ya faru to dukaninsu sun hallara a dakin taron kowa na sa'ke-sa'ke da tunanin wane irin hukunci maimartaba zai yanke kan Omar din.amma gaskiyar magana abunda Omar din ya aikata ba karamin abu bane tunda har yanzu a cikinsu babu wanda ya tabbatar da cewar ayshan na amatsayin matarsa kamar yanda shi yake fada cewa har yanzu matarsa ce.
A nutse ya kalli Omar din ya ma rasa wane irin hukunci zai yanke kansa kwata kwata bashi da kwanji da kwarin gwiwar da zai yanke hukunci hakika Omar bai ta'ba bata masa rai irin yau ba.
Dakin taro yayi tsit! kowa na jiran yaji ta bakin Sarki amma yayi shiru kawai ya zubawa Omar ido.....Yana kallonsa.
Safarau da Ikilima ne suka shigo dakin a nutse suka gaishe da kowa kana suka nemi guri suka zauna suma kansu a kasa.
Kimanin mintina goma da shigowarsu har yanzu babu wani cigaba domin wanda ake jira yayi maganar ya'kiyi ba don ya rasa abin cewa ba Sarki ya saba wakilatar kowa ce shari'a ce ya magance ta kuma ya bawa mai gaskiya gaskiyarsa kana ya bawa mara gaskiya gaskiyar sa amma abin mamaki da daure kai wannan sharia ta Omar da aysha ya rasa inda zai yi da ita.
Safarau ta dago kai a nutse tace"Allah ya baka yawan nasara ina da magana idan banyi katsalandan ba."
Baba Waziri yace."Kina da damar fad'in abunda ke tafe dake Safara'u."
Ta gyara Zama sosai tace"Yau da safe ina zaune a palo wannan baiwa Mai suna Ikilima ta shigo ta same ni." Ta nuna Ikilima da hannunta dukaninsu hankalinsu ya koma kanta mussaman Omar duk ya kosa yaji abunda ke faruwa.
Safarau ta cigaba da cewa "Ikilima ta tabbatar min da cewar taji lokacin da Omar ya furta kalmar ya mai da aysha dakinta a dai-dai lokacin da take kokarin fitowa daga kicin bayan ta gama aikace aikacenta Ikilima ta tabbatar min da cewa Wallahi taji da kunnanta sanda Omar ke fadi " Aysha na mai dake dakinki kaddara ce ta sa na sake ki amma na mai dake....Ikilima tace ko za'a bata al'kur'ani ta dafa zata fad'i wannan maganar tunda Allah yasa taji da kunnenta shine ni kuma nace to dole zan shigo muku da ita gabanku ta rantse kamar yanda ta rantse a gurina kuma ta tabbatar muku da abunda na fada muku a yanzu.
Baba Galadima ya kalli Ikilma dake zaune kai a kasa yace."Yarinya nan ba gurin wasa bane muna so ki shaida mana kuma ki tabbatar ma da gaskiyar abunda kikaji ko kika gani domin muna so mu kawo karshen wannan matsalar ne."
Ikilima tace"Na rantse da wanda rai na yake a hannunsa ranka shi dad'e naji lokacin da Sadauki ya furta wannan kalmar wallahi banyi karya ba ranka ya dade Auny Gimbiya har yanzu matar Sadauki ce saboda ni shaida ce kan haka ina so yanzu in daura alwala sai abani al'kur'ani nayi rantsuwa a kan wannan maganar na yarda idan karya nake ubangiji ya tarwatsa ni."!
Dakin taro yayi shuru na Minti biyu kafin maimartaba yace."Alhamdullahi!" sai yayi shiru na minti biyu kafin ya cigaba da cewa"Yarinya baza mu karyataki ba saboda irin rantsuwar da kikayi damu da dake mun san cewa Allah da Annabi ba abun wasa bane kuma alamun sun nuna maganar da kika fada gaskiya ce dama irin wannan shaidar muke bukata mu gani! saboda haka ba sai Kinyi rantsuwa da al'kurani ba tabbas dukaninmu nan mun amince da maganar da kika fada Allah yayi miki albarka." Suka amsa da ameeen." Maimartaba ya bawa Ikilima Umarin tafiya.
Omar sai wani sinne kai yakeyi yana farin ciki babu shakka addua takobin mumini ce shi kam wane irin so Safarau take masa wane irin tukwici zai bawa Wannan yarinya Ikilima ashe dama ko wane mutum akwai ranar sa, insha Allahu daga yau zai cigaba da karrama mutane komai 'kaskancinsu gashi Baiwar gidansu tayi masa rana.
