Author : Binta Umar Category : Complete Novels
ta tu'ka nan ta iske shi yana 'karbar key hannun direban sa ya bude masa mota ya shiga ya sanya shi ya bude mata mota ta dinga kokarin hawa ta kasa Omar ya umarci direban sa da ya kira su Sitela wasu in ya murai da suke aiki a company suka taimaka suka cicci'bi Azima suka sanya ta a mota sannan suka kwance keken nata suka sanya bayan boot da kansa yaja motar suka bar gurin.
Cikin mota Azima kuka take wiwi tana bashi hakuri da nuna mata nadamar da tayi yace."Ta daina damun kanta da kuka da sauransu shi tuntuni ya riga da ya yafe mata sai sai ta cigaba da istigifari gurin Allah.
Azima taji dadi sosai da sosai sai ta soko masa maganar da ta sanya ya sha kunu bai kara tanka mata ba har suka isa katafaran gidan nasa.
Azima tayi tsuru-tsuru nadama da dana sani duk sun cika mata zuciya da kyar ta samu ta muskuta ta futo daga motar ya dai-dai data mata keken ta hau.
Gaba yayi masu gadinsa na gaishehi hannu kawai ya daga musu.
Azima ta tura keken tana binsa a baya sai rarraba ido take a harabar gidan idan ka shiga gidan tsaf zaka dauka kana ingila ne ko america saboda yanayin yanda suke gina ginansu kenan mai tsayi.
Kai tsaye part Din Safarau ya nufa saboda yana da tabbacin suna can....Yayi sallama cikin nutsuwa
Mikewa tayi taje ta rungume shi ya manna mata kiss a kumatu yana rarraba ido a palon kafin yace."Ina Safa."!? Tace."Yanzu ta shiga daki wai fitsari take ji nifa na soma zarginta wallahi kasanta da zurfin ciki ina zargin nakuda takeyi taki fad'a min."
Yace."Koma me takeyi tunda na dawo gidan sai ta fad'a."
Aysha tasa dariya tana fad'in"Ai dama ka dawo ne ka takura mana dole ka fadi haka mana.".
Yace."Kin san meke faruwa yanzu."? Girgiza kanta tayi tana saurarasa
Yace."Ga Azima can waje tana so ta shigo."
Aysha sai ta rasa wacece ma Azima sai tayu jimm! tana tunani gabanta ne ya yanke ya fad'i! Baki na rawa tace"Me!!! taz me tazo yi mana a gida kuma."!?
"Kinga Aysha kwantar da hankalinki ba komai tazo yi miki ba sai ya fad'a mata yanda abun ya faru da dalilin da ya sanya Azimar zuwa ofis din sa.
Ajiyar zuciya ta sauke ta nemi guri tana cin magani! Yace." Matsalata dake kenan aysha na fad'a miki ba wani abu ya kawota ba hakuri zata baki amma kin wani 'bata rai kina d'acin zuciya ni a yanzu ko d'aura min mace akayi a 'kafafuna zan kwance na yar na gudu ku kad'ai kun isheni rayuwa a baya ma rashun godiyar Allah ne."
Ta kalli tare da dan sassauta fuska tace"Nifa ba wani abu nace ba kawai don na zauna sai ka fassara ni kaje ka shigo da ita."
Ya juya ya fita yana mamakinta wai aysha ce zata fad'a masa wata magana wanda ko 'kifta ido tayi ya san abinda take nufi yana tunanin yanda ya santa ita bata san kanta ba.
A hankali keken ya shigo palon Omar da kanshi yake taimaka mata Aysha na kallonsu har suka 'karaso....Wani irin imani yazo mata ganin yanda Azima ta lalace ta zama musaka babu kafafu tabbas ta yarda Allah abin tsoro ne.
Azima na kuka Aysha na kuka haka Safarau ta fito daga dakinta ta same su.
Ganin wata a zaune kan keken guragu kamar ta santa ya sanya ta kalli Omar din tana masa nuni da hannu.
Yace."Azima ce tazo ku gaisa sannan ta nemi yafiyarku.
