Author : Binta Umar Category : Complete Novels
musu kofar motar suka shiga ya zauna mazaunin dravar da kansa yaja su suka nufi asibitin da aysha ke kwance.
Lokacin da suka isa asibitin aysha bacci take sosai Dr Hamisu ya jagorance su zuwa dakin da take to ganin halin da ayshan ke ciki ya sanyaya musu jiki Galadima mahaifinta ma ya shiga halin damuwa gami da dana sani hukuncin da ya sanya omar din ya yanke kan ayshan ai hannuka baya ru'bewa ka yanke ka yar! futa kawai yayi daga dakin ya bar Maimartaba da Waziri dashi Omar din suna kara tambayar Dr yanayin jikin nata. Dr Hamisu yace."Jikinta alhamdullhi domin muna sanya rai idan ta tashi daga wannan baccin zata dawo normal sai kuma abunda ba'a rasa ba sai dai kuma tana bukatar nutsuwa da kwanciyar hankali domin bunkice ya nuna tana cikin fargaba da damuwa da alama akwai abunda ke damunta."
To dukaninsu sun san abunda ke damun Ayshan don haka tsakaninsu da ita addua ce kawai......Sarki! Da Waziri sun jima a dakin kafin su fito daga d'akin ko wanne na dauke da damuwa kan faruwan al'amarin.
Can dakin da babys din suke suka nufa gabakid'ayansu yaran an shiryasu gwanin sha'awa suna cikin kaya iri d'aya sai bacci suke....Sarki ya daukesu daya bayan daya yayi musu addau yana cike da farin cikin wannan baiwa da Allah yayi masa.
Kowa sai da ya dauki babys din yayi musu addua Omar ya kasance nakarshe gurin daukar yaran ya jima yana musu addua sannan ya mi'kawa nurses din yaran ya kama hanya ya fita daga dakin, yayi murna da samunwar yaran amma idan ya tuno abunda ya afku sai yaji komai na duniya ya gundireshi ya zaiyi ne da wannan kaddara komai ya samu bawa to da sanin ubangiji amma kuma wani lokacin dan adam shike janyowa kansa shiga matsala sai daga baya kuma yazo yana fad'in Allah ne ya jarrabeshi.
A ranar dai haka kowa ya kwana zuciyarsa babu dadi Safarau da gwaggo da Jakadiyar Nanne sune suka zauna asibiti tare da aysha har garin Allah ya waye babu wacce ta rintsa a cikinsu fargaba da damuwa duk sun damesu mussaman safarau sai tuno rayuwar da sukayi da aysha takeyi shikkenan duk wannan ya shud'e yanzu zata sauya sabuwar rayuwa da zama da wata kishiyar ba Aysha ba a zaman da sukayi da aysha sam bata dauketa a matsayin kishiya ba sai 'yar uwa domin ba karamin 'karuwa take da ayshan ba ta fanni zamanrakewar aure tasab ayshan tafi ta dubara a nan tayi mutukar 'karuwa da aysha kuma bata ta'ba tsammanin tana da saukin hali ba sai da Allah ya dai-daita tsakaninsu tana gani itama watarana abunda Omar yayiwa aysha 'yar uwarsa to zaiyi mata wanda yaci uwar nata dole ne tayi taka tsantsan! idan da hali ma itama ya sawwa'ke mata kawai sai ya zauna da 'yar gwal.
To alhmdullhi aysha ta samu domin da tashi garau ta tashi Dr ya shigo ya dubata sosai shima yayi farin ciki ganin ta sake kuma da ya dubata yaga ta rage damuwa sai yace su Safaraun su zauna su d'ebe mata kewa........Cikin hikima da dubara irin ta mutanan da gwaggo take rarrashin ayshan da nuna mata misalai iri-iri da kuma nuna mata muhimamcin hakuri a rayuwa, Sosai nashihar gwaggon take ratsa tace"Gwaggo abubuwan da sukayi ta faruwa tsakanina da Omar na sani wallahi akwai halina yanzu nake sake gane ya rayuwa take yanzu nake da nasanin abunda na aikata a baya hakika nayi amfani da damar da na samu a baya na aikata ba dai-dai ba amma insha Allahu zan kiyaye gaba kuma zan dinga mayar da komai ba komai ba a rayuwa gwaggo yanzu bana nadamar auran Omar da kawata Azima Allah ya sanya alkairi ya basu zuria mai albarka....Tsabar tausayin aysha ya sanya gwaggo share hawaye tace"Yawwa aysha haka nake so ki zama nutsatstsiyar mace mai sanin ya kamata ina mai tabbar miki da cewar dukkanin abunda aka ginashi kan turba mata kyau hanya ta cin amana to baya wani tasiri zakiga gaskiyar lamari ya fito kinanan a zaune za'a dawo gurinki ana nadama to kinga hakurin ki yayi riba ko kuma baki sa'bi Allah ba, shi namiji idan yace zaiyi aure zuba masa ido akeyi domin a irin wannan lokacin duk abunda za'a fada masa ba zai dauka ba, ke idan kika tsananta ma auranki sai ya mutu kamar yanda ya faru akanki saboda haka irin wannan abu bama fatan ya sake faruwa a tsakaninku aysha kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki ki koma dakin mijinki ki rungumi 'yayanki dakin mijinki shine yafi miki daraja da mutunci."
Aysha tayi murmushi mai ciwo tace"Gwaggo ba zan iya komawa inyi zaman aure da Omar ba har a zuciyata nake jin na rabu dashi har abada hakan ba yana nufin na 'kullace shi ba wallahi ko d'aya kawai na hakura dashi Zan raini yarana har su girma idan da akwai rabon na sake aure sai nayi amma na hakura da zama da Omar."
Safarau tace"Haba aunty Aysha ashe dai baki hakura din ba, ko wane d'an adam yana kuskure a rayuwarsa wallahi shima na tabbata ba'a son ransa haka ta faru a tsakaninku ba, kuma a halin yanzu yana cikin nadama kiyi hakuri don Allah ki dawo mu cigaba da zama da juna aunt aysha."
Aysha shiru tayi kawai ba tare da ta sake cewa komai ba, nurses suka shigo dauke da babys Gwaggo tace"Har sun gama baccin kenan."? daya daga cikinsu tace"Eh gashi an shiryasu yana da kyau mamansu ta gwada basu nono su sha." Gwaggo tace"Gaskiya kam ai sunyi hakuri ma....Safarau ta kar'bi d'aya gwaggo ma ta kar'bi daya....Daya daga cikin nurses din ta d'an gyarawa Aysha zamanta ta kar'bi d'aya ta ra'ba mata a jiki Safarau ta taimaka mata suka ciro nono suka sanyawa yarinyar a baki aikam ta kama tana tsotsa aysha tace"Wai wacece babba a cikinsu."
Narse din tayi murmushi tace"To Allah ne masani wanda dai aka fara cirowa ita za'a kira da babba." Gwaggo tace"Bari ki gani ni zan gane wacece babba idanunsu take kallo duk iri daya komai nasu iri daya hatta da 'yan yatsu tace"Anya zan iya ganewa kuwa wannan ai sai su dinga rikita mutane domin kamaninsu yayiwa." Safarau tace"Tabbas gwaggo amma kuma kamar wannan ta hannuna tafi haske ita waccen tana da duhu ko." ? Narse din tace"Kwarai kuwa tanan ma za'a iya ganesu." Aysha kam mirmushi kawai takeyi tace"Gwaggo a bani d'ayar na bata tasha itama." Narse din ta kar'bi wacce take hannunta gwaggo ta d'ora mata wacce take hannunta.....Shayar da yarinyar take tana kara jin kaunarsu cikin zuciyarta ta d'ago kanta tana kallon gwaggo tace"To tunda an kasa gane wacece Hasana ni zan sanja musu suna dama gwaggo kin ta'ba fad'a min cewar idan na haihu a gaba ina da 'yancin sanyawa yara na suna ko."!?
Gwaggo tace"Aysha yaushe mukayi wannan maganar!?bana son neman fitina da." 'Yar dariya tayi kad'an tace"Gwaggo kin manta ne amma wannan maganar tamu dake bai wuce shekara biyu ba." Gwaggo tace"To aysha na manta ne ai." Gwaggo na sane take bagarar da maganar saboda tasan halin ayshan da neman fitina da tashin hankali son samu a barwa yaran sunansu wato Hasana da Husaina.
"Safarau ta kalla a nutse tace" Safa nayi miki takwara da wannan dake hannunki insha Allah sunanta Safarau." Cike da farin ciki tace"Da gaske aunty! wayyo naji dadi wallahi na samu takawara auntyna nagode sosai." sai ra rungume yarinyar a jikinta tana goge hawaye.
Tace"Gwaggo ita kuma wannan taci sunanki Sa'adatu." gwaggo tace"To maddalah ina godiya da wannan karamcin aysha Allah ya raya masu tafarkin addinin isalama." Aysha ta amsa da 'ameen tana jin kaf duniya bata da masoya kamar gwaggo da Safarau tunda sune suka tsaya kan al'amuranta.
****
To can Gidan sarautar kuwa al'amura sun soma daukar zafi domin angwaye dai sai kai kawo suke tare da abokansu gida ya dauki harami jama'a ba'a magana jama'ar Kawun Azima ma duk nan suka had'u Sarki ne ya bada umarin haka sai da jama'a suka hallara tukkuna aka fara daurin aure.
Auran Omar aka daura da Axima kan sadaki dubu dari sannan aka daura auran Faisal shima sadaki dubu dari daganan sai limami yayi addua tare da fatan zaman lafiya ga amare da angwaye jama'a suka fara shiga Fada domin mi'ka gaisuwarsu......Sai bayan da aka daura auran ne ya samu nutsuwa hankalinsa ya dawo jikinsa ya tuna da Aysha a asibiti.....Nan yaja tawagar abokanshi na gurin aiki da suka samu damar hallatar daurin auran suka nufi asibiti domin duba ayshan.
Kan idonta suka shigo dakin sun kai su bakwai ko sama da haka, suka gaisa da gwaggo suna tambayar ta mai jiki tace"Jiki kam alhamdullhi har bakin gadon da take kwance suka karasa suna gaisheta da jiki, Aysha ta sanya dauriya a ranta tana amsa musu ba tare da ta nuna komai ba...shi kuma ganin haka sai ya dinga gabatar mata dasu da sunayensu d'aga kai kawai takeyi ba tare da tace komai ba......Ya karasa inda Safarau ke zaune ya kar'bi Yarinyar dake hannunta ya mika musu sai wani washe baki yake yana fad'in "Allah ya albarkace ni da samun 'yara kyawawa masha Allah yanzu burina mamansu ta samu lafiya....Sulaiman dake mutum ne mai barkwanci yace." Kai Yalla'bai gaskiya kai d'an gata ne ga sabon aure ga kyautar babys masu kyau to Allah yasa shekara mai zuwa mu dawo mu dauki irin wannan guda biyu." Sai kawai suka d'auki dariya gabakid'ayansu har dashi......Sukayiwa aysha alkairi sosai kana sukayi musu sallama Bayansu yabi yana baza babbar riga.....Gwaggo da Ayshan da Safaraun suka bishi da kallo cikin d'umbin mamaki! Gwaggo tace."Babu shakka! dubeshi don Allah!! wai dariya ma yakeyi oh! ni Sa'adatu namiji komai 'kan'kantarsa namiji ne sai yayi halinsa."
Safarau tace"Ni gwaggo baki ga ma na kasa cewa komai ba hummm."!!! Aysha kam rintse idonta tayi tana jin wani irin kunci cikin zuciyarta Wai Omar ne ya gayyato abokanansa suka zo suna yar mata da magana rayuwa kenan! ai idan shine kad'ai ne yayi saura a duniyar nan ta hakura dashi har abadah.
Dakin ya dawo fuskarsa a sake yaji dad'in ganin ayshan ta samu lafiya ba kamar jiya ba, shine dalilin da ya sanya walwalarsa ta 'karu ya tsaya gefan gadon yana tambayar gwaggo yanayin jikin nata tace"Jiki alhmdullhi ai gatanan kana kallo mu kam mungodewa Allah." Sai ta mike ta bar dakin.
Shiru ya ratsa tsakaninsu Safa tace"Hala an daura auran naga sai washe baki kake kamar anyi maka albishir da gidan aljanna."! Ya kalleta a nutse yana nazarin maganarta ganin irin hararar da take kwad'a masa ne ya sanya ya d'auke kansa ya mayar kan Aysha...'Kasa-'kasa yace."Gimbiyar mata aysha ya jikin naki ina fatan dai babu wata matsala ko."!? Aysha ta d'aga kanta ba tare da tace uffan ba.
Safatau taja tsaki tana watsa masa kallon raini tace"A'a ina kake kiran gimbiya anan? ai duk gurin nan babu gimbiya kaje dai can ka nemi gimbiyarka."
Yace."Ke kuma meye haka Safa! duk me ya kawo wannan maganar ne? tsakanina da aysha akwai kyakyawar fahintar juna mun fahimci junanmu tun jiya idan kika ce zaki shiga abunda be shafeki ba zaki sha wahala ne."!
Ta'be bakinta tayi ta kauda kanta....Sai ya ja karamin tsaki ya mai da hankalinsa kan Aysha duk ya rasa ma abunda zai ce mata. Yace."Aysha ina fata dai babu wata matsala ko." ? ta bude idonta tana kallonsa a nutse tace"Me ya dame ka da abunda ya shafeni ina ce yanzu baka da hurumi da abunda nake ciki saboda haka ni bana son damu da takura kaje kawai ka cigaba da sabgarka Allah ya sanya alkairi."
Ya zauna kusa da ita yana tattare babbar rigar dake jikinsa hanninta ya rike a sanyaye yace."Wannan maganar banji dadinta ba aysha nine nake da hurumi dake da dukanin abunda ya shafeki saboda har yanzu kina a matsayin matata ta sinna kinga kuwa dole in damu da halin da kike ciki."
Ta kalleshi tare da sakin murmushi na karfin hali tace"Bayan ka sakeni kuma kake maganar ni matarka ce ta ina na zama matarka." ?
Kansa ya dafe yana jin wani irin kunar zuciya yace."Bana so kina 'kara tuna min da wannan mummunar 'kaddara aysha ba laifi na bane? amma ai ina furta kalmar saki a gareki nace na janye aysha har yanzu ke d'in halaliyata ce."!
"Humm." ! Abunda tace kenan domin bata kaunar wata magana me tsayi ta sake had'asu sam bata yarda da wannan 'kaulin ba tunda ya saketa ta haihu to ta bar hannunsa har abadah."
Maganganu yake mata yana sake bata hakuri da rarrashinta kan ta kwantar da hankalinta a tsakaninsu komai ya wuce kaddara irin wannan baza ta sake faruwa ba." Aysha dai shiru tayi masa......Safarau ta mike zata fita ya kira sunanta cikin wata iriyar murya jiyowa tayi tana watsa masa harara yace."Zo ki tayani rarrashinta.....Girgiza kanta tayi ta bude kofa tayi fucewarta wani irin haushi yake bata ta lura shi mutum ne wanda ya fiye son kansa da yawa.
[6/6, 9:10 AM] Bintu Novel: l73
Bin ta yayi da kallon mamaki har ta futa daga dakin. Ya lura Safaraun ta dauki al'amarin da zafi wanda a ganinsa abu ne da bai shafeta ba zata ara ta yafa har tana kokarin yi masa rashin kunya abunda bai ta'ba faruwa ba a tsakaninsu dole ne ya taka mata burki kan abunda takeyi domin tana nema kuma ta wuce makad'i da rawa a yanzu kuma sai yaji ya tsani kyakykyawar ala'kar dake tsakanin Safaraun da Ayshan don da kansu ba a had'e yake ba yana ganin da duk haka baza ta faru ba zai samu sassauci ta 'bangaran Safara'un....To koma dai menene aikin gama ya riga ya gama a yanzu duk wani abu da zasuyi sai dai suyi su gaji su hakura don aure an daura shi, a halin yanzu bashi da wata damuwa kuma sai ta aysha burinsa bai wuce ta samu lafiya ba ta koma dakinta tunda dai Allah ya taimakeshi yana furta kalmar sakin ya janye shine babban abunda in ya tuna yake godewa Allah yasan da bai yi gaggawar mai da ita ba ta haihu to da akwai matsala babba a gareshi.
Cikin wani mayaudarin kallo ya juyo da fuskarta yana narke mata shanyayyan idanunsa da wata iriyar siga ta yaudara irin tasa yace." Aysha ko a mafarki ban ta'ba tsammanin zan auri wata ba bayan ke! banta'ba tsammanin zan auri 'kawarki ba Aysha! ki sani duk abunda Allah ya kaddarawa bawansa to babu makawa sai ya faru ban auri 'kawarki domin na tozarta ki ba aysha har abadah tsakanina dake babu cin zarafi ina so ki sanya a zuciyarki cewar Omar bai iya yin rayuwa sai dake dani da duk wani wanda ke 'kar'kashina kece walwalarmu idan babu ke aysha nima babu ni! Na ro'ke ki kan wannan abu da ya faru a tsakanimu ki mayar dashi kaddara karki 'kullace ni aysha! domin nima ba'a son raina na furta wannan mummanar kalma a gareki ba, nasha fad'a miki tsakanina dake babu saki bare yaji don haka ina so ni dake mu kashe mu binne mu magance matsalarmu."!!
Maganganunsa sun so su kashe mata jiki saboda yanda yake wani sassauta murya yana matsa mata hannu yasa ta d'an ji tausayinsa amma bata nuna masa ba ko a fuska.....Ta motsa kad'an tare da zare hannunta dake cikin nasa a nutse tace"Yanzu an dai d'auran auran ko."!?
Yace."An d'aura Aysha ko akwai damuwa a ciki nifa idan kikace bakya so wallahi zan iy.......! kafin ya 'karasa ta katse shi ta hanyar d'aga masa hannu kallonsa take cike da mamaki! Lallai Omar ya raina mata hankali wai ita zaiyi wa barazana mtwwww!!
"Ni dai ban ce komai ba cewa nayi an daura aure sai kace " Eh an daura ba sai kaja wata magana." Shiru tayi tana dan sauke numfashi kana ta cigaba da cewa " Ai magana ta 'kare kuma ni dakai kar ka 'kara tunanin zan sake zaman aure da kai! Wallahi na gama har abadah yanzu babu abunda ke gabana illah in samu lafiya in raini 'yayana ina so ka cire aysha daga cikin rayuwarka....duk abunda kake so na fahimta na fahimta kuma yanzu nagane cewa kaddara ce ta sanya ka auran Azima kamar yanda ka fad'a to yanzu ma ina so ka jingina abunda ya faru a tsakanina da kai a matsayin allon kaddara.......Ka saki Aysha Allah ya musan ya maka da wata matar saboda haka ni bani da wata damuwa a halin yanzu kuma kar kayi tunanin zan'kullace ka a cikin raina ko d'aya zan ta d'aukar abunda ya faru a tsakaninmu a matsayin kaddara Allah yasa haka shi yafi alkairi."!!
Ya lalubi hankici cikin aljuhunsa ya tsane gumin fuskarsa kana ya dago kansa yana kallonta a halin yanzu kunyar had'a ido yake da ita saboda yanzu ya lura duk wani abu da zai fad'a ba zaiyi tasiri a gareta ba Aysha ta riga ta gama fahintar son zuciyarsa ne yasa ya auri kawarta, wanda shima wani lokacin idan ya zauna sai yayi ta nazarin al'amarin wani sashe na zuciyarsa yana fad'a masa cewar abunda ka aikatawa aysha bai dace ba....To sashen da yafi karfi a zuciyarsa shike 'kara tunzura shi da fad'a masa ai ba haramun ka aikata ba don ka auri kawarta zata iya mutuwa ma ka auri yayarta ko kanwarta saboda haka ka kwantar da hankalinka kishi ne kawai irin na mata idan tagaji zata daina.
Fuskarsa da akwai alamu na 'bacin rai! yace."Idan kina fad'ar wannan magana aysha sai naga tamkar wata jahila wacce bata da ilimin addini shin kin manta da cewar har yanzu kina a matsayin matata ko kina so ko bakya so akwai sauran igiyoyina a kanka saboda haka ki kiyayi furta irin wannan kalamai idan ba haka ba zaki shiga fushin ubangiji."!
Kallonsa tayi cikin wani irin yanayi tace"Kamar yaya? ban fahimci inda maganarka ta dosa ba yaushe ka janye kalmar sakin da kayi min? kaje ka zauna kayi tunani mai kyau ka bincika sosai shin tsakanina da kai wa za'a kira da jahili ni dai a iya sanina shine idan namiji ya saki mace da tsohon ciki daga ranar data haihu shikkenan ta 'kare iddah tana da damar tayi abunda take so ta kuma za'bi mijin da take son auran babu wani wanda