Advertisements
Chapter 1 Reading ZAKISAN KONI WAYE by ummu maryam BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ZAKISAN KONI WAYE by ummu maryam

Author :  ummu maryam Category :  Complete Novels

Chapter   1 / 44

1 to 3K   out of 130.5K words

VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching
this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.



We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction,
non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors



We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with
thier permission.



AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ?auke da littattafan hausa, dalilin
bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.



Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin,
soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu
a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.


ZAKISAN KONI WAYE

®zuwairat(ummu maryam)
1⃣

Ahamdulillah. Ya rabbi ya amshi ibadunmu. Happy sallah to all muslims.

Ban yarda wata ko wani ya maida wannan novel din document ba saida izinina.

Wata babe ce zaune cikin wani katafare falo wanda girmanta zai yi 100by100, fadin
tsarin falon is a waste of time amman kuyi imagining kyawun falon masu hannu da
shuni, budurwan sai kada kafa take da alaman ba gidan ta bane, kaman mai gidan take
jira. Wasu hadaddun designer english wears ne jikinta, sai kamshi take, da ganin ta
kaga wayayyun babe masu aji.

Bayan kaman minti talatin aka bude kofa, wata kyakyawa babe ta shigo, aikam afusace
wacce ke zaune afalon tamike fuskanta daure, ta nuna wacce ta shigo da dan yatsa
sannan tace
"wato mimi baki ji ko.." bata karasa ba wacce aka kira da mimi ta tuntsure da
dariya sanna tace
"ke uban wacece da zaki nuna ni da dan yatsa...ko kin manta ni fina na fiki tunda
ubana ba hannun efcc yakeba..banza karuwa.." bata karasaba taji saukan mari
"dan uwarki ni mate dinkice dazaki gayamin magana?...sau nawa nake gaya maki ki
rabu da slim...
." itama bata karasaba aka dauke ta da mari
"ke har kin isa ki rabani da slim..uban wa ke baisan ke kike binshiba?..kuma kowa
yasan duk big boys din abujan nan ke kadai ke binsu ...kariya" haba nan suka shake
junasu.

Sunfi minti biyar suna dukan junansu at the same time suna gayawa junansu bakaken
magagganu. Ni kam mamaki nake wanene wannan guy din da kyawawa yanmata ke dukan
junansu sabodashi. Fina rike gashin mimi tayi da niyyan janta waje amman weavon din
dake kanta ya cire, afusace mimi ta juyo tare da cire designer shoe din dake
kafanta ta wullawa fina, da sauri ta kauce ya sami wani katon canema dake jikin
bango nan take ta tsage. Itama fina cire nata takamin tayi ta wullawa mimi itama ta
kauce ya sami wasu glass decor dake kan dinning nan take suma sauka tarwase,
dukkansu babu wacce ta kalli barnan datayi suka cigaba da fadansu fina na cewa
"wallahi bari slim ya dawo....yau sai ya zaba tsakanina dake.." mimi da kanta babu
wani gashin kirki kuma fina ta cire karin datayi ta rike a hannunta gam, mimi sai
kokarin amsan brazilian hair dinta take tana cewa
"dalla bani weavon dina, don kudinta ya fi karfinki...."
"bazan badaba..ki tsaya ahaka har slim ya dawo ya ga kwalkwalin kanki". Itama mimi
kaman kan fina tayi ta fixge nata karin gashin. Nan take itama kanta ya bayyana.
Dukkansu biyu babu mai gashin kirkin amman kansu kyare suke . Da weavon mai suna
brazilian hair wanda kudinta yakai 600k suke amfani. Kowannesu klokarin amsan karin
gashinta take.

