Author : Binta Umar Category : Complete Novels
da binta da kallo....Daf da zata shiga toilet din tace"Bani dashi."! ta shige tare da bugu kofar.
Ya zauna kan sofa yana jijjiga shi yaron sai kuka yake gwanin tausayi da'alama nono yake so.
Daure da guntun towel ta fito tana cin magani wanka tayi hade da wanke gashinta.....Cikin wata iriyar tafiya ta jan hankali ta gifta shi dressing mirror ta nufa ta zauna kan stool tana busar da gashinta.
Ya mike ya isa inda take tare da tsayuwa a bayanta ta cikin mirror din yake kallonta ta shareshi cigaba tayi ta gyara sumarta ta shafeta da mai kana ta samu katon ribbon ta daure cream ta shafa a jikinta ta shafa turaran jiki mikewa tayi yayi saurin tareta da kirjinsa fuskarsa ya murtuke yace."Karbeshi ki bashi abincinsa aysha bana son rashin imani."!
Zumbura baki tayi tayi gaba wardrobe ta bude ta dauka mitsitsiyar rigar bacci ta sanya ta zira wani shegen wandon rigar wanda dashi gwara babu.
Duk yana kallonta take sha'aninta ga Abdul din sai kuka yake da buge buge nono kawai yake so.
Cike da dauriya ya karisa gurinta yace."Kina kaunar bacin raina ko Aysha shin Abdul ne yayi miki laifi ko ni? Wanda yayi miki laifi akansa zaki rama wannan shiga hakki ne."
Ta wasa masa wani kallo tace"Da bakina kaji nace kayi min laifi? yayi shiru yana kallonta.
"Nonona yake ta tsotsa tun dazu yaki koshi ni kuma nagaji gaskiya."
"Shin dama haka kike masa a sashen Nanne."?
Tabe bakinta tayi yace." Wallahi hakkin! wannan yaron da kike dauka Allah ba zai bari ba."
"Ni kuma nawa hakkin fa."!? Tafada idanunta a tsaye a kansa.
"Sai ki barwa Allah zai saka miki kan wanda ya zalince ki."!
" Humm Allah ya kyauta dama ai hakane sai an cuceka sannan sai ace ka barwa Allah."
"Eh naji na cuceki kiyi hakuri kinjiko taimaka ki bashi yasha kafin ni." Cikin wata kasalalliyar murya ya fadi maganar.
Dora mata shi yayi a cikinta ta mike zaune tana dauke kai kokarin ciro nonon take ya sanya hannunsa ta baya yana d'age mata rigar jikinsa sai wani kyarma yake.
Wai brest din sun sake girma ds cikowa gasu sumul sumul dasu shatin nippels din yayi baki sosai tsigar jikinsa ta dunga tashi ji yake tamkar shine yake tsotsar nonon ba Abdul ba....Idonsa kur!! a kanta yana kallo don har ya fara futa ma daga nutsuwarsa
Tsaki! taja ta juya bayanta wanda ya dawo dashi nutsuwarsa ya kwanta rigingine gefanta rufin dakin ya tsirawa ido yana kallo tabbas yau sai ya taki aysha sai dai duk abunda zatayi masa tayi masa.
Bacci yayi ta mike ta isa inda gurin kwanciyarsa yake ta kwantar dashi a hankali yaron tsotso ne dashi ita kuma bata kaunar tsotso ko kad'an.
"Ka tashi zan kwanta."! tafada lokacin da take tsaye a kansa.
burkitattun idanunsa ya bude yana kallonta yana lumshesu.
Ta sake maimata maganar ta.
A hankali yace." In tashi inje ina? kizo kiyi kwanciyarki kawai nima ai anan zan kwana."
Ta watsa masa harara tare da fad'in"Wane irin a nan zaka kwana ina dakin amaryar taka kaje ku cigaba daga inda kuka tsaya mana."!
"Addini kwana bakwai ya halasta min nayi da ita kuma nayi kamar yanda addini ya gindaya saboda haka yau anan nake."!
" Mtsssw! Addini ya halatta maka kwana bakwai tare da amaryar ka ni kuma na halatta maka kwana dubu tare da ita saboda haka kaje kawai aysha bata bukatar ka anan gurin.
"Baki isa ba." Yafada yana mikewa zaune.
Matsawa tayi baya ta jingina da bango yace ." Ba zaki sanya ni ranar lahira na tashi da shanyayyan jiki ba wallahi sai nayi adalci."
"A'a to na hanaka kayi adalci ne? nifa cewa nayi kaje nawa hakkin na bar muku kuma wallahi tallahi har ga Allah nake fada maka kar ka wani damu."
"Bana so.''! yafada a hasale. Tabe baki tayi....Ya cigaba da cewa " Nace nan dakin zan kwana saboda ina da iko da ko ina na gurina wai me kike tunanin zai faru ne ? da kike ta wani damun kanki kizo kiyi kwanciyarki babu abunda zanyi miki in baki sani ba to yau ina so ki sani a yanzu wannan abun da kike tunani ni baya gabana dama kece kika sanya ni nayi to yanzu ni komai ma baya burgeni zaman lafiya kawai nake so dake in yaso koma meye sai ya biyo baya.
"To gwara da kace haka hankalina sai ya kwanta nima naji dadin maganarka domin tuntuni ka daina burgeni zaman lafiya kuma idan kaso za'ayi a cikin gidanka."
Shiru yayi mata ta gama tsigalar ta da rashin kirkinta sannan ta nemi guri ta kwanta kai da kafa ita dashi.
Mikewa yayi zaune ya dafe kansa yunwa yake ji amma masifar aysha ta hanashi samun nutsuwa mikewa yayi ya nufi kofae fita key din ya zare ya ja kofar ya futa....ta mike da sauri zata kulle kofar sai taga babu key din a jiki tsaki taja ta koma ta kwanta itama yunwar ke damunta ga Abdul duk ya tsotseta.
Dakin Safa ya shiga ya tarar da ita lamo a kan bed shigowarsa yasa ta mike da sauri tana ya'ke! yace."Na duba inda kike aje mana abinci babu bakiyi girki bane."!?
Kasa tayi da kanta a sanyaye tace"Eh wallahi dazu na nufi kicin din naji ba zan iya ba shine kawai na hakura kaina ne yake ta ciwo har yanzu."
Yace."Tashi ki sanya kayanki na arziki muje a dubaki in yaso daga nan mutsa mu siyo abunda zamu ci."
Mikewa tayi shi kuma ya futa daga dakin nasa ya nufa domin shiryawa.
Tana sanya kaya tana tunani tasan karya take bata wani ciwon kai kawai dai tana so ta kare kanta ne tana jin tsoro kar likita ya dubata yace bai ga wata matsala ba jikinta duk a sanyaye ya ta futa palo ta zauna kan kujera tana jiran fitowarsa.
Cikin jallabiya ash color mai karamin hannu ya fito daga dakinsa tana kallonsa ya nufi dakin aysha sai ta dauke kanta da sauri tana sakin ajiyar zuciya.
Bacci har ya fara daukarta lokacin da ya shiga dakin sai ya dan ja kafarta guda.
Bude idonta tayi wanda suka wani lumshe alamun bacci ya hau kansu....Ya dauke kansa da sauri tare da fad'in"Zamu fita da Safa yanzu zan kaita a dubata tana ciwon kai please kar kiyo dogon bacci nasan baki ci abincin ba."
Ta mike a tunzure tace"Sai me? menene dalilin da zai sanya ka tasheni daga bacci kan wata 'yar iskar yarinya nice na d'ora mata ciwon kome? sai kawai in hana idona bacci saboda zaku futa wato gadin gidan zan yi muku ko."!? Tom na fasa ma baccin wallahi kan dai ku futa ku barni ni kadai a cikin gidanan gwara in rigaku fita in yaso idan kun dawo sai na dawo."
Fuuuuu! ta mike ta isa jikin wardrobe doguwar riga ta dauko ta zura a jikinta sai wani irin huci take wannan ma ai rainin hankali ne zasu fita da matarsa sai yazo ya fada mata har da cewa da ita kar tayi bacci sun ma mayar da ita maigadi kenan."
Karamin hijab ta zura ta nufi gadon Abdul tana kokarin daukarsa ya karasa gurin a gaggauce!.
Tureta yayi sai da ta kusa faduwa yace."Wai ke wace iriyar mara hankali ce ne aysha? kawai daga magana sai ki fassarata da wani abu ke duk abunda za'ayi miki ba'ayi miki dai-dai ba wallahi kika sake kika tashi yaron nan yana bacci sai ranki yayi mummunar 'baci! Shashasha! kawai mara hankali."! Yanda ya fadi maganar zaka gane a kufule yake da ita don yau sha rabon da ya kirata da shashasha duk abunda take masa kawai sai da ya girgiza kai amma yau kam ta gama kaishi bango daga magana sai ta fara yiwa mutane ihu!!!
Tamkar zatayi kuka tace."Ni kake kira da shashasha."!? yace."An kira ki d'in! ke idan ma da sunan da ya wuce shashasha! aka kiraki dashi ba laifi bane." Tsaki yaja ya juya da rai a 'bace.... Da sauri ta bishi ta rike gefan rigarsa tana ja yana ja aljihun rigar ya yage da mugun karfi ya murd'e hannunta ya cire rigarsa tare da tureta ya bude kofar ya fuce tare da murza key a kofar dakin..
Zubewa tayi tana kuka tare da rike hannunta dake mata zafi Omar ba karamin mugu bane wallahi.
Kuka taci ta koshi ta mike sam bata yi yunkurin bude kofar saboda tana ji ya murza key a jikinta yanzu ya tabbatar mata da cewar dole ne tayi musu a gadi a gidan....Takaicin haka ya sanya ta kwanta ba tare da ta cire rigar ba ta dinga wani irin kuka mai ciwo.
Tunda ya fito daga dakin ta fuskanci yana tare da bacin rai sai jikinta yayi sanyi kwata kwata bata son taga ransa ya baci.
Yace."Tashi muje."
Mikewa tayi da sa'bulallan jiki suka fita.....Suna tsaka da zamansu mai dadi tazo duk ta sanya musu kunci da damuwa rana daya kacal duk gidan ya hargitse gaskiya aysha bata kyautawa abunda take.
Cikin zuciyarta take wannan maganar....dreving yake fuskarsa a hade tamau duk wasa da dariyar da suka saba shi da ita yau babu sam yaki sakin fuskarsa.
A hankali tace"Yayana kayi hakuri kaji ko."!?
Ya d'an kalleta tare da mai da hankalinsa kan abunda ke gabansa yace."Me kikayi min wanda zaki bani hakuri."!?
Jiki babu kwari tace"Banyi maka komai ba amma naga kamar kana cikin damuwa ne shiyasa nayi magana kasan bana son ganinka cikin halin damuwa."
Sanyi yaji a cikin ransa yace."Nagode kwarai da kulawarki a kaina Safa Allah ya barni tare dake."!
Yar dariya tayi tace."Ameeen ya rabbi."!
Sama-sama take jansa da hira yana amsawa kadan kadan yace."Naga kamar ma kan naki ya daina ciwo ko."!?
Tace."Haka yake min dama hawa da sauka amma dai gwara muje asibitin a bani magani."
Ya kalleta yana kanne mata ido daya yace."Ko dai nayi ajiya ne ban sani ba."!?
Rufe fuskarta tayi tana yar dariya.
Yace."Ko bakya sha'awar haihuwa tare dani."?
Bude fuskarta tayi tana kallonta yanayin fuskarta duk ya sanja.
"Haba Yayana ya kake irin wannan maganar wallahi ina matukar son inga na haifa maka baby girl irin wacce kakeso ina so inta haihuwa da kai har sai kace ka gaji."
Dariya yake yana shafa sajensa yace."Babu shakka kice sai in zage dantse nima in dunga bada 'kwayayen 'yan biyu domin so nake ki haifa min yara sama da shirn."
Zare ido tayi tana 'yar dariya tace"Gaskiya bazan iya ba Yayana sunyi yawa."!
Ya dinga kyakyata dariya yana kallonta yace."ashe duk karyar banza ce Safa kece fa kika ce zaki ta haifa min yara har sai na gaji."
Tana dariya tace"To ai kane naji kace sai na haifi sama da ashirin nazo na tsufa ka auro budurwa tabdijam."!!!
Dariya yake yana kallonta yace."Ko kin tsufa ko baki tsufa ba Safa idan lokacin aurena yayi sai nayi Kar ki manta aysha mana ai bata tsufa ba na aureki saboda haka ina so ki san da cewar shi aure lokaci ne dashi idan Allah ya nufa zakayi sai kayi babu makawa."
Jikinta yayi sanyi 'kalau ta tsura masa ido tana kallonsa yana draving tace."Yayana aure zakayi da gaske."!?
Ta gefan ido ya kalleta ya danyi mirmushi ya lura fa da cewar yarinyar nan tana da kishi mutuka yace."Sosai kuwa Safa idan Allah ya kaddara zanyi amma dai a yanzu babu shi a zuciyata kuma bani da budurwa ko bazawara idan kuka iya kula dani kun isheni har karshen rayuwata."
Shiru tayi yace."Ya dai kinyi shiru ko? saboda kinji maganar aure."
a marairaice take kallonsa tace"Allah Yayana bakaji yanda kirjina yake min zafi ba Allah bana so ka auri ko wace mace na fiso ka zauna damu mun isheka."
Dariya kawai yake mata yana draving ita kuma sai kara marairace masa take wai kar yayi aure Jinta kawai yakeyi shi kam babu wacce ta isa ta hanashi aure idan lokacinsa yayi.
Haka suka isa asibitin dr Rakiya ce ta dubata ita dai bata fahimci abunda ke damunta ba kawai sai ta bata maganin karfin jiki da sauransu....Sallama sukayi mata tare da godiya.
Dai-dai Mai takobi restaurant yayi parking ya fito a nutse ya shiga gurin minti goma yayi ya fito hannuwansa rike da ledoji ya bude motar ya shiga suka dauki hanya.
Har daki sai da ya rakata ya aje mata leda guda daya kafin ya futa sai da ya jadda mata cawar kafin ta kwanta ta tabbatar tasha magungunanta sannan.
Lokacin da zai futa ji tayi kamar ta jawo shi ta hanashi futa kwalla duk ta cika kwarimin idonta kwanciyarta tayi ba tare da ta kalli ledar abincin ba ballanta ma ta bude ledar maganin....pillow ta rungume a kirjinta hawaye na zubo mata.
Ta kwance kan bed hannunwanta harde a kirjinta rufin dakin kawai take kallo taci kuka ta koshi tunanin irin matakin da zata dauka take a kansa.
Ko da ya shigo sam bai kalli inda take ba ya aje kedar kan drowar gefan gado ya cire jallabiyarsa daga shi sai gajeran wando ya nufi toilet.
Wanka yayi ya fito da gajeran wandon a jikinsa da karamin towel a wuyansa.
Ya tsaya gaban mirror ya tsane jikinsa da sumarsa kana ya dauki leda daya ya koma can gefe kan wani chanis cafet ya zauna tare da bude ladar.
pride rice ce taji hanta da hadin cowsolow kamshi kawai take gefe guda kuma tsirene wanda yaji kuli kuli da albasa da tumaturi cikin wata katuwar takarda mikewa yayi ya dauko ruwa da lemo a frge ya dawo ya zauna abunsa ya fara cin abincinsa a nutse....Wa'kar mutumin sa *Shata* ya kunna a wayarsa yana saurara sai gyada kai yake kai kace yana cikin nishadi nan kuwa daurewa kawai yakeyi yana jiran abunda zai afku anan gaba.
Aysha kam taji zuciyarta kamar ta tsage saboda takaici dama ya saba yi mata haka duk sanda sukayi fada sai ya kunna mata wa'ke-wa'ke yana mata habaici.
Mikewa tayi zaune yayi saurin kauda kansa....Sai ma ya fara bin wa'kar da yake saurare, mai taken *'Kudi a kashe su ta hanya mai kyau!*
Da sauri ta isa bakin kofar fuuuu! ta bude ta futa ya bita da kallo cike da mamaki....Girgiza kansa yayi ya cigaba da cin abincin sa sai da ya kammala tukkuna ya mike ya futa palon.
Kan kujera ya tarar da ita a kwance.
Ya tsaya a kanta tare fad'in "Tashi ki koma dakin ki na fito."
Banza tayi masa ya runkufa dai dai fuskarta har nuffashinsu na haduwa rintse idonta tayi takaici da bakin ciki yana cin zuciyarta.
"Aysha.!" ya ambaci sunanta cikin wani irin voice wanda ya sanya tsigar jikinta mikewa.
Ta bude idonta had'a ido sukayi yace."Kiyi min afuwa kinji ko na fito idan nine bakya son gani ki koma dakinki."
Mikewa tayi tana kokarin barin gurin saboda yanayin yanda ya babbake gurin yasa tayi taga-taga zata fad'i sai yayi saurin tare ta tafad'a jikinsa rungumeta yayi tsam! tsam! yana sauke wata irin ajiyar zuciya mai zafi!
Ture fuskarsa take yi dake kan kafadarta tana kokarin kwace jikinta tace"Dallah ka sakeni na tashi mtsww!! ya sake riketa a jikinsa yana yawo da hannayensa a sassan jikinta.
Cizo ta gartsa masa fatar kunnansa tana bugunsa ta ko'ina shi kuma kamar wani maye ya riketa tam! sai faman shafarta yake yana kokarin cire mata riga ihu!! ta kurma jin hannunsa kan brest dinta ya damka yana ya matsawa sai kawai ta haukace masa a palon tana bugunsa ta ko'ina.
Sakinta yayi ya mike tsaye yana kallonta duk ya futa daga hayyacin sa ta mike kamar wata zararriya ya rike hannunta sai ta zube a gurin tare da rike kafar kujera duk yanda yaso da ya dauketa a gurin abun ya faskara ta rike hannun kujera tamau! tana kuka da gaggaya masa maganganu na 'batanci.
Da kyar ya saisaita zuciyarsa yace."Idan na barki ina zakije cikin daran nan aysha."!?
Ba'a sani ba! ina ruwanka da inda zani? Wallahi tallahi dukkanin abunda kake min Allah sai ya saka min mugu azzalimi kawai."
Yace."Tashi ki koma dakin ki na kyaleki......Banza tayi masa Ya tsuguna yana kallon fuskarta "Aysha ni mijinki kike jifa da mugwayen kalamai ko."!?
" To nima me yasa kake zalinta.'!? tafada tana goge fuskarta.
Yace."Ni ban zalince ki ba aysha kece kika zalinci kanki kuma wannan tashin hankalin da kikeyi babu abunda zai hanani yi idan kan Safarau ma kikeyi kina wahalar da kanki ne wallahi gwara ki zauna dani lafiya."!
"Wallahi ba zauna da kai lafiya dole ka zauna dani ance ba'a sonka ba'a sonka so dole ne kaje ka zauna da matar so mana."
Safarau ta bude kofa ta fito ta tsaya tana kallon ikon Allah.
Yace."Sai me aysha idan bakya sona kawai ki san yanda sakiyi dani amma ni ki sani har abada ba zan ta'ba sanja ki a zuciyata ba."
"Yayana."! muryar safarau ta bayyana a gurin. Ya juya da sauri yana kallonta kana ya juyo kan Aysha cikin sigar kunsa ba'kin ciki yace.''Kinga illar ko? haka kawai tana baccinta kin tasheta saura ki tashi Abdul ma sai bukatar ki ta biya."
Ta mike ranta a tsananin 'bace tayi kan Safarau tana d'ura mata ashar""Ubanki kika fito yi anan gurin shegiya ba'kar munafuka mayyar miji daga jin motsi kin fito munafurci 'yar iska maciyar aman.....! "Keee! Aysha."! ya ka tseta da wata iriyar tsawa! ko kallonsa ba tayi ba ta nufi inda safaraun take ita kuma tayi tsili-tsili....Tana zuwa ta gaura mata mari!! " Don ubanki bukatarki ta biya shine zaki fito kina makale murya da kiran Yayanki ko yar isk..........Tsawar da ya kwatsa mata ce ta katse mata maganar ta ta Juyo tana watsa masa wani banxa kallo tamkar idanunwanta zasu fad'o 'kasa.
Rai a 'bace ya kalli Safarau dake tsaye idanunta sunyi jawur! saboda 'bacin rai yace."Safa koma daki kiyi kwanciyarki kinji ko, dama idan ban manta ba kwanaki na fad'a miki cewar dukanin abinda kikaga munayi da Aysha babu ruwanki ido ne naki so wannan ma ba wata matsala bace kije ki kwanta abunki."
Ta juya da sanyin jiki bakin ciki tamkar ya kasheta yana kallo ta gaura mata mari bai ce komai ba sai ma korar ta da yayi daga gurin wallahi baza ta dauka ba komai daran dad'ewa sai ta rama marinta kuma ta rama zaginta, kwanciya tayi tana ruzgar kuka.
Ya juyo ya kalleta da jajayen idonsa sai sirfa masa rashin mutunci take zuciyarsa na tunzurashi kawai ya tattakata a gurin wata zuciyar tana hanashi cikin 'kunar zuciya ya nuna mata hanyar dakinsa da hannunsa yace."Wuce ki bawa mutane guri mahaukaciyar banza da wofi.'
"Oho! ko da wane suna zaka kirani kayi ta kirana dashi ehee!