Author : Binta Umar Category : Complete Novels
fa ba dawowa zaiyi yanzu ba saboda haka ni kam zanje na kwanta sai da safe."
Safarau ta mike tana fadin"Aunt xaman me zanyi nima Allah ya tashe mu lafiya." ko wacce ta shige dakinta rayukansu duk babu dadi.
Tana toilet tana wanka ta jiyo motsi kamar an shigo dakin....Tana fitowa taganshi yana cire rigarsa ya cire dogon wandon ya zauna daga shi sai singilet da gajeran wando
Jikin dauriya tace"Ka dawo kenan." Tsabar yanda yake a matse ya sanya ya kasa amsa mata ya 'kura mata kafiran idanunsa masu cike da zallahr sha'awa har ta karaso inda yake.....Tsaf ta fahimci halin da yake ciki sai ta dauke kanta ta fara kokarin sanya rigarta....Rikota yayi yana sansanta "Aysha ina al'kawarinmu." ? yafada murya a sha'ke!
Zuciya ta ciyota a d'an harzu'ke! tace"Wane alkwari kuma."!? yana matsa mata jiki yace."Kin manta ko."!? ta'be bakinta tayi tayi bala'in shan kunu "Don Allah sakeni in sanya rigata"!
'Kin sakinta yayi sai ma ya hau warware towel din jikinta yana mata shu'umin kallo ranta yayi masifar 'baci ta sanya iya karfinta ta tureshi tana ja masa karamin tsaki! kamar maye ya mike da sauri zai janyo ta... Hannu ta d'aga masa! " Dakata." tafada babu wasa a fuskarta....Ya rungume hannu a kirji yana kallonta ta zura rigar baccinta ta kalleshi tar!! tace"Wai don Allah kai me yasa baka da amana ne? meya sa zamu amince maka ka dinga ha'intar mu waye ka mayar yaro a cikin mu? idan ka dauki Safarau yarinya to ni kasan duk abunda zakayi sai dai na kalleka wallahi na tsani munafurci a rayuwata bana so in amince da kai ka munafurce ni meye don ka fada mana cewa aure kake nema? Ko kuma ka fad'a mana cewa zance ka tafi zamu hanaka ne? bamu isa mu hanaka abunda Allah ya halasta maka ba! Naga test din budurwar taka to me zaka 'boye min wallahi kome zakayi a halin yanzu sai dai na kalleka kawai."!!
Jiki a sanyaye yace."Zo ki zauna in fada miki abunda ke faruwa."
Harara ta watsa masa tace"Ni bana son borin kunya kasan dai ba karya nayi maka ba ko."!? yace."Eh bakiyi karya ba gaskiya ne shine dalilin da ya sanya ma nace kizo ki xauna na fad'a miki komai."!
"Magana ai ta wuce kawai ni ina so duk abunda zakayi ka daina rufa-rufa ka fito fili ka fad'a min komai ni wannan halin naka shine yasa nake bala'in jin haushinka wallahi."
Yace."Allah ya baki hakuri gimbiyar mata ai shine nace kizo in fad'a miki yanda al'amarin yake." Fuska a tur'bune taje zata zauna sai ya rike hannunta ya d'ora ta a cinyarsa wuyansa ya d'ora a kafad'arta, kana ya fara magana kamar haka.
"Aysha kamar yanda kika fahinta hakane aure nake nema insha Allah abunda ya sanya nake 'boye muku saboda ina gudun tashin hankalinku shine kawai dalilina amma yanzu naji dadi sosai da kika fahimta kuma baki dauki lamarin da zafi aysha shiyasa kullun nake alfahari dake a cikin rayuwata."
Ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin danne damuwarta tace"Yanzu akan wane mataki ake kan maganar auran kuma matar taka a ina take nifa bana so kaje ka dauko wacce zata lalata mana zamantakewar mu."
Gabansa ne ya fad'i da sauri ya aro dauriya da jarumta ya dora aransa ai ko da wasa ba zai fad'a mata cewar Azima bace sai dai kawai in an daura aure ta gane dama baiyi niyyar had'asu gida d'aya ba yayi niyyar warewa Azima gidanta daban domun samun zaman lafiya.
Yace."Zakuji dad'in zama da ita aysha domin itama kamar Safa take bata da hayaniya gata da nutsuwa bama tare zan had'aku da ita ba."
Ajiyar zuciya ta saki tace"To Allah ya sanya alkairi." Ya amsa da '"ameen yana jin wani irin kunyarta da tausayinta....Aysha kam daurewa kawai take tana addua cikin ranta tabbas Allah ya jarrabeta da miji mai son matan tsiya to babu yanda ta iya akan yaje ya nemi matan banza gwara yayo auran sun xauna.
Da lallashi da banbaki omar ya hillaceta ta amince masa suka kwana suna soyayya babu irin sambatu da ihun! da baiyi ba gogon naku ya rikice har da 'kananun hawaye a gaskiya samu mace kamar ayshan sa sai an tona duk da tana cikin halin damuwa da kuma yanayi na ciki hakan bai hanata ta rikitashi da salonta ba.
*****
Mahaifiyar Azima batayi 'kasa a gwiwa ba ta nufi gidan Kawun Azima ta fad'a masa abunda yake faruwa Alhaji Ayuba yaji dadin lamarin dama a 'kagare yake sam baya kaunar ya 'bude ido ya dinga ganin Azima na yawo a gari ita ba budurwa ba ita ba bazawara ba, nan take yace."Zaije gidan Sarki domin a tsaida magana hakika yaji dadin wannan lamari sallama sukayi itama ta fito cike da farin ciki da annushuwa Azima zatayi aure gidan sarauta habaici da sharrin da mutanan gari keyi a kan Azima duk ya kare itama za tayi aure insha Allahu.
*****
Washe gari ya kasance ranar babu aiki Saturday yaci baccinsa ya koshi a dakin Aysha don sai kusan karfe goma sha biyu na rana ya fito duk suna zaune a palo suna kallo suka ga ya shiga dakinsa, Safarau ta mike ta bishi dakin....Yana cire jallabiyar jikinsa tace"Nasan dai wanka zakayi ko."!? yace."Kwarai kuwa jikina duk yayi nauyi Ki had'a min ruwa mai d'umi.
Toilet din ta shiga ta had'a masa ruwan tana kokarin fitowa ya shiga sai ya rike hannunta ta kalleshi kashe mata ido d'aya yayi yana d'age mata gira sai tasa dariya ta gane abunda yake nufi ya tsirawa bakinta ido tace"Me zanyi maka wai." Harararta yayi yace."Kema kin sani ai."!
Tace"Tom cire kayan." A shagwabe yace."Cire gajeran wando babu wahala kece zaki cire min da kanki."
Sai ta gyada kanta tana murmushi taje ta matsa masa man goge baki ta mika masa ya fara wanka bakinsa sai da ya gama tukkuna ya shige cikin kwamin wanka ita ta shiga ta fara cud'ashi yana mata wasanni na soyayya kai Omar mayaudari ne yasan duk yanda yakeyi gurin siye zuciyar mace cikin kwamin wankan nan sai da ya gama ya mutsa mata jiki kana ya kyaleta.
***
Aysha na kallasu suna dirma gurin karin kummalo ma ya langwa'be wai dole sai ta zauna a cinyarsa ta bashi a baki ita kuma ta'ki aminta saboda tana jin kunyar Aysha, wanda ita kuma ta 'bangaranta take ganin hakan ba wani abu bane a yanzu ta d'auki Safarau a matsayin kanwarta kuma abokiyar zamanta shiyasa dukkanin abunda zasuyi da Omar din a gabanta bata wani damuwa saboda tasan itama idan ta kama hakan zasuyi a gabantam....Idan ma da akwai kishi a tsakaninsu to duka suna kokarin dannewa.
Sai da ya gama sangartasa sannan ya mike ya fita kai tsaye Fada ya nufa sai yaci sa'a iyayen nasa ne kawai a cikin fadar yaji dadin hakan ya zauna suka gaisa a nutse yace."Dama ina tafe da wata mahimiyyar magana ne." Duka sai suka mai da hankalinsu kansa, domin suji maganar da yake tafe da ita.
[6/3, 9:29 AM] Bintu Novel: 70
Galadima yace."Ka fad'i ko wace irin magana ce Sarki na sauraran ka muma muna sauraran ka da kunnan basira."
Omar ya gyara zama kai a kasa yace."Allah yaja mana da ranku ya kara muku lafiya da nisan kwana maganar da nake tafe da ita shine............Omar ya zayyana musu maganar neman auransa na Azima da yanda sukayi magana da mahaifiyarta ya cigaba da cewa yana so ayi komai a gama cikin 'kankanin lokaci."
To cikinsu babu wanda maganar ta girgiza sai ma farin ciki da Sukayi Galadima yace."Hakika babu wani bunkice da zamuyi mai tsauri kan mahaifin yarinyar saboda sananne ne a siyasan ce ya bada gudumarwarsa kafin Allah ya dauki rayuwarsa sai dai ita yarinyar da kake nema a kanta zamu tsaurara bunkicenmu idan babu wata mishkila a tare da ita insha Allahu za'a daura maka aure da ita kamar yanda kaso."
Waziri yace."Haka shine dai-dai Omar muna tayaka murna ubangiji Allah ya sanya albarka."
Omar ya amsa da "ameen." yana jin wani irin farin ciki na ratsa shi.
Mai martaba kuwa kana kallon fuskarsa zaka gane yana cikin walwala da farin ciki Hakika ta ko wane fanni yana alfahari da d'ansa Omar tabbas yaci sunansa Sadauki Ya tabbatar da cewar yaronsa zai iya gadar kujerar sa ta mulki saboda a'kidunsa da kuma zurfin tunanin sa yana gani duk namijin da ya iya wakiltar mace sama da d'aya to ba 'karamin jajurtacce bane.
***
Ko da ya fito fada kai tsaye sai ya wuce sashen mahaifiyarsa Ita da Faisal ne a zaune a palon kan wata katuwar dadduma suna hira Abdul na cinyarta yana wasa.
Ya shiga da sallama a bakinsa da gudu Abdul din ya mike yaje ya rungumeshi shi kuma ya daukeshi yana sumbatar kumatunsa.
Faisal yace."Mama wannan yaron ja'iri ne wallahi duba ki gani har ya gane Ubansa."
Fulani tayi murmushi kana tace"Af a gayawa Abdul wayo yana sane da kowa a gidanan yasan babansa sarai."
Omar na dariya ya karaso ya zauna dashi a jikinsa Faisal ya mika masa hannu sukayi musabah ya gaishe da Fulani ta amsa a sake tana tambayarsa iyalinsa yace."Duk lafiyan su lau."
Hira suka shiga yi a tsakaninsu kafin Omar din ya shigo da maganar dake tafe dashi.
Fulani tayi shiru tana nazarin maganar ta dago kanta tana kallonsa babu yabo babu fallasa tace"Jarumi gidanka ya soma samuwa da zaman lafiya amma kake nema ka rakitowa kanka aure yanzu shin ko dai matan naka nayi maka wani abu ne."?
Murmushi yayi ya dan shafa sumarsa yace."Ko d'aya mama wallahi a halin yanzu babu wacce nake samun matsala da ita dukaninsu muna zaune lafiya mussaman Aysha, kawai ina da ra'ayi had'a mata ne ina so in cika sinnar Annabi Muhammad SAW."
Fulani tace"To babu laifi A'ina ka samo yarinyar kuma?"
Sai ya hau dawurwura! ta dinga kallonsa cike da zargi tace"Yaya ne naga kana sin'ke kai! karfa kaje ka dauko mana 'yar 'kananun mutane mara tarbiya."
Yace."Mama wannan dai yarinya ce nitsatstsiya mai hankali kuma mahaifinta sananne ne a gari kafin mutuwarsa ina ganin baza'a samu wata matsalaba daga gurinta."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"To Ubangiji Allah yasa za'ayi damu." Ta kalli Faisal tace"To kaga yanda akeyi ko cikin shekara biyu ya had'a mata uku kai ka tsaya shashanci Faisal wai meke damunka ne."!?
Sai ya sunkuyar da kansa kasa yace."Afuwa mama nima na kusa aure insha Allah kuma 'yar gida zanyi ina fatan babu matsala."
Fulani tace"Wace irin matsala kuma? Ai kawai ka sanar dani a'ina ka samu matar ko can 'bangarena ka nufa ne."?
Ya sosa kansa tare da yin kasa da kai yace."Aarifa ce Ta 'bangaran Baba Waziri." Sai ta saki fuska sosai tace."Kayi dace da samun kintsatsiyar yarinya Allah ya sanya za'ayi damu saura wancan shima yazo ya duba cikin dangi idan bai samu a nan ba to sai ya nufi zaria zai samu."