Afarfajiyan gidan wani katafaren gate ya bude, wasu manyan motoci kiran bentley
guda uku suka shigo gidan, wurin parking suka nufa, suna gama parking da sauri wasu
guys guda uku suka fito daga cikin motan gaban at the same time guys biyu suka fito
daga cikin motan baya suka nufi motan tsikiya, ahankali daya daga cikin guys din ya
bude murfin motan tsakiya. Wani hadadden kafa nagani sannan mai kafan ya fito,
wooooow, kawai nace don fina da mimi basuyi laifiba da suke cin abun junansu
sabodashi, don guy din tamkar shi ya hallici kanshi, wani suitmai tsada ne kwance
jikinshi , ahankali ya mika hannu ya amshi briefcase din dake hannun daya daga
cikin guards dinshi sannan ya sakar masu murmushiai bayyana hakora, wow nasake cewa
don wasu fararen hakora nagani tare da wushirya tsakiyansu. Nikam ban taba ganin
mutum mai kyau har cikin hakoraba don komai nashi wonderful
"alhajis na gode" naji yace, nikam wooow na kara cewa don muryanshi so cool and
gentle. Suma guys din murmushi suka sakar mashi, juyawa yayi yafara tafiya, yana
daga kai yaga wani range rover sport tare da hummer tsaye, nan take ya hada giran
kasa dana sama, don yasan masu motocin. Girman gidan yayi hecter daya, da akwai
manyan flat a farfajiyan gidan, amman wanda yafisu girma ya nufa, su kuma guys din
sukayi wani bangare daban.

Yana zuwa bakin kofan falonshi ya taddata bude, afusace ya shiga falon, adaidai
lokacin da su mimi da fina sukayi wa karin gashinsu kacakaca a falon, suna ganin
shi kowa yasha jinin jikinshi
"kam babban burouban nan!!!!! " saurayin ya fada a fusace, wanda yasani rasana don
yanda yayi magana sai ya firgita duk wanda ke saurarenshi, yacigaba dacewa
"who the fuck gave you bitchies permission to enter my house? " dukansu shuru
sukayi, ahankali mimi tace
"slim ni kake kira bitch? " ta fada tana nuna kanta, a fusace yace
"aa sugar badake nakeba da uwarki nake... I said uban waye ya bude maku falona? "
fina na gani ya watsawa mimi bakar magana ta saki murmushi tare da nufoshi tana
cewa
" habibi welcome " harara ya watsa mata tare dacewa
"gidan ubanki nazo? Banza yayan barayi" itama fina cewa tayi
"are referring to me" dan girgiza kanshi yayi sannan yace "da lankwaceccen ubanki
nake... Bazaku gayamin ubanda ya baku izinin shigowa gidanaba kafin insa guys dina
suci uban da ya haifeku? " fina tace
"ni na bude"
"who gave you my password? " ya kara daka mata tsawa
"last weekend da mukazo b day dinka na rike passwords din... Kasan am smart "
"kika rike passwords dina don in bana nan kizo kiyimin sata ko" ido mimi ta bude
"sata kuma slim... Ni kake cima mutunci haka? "
"eh mana... Ba sata ubanki yayi efcc suka kamashiba? Nasan ko kin gada?" fina
bata kara cewa komaiba ta koma baya, takalminta ta dauka da niyyan sakawa, itama
mimi designer hand bag dinta ta dauka, ajiye briefcase dinshi yayi gefen inda yake
tsaye tare da harde hannuwanshi kan kirjinshi yan kallon yanda fina ta duka ta saka
takalminta, mimi zuwa tayi zata wuceshi, ya fixgeta tare da wullata cikin falon
"where did you think you are going?... Ubanwa kuka barwa gashin doki chan" ya nuna
weavon din dake sakar falon sannan ya kara cewa
"in kun bar gidan nan sai kun gama gyaramun falona... Banzaye second hand bitchies"
irin fixgan da yayiwa mimi yasa batayi gardamaba ta koma tafara kwace karin
gashinta tare da maida tro pillows din da suka wullawa junansu. Magananshi kara
batawa fina rai yayi, bata kalleshiba tazo zata wuce inda yake, wani irin damka
yayi mata tare da turata baya
"safina kina son nuna min taurin kai ko?... To wallahi in baki gyaramin falonaba
dukan tsiya zansa ayi miki kuma kisan nothing will happen " murtuke fuska tayi
kafin tace
" gaskiya ko agidanmu ban aiki so yanzu ma bazanyiba" wani irin dariyan rainin
hankali yayi wanda ya kara bayyana kyauwunshi
"ai yarinya kwanda ki fara koya don satan da ubanki minister yayi aka
kamashi...bailing shi zai maidaku matsiyata..." bai karasaba ta yaji tace
"dadin abun ba ubanmu kowai ke barawon government ba.... " dauketa yayi da mari.
" kio ubanki baya magana in inayi balleke...." bai karasaba ya daga kai yaga cinema
dinshi fashe, wani ashar ya kara saki sannan yace
" wacece ta fasamin plasma! " ya fada afusace, fuskan fina murtuke tace
" nice ko abiyakane....tunda kasan ba matsiyaciya bace"
"abinda ya zama dolema..ai comfirm sai kin sa an kawo zaki bar gidan nan" batace
kara cewa komaiba ta kira bodyguard dinta dake waje ta sanar dashi yayi amfani da
ATM dake hannunshi ya sayo mata the largest plasma.

Fina kallon mimi dake tsaye tayi sannan tace
"malama kema ki kisa akawo mashi glass decor dinshi" sai lokacin slim. Ya kalli
wurin dinning dinshi yaga barna da sukayi mashi, still cewa yayi sai mimi ta
biyashi, itama bodyguard dinta takira yazo. Ciki ta bashi ATM dinta tare da nuna
mashi abinda zai sayo.

Har lokacin salem bai bar inda yake tsayeba, mimi da fina zuwa sukayi zasu wuce ta
inda yake, rike masu hannu yayi tare da kallon fuskan ko waccensu sannan yace
"meyasa kuke fada sabodani? " dukkansu babu wacce tace komaiba, yacigaba dacewa
" ko dan kudi da neman connection?" ahankali mimi tace
" haba slim why are you saying this.. Kasan ni badan wani abu naka nakesonka... "
itama fina cewa tayi
"kaima kasan i love you" dan tabe baki yayi don yasan karya suke
" naji...amman kuna iya fada saboda security ko wani mara hali? " dukansu shuru
sukayi sannan yakara cewa
".kuna iya bin mai gadin gidanku gidanshi?..." kaman hadin baki sukace
" i love you!! " suka juya tare dawullawa junasu harara, shi abinma dariya ya bashi
" naji...muje bedroom dina in nuna maku wani abu" su biyu kallionshi sukayi alaman
yana son kwanciya dasu lokaci. Babu kunya fina tace
"gaskiya slim i can't share you with her" ta fada tana nuna mimi, shidai baice
komai ba yacigaba da tafiya dasu har bakin wani katon kofa, daidai wani scanner
dake jikin bango ya tsaya tare da dukawa, abun yayi scanning idonshi, nan take
kofan yayi sliding gafe daya sanna ya shiga rike da hannun ko waccensu.


[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ♥❤💙
ZAKISAN KONI WAYE

♥💛
®zuwaira(ummu maryam)
2⃣
Suna shiga dukansu suka bude baki don tunda suke basu tabha ganin bedroom mai girma
da kyau irin nashibha don ana iya gina katon three bedroom flat da filin bedroom
dinshi. Sakin hannunsu yayi ya shiga bathroom dinshi ya daure alwallah ya fice daga
dakin ba tare daya kallesuba
Bayan sun dawo daga daga masjid direct inda cook ya shirya masu dinner kan carpet
suka wuce. Suna cin abinci suna hira, inkazo wurin baka gane waye oga don sai
dariya suke.
Around 8pm suka gama dinner still masjid suka koma don sallan ishai. Shidai salem
kullum bashi da aduan da yawuce Allah ya bashi mata tagari.

Suna dawowa suka zauna tsakar gidan wanda ke da haske tamkar rana. Su shida ne tare
da salem su bakwai. Hira suke suna daria, bayan kaman minti 30 daya daga cikin
guard dinshi mai suna Jibril yace
"sir in babu abinda zanyi maka ni zan tafi wurin madam,," dukkansu daria sukayi
"kaji masu iyali" inji daya daga cikinsu mai suna abdul.
"ai sunji dadinsu...inama ni" inji Salem, dukkamsu kallonshi sukayi sanna Jibril
yace
"sir ai kai ke bakason auren..don don nasan ko mata hudu kakeso kana iya aurensu
rana daya...tunda ga naira ga kudi" dan tabe baki Salem yayi sannan yace
" ai abinda bana so kenan...so nake in aure macen da zata soni don allah ba don
connection ko kudinaba" dan daria sukayi sannan daya daga cikinsu mai suna majid
yace
"ai sir da wahala ka gane macen dake sonka don Allah yanzu tunda ko wacce mace
pretending zatayi tana sonka don abin hannunka"
"kaji problem din" ya fada sannan ya kalli Jibril
" alh Jibril yaushe ka auri matanka" yace mashi don haka yake kiransu ALH
kasancewan dukkansu sunje hajj a sanadiyanshi. Ahankali Jibril yace
"Yanzu shekaranmu biyar da aure...dukda dai nasan mata kudi sukeso gaskiya sir
banda matata... Don sanda mukayi aure teaching nake a private school kuma albashina
15k.. " bai gamaba Salem ya kwalo ido waje tare dacewa
"alh Jibril 15k fa kace?:" ya fada with disbelieving voice " daga mashi kai Jibril
yayi tare dacewa
"yes sir.. " da sauri salem ya sake cewa
"ya mutum zai yi surviving da 15k balle har da mata? " dan murmushi Jibril yayi
sannan yace
"sir shi yasa nace matata is different don a wannan lokacin ita ke karfafa mani
gwaiwa...wallahi sir da akwai lokacin da zamu kwana babu abincin kirki...amman she
stands beside me with love" duk jikin Salem da sauran guys din yayi sanyi, ahankali
Salem yace
"inama ni.. " da sauri Jibril ya katseshi dacewa
"sir kar kayi fatan shan wahalan da ni da matata muka sha" ahankali Salem yace
"but you have true love..and it's among what matters most in life...i wish ina iya
samu macen da zata soni.. I can do anything for true love..don gaskiya ban iya aure
sai na sami true love " dukkan guys din shuru sukayi suna tunanin maganan ogansu.

Few seconds later abdul yace
"sir kaman yanda majid yace da kyar ka gane mai sonka, don ina tabbatar maka babu
macen dazata ki ka" yadan tsaya sannan yacigaba dacewa
"sir tunda kana neman true love... Ina da shawara... " dukkansu harda Salem suka
maida hankalinsu kan abdul
"am all ears" Salem ya fada mashi. Abdul shiru yayi ya kasa magana, don yasan Salem
baya daukan rubbish,
"kaifa nake jira... " Salem ya sake cewa. Shuru Abdul yayi for a while sannan yace
"sir abar maganan kawai" don yana tsoron abinda zai faru in har ya fadi abinda yayi
niyya
"ai baka isaba... Am listening " Salem ya ce mashi.
Sadakarwa Abdul yayi yafara cewa
"sir.. Da cewa nayi why not ka dan maida kanka talaka for a while.... " darian guys
din ya hanashi karasa abinda zaice, shi kam salem kallon Abdul yake ba kiftawa,
daga kai yayi ya kalli guys din, nan take sukayi shuru sannnan ya kara maida kanshi
wurin ABDUL din da yayi tsuru2 sannan yace
"alh Abdul taya zan maida kaina talaka bayan ni ba talakan bane... Please explain
your self " ahankali Abdul ya ce
"sir..ina nufin kayi disguising kanka... I mean kana iya maida kanka taxi
driver...." wani irin dariya dukkansu suka sakeyi, banda Salem daya hada giran sama
dana kasa, a hankali ya mike ya taka zuwa gaban Abdul sannan ya dafa gaban
goshinshi don tabbatar ba zazzabi yakeba. Jiya yayi temperature dinshi normal, shi
kam Abdul gabanshi sai disco yake.

Salem bai ce komaiba ya wuce side dinshi. Dukkan guys din kallon Abdul sukayi suna
cewa
"you fucked up... Yanzu kasa ran sir ya baci..."
Salem kam tunani yake ya sakar wa bodyguard dinshi jiki da yawa tunda abun ya fara
kawo raini tsakaninsu...
"wai ni taxi driver...hmmm i will treat your fuckup" ya fada yana bude kofan
falonshi, yana shiga agogon hannjunshi ