Advertisements
Chapter 14 Reading Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Sadauki Omar Zukatan Kishi By Binta Umar

Author :  Binta Umar Category :  Complete Novels

Chapter   14 / 29

39K to 42K   out of 86.8K words

DA
*AZIMA AMBASSADOR ILIYASU*

*FAISAL SARKI SALISU*
DA
*ARIFA WAZIRI ABDULLAHI*



Wani irin kyarma! jikinta ya hau yi sai ta kasa tsayuwa da kafafunta ta zube a gurin gumi sai yanko mata yake a take taji wani irin jiri na d'ibar bakinta ya bushe 'kam! sai 'kakalo miyau takeyi babu hali domin ma'kogwaronta ya riga ya gama bushewa katin daurin auran kawai take ta kallo tana jin yanda kanta ke wani irin bugawa da mugun karfi.....Cikin wannan yanayi ya shigo dakin ya same ta sam bai lura da halin da take ciki ba ya wuce kan mirror dinsa yana kara dubawa tare da fad'i sai kace "Almara Aysha na aje abu da hannuna nazo ina nema.''

Shirun da yaji tayi ne yasa ya juyo yana kallonta ganin halin da take cikine ya sanya gabansa ya fad'i da sauri ya kalli abunda yake hannunta yaji wata iriyar fargaba ta kamashi 'Karshen tika tiki tik!!!!! Aysha taga abunda yake ta 'boyewa rashin abun fad'a ne yasa ya kama hanya zai fuce daga d'akin.....Cikin wani irin zafin nama! ta mi'ke tsaye! jikinta na kyarma!!! ta tunkareshi da katin daurin auran a hannunta yana kokarin bude kofar ta doke hannunsa....A sha'ke! tace" Wannan katin d'aurin auran waye."!?

Ya kar'ba yana dubawa tamkar me neman wani abu a jiki ya d'ago kansa da kyar yace."Nawa ne."? Kafin yayi aune! ta yanka masa wani bahagon mari!!! Tana wani irin huci!!!!! taci kwalarsa wani irin karfi yazo mata a lokaci tace"Ni zakayi wa haka ko? ni zaka cuta ko! Allah ya isa tsakanina da kai! Allah ya isa!!!!! ta fad'a da wani irin sauti!!!! hankalinsa ya tashi matuka Aysha ce ta mareshi tabbas da ba don cikin dake jikinta ba da sai yayi kasa-kasa da ita a gurin sai yayi mata dukan da bai ta'ba yi mata irinsa ba.


Yana wani irin huci! ya fuzge hannunta dake sha'ke da wuyansa ya tureta dan saura kad'an ma ta fad'i saboda yanda ya sa mata karfi ya bude kofar dakin ya fita.....Ta biyo bayansa a gigice ko nauyin cikin jikinta ba tayi wani irin zagi take masa na "Idan ka cika kai d'an uwarka! da ubanka ne! ka sakeni! macuci Azzalimi na gama auranka."!!! Wuyan rigarsa ta ri'ke tamau! yayi yayi ya cire ya kasa, Safarau ta fito taga halin da ake ciki sai ta tsorata mutuka don ganin yanda siffofin ayshan duk suka sauya ga Omar din ya tsaya kawai yana kallonta tana zaginsa ya kasa kata'bus!! tazo tana kokarin cire hannunta daga wuyansa murya na rawa take cewa" Haba Aunty Aysha me yayi zafi ke dashi haka! karfa ki manta mijinki ne a tsakaninku babu haka aunty aysha komai yayi miki kiyi hakuri don girman Allah ki daina cewa ya sakeki."!!

"Safarau wallahi tallahi yau sai wannan d'an iskan mutumin ya sakeni gwara na kare rayuwata a haka kan in zauna dashi dama tuntuni na fad'a masa ko ni ko Azima to tunda ya za'bi Azima a kaina sai ya sakeni."!!!

Safarau gabanta ya yanke ya fad'i! " cikin inda inda tace"Aunty ban fahimci maganarki wacece kuma Azima bayan tuntuni an riga an rufe shafinta."

''Ke da Allah yi mana shiru shashasha kawai ta ina aka rufe shafin Azima to bari kiji gobe kina tare da ita a cikin gidanan a matsayinta na matar mijinki."

Jiki a sanyaye Safarau ke kallon Omar yana tsaye idanunsa sunyi jawur kamar gauta tace"Yayana da gaske Azimar zaka auro mana." ? Dauke kansa yayi ya ma yar kan Aysha a kufule yace."Wallahi Aysha idan baki cika min wuya ba ranki zai 'baci mara hankali kawai wacce bata san ciwon kanta ba wai da kike wannan abun kin isa ki hanani nayi abunda nayi niyya ne? a da na janye auran Azima daga baya Allah ya bijoro da al'amarin ke baki isa ki hanani na raya sunna ba."

Tace."Ka gama magana babban munafiki maciyin amana ai bance kar ka aureta ba ka aureta amma ka saki Aysha yanzu."!!!


Da karfi ya fuzge hannunta ya kama hanya zai futa ta bishi a guje!! ta baya taci kwalarsa har sai da ya jiyo hankali a tashe tace"Wallahi sai ka sakeni zaka futa." Omar ya dinga zufa yana gargadinta ta sake kar ta kara furta kalmar saki.....Aysha idanunta sun rigama sun gama rufewa zaginsa take ta uwa ta uba....Wanda yayi dai-dai da shigowar Baba Galadima Nanne cikin palon lokacin ne ita kuma ta kara rike masa kwalar riga tana wata girgiza tace"Idan ka isa kai haifaffe ne cikin Uwarka da Ubanka to ka sakeni a yanzu."!!


"Innalilihi Wa'ina ilaihi raji'un!!!! Baba Galadima da Nanne sukayi sak! suna kallon d'iban albarkar da 'yarsu takeyi.......Cikin wani irin yanayi na 'bacin rai Galadima ya 'karasa inda suke tsaye wanda ganinsa bai sanya Ayshan ta dawo hayyacinta ba....Ya kalli Omar rai a 'bace! yace." Saketa kamar yanda ta bukata."!!! Omar ya d'ago jikitattun idanunsa yana kallon Galadiman dake tsaye a kansu, sai kawai bakinsa ya hau motsi! Galadima ya buga masa wata iriyar tsawa tare da fad'in "Nace ka saketa kamar yanda ta bukata ka nuna mata kai d'in haifaffe ne cikin Uwarka da Ubanka!!!Nanne ta 'karaso gurin da sauri baki na rawa zatayi magana! Ya d'aga mata hannu tasan halin mijinta sarai bai iya 'bacin rai ba shiyasa ma ba sosai take fad'a masa abubuwan da Ayshan keyi ba take barin abun cikin ranta don da ya sani da tuni aysha ta gane bata da wayo.....Gefe ta koma tana sharar hawaye shin wannan masifa dame tayi kama.


Omar ya dinga dawurwara yana ya'ki da zuciyarsa tamkar wanda ake rurawa wuta ake ingizashi yace." Aysha kije na sakeki saki d'aya!!! Safarau ta kwallara wata razananniyar 'kara ta dora hannu aka tana kuka tare da fad'in "Wallahi nima sai ka sakeni!!! Galadima kam najin Omar ya ambaci kalmar saki sai ya kama hanya ya fita abinsa.....Aysha ta cika masa kwalar riga tayi wuri-wuri! tana kallon palon Can ta hango Nanne kan kujera kanta a 'kasa, sai d'akin ya soma juyawa da ita yayinda gunjin kukan Safarau ya dinga ratsa kwakwalwarta sai ta zube a gurin wani irin mahaukacin jini ya yanke mata.

Safarau tayi kanta a guje ta rungume tana wani irin kuka na fitar hankali "Aunt Aysha ki tashi innalilihi wa ina ilahi raji'una yau mun shiga uku! Allah ka kawo mana d'auki wayyo Nanne kizo kiga Ayshanki kar ta mutu."!!! Tana wannan maganganun tana tatta'ba Ayshan.....Nanne ta mike jikinta a sanyaye ta kama hanya zata futa daga palon wani irin sarawa kanta yake da ta san abunda zata gani kenan da bata shigo ba Gwaggo ce ta sanar mata da cewar ayshan babu lafiya dalili kenan da ya sanya ta lalla'ba Mijin nata suzo su duba jikinta kuma sun tadda tashin hankali....Ita wani irin yanayi takeji a jikinta mara misali....." Nanne kar ki tafi ki dawo Ayshanki tana cikin halin taimako Nanne ki dawo."! Safarau ke wannan maganar tana ihu!! Nanne bata jiyo ba ma ballanta ta dawo ta fice cikin yanayi na tashin hankali da rashin makama.