Sadauki da Faisal sukayi dariya tace"To ai idan ba haka akayi ba sai ya zauna domin naga kamar ba auran ne a gabansa ba. Hira suka cigaba dayi har Abbas din ya shigo anayi dashi nan ta shigar masa da maganar da ake tattaunawa yace."Shi a yanzu bashi da matsala yana da matar aure a hannu suna dai-dai ta kansu ne.
***
To a tsakankanin kwanaki biyu Omar duk ya tsangwami kansa dalili yana ta sauraran kira daga gurin mahaifansa yaji shiru shine ya takure kansa ya rage walwala cikin iyalinsa kullum fuska a daure idan Sunyi magana sai yace su kyaleshi Aysha tunda taga yana wannan iskancin sai ta tattara shi ta watsar dashi yanzu ta kanta take cikinta ya shiga watan haihuwa yau da lafiya gobe babu Safarau ce mai shishshige masa wataran su rabu lafiya wataran kuma suyi kaca-kaca don yanzu itama ta daina raga masa wani abun yanayi take taka masa burki sai ya shiga taitayinsa mussaman idan yana neman biyan bukatarsa.
Yau wata biyu kenanan da Maganar auransa da Azima babu wani cigaba ta fannin iyayen nasa don har kawunta Yazo sunyi magana da Galadima yace."Ya bari suna wani bunkice ne idan an kwana biyu zasu nemeshi. haka ya tafi duk gwiwoyinsa a sage.
Kullum suna manne a waya idan yaje ofis bashi da aiki sai waya da Azima duk ya wani susuce duk kwanan duniya ana kara rura wutar sonta a cikin zuciyarsa, Wanda ita kuma take samun wannan damar take kara rikitashi tana d'aga masa hankali da kuka kan itafa ta gaji da zuba ido shiru har yanzu Basuyi magana ba
Duk ranar da haka ta kasance a tsakaninsu to daga aiki can gidansu yake nufa ya raba dare yana aikin rarrashinta da lallabata, anan take samun damar ciyar dashi kayan asirinta da take yawon kar'bowa babu dare babu rana haka yaje dawowa gida cikinsa a cike da abincin Azima wanda yaji kayan tsubbu Ko kallon Abincin Safarau bayayi idan ta matsanta masa sai yaci sai ya hau kanta da masifa da bala'i......haka ta ta'ba faruwa a gaban Aysha ya dinga falla mata rashin kirki da arziki Aysha tayi bala'in jin tausayin ta sosai wai sai ta tsaya tana masa kuka Girgiza kai kawai take tana jin da ita yayiwa wannan iskancin babu shakka baza su kwashe kalau ba....Tana da can kan kujera ta kira Safarau taje ta zauna kusa da ita shi kuma yazo ya wucesu da key a hannunsa da alama fita zaiyi babu wacce ta tanka masa a cikinsu ya kama hanya ya fita suna kallonsa yana harararsu.
Sai bayan ya fita aysha tace"Wallahi ki daina zama gabansa kina kuka Safa domin zaiyi masifar raina ki ni meyasa bayayin wannan masifar saboda bai ga fuska ba, shin dole ne sai yaci abincin da kikace ga abinci yaci yace baya ci ba sai ki rabu dashi ba cikin ki ko nasa, ni ban hanaki kiyi masa girki ba amma wallahi kiyi kokari ki kwaci 'yan cinki da mutuncin ki tun kafin dare yayi miki......To tun daga lokacin Safa ta sanja taku ba komai yake mata ta hakura ba, Akwai ranar da ta'kiyin girki dashi ya saboda baci yake ba sai dai a zubar ya dawo aiki da wuri yace ta kawo masa abinci wannan karon ma a palo sukayi dramar Aysha na zaune turus!!! da ciki a gaba tana kallonsu.....Safa tace"Ni kam banyi girki da kai ba wallahi."!
Yace."A kan me? abincin ki ko nawa? ko kuma kece kike aurena da har zaki d'ora tunkuya ki sauke kice bakiyi dani ba okey sai ki shiga kicin kiyi min domin yunwa nakeji yau babu inda zani."
Aysha tayi sakare tana jiran amsar da zata bashi aikuwa sai ji tayi tana fad'in"A gaskiya Yayana sai dai kayi hakuri yau ma kaje can inda ka saba ci su baka amma mu nan mun riga mun sauke mun cinye abunmu."
Ya fusata iya fusata! dama me neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki ya dinga sirfa bala'i a gidan yana masifa da tashin hankali lokacin Safarau sai jikinta yayi sanyi har tayi nufin zuwa kicin din tayi masa Aysha tace"Ke Safa kizo kiyi zamanki ina dalili kina tsaye a gurun nan idan da tsautsayi zai iya marinki domin ba a cikin hayyacinsa yake ba."
Fad'ar wannan magana da Aysha tayi sai fad'an ya dawo kanta"""Dama nasan duk abunda Safarau takeyi min kece kike zugata to sai me! don kun hanani abinci eyeee! sai akayi yaya? don kun hanani na samu nutsuwa daku! Ko yanzu ina da inda zani inci abinci irin wanda nake so kuma bani kulawar data kamata kuje ku ri'ke duk wani abunda ya shafeku bani da ra'ayi."!! ya shige dakinsa a fusace! ya fito cikin shiri! fita yayi ya barsu a gurin suna mamakin Al'amarin.
Safarau ta kalli Aysha dake cije bakinta saboda tsananin bacin rai! ta riga ta gama gane abunda ke sashi wannan zafin zuciyar *Maganar Auransa ce* Domin Nanne ta riga ta sanar mata da cewar maganar auran tana a matsayin 'kila wa'kala saboda bunkicin da Galadima ya sanya akayi musu ya nuna musu cewar yarinyar bata da tarbiya shiyasa sukayi masa shiru kan maganar......"Aunty Anya kuwa Yayanmu na cikin hayyacinsa kuwa ki duba kiga abunda yakeyi kamar wani zautacce."!
"Lafiyarsa Lau Safa yana so ya huce fushinsa a kanmu ne."
"To aunty me mukayi masa da zai dinga yi mana haka.!"?
Aysha tayi murmushi me ciwo tace" An hanashi aure shine yake jin haushin mu."
Safarau ta ta'be bakinta tace"Aunty meye namu a ciki don Allah? gaskiya lamarinsa sai addau anya ma kuwa wannan yar iskar budurwar tasa tq barshi haka ba kuwa."!?
"Safa sanin gaibu sai Allah nima jikina ya soma sanyi da abunda yakeyi wallahi Mu cigaba da zuba masa ido kawai yanzu dai tunda hakane ki cigaba da girkn dashi gudun samun matsala idan yaci shikkean idan baici ba an dai futa hakkinsa."
*****
Kwanaki uku ya tsira yana fushi dasu sai ana hud'un ne ya sauko yw dinga raragefe da neman shiri saboda jarabarsa ta ciyo shi ya dinga jan safarau da wasa da dariya dama aysha ko giyar wake yasha ba zai tunkare ta ba saboda yaga ko kallon nahiyar da yake ma batayi.
Safa kam ta d'an sakar masa jiki babu yabo babu fallasa ya zauna cikinsu wai dole sai sunyi hira dashi Idan Aysha na magana sai yayi tsilim ya sanya baki Aysha tayi shiru tana harararsa oho!! ko a jikinsa idan ta sake wata maganar sai ya sa baki karshe da haushi ya isheta sai ta mike da kyar ta bar musu gurin....Safarau ma ta mike tayi shigewarta daki....Sai dai ko zama ba tayi ba ya shigo dakin.....Ya dinga yi mata wayo da dubara ya samu ya ra'bi jikinta ya sauke nauyin dake damunsa.
****
Ranar Juma'a bayan an sauko daga sallah Omar ya nufi sashen Nanne saboda a lokacin yana da tabbacin Baba Galadima na sashen,
Suka gaisa da Nanne cikin mutunci da girmama juna yace."Yana son magana da Galadima Nanne ta shiga ta sanar masa, ta fito tare da fad'in"Kana iya shiga Sai kuci abincin tare." Yace."Nagode Nanne."
Baba Galadima na zaune kan wata dadduma gabanshi kwanonin abinci ne kusan guda shida sai lemuka da kayan marmari birjik ya amsa sallamarsa A nutsr yace."Bisimillah *Magajin Sarki!* dake wani lokacin da sunan suke kiransa.
Omar ya zauna a nutse yana mi'ka gaisuwarsa
Galadima yace."Na riga na san abunda yake tafe da kai kafin mu fara maganar mu fara cin abinci tukkuna."!
Omar ba don yaso ba ya sanya hannu da bisimillah ya fara cin abincin....Sai bayan sun