Advertisements
Chapter 3 Reading Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar

Author :  Binta Umar Category :  Complete Novels

Chapter   3 / 29

6K to 9K   out of 86.8K words

jikina ne dai ba zaka samu ba." Fuuuuu ta shige daki ta buga kofar....Ko banza ta rama abunda yayi mata yanzu zatayi bacci sakayau! tunda ta sanya zuciyoyinsu cikin damuwa da tashin hankali.






*Kika futar min da littafi Allah ya isa!/Kika karanta baki biya ba kema Allah ya isa!*


My numnars
*08089965176_07084653262*
accont numbar
*0542382124...........Binta Umar gtbank*





25/4/2020





*BINTA UMAR ABBALE*
[5/26, 9:55 AM] Bintu Novel: 62


Omar kam zama yayi kan kujera wani irin gumi na yanko masa, hannu biyu ya dafe dakansa da sara masa yana tunanin lamarin kwata-kwata bashi da ra'ayin raba iyalinsa, amma yana ganin idan haka zata cigaba da faruwa to kam babu shakka zai dauke Safa ya sauya mata gurin zama in yaso ita ayshan sai ta zauna anan din....Kwanciya yayi kan kujerar ya rintse idon sa dole ne yayi wani abu akan tashin hankalin nan na aysha.


Aysha kam wani sabon wanka ta sakeyi ta saka rigar bacci mara nauyi ta isa inda ledojin abincin suke ta bude ta fara cin abunta babu wata damuwa a tare da ita tana ganin wannan abun da tayi shine dai-dai sai da taci ta koshi sannan ta mike ta bar gurin toilet ta shiga tayi brush ta fito tayi kwanciyarta 'kankanin lokaci bacci ya dauketa.


Safarau kam kuka taci ta koshi wanda ya haddasa mata ciwon kan da take karyarsa.

Yanda yaga rana haka yaga dare domin kiran sallahr farko a kunnensa ya mike ya nufi dakinsa a gurguje ya dauro alwala ya fito jallabiya ya sanja ya dauki carbi ya nufi masjid.


Sai kusan goma ya koma sashen Dalili ya d'an jima tare da Limami suna tattauna wata magana mai muhimmanci Omar ya roki limami kan yana so ya sanya kullum ayi masa saukar al'kurani mai girma kan wata bukata tashi, bayan sun gama dashi ne sai ya nufi sashen mahaifiyarsa nan ya zauna ya karya sukayi hira ya samu sassaucin abunda ke damun zuciyarsa.


Koda ya shiga palon shiru ko wacce tana d'akinta Ya nufi dakin Safarau ya nufa ya tadda ta a kwance cikin bargo tsayuwa yayi a kanta tare da kiran sunanta.

Ta mike zaune a sanyaye ta gaishe shi....Ya amsa yana jin wani irin tausayinta na ratsa shi yasan abunda akayi mata jiya ba a kyauta mata ba amma kuma duk laifin ta ne mai zai sanya ta fitowa tunda ba da ita ake ba bayan nan kuma ya fad'a mata cewar ta dauke kanta akan dukanin abunda taga yana faruwa tsakaninsa da aysha.


Zama yayi gefanta ta takure jikinta ya rike hannunta a hankali yace."Safa daga ni wannan idanun naki basu baccin kirki ba kuma kinyi kuka ko."?

Cikin kokarin danne abunda ke damunta tace"Nayi bacci Yayana kaina ne dai ya matsa min da ciwo wallahi."

Yace."Sannu kinji ko."! gyada kanta tayi tana jira taji zaiyi mata wata magana da ta danganci abunda ya faru jiya don gaskiya taji masifar haushin marin da aysha tayi mata bai dauki mataki ba.


Yace."Da'alama dai yau ni zan shiga kicin kenan in shirya mana bresk fast tunda dai baki jin dadi ki kwanta ki huta kawai.


Cikin ya'ke tace"Yanzu nake so in tashi wallahi haba ai mutukar ina raye ba zakayi wannan aikin ba insha Allahu."


Rungumeta yayi ya dan buga bayanta a hankali yace."Allah yayi miki albarka Safa kiyi hakuri da abunda ya faru jiya aysha bata kyauta ba amma ki barni da ita kinji ko."!


"Babu komai ya wuce a gurina ni dai don Allah kace mata ta daina zagina wallahi ina jin ciwon abun sosai."


Yace."Bake kadai ba Safa nima ina jin ciwon abunda aysha keyi ki ta yani da addua kinji ko."

Lumshe ido tayi tace."Insha Allah Yayana."

Sakinta yayi ya mike sai ta yaye bargon jikinta ta mike tana sanye da riga ita gwiwa ya bita da kallo hamdala yayi cikin zuciyarsa Safa ta soma zama cikakkiyar mace gashinan ko ina na jikinta na bud'ewa zanin atampah ta daura kan rigar sannan suka fita tare kicin ta nufa shi kuma ya nufi dakin Aysha.


Tana zaune gefan gado taci uwar kwalliya tare da kashe d'auri Jakadiyar Nanne na gefanta da Abdul a hannunta tana shiryashi hira sukeyi aysha sai dariya take kana ganinta zakace bata da wata damuwa.


A nutse yayi sallama ya shiga.

Jakadiya ce ta amsa masa kana tayi kasa da kanta cikin girmamawa ta gasheshi dama ta gama shirya Abdul din sai ta mika masa yaron ta mike ta futa tare da fad'in"Na barku lafiya."

'Dakin yayi shiru bayan futar jakadiya Mutuniyar ta wani sha murr!! tare da d'auke kanta daga inda yake tsaye.

Shi kam ganin yaronsa ma yasa ya manta da wani abu ya zauna cikin kujera yana dariya tare da lakutar kumatun yaron yana masa wasa shi kuma sai bangale baki yake.

Wani irin farin ciki ne yake ratsa shi yaronsa wayo yakeyi kullum duk muguntar da Aysha ke masa bai hanashi kuzari ba.


Haushin abunda yakeyi takeji sai ta mike ta bar masa d'akin.....Palo ta zauna kan kujera tare da d'ora kafa d'aya kan d'aya tana karkad'awa.......Kwanciyarsa yayi kan Sofa ya d'ora Abdul din saman ruwan cikinsa suna wasa abunsu Omar yaji duk wani kunci dake damun zuciyarsa ya d'auke dalilin ganin gudan jininsa Abdullahi.


Safarau na fito taji gabanta ya yanke ya fad'i ganin *Hakima* a hakimce kan kujera 'kafa d'aya kan d'aya tana karkad'awa. Ganinta cikin uwar kwalliya yayi masifar tashin hankalinta wai dama haka ayshan take da kyau da gayu ? duk sai taji ta sare.

Da 'kyar ta dai-dai ta nutsuwarta ta fito sosai Aysha ta d'auke kanta tana ya mutsa fuska tamkar taga kashi.

Cikin dauriya tace"Aunty Ina kwana."!? ko kallonta batayi ba ballantana ta amsa mata.

Safa ta ta'be bakinta ta wuce d'akinta cikin zuciyarta tace"Idan kin amsa kanki idan baki amsa ba ke kika jiyo ni dai na fita hakkin ki."

Abunda ya shiga da ita dakin ta dauko ta fito ta koma kicin din a gurguje ta had'a musu bresk fast ta fito da kayan tana shirya daining, tsaf ta kammala ta nufi daki ta she'ko wankanta itama zama tayi ta tsara kwalliya mai k'ayatarwa ta shirya jikinta cikin les mai ruwan zuma tayi kyau sosai 'barin turare tayi a jikinta ta cokala dauri kusan irin na aysha amma baiyi kyau da tsari irin nata ba saboda ita ayshan Shadda kamfala ce a jikinta duguwar riga wacce muke kira da (buba) anyi mata wani irin sirfani a jiki sosai tayi kyau mutuka.

Palon ta fito itama ta zauna kan kujera tana baza kamshi....Aysha ta kalleta a fakaici ta dauke kanta Yarinya sai iyayin tsiya da gasa wato tana nuna mata itama matar gida ce kenan tazo tayi zaune a palo shashasha kawai.

Tana tunanin mi'kewa ta bar gurin ya fito daga d'akinta kafad'arsa sa'be da Abdul.

Ganinsu a hakimce a palon sai ya bashi mamaki ya kalli gefan da Safa take zaune tayi kwalliya ta bam mamaki kwalliyar da bata ta'ba yin irinta ba tunda ya aureta, Sosai ya shiga tunani Aysha dama kwalliyarta ba sabon abu bane a gurinsa shiyasa bai wani mamakin gani ba.


Cikin Fara'a ta mike da sauri ta isa inda yake ta kar'bi Abdul din tana masa wasa sai dariya take ta kalli Omar din tare da fad'in "Yayana Abbana ya girma sosai wallahi."

Yace."Yace."Ni kaina ina mamakin girmansa." Dariya takeyi tana lakutar kumatunsa shi kuma sai bangale baki yake yana mata dariya tace''Gaskiya yana da fara'a sosai." Yana zama Aysha ta mi'ke ta shige dakinta wannan rawar kan da yarinyar nan keyi shine yake masifar 'bata mata rai.

Safa tace" Ga break fast nan na had'a mana ga aunty kuma ta koma d'aki."

Yace."Rabu da ita Safa muje ki hada min nawa duk da dai na karya sashen Mama amman dole in cin abincin matata."


Cike da farin ciki suka isa daining din ta hada masa komai ita kuma ta zauna kan kujera sai wasa take da Abdul tana dariya.


Ko da ta shiga daki sai ta rasa tunanin ma da zatayi ta lura fa yarinyar nan dukanin abunda za'ayi mata bata nuna taji haushi dubi makirci don Allah ta daukar mata yaro ta rungume sai surutan banza takeyi itafa tafi son mutum mara boye abu a ransa tafiso idan tayi mata ta rama bata dunga wani nu'ku-nu'ku ba tabbas yarinyar ta cika shaid'aniya.


Wayarta ta dauka ta kira Nanne suka gaisa marairacewa tayi tace"Nanne don girman Allah ki turo min Ikilima wallahi duk cikin bayina nafi amincewa da ita sosai zata taimaka min zata kuma d'ebe min kewa."


Nanne tace"Shikkenan zan turo miki ita insha Allah amma kafin nan ina so in san cewar mijinki ya san da zuwanta."


"Eh Nanne shine ma yace nayi miki magana saboda wani lokacin sai Abdul yayi ta rigima na rasa abunda zanyi masa kinga dama gwaggo ce ke goyashi ni kuma ba iya goyo nayi ba."

"To shikkenan zata zo in anjima yanzu ina Abdul din."?

" Yana gurin babanshi."!

Tace."To ki shafa min kansa Allah yayi miki albarka."!

"Ameeen Nanne."! sallama sukayi ta aje wayar a kusa da ita yunwa takeji gashi tayi alkawarin ko da wasa baza ta ci abincin yarinyar ba sai dai idan taci bata sani ba.


Mikewa tayi ta isa frge ta dudduba babu wani abunci sai lemuka da ruwa kawai. ta rufe tana jan tsaki.

Can gurin da suka ci abinci jiya taje tana dubawa akwai sauran nama fal takarda ta dauka tana sansanawa ji tayi a hancinta kamar ya lalace gaskiya baza taci nama da safe ba, kyau ta samu kunun gyada tasha da madara da kosai gwaggo ta riga ta sangarta da cima iri-iri.


Zama tayi tana tunani can ta mike ta bude drwar gefan gado inda ta aje kayan da gwaggo ta bata.

Ta d'auko jarkar zuma ma dai-dai ciya zama tayi ta bude ta tsiyaya karamin cup ta fara lasa tana ya mutsa fuska a hankali a hankali za'ki da bauri ya game bakinta sai da tasha zumar sosai ta aje ragowar kan drowar kwanciya ta gyara kan bed din tana jiran zuwan ikilima.

Tura kofar dakin yayi ya shiga koda ta d'ago kanta taga shine sai ta dauke kanta tare da sake tamke fuskarta.

Ya tsaya daga bakin kofa babu fara'a a tare dashi yace."Wannan yarinyar me ya kawota sashen ne."?

Ta mike zaune tana kallonsa a she'ke tace"Wai kana nufin Ikilima."?

Yace."Kwarai." Cikin gadara tace"Nanne ce ta turo min ita ta taimaka min da wani abun."!

Yayi jim! yana nazarin maganarta juyawa yayi ya futa daga dakin ta bishi da wani irin kallo wani irin haushinsa takeji wanda bata so ko fuskarsa ta kalla.


Ikilima ta shiga dakin bakinta da sallama.

Rankwafawa tayi tana gaishe da ayshan ta amsa a dan sake tace"Ikilima kin dawo sashen nan zaki dinga taimakona kinji ko."


Ikilima tace."Hakika naji dadin sake kasancewa tare dake ranki shi dade Allah ya barmu tare."


"Yawwa ki shiga kicin ki dafa min indomee da busassan kifi."


Ikilima tace"Angama ranki shi dade." Ta juya ta futa daga d'akin ita kuma ta cigaba da charting da Azima.


Safa na kicin tana gyare-gyare Ikilima ta shiga da sallama ta gaisheta a nutse ta soma ayyukanta.


Safa ta bita da kallo cike da mamaki kawai ta shigo kicin babu wata doguwar magana tana hada-hada ranta a 'bace ta futa daga kicin d'in.


"Don Allah da gaske kike zaki zo Azima."?

Daga daya bangaran Azima tace" Allah zai zo aysha amma sai na dawo daga dubai insha Allahu zanzo nayi sati biyu."


Tace."Yaushe zaki dawo."
"Cikin sati mai kamawa insha Allah."

Tace."Shikkenan ina sauraron zuwanki akwai labarai 'kawata."


Azima tace''Komai yake faruwa idan nazo naji.


Sallama sukayi da juna 'bangaran Azima taja tsaki tare da fad'in "Zuwan da zanyi ba naki bane aysha zanzo ne in kafa kaina gurin mijinki kowa tasa ta fishsehi....Test messages din data saba tura masa ta zauna ta tsara kalmomi masu dadi da ma'ana gami da sanyaya zuciyar masoyi ta tura masa.


Tsaf Ikilima ta gyara mata dakinta da palo ko ina sai kamshi yake Safarau kam takaici da ba'kin ciki ya sanya ta kulle kanta a d'aki....Aysha kam bayan taci indomeen ta palo suka fito ita da Ikilima ta zauna suna kallo suna hira.


Hakan ma ya 'kara d'aga mata hankali duk sai ta tsargi kanta tayi shiru a daki motsi ma bata so tayi.

Oho!! Aysha ta ma manta da ita sabgar gabanta kawai take dama Abdul tun safe da babanshi zai futa fada ya tafi dashi sashen Fulani can yake yini taji dadin hakan dama ba kaunar tsotso take ba.


Sai kusan karfe biyar da rabi Safarau ta daure ta fito daga dakin ba tare da ta kalli inda Ayshan ke zaune ba ta nufi kicin domin dora sanwar dare hakika dawowar ayshan gidan ya sanya ta cikin damuwa gami da takura.


Suna da miyar nama sai kawai ta dafa farar shinkafa da taliya ta soya dankalin turawa babu kwai ta tsane tsaf ta had'a musu abinci ta jere a daining tana ta nukufurci wanda ita Ayshan ma bata san tanayi ba zurga zurgar ta da yayi yawa a gurin ne ma ya sanya ta mi'ke ta shiga daki abunta....Wanka tayi ta shirya jikinta cikin ingilsh wear riga da siket wanda sukayi masifar fito mata da tsarin jikinta ta gyara gashinta kana ta sanya wata hula mai kyau Palo ta fito tana jin sauyin yanayi a jikinta sha'awa ce kawai ke taso mata dama hakane duk ranar data sha wannan zumar yini take tana jin 'kaikayi a gabanta jiki babu kuzari ta zauna.....Ikilima tace"Ranki shi dade me za'a dafa miki na abincin dare."?

Kai tsaye tace."Koma meye kiyi Ikilima." Ta mike ta nufi kicin din wanda yayi dai-dai da fitowar Safa suka buga karo da sauri Ikilima tace"Sannu." Wani wawan kallo ta watsa mata ta wuce...Ikilima tabi da kallo na mamaki....Safa na fitowa sosai taga Aysha zaune a palo cikin shigar kananun kaya da sauri ta dauke kanta wani irin abu taji a zuciyarta dangane da Aysha.....Dakinta ta shige ta nufi toilet wanka tayi ta fito itama kananun kayan ta fito dasu riga da wando masu bala'in fitar da sura ta sanya a jikinta Safa akwai gashi sai ta gyarashi sosai ta daure ya sauke a bayanta turare ta fesa a jikinta kusan kala goma domin kamshin turaran da taji ayshan nayi yayi masifar daga mata hankali shiyasa ita ta watsa a jikinta palon ta fito ba tare da ta daura dankwali ba jelar gashinta sai reto yake a bayanta.....ba palon da ayshan take zaune ta zauna ba na gaba dashi ta nufa ta wuce Ayshan taje ta zauna itama tv ta kunna tana kallon catoon Aysha ko a jikinta ballanta ta wani damu kanta da kwalliyar da tayi A yanda take jin kanta babu 'yar iska fad'in duniyar nan da tafi ta komai shiyasa in taga mutum na gasa da ita abun baya damunta.

Da sallama ya shigo palon ba tare da ta kalleshi ba ta amsa a ciki, Tsayawa yayi bakin kofar ya kasa shigowa kallonta kawai yakeyi ta d'an juyo tana zum'bura baki.

Saurin dauke kansa yayi ya wuce ciki....Sai ya rasa ma wane daki zai shiga nashi ko nata Alwala ya shigo ya daura domin magariba ta gabato.

'Dakinta ya nufa ya d'auro alwalar ya fito yana gyara hannun rigarsa .


"Aysha lokacin Sallah yayi yana da kyau ki kashe kallon nan kije ki daura alwala." Wannan maganar da yayi mata itace ta farko tun tashin su ita dashi sai dai kallo kowa jiji da kai da izzah ya hanashi kula dan uwansa....To shima ya fad'a mata hakane saboda rashin abun fad'a yasan dai ba'a kira sallah ba kwalliyar ta ce ta tafi da hankalinsa har ya manta da fad'ansu na jiya.

Safarau nacan na kallo taji maganarsa sai ta mike ta d'an fito daf da zai fita ta kira sunanshi "Yayana." A marairace tayi maganar.

Ya juyo Saurin dauke kansa yayi chai!!!! Zankad'aziya sunan da ya ambata kenan a zuciyarsa Tayi masa kyau sosai da sosai kayan da yake ta bala'in so ta sanya masa su ta'ki wai kunya takeji yau kuma gashi tasa babu zato.

Yace."Safa bari inyi sallah in shigo kinji ko."!

'Daga kanta tayi kamar wata yarinya ya fita da sauri domin ba yaso ya tsawaita tsayuwarsa a gurin kar su kassara shi ya lura ko wacce ta bud'e wuta ta 'bangaran aysha al'amarin ba sabo bane a gurin sa na Safaraun ke bashi mamaki wata zuciyar tace "Watakila tana kwaikwayon Aysha ne aikam yaji dadin hakan.Safa ta soma wayewa.


Takaici da mugu mugun 'bacin rai ya sanya ta mi'ke ta bar gurin....Wai shin me yarinyar take nufi ne da wannan abun da take? Wannan ai jahilci ne shiyasa fa tace Ita baza ta zauna da ita ba idan banda hauka da gidadanci kawai daga taji suna magana tsilim! sai ta fito ta sa musu baki tabbas sai tayiwa tufkar hanci domin ta lura yarinyar mugun gasa taje da ita saboda ta rainata.


Safarau kam da taga ayshan ta bar gurin itama sai ta nufi dakinta har yanzu zuciyarta babu dadi daurewa kawai take.


Sai bayan sallah isha'i ya shigo shiru Safa ta kasa ta tsare ita kad'ai a palo domin tana so ya shigo a gaban idonta kuma ya yabi kwalliyar ta, domin a ganinta kamar yafi kallon aysha ita bai ganta ba sosai.

Aikam da ita yayi arba ta mike tsaye da sauri ya saki fuska sosai tare da fad'in" Kina jira in shigo in ga kwalliyarki ko."? rufe fuskarta tayi tana dariya tace"Ba haka bane Yayana ina so ka shigo kaci abinci ne."!

Yace."Muje ki bani naci matata." gaba tayi tana wata iriyar tafiya ta daukar hankali Omar kam dauke kansa yayi sanin da yayi da cewar yau ba dakinta yake ba gefe guda kuma baya so sha'awarsa ta tashi bashi da tabbacin aysha zata biya masa bukata shiyasa bai wani zage yana kallonta ba.


Tsaf! ta hada masa abincin ta tsiyaya masa lemo ya dauka ya kurba yana sakar mata murmushi ita kuma sai dariya take masa.


Cokali ya d'auka yayi bisimillah zai kai bakinsa kenan ta fito daga dakinta ganin inda suke ta nufo ya sanya yin sakare da cokali cike da abinci yana kallonta.

Safaraun ma kallonta take har ta 'karaso inda suke tace"Wannan shine adalci ko adali."!? Ya kalleta cikin sigar tambaya yace."Me ya faru kuma."?

"Wannan abincin da kake ci itace take da hurumin baka ko ni."!? Sakare yayi yana kallonta....Ta d'aga masa gira ''Ka bani amsa ta mana."!? tafada tare da rike 'kugu ta tsareshi da dara-daran idanunta.

Cokalin ya aje babu yabo babu fallasa yace." Idan

3 / 29