A gigice ta mi'ke tana kallonsa yana tsaye 'ki'kam! a kansu zai had'a zufa yake tace"Idan wannan baiwar Allah ta mutu kaine sila Wallahi banta'ba tsammanin haka kake ba sai yau nima nayi nadamar auranka."!!! tana gama maganar ta kama hanyar futa.


Omar ya zube gaban Aysha dake kwance cikin jini! ya d'aga hannunsa yana dubawa tamkar yana neman wani abu fuskarta ya tsirawa ido, sai ga hawaye a fuskarsa tattaro ta yayi ya rugumeta 'kam! 'kam a jikinsa yana wata iriyar shashshekar kuka......sai sumbatar fuskarta yake da kumatunta duk ya rasa ma me zaiyi hawaye sai fita yake a idonsa in banda ambatar sunanta babu abunda yakeyi "Ayshana na janye wannan sakin da ya ratsa a tsakaninmu dake na mai dake dakinki kiyi hakuri ki zauna dani da halina nace miki babu wata 'ya mace da zata kaiki matsayi a gurina aysha me yasa kike min haka!? me yasa bakya yarda dani Aysha kin jawo mana shiga matsala! innalillhi wa'ina ilahi raji'in!!! Ya dinga nanata kalmar yana shashshekar kuka gashi ya rungumeta 'kam-'kam a jikinsa cikin wannan hali Fulani da gwaggo sula shigo suka same shi.


Gwaggo ta dauko ruwa mai sanyi ta fesa a fuskarta ganin nuffashinta ya dan dawo ya sanya Fulani ta umarceshi da ya daukota su wuce asibiti.

Ya ciccibeta cikin rashin karsashi gami da karyewar zuciya suka fita a wannan lokacin Omar ji yake zai iya hakura da komai mutukar ayshansa zata rayu.


Kai tsaye asibitin Malam suka nufa ko da suka isa cikin gaggawa ma'aikata suka fito da ayshan suka dorata kan wani gado emagency aka nufa da ita likitici kusan biyar a tsaye a kanta domin ceto rayuwarta.

Dr Hamisu wanda ya kasance d'aya daga cikin likitocin dake duba iyalin gidan Sarki ya fito yana goge fuskarsa Omar yaje gefe ya fad'a masa abunda ke da akwai Hannu na rawa ya kar'bi takardar ya sanya hannu Dr Hamis ya koma cikin dakin cikin gaggawa suka shirya aysha domin yi mata Cs saboda ta riga ta gama galabaita ba zata iya haihuwa da kanta ba......Cikin ikon Allah da nasara suka samu nasarar ciro kawawan yara duk mata masu kama da junansu wasu narse dake tsaye a gefe suka fara aikinsu na gyara yaran....Sai da komai ya kammala sannan Dr Hamis ya fito yayi musu albishir cewa ta haihu an samu twins duk mata, Omar ya kalleshi da jajayen idanunsa yace."Ya jikin mamansu." ? Dr Hamis yace."Alhamdullhi tana bacci yanzu sai zuwa dare idan ta farka insha Allah zata tashi garau! sai ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya bar gurin can wani guri ya nufa cikin asibitin ya zauna yana kukan zucci wanda har sai da ya fito fili ya ciro hankici yana tsane hawayen fuskarsa shin wai wace iriyar kaddara ce ta rikito musu shi da aysha ne? me yasa bai hakura ya zauna da ita da halayenta ba, to wai shin ma meye dalilin da ya sanya ya nace lallai sai ya auri Azima meye abunda ya burgeshi a tare da ita!! to duk wad'an nan amsoshin bashi da mai bashi amsarsu sai kawai ya mike ya hau zaga gurin yana tunanin mafita.[6/5, 10:52 AM] Bintu Novel: 72

Yana tsaka da zagaye gurin wayarshi ta fara ruri sai ya share bai dauka ba har ta gaji ta katse aka dinga kiran wayar kamar babu gobe tilas tasa shi fito da wayar daga aljuhunsa yana dubawa dama sai da ya tsammaci ita ce ya dauka tare da kara wayar a kunne.

Ajiyar zuciyarta yaji kafin narkakkiyar muryarta ta fara magana.

"Haba Yalla'bai laifin me nayi kuma inata kiran waya ka'ki d'agawa idan nayi laifi ayi hakuri."

Koda jin muryar Azima sai ya rikice murya na rawa yace."Azima bana cikin nutsuwa ne kiyi hakuri Aysha na asibiti a halin yanzu anyi mata aiki an ciro tagwayen yara yanzu haka muna asibiti."

Sai ta sake narke muryarta gwanin tausayi tace"Ayya Allah Sarki 'kawata kace ina gaisheta da kyau kafin nazo dubata." Yace."Karki damu in ta dawo hayyacinta zan fad'a mata."

Tace."Shikkenan yanzu zuwan naka ya ruguje ko gani na shirya tsaf kai nake jira." Yace."Kiyi hakuri a yanzu dai bani da nutsuwar da zanzo gurinki muyi wata magana koma meye da akwai ki bari sai Allah ya kaimu i war haka ina tunanin kin zama matata."

"Shikkenan." kawai tace ta kashe wayar....Hasina dake gefanta a zaune tace"Wai me yace miki ne."!? Azima ta ciji d'an yatsanta cikin takaici da jin haushi tace"matarsa ce ta haihu shine ya manta dani yana can yana rawar jiki a kanta humm! baki ga ma kafin ya dauki wayar tawa ba sai da yaga dama anya ba sai nayi wani abu kan aysha ba."

Hasina tace"Kece ai tuntuni nake fad'a miki cewar ba shi kadai zaki mallake ba har da ita shegiyar tunda dai kin fuskanci yafi sonta to me zaki tsaya jira da ita."

Azima tace"Ki bari tukkuna na shiga daga ciki idan naga al'amarin babu sauki wallahi sai nayi maganinta yanzu ni takaicina wannan lemon dana had'a masa shikkenan anyi asara kuma ya kwana lalace za'ayi."

Hasina tace"Ki sanya a firji kawai ko kankara yayi sai ki dauko shi kisa masa ruwa kin san dai ba xakiyi asarar kudinki ba kuma wasu malaman ba azubar musu da magani idan kinyi haka mybe duk wani shiri da kikeyi a kansa ya ruguje gwara ki san yanda zakiyi yasha lemon nan."


Tace."To ko muje asibitin ne da sunan munzo duba ayshan sai in jashi in bashi yasha lemon." Hasina tace"Ki dai bari gobe tayi idan an daura aure ai dole yazo inda yake ke kuma sai ki aikata aikinki."

Tace."Shikkenan haka za'ayi kawar arziki." Tafawa sukayi suna kyalkyala dariya.


****

A hankali ta bud'e idonta ta dinga bin dakin da kallo dishi-dishi take ganin iyayen nata a tsaye a kanta ta d'an waiwaya gefanta Safarau ce a tsaye ta 'kura mata ido hawaye sai kwaranya yake a fuskarta, hannu ta mi'ka a hankali ta kamo nata hannun ta ri'ke tamau! safarau ta matsa sosai kusa da ita.....'Daya gefan nata ta kalla sai ta ganshi 'ki'kam! a tsaye ya hard'e hannuwa a 'kirji yana kallonsu. Da sauri ta d'auke kanta wasu zafafan hawaye suka shiga zubo mata.


Fulani da gwaggo suka 'karasa bakin gadon suna mata sannu kai kawai take iya d'aga musu tana nuna musu cikinta da hannunta bakinta duk ya bushe saboda tsabar wahala da fargaba duk abunda ya faru ya shiga dawo mata daki-daki!


Gwaggo tace"Ki kwantar da hankalinki aysha kin haihu lafiya kin samu yaranki 'yan mata masu kyau da lafiya kamar ki yanzu abunda ke gabanmu shine samun lafiyarki."


Sai ta bud'e baki da kyar tace"Gwaggo gwara min mutuwa da wannan rayuwa."!!!! 'Dakin yayi tsit!! kowa na sa'ka abunda ke ransa....."Kaico! kaico Gwaggo me yasa na kasa Hakuri ne! gwaggo kullum sai kunyi min nasiha nayi hakuri da rayuwa! Gwaggo da inga wannan rana gwanda Allah ya d'auki raina na huta."!!!!!!! Sai ta fara shashshe'kar kuka tana tari tare da ri'ke ciki.

Safarau tace"Aunty ki daina kuka akwai matsala akwai damuwa a ciki kina cikin halin ciwo ba'a son motsi 'kwakkwara a tare dake." Tana kuka take maganar Aysha kam tari ta cigaba dayi ma'kogwaronta ya wani bushe ruwa kawai take so tasha.


Fulani ta kalleshi da jan ido yayi wani sakare a tsaye kamar wani sakarai tace"Kayi tsaye kan mutane malam mara tunani da sanin ya kamata kaje ka kira likita wannan tarin da take kar ya tsanatsa yazo ya magance shi."


Ya kama hanya ya futa salau-salau!! aysha har ya fita idanunta na kansa tana ayyana abubuwa da dama a tare dashi Wai Saki!!! ita abun ma mamaki yake bata.


Tare suka shigo da Dr Hamis yaga halin da take ciki ransa yayi masa rashin dad'i don dai duk sun fi karfin yayi musu fad'a ne yasa yace."Yana so suje waje zuwa anjima sa dawo." Hakanan suka fita Fulani tana takaici da jin ciwon abunda yaron nata ya aikata.


Dr ya shawo kanta da kyar ta daina tarin sai dai kirjinta na harbawa sosai ya duddubata a nutse ya kalli Omar din yace."Akwai damuwa tare da ita yalla'bai yana da kyau a dinga kiyaye abunda zai tayar mata da hankali a irin wannan lokacin babu abunda take so sai kulawa da rarrashi."

Omar ya sauke ajiyar zuciya mai zafi ya furzar da huci daga bakinsa yace."Dr Insha Allah za'a kiyaye.....Idanunta ta bude wanda sukayi mata nauyi sosai tace"Dr Bani ruwa insha." Yanda ta fad'i maganar dole ka tausaya mata Dr Hamis yace."Kiyi hakuri Madam zaki sha ruwa amma ba yanzu ba."
Murya a hard'e tace"Sai yaushe kenan." ? Yace."Nan da wani lokaci kankani." Lumshe idonta tayi kawai tana kalato miyau da kyar tana had'iyewa a wannan ga'bar tafi bukatar mutuwa da rayuwa shiyasa take addua kan Allah ya dauki ranta ta huta da bakin ciki.


Tana jin sanda aka bude kofa aka fita daga dakin batayi yunkurin bude idonta ba sai da taji hucin numfashin mutum akanta sannan ta bude ido ta sauke kansa fuskarsa daf da tata....le'bansa ya kai saman goshinta ya sumbata kana ya zauna gefanta had'e da ri'ke hannunta guda duk ya wani susuce ya koma tamkar maraya


Ta dinga kallonsa yayinda hawaye ke zirara ta gefunan idanunta bakinta sai motsi yake tana so tayi magana amma ta kasa saboda rashin abun fad'a.

"Aysha."!!!! Ya ambaci sunanta can cikin ma'koshi!! dauke kanta tayi a hankali tana kokarin cire hannunta daga nasa.


Ya sake kiran sunanta cikin wata iriyar murya mara amo " Aysha! Na maidake d'akin ki kimin afuwa kinji ko duk abunda ke faruwa a tsakanina dake da zamantakewar mu akwai sharrin shaid'an da kuma rashin hakuri na fad'a miki babu wata mace a gabana data zartaki tsautsauyi da kaddara suka sanya na datse igiyar aurena guda daya dake kanki da kuma bin umarnin Baba galadima Aysha nace na mai dake dakinki ina so ki sanya a ranki dani dake mutuwa ce zata rabamu."!

Jinsa kawai takeyi ba tare da tana fahimtar sambatun surutan da yake mata ba dalilin baccin da ya fara cin karfinta....Shi kuma bai gane ba sai surutai yakeyi mata da bada hakuri amma har yanzu bai furta cewar ya hakura da auransa ba.


Sai da ya lura tayi bacci sannan ya mike da kyar ya futa daga d'akin! kana kallonsa a lokacin sai ka dauka sabon mahaukaci ne saboda rashin nutsuwa yana fita iyayen nasa suka bishi da kallo mussaman Fulani girgiza kanta kawai takeyi cikin ranta kuwa bata ganin laifin kowa sai nashi a ganinta duk shine ya jawowa kansa shiga wannan matsala domin dai itama bata san abunda ke faruwa ba sai da gwaggo ta sanar mata irin dauki ba dad'in da ake ta fama sannan ta sani hakika abunda Omar yayiwa aysha sam bai kyauta ba kuma dole ne itama ta zauna taja kunansa idan da hali ma ya fasa auran Azima domin samun kwanciyar hankalin Ayshan.

***

Gida ya koma yayi wanka ya shirya a gurguje komai yakeyi yanayi ne ba don dad'i ba fada ya nufa inda iyayen sa maza suke, dama shi suke jira don haka sai suka mi'ke a nutse suka fito fadawa na baza musu babbar riga Omar da kansa ya bude

14 / 29