Sarki ya kalleshi da fuska a hade yace."Omar Allah yaso ka wannan yarinya ta tabbatar mana da gaskiyar lamari amma da ba haka ba sai ka fuskanci fushina domin wannan abu daka aikata yayi tsanani da yawa to alhamdullahi baka "bata min zuria ba yarinya ta tabbatar min da cewar itace shaidarka akan aysha saboda haka na baka kwana biyu kacal ka tattara iyalinka ku bar wannan gida sannan ina mai kara gargadinka kan ka kiyaye ba dokar masarautar nan bace saki ka rike matanka da mutunci kana kayi adalci a tsakaninsu karka kuskura wata tayi kuka da kai ko ta kawo 'korafi a kanka ka kula da kyau da iyalinka kaine babba kaine muke sanya ran zaka gaji mulki shiyasa muke so ka zama nagartaccen namiji mai tsayayyayir zuciya wannan itace nasiha ta a gareka."
Sai dakin taron ya har'ke da magana kowa na tofa albakacin bakinsa kan lamarin Shi dai Omar farin cikin da yake ciki ma ya hanashi magana sai kallonsu yake yi suna masa fad'a da gargadi shi kansa baba galadiman da ya sanya yayi sakin Fada yake masa gaba kar ya kara aikata abu makamancin wannan.
*****
Aysha na can kwance bata san wainar da ake toyawa ba......Safarau ta shigo dakin cikin farin ciki da walwala bakin bed din ta nufa ta zauna sosai tare da riko hannun ayshan tace"Aunty Aysha Alhamdullahi Allah ya cika mana burinmu Allah ya kawo karshen wannan matsala."
Aysha ta ya mutsa fuska ba tace komai ba saboda rashin kwarin jiki.
Ya shigo dakin hannunsa goye a bayansa yana wata iriyar tafiya ta ta'kama da izzah! da nuni ni nake da nasara a kanki.
Idonsa 'Kur! a kanta ya karisa bakin bed din yaja tunga ya tsaya.
Aysha ta dauke kanta tana ji kamar ta mike ta zazzabaga masa mari sabida takaici.
Ya kalli Safarau yana mata magana da ido."
Ta riga ta gane abunda yake nufi sai tayi 'yar dariya tare da kallon aysha data rufe idonta tace"Auntyna ki bude idonki mijinki ya shigo."
Aikuwa ta bude idonta da sauri ta watsa mata wata harara.
Safarau ta rufe bakinta da tafin hannunta tana boye dariya.
Tace "Aunty wannan hararar fa sai idonki ya fad'o ai ni dai ayi hakuri dani aunty Aysha Duk abunda kikaga nayi miki kaunace ta sanya don Allah ki tausayawa mana ki dawo garemu muna bukatar ki aunt."!!!!
" Safara'u kin mai dani abokiyar ki."!? tafadi maganar a sanyaye.
Safarau tace"Aunty babu raini a tsakanina dake wallahi yau ina cike da farin ciki ne shiyasa Allah ya tabbatar mana da alkairi." Mi'kewa tayi tana d'an cije baki Omar ya rike mata hannu yana kallonta cike da kulawa yace."Babu wata matsala ko."!?
Dariya tayi duka dadashinta ya bayyana tace"Duk sanda na dade a zaune idan zan tashi sai naji ciwon baya cikin 'yan kwanakin nan abunda nake ta fama dashi kenan."
Yace."Allah yasa ki haihu ki huta Safa." Tace."ameeen Yayana." Hanyar fita ta nufa tace "Zan shiga sashen Mama idan ka fito sai ka same ni a can ko."!? Yace." Karki damu yanzu zan fito zan kaiki ma likita ya duba min ke yanzu." Tace"Ni lafiya ta fa kalau." Yace."A haka kike kalau motsi kadan ki cije baki.." Dariya tayi ta bude kofa ta fita.
Bayan futar Safarau daga dakin sai ya dawo da hankalinsa kan aysha dake kwance tana kallonsu, a nutse ya karisa gefan bed din ya zauna sai ta dauke kanta ya sanya hannu ya juyo da fuskarta suka kalli juna hawaye ya wanke mata fuska wannan bakin ciki dame yayi kama a dake ka a hanaka kuka Omar ya zame mata kaska Ya zatayi dole ta sauke duk wani abu da takeji dashi ta rungume shi tunda shine uban 'yayanta babban abunda ke bata haushi shine daga ya zungureta sai ta dauki ciki ko da yake wannan baiwa ce wacce ba ko wane mutum Allah yake bawa ba.
Kwanciya yayi gefanta jikinsa duk ya shika hakika farin ciki da walwalar aysha itace tashi idan ya rasa Aysha yana ganin duk wani jin dadi na duniya ya rasa shi da zasu hakura su rungumi juna su rungumi auransu da zaifi Hawayen fuskarta yake lashewa yana had'awa da le'banta yana tsotsa duk sun zama wani abun tausayi ita dashi.....Murya a sar'ke yace."Aysha kin amince zaki cigaba da zama dani a matsayina na mijinki uban 'yayanki."?
Kai kurum ta d'aga masa hawaye na sake zubo mata sai ya rungumeta 'kam!kam! yana fad'in"Ubangiji Allah yayi miki albarka Aysha Allah ya dai-dai ta tsakanina dake ya bamu zaman lafiya mai d'orewa Aysha Allah ya raya mana zuriarmu tafarkin addinin muslunci."
A hankali tace"Ameen Ya rabbi ina neman afuwa a gurinka a bisa abubuwan da duk nayi maka marasa kyau wanda na sani da wanda ban sani ba ka yafe min nima na yafe maka wanda kayi min."
Rungumeta yayi sosai yana shafa bayanta yace."Aysha waye yace miki kinyi min laifi ? duk abunda kikayi min ni ban dauke shi a matsayin wani abu ba aysha Kin isa kin kai matsayin da zaki iya yi min komai na jure ba tare dana kullace ki ba karfa ki manta ke 'yar uwata ce matata uwargina uwar 'yayana sannan first love d'ina duk wani abu da zaki min bana aje shi a raina balle ya dame ni saboda haka na yafe miki har zuciyata ina fatan zamu cigaba da zaman lafiya a tsakaninmu mu gina rayuwarmu data 'yayanmu.".
"insha Allahu baza ka sake samun wata matsala dani ba in Allah ya yarda na amince nima kaina mahad'in rayuwata."
Aysha tafada a lokacin da take shafa gadon bayansa.
"Alhamdullahi! Alhamdullhi! Alhamdullahi! Abunda yake ta fad'a kenan yana shafa gashin kanta da bayanta.
[6/13, 8:19 AM] Bintu Novel: 83
Laifin dad'i 'karewa Afuwa masoya book din sadauki nasan yau zaku sha jimami littafi ya kare da izinin Ubangiji ina rokon Allah yasa abunda na rubuta a wannan littafin ya zama silar abun alkairi kuskuran dake cikin littafin ina rokon ubangiji ya yafe min.
🔚🔚🔚🔚
Omar ya jima tare da aysha yana rarrashinta tare da sake jadadda mata cewar irin wannan al'amari da ya faru ba zai sake faruwa ba a tsakaninsu yayi mata alkawarin cewa insha Allahu ita dashi mutawa ce zata rabasu sannan yana godewa Allah da ya kawo karshen al'amarin ba tare da ran kowa ya 'baci ba ya tabbatar mata da cewar itace kwanciyar hankalinsa da nutsuwarsa saboda haka ita dashi duk rintsi su rike junansu a bisa amana....Duk wani kalami da ku kasan namiji na amfani dashi gurin rarrashin mace to a ranar Omar yayiwa aysha irinsa, Ta inda ita kuma jikinta yayi sanyi sosai ashe soyayyarta a cikin zuciyarsa har ta kai haka tabbas ya kamata ta rike mijinta hannu biyu ta mutunta abokiyar zamanta tayi al'kawarin zata bashi dukanin gudumawar da ta kamata a rayuwa, saboda ya cancanci komai a gurinta duba da irin kauna da so da yake nuna mata ta tabbatar da cewar Omar zai iya sadaukar da ransa a kanta sai ta dinga tunanin zamansu A unguwar Kadawa Yanda ya dinga yi mata bauta da wahala tana masa rashin kunya ta tuna lokacin da maciji ya kusa harbinta ya tseratar da ita.....Hawaye ya wanke mata fuskarta ta tsira masa kyawawan idanunta tana kallonsa wani irin kaunarsa na kara ratsa jikinta Rungumeshi tayi 'kam!'kam! tana shashshekar kuka Shi kuma duk ya rikice ya dinga rarrashinta da dad'an kalamai wanda ya tanade su domin ita kawai......Da kyar ya samu tayi shiru ya bata abinci da hannunsa tana ci suna hira tamkar wanda basu taba samun sa'bani da juna ba. maganinta ya bata tasha kafin yayi mata sallama ya nufi masaalaci kasancewar an fara kiran sallahar magariba.
****
To kamar yanda Maimartaba ya umarce shi hakane ta faru ranar Juma'a da asubah ya tare da matansa a sabon gidansa dake unguwar Sharad'a, Sai da gari ya waye sannan jama'a suka dinga zuwa suna sanya albarka a ciki Sarki da Waziri Da Galadima ma sunje sun ga gida tubarkallah sun sanya albarka a ciki kuma sunyi farin ciki daukakar da Yaronsu ya samu ta ko wanne fanni Omar ya zama abin kwatance a gurin jama'a hakika suna matukar alfahari dashi a rayuwarau.
Tare suka zo da Ikilima da Atika da yanzu ta shiga taitayinta tunda ta riga ta gane bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane Omar yafi karfinta ta ko wane fanni sai ta kaskantar da kanta ta zama 'yar d'akin Safara'u itace ke mata hidima ita kuma Ikilima na bangaran Aysha.
Abdul na can gurin Fulani tace"A bar mata shi tunda ya saba da zaman nan din tana ganin ko yaje inda suke ba zai zauna ba bayan haka kuma dukaninsu suna dauke da juna biyu dole su samu hutu....Aysha ba tayi musu ba sai uban gayyar da ya nuna 'bacin ransa shi yafi so duk ya had'a kan iyalinaa guri guda hankalinsa zaifi kwanciya amma dake yasan bashi da wani kwanjin da zai tunkari mahaifiyar tasa kan maganar kawai sai ya hakura ya bar mata.
To sai Mimi ma ta soma nata rikicin da kiran gwaggo kwana take kuka tana hanasu bacci gashi ta'ki cin komai wanda dama tuni yarinyar ta yaye kanta ta daina shan nono baby Safa ce kawai take sha itama ba sosai ba don wataran sai ta yini bata shaba Dr Rakiya tace"A hankali itama nonon zai fice mata daga rai kamar 'yar uwarta.
Ganin kukan da Mimi take ya'ki 'karewa ne ya sanya shi tattara ta da ita da kayanta ya kaita gurin gwaggon aikuwa tun kafin ya bar sashen yarinyar ta sake ta dinga walwala da farin ciki tana dariya da kiran gwaggo.....Girgiza kai kurrum yayi Gwaggo kam dariya take masa ganin yanda yake mamakin yarinyar.
Wannan karon ba guri d'aya suke ba ko wacce na part dinta amma kusan kullum suna tare da juna idan Aysha bata gurinta to tana gurin safarau hakanan idan Safa bata gurinta to babu tamtama tana gurin aysha.
Amma dai duk da haka Aysha tafi zuwa part din Safarau saboda ganin yanda cikinta ya tsufa haihuwa ko yau ko gobe wanda ita kuma a lokacin laulayin da takeyi yayi mata sauki ba kamar farkon samun cikin ba.
Hajiya Abida matar Kawu Lado tazo har sau biyu ganin Safarau wanda bayan tafiyarta ya kasance kullum sai sunyi waya sun gaisa Kawu Lado yace insha Allah idan ta haihu zai kaita can garinsu domin taga sauran 'yan uwa
****
Aysha na 'Bangaran Safara'u suna hira kira ya shigo wayarta ko da ta duba sai taga maigidan ne ta d'aga cikin nutsuwa ta gaishe shi ya amsa cike da kulawa yana tambayarta Safa tace gatanan kusa dani ko in bata? Yace."A'a ba barta kawai yanzu yanzu zan shigo gida ina tare da ba'kuwa ne."!
Cike da mamaki tace"Yanzu fa ka fita wace irin bakuwa kuma."!? Yace."Idan tazo zaki ganta." Tabe baki tayi tana dan jin kishi tace."To Allah ya kawo ku lafiya."
Yace."Yawwa Gimbiya." Kashe wayar yayi kana ya mike daga kujerar da yake zaune ya fito daga ofis din nashi masinjan sa ya mike tsaye da sauri yana nuna masa ita
Tana zaune kan wata shirgegiyar kujera dake reception din gefanta keken ta ne a jiye Azima ce ba wata ba.
Ya karaso har inda take suka gaisa tana ta 'boye fuska duk kunya ta isheta yace."Ya jikin naki." ?
Murya na rawa tace"Alhamudullahi naji sauki wallahi shine ma nace bari nazo mu gaisa kuma ka sadani da Aminiyata aysha na nemi afuwarta."
Yace."Eh duk na karanta test dinki karki damu ki same ni a mota da kaina zan kaiki gurin aysha."Gaba yayi ita kuma tayi 'yan dabaru ta hau kan keken