Safarau ta zauna kusa sa aysha da kyar yanzu ganin Azimar ya sake tayar mata da ciwo duk ta tsorata ta kalli aysha a nutse tace"Aunty Aysha don Allah ki daina kuka ki saurari Azima da abunda tazo dashi Allah na muna yi masa laifi amma yana yafe mana.Autyn ban sanki da wannan ri'kon ba ki daure ki saurari Azima tunda har ta tako tazo inda kike.
Aysha ta kauda kanta ba tare da tace komai ba Azima kam sai matsar fuska takeyi abun duniya duk ya isheta ganin irin yanda Allah ya mai da aysha hamshakiyar mace sannan ta fuskanci har yanzu Omar na rawar jiki a kanta sannan ta lura yanzu zaman su da Safara'u sai wanda ya gani domin ma irin atamfa daya ce a jikinsu dinki iri daya ta tabbatar yanzu zaman lafiya gami da kwanciyar hankali ya samu a cikin gidan Omar nadama mai tsanani ta baibayeta.
Wasu zafafan hawaye ta goge murya na rawa tace "Kawata gurinki nazo domin in nemi gafara akan dukanin abunda nayi miki wallahi aysha sharrin shaidan ne kawai da son zuciya irin nawa ni nasan Mijinki yafi karfina amma saboda tsabar son zuciya nabi boka na bi malam sai da na janyo hankalinsa gareni ya aureni duk dan in muzguna miki amma da yake al'amarin babu Allah a ciki bai je ko ina ba ya ruguje kinga dai yanda Allah ya mai dani musaka babu kafafu ina yawo kan keke me yafi wannan nadama." Kuka take wiwi! Tausayinta ya sanya Aysha da Safarau share hawaye Azima ta cigaba da cewa"Babu shakka Allah ba azalimin sarki bane gashi lokaci guda ya nuna min ni ba komai bace a duniya ya nuna min iyakata shiyasa kullum nake neman gafara a gurinsa da kuma gurin wanda na zalinta Aysha ina neman gafara a gurinki dake da Safarau ku gafarta min don Allah."
Aysha tace"Azima ki daina kuka ki fawwalawa Allah al'amarin ki hakika Allah yaso ki da har ya fargar dake kika gane gaskiya da wuri ni aysha baki min komai ba ke idan ma kinyi min to Wallahi na yafe miki Allah ya yafe mana gabakidaya."
Azima na share hawaye take godiya......Hira suka d'anyi sannan Azima tace zata koma gida.
Aysha da kanta ta tura kekenta har suka fita harabar gidan Omar ya bude mota cikin dubara ta taimaka mata ta shiga daya daga cikin masu aiki gidan ya kwance keken nata ya sanya a boot Omar yaja motar ya nufi gidansu da ita.
Da daddare da ya dawo sai ya dinga tsokanarsu wai ko ya dawo da ita ne yaga suna da tausayi da jinkai tunda har kuka sukayi mata ya kamata su bashi kofa kawai ya dawo da ita su zauna su uku.....Yana tsokanarsu yana dariya sai da yaga mutuniyar tashi taci kunu sannan ya shiga taitayinsa.
To cikin ikon Allah rabar Lahadi da Safe Safarau ta haihu a cikin dakinta tare da taimakon Uwargidanta aysha Safarau ta haifi kyakykyawan yaronta mai kama da ubansa kaf 'yayan Omar kamaninsa suke daukowa da alama ya fisu karfin jini
Aysha ita ta yanke cibiya ta gyara yaro ta shirya shi tsaf kana ta hadawa Safarau ruwa mai zafi ta taimaka mata tayi wanka ......Lokacin da duk wannan abun yake faruwa mai gidan baya nan ya fita da wuri can gidan sarautar ya nufa domin dama duk ranar da babu aiki to can yake wuni a Fada yana gudanar da harkokin da suka shafi sarautarsu Maimartaba yanajin dadin yanda Omar din ya iya mulki da iya gudanar da sharia shiyasa yaci alwashin nan gaba zai umarce shi da ya aje aikin kawai ya dawo gida ya jagoranci al'umma.
Ikilima da Atika sune suka gyara ko ina na gidan sai kamshi turaran wuta yake Aysha ta kira waya gida ta shaida musu Haihuwar kana ta kira wayar uban gayyar lokacin yana fada babu damar amsa waya hasalima wayar a kashe take tana can gurin mamashi dama duk sanda zai zauna a fada yana kashe wayoyinsa ne ya aje sai ya tashi sannan yake kunnawa.
Da jin wannan daddan labari sai gwaggo da Nanne Fulani Wannan karon harda Kulu da ta zama mujiya a cikinsu suka shirya tsaf direba ya daukesu suka nufi gidan Omar din domin su gano dan jinjiri.
Albarka da yabo ta ko wanne fanni aysha tasha daga gurin iyayenta Kulu sai ya'ke takeyi tana binta da kallo cike da sha'awa ita kuwa aysha bata nuna mata komai ba yanda ta sake da iyayenta haka ta sake da Kulu suna hira
Sai bayan sun tabbatar da lafiyar Safarau da jinjirinta sannan suka dawo gida cike da farin ciki mussaman Fulani da Nanne da abun yafi shafa.
Sai bayan sallahr isha'i ya samu labarin haihuwar daga bakin mahaifiyarsa Farin ciki mara misaltuwa ya shiga lokacin da ta sanar masa ya zube a gurin yayi sujjada ta godiya ga Allah. Kai, tsaye ya nufi gidan domin yaje yaga baiwar da Allah yayi masa Safaraun sa amanarsa ta haihu tarw da taimakon aysha wacce ta zama rayuwarsa gabadaya shi kuwa wane irin tukwuci zai yi wa aysha tabbas ta sake samun wani matsayi mai girma a cikin zuciyarsa.
****
Tafida
Tafida Direba Shine ya zama silar bayyanuwar iyayen Safarau yanzu haka kuma suna tare da Alhaji Lado shine yake jan sa a mota duk inda zashi yanzu ma shine ya kawo su garin kano ganin albarkar da suka samu.
****
Safarau tayi murna da farin cikin ganin Kawunta da matarsa gami da 'yayan uwanta bangare guda suka yada zango har sai da akayi suna sannan suka koma gida cike da murna da farin ciki Yaron Safarau yaci sunan Maimartaba Sarki Salisu aikuwa yaron ya samu gata gami da kyautuka ta ko wane fanni..........Safa ta cigaba da wanka tana kula da yaronta Jakadiyar Mama Fulani itake dauwainiya da ita Aysha na dan taimaka mata da wani abun....Kullum zaka same ta a sashen Safaraun sai yamma take komawa nata Yanda suke gudanar da zamantakewar su ko kai wanene sai kayi sha'awar su .
Safarau nayin air'bain ta gudu bauchi ta bar aysha da kewa Ita sai ta tsiri zuwa gida yau idan ba taje gidan sarautar ba to gobe sai taje Omar kam yana son suk abunda take so shiyasa baya hanata wataran ma shi da kansa yake kaita kafin ya wuce aiki idan ya dawo yaje ya daukota su dawo gida.....Kullum sai sunyi waya da Safarau da rana da dare sannan take jin dadi to bangaran Safarau ma hakane duk kewar aysha da mijinta ya isheta sati biyu kacal tayi tace gida zata dawo da kyar Hjy Abida ta rarrasheta ta hakura ta kara sati guda to a cikin satin ne suke je can garin iyayen nasu Safarau taga dangi dangi suka ganta masu kuka nayi masu mamaki nayi wai dama ashe zasu ga jinin abdu a duniya Allah kenan.....Lokacin da zasu dawo suka hado mata tsaraba iri-iri irin ta kauyw sukace sunanan zasu zo suga dakinta kuma su gaisa da Sarkin Kano Salisu.
Koda suka isa bauchi kwana biyu kacal ta kara tace gida zata koma ita Alhaji Lado ya dinga rarrashinta ta tubure dole ya shirya da kansa ya dauketa a mota ya kai ta har dakinta kana ya dawo gida cikin iyalinsa.
Ranar da ta dawo Aysha tayi ta murna suka rungume juna Aysha ta dauki Al'amin tana fad'in"Me kike bashi a can ya girma haka." Safa tace"Auntyna kenan me kuwa nake bashi nono ne kawai wallahi yaron akwai tsotso sai ya kwana da nono a bakinsa baya gajiya."
Aysha tayi dariya tace."'yan uwansa masa haka suke da wannan tsotson.
Omar da wuri ya dawo gida amarya Safarau ta dawo ya barje guminsa Aysha kam dama tunda taga ya dawo da wuru tasan abunda yake wa ta dinga zabga masa harara ko kunya bayaji sai rawar jiki yake
Itama Safaraun ta gane abunda yakewa kawai sai ta shareshi ta nemi guri ta zauna suna ta hira da Ayshan da yagaji da saka musu baki cikin hirar kawai sai ya mike ya barsu dakin aysha ya shige ya kwanta bacci ya daukeshi.
Aysha ta kalli Safarau a nutse tace"Ina fatan dai kin shirya kanki sosai da sosai ko? domin wannan mutumin yanda na lura dashi yau zai fatattaki duba ki gani don Allah har da dawowa gida da wuri."
Safa tasa dariya tace"Wallahi aunty ni babu wani shiri da nayi nima na lura dashi kai!!!! Ni ban ta'ba ganin mutum mara hakuri ba irinsa ba wallahi."
Aysha ta mike da kyar! tace"Ina zuwa."
Dakinta ta shiga ta tarar yayi rashe rashe a kwance ya kasa bacci domin da ya fara zai mafarki gashi yana sex sai firgita ya bude ido Saurin kauda kai tayi ta fara duba abunda ya shigo da ita dakin......Ya mike ya isketa inda take tsaye ya rungumeta kam yana sansanata tunda cikinta ya tsufa ta daina sakar masa jiki shiyasa sha'awa tayi masa yawa.
Cikin kulawa tace"Kaje gatacan ta tafi part dinta nasan abunda ke damunka kenan."
Girgiza kai yayi yace."Na hakura Ayaha naga kamar zan takura mata in bari ta huta gajiya ko."?
Harara ta watsa masa.....Sai yasa dariya yana shafa sajansa tace"Kaine zaka hakura wallahi ko suma kaga tanayi a yanda kake a haka sai ka biya bukatarka.....Yace."Banda suma dai aysha wai me kika daukeni ne."!? Tana tafiya tace"Abunda ka dauki kanka."
Murmushi kawai yake yana binta da kallo har ta fice daga dakin.
Wani magani ne na mata mai kyau ta bata tace "Kina zuwa sashen ki ki hada da madara kisha insha Allahu kafin awa guda maganin zai bi jikinki karki yarda ya kusance ki har sai kinji sauyi a jikinki."
Safarau ta karbi maganin tana godiya ta nufi part dinta
*****
Yunusa da Ashiru sun dawo gidan Omar da zama inda Tsohowar mai'aikinsu Nafisa itama ta dawo gidan da zama bangaran su Ikilima kenan, suna zaune cikin kulawar mai gayya mai aiki a haka har soyayya ta shiga tsakanin Yunusa da Nafisa Ikilima da Ashiru Omar yaji dadin kasantuwar wannan al'amarin sai ya zame musu uba jagoransu sai da ya tabbatar da ya kulla auran sannan hankalinsa ya kwanta gidaje masu kyau ya siya musu ya zuba musu komai na more rayuwa kana ya basu jari ko wanne ya nemi na kansa ya tsaya da kafafunsa.....Yunusa da Ashiru suka rasa bakin godiya addua da fatan nasara kawai suke masa....Omar yasa aka kawo masa wasu sabbin ma'aikatan.
Rayuwa kenan duk abunda yayi tsanani maganinsa Allah kuma dukanin mugun halin mutum tilas zaka same shi da kyakykyawan hali ko guda daya ne......Aysha yanzu ta zama kamilar mace cikakkiyar mace mai dattako ta zama garkuwa a gidan Umarulfaruk Aysha ta zama garkuwa ga 'yar uwarta Safarau wance ta dauke a matsayin 'yar uwa ba kishiya ba rayuwa sukeyi mai tsabta da inganci.
Aysha ta haifi yara shida hudu maza biyu mata.
Abdullahi Sa'adatu Safarau Ahamad Wanda yaci sunan mahaifinta galadima tana kiransa da suna (Danbaiwa) Sai kuma Usuman da yaci sunan Waziri Suna kiranshi da (Magajin gari) sai aunta Sunusi mai sunan tsoho kenan shi kuma suna kiranshi da (Fahat) Safaru kuma irin haihuwar ra'kuma takeyi domin bayan haihuwar Mai sunan Sarki Salisu sai da tayi shekara bakwai kafin ta sake haihuwar da namiji inda Omar ya sanya masa sunan Kawu Lado wato Al'amin......To yanzu haka karamin ciki gareta tana ta burin ta haifi 'ya mace.
Bayan shekaru goma da suka wuce. Wadata da kwanciyar hankali ta samu a gidan Omar inda ya tattara kan iyalinsa suka nufi kasa mai tsarki domin suyi addua ga Allah da ya rayasu yayi musu ni'ima da ba kowa yake wa irinta ba......Satin su uku a kasar saudia sukayi nufo gida cikin aminci da yarda da juna.....A washe garin ranar da suka dawo aka tashi da Azimi sai suka fara ibada da tsarkakkiyar zuciya duka suka mika lamuransu ga Allah......Babu ranar da zata zi jama'a basu dafifi da kafa layi a kofar gidan Omar ba suna kar'bar sadaka ta abinci ta suttura ta kudi da sauran abubuwan bukata Addua daga bakin mutane Omar da iyalinsa suna samu al'amarin dai sai godiyar Allah.
Alhamdullahi
Alhamdullahi
Alhamdullahi
*To Hausawa sukace komai yayi farko yana da karshe jama'a nan na kawo karshen wannan littafi mai suna Sadauki Omar! ina rokon Allah ya yafe min kusakuraina dake cikin littafin ladan dake ciki kuma Allah ya sadamu dashi dani da ku masoyana.*
*GODIYA TA MUSSAMAN*
GARE KU
H.Rabi 'Kofar bai
Momyna Fatima Musa Nijar
Rahima Aliyu Abuja
H.Nasiba Saleh
Khadija Husaini
Binta Isa Umar.
Sistar Zahra Kaduna.
Jamila Yusha'u
Maimuna bichi
Nafisat Ahamad
Dota Zainab Khabir Ishak
Dota Maryam Salihu
H.Surayya
Sistar Jamila
H.Jamila Abubakar
H.Rahama Tanimu
Aunty zeey kazaure
H.Fatima Zahra
Da duk wanda ban ambaci sunansa ba duk ina mika godiya ta a gareku ubangiji Allah ya bar kauna nagode kwarai da kuka 'bata lokacin ku kuka tsaya gurin karanta wannan littafin ina fata zakuyi amfani da darusab dake cikin littafin ku watsar da mara amfanin dake ciki nagode kwarai.
Sai mun sake saduwa daku a cikin sabon littafina mai suna..........
*NI DA YAYA SADAM!*
Humm! Wannan littafin yazo da sabon salo mai ban mamaki! kada ki/ ka sake a baku labari *Ni da Yaya Sadam!* Littafin na dauke da soyayya tsantsa bandariya sangarta shashanci kuruciya miskilanci Sadaukarwa Hakuri kawaici kai littafin ya na tattare da abubuwa da dama wanda sai wanda ya gani ko ya karanta shne zai fahinta don haka kar ku sake a baku labarin wannan littafi yanan tafeee!!!💃🏻💃🏻💃🏻
22/5/2020
*BINTA UMAR ABBALE*
Kika futar min da book Allah ya isa/! kika karanta baki biya ba kema Allah ya isa in kina bukatar karantawa to ki same ni ta wannan numbars din
07084653262_08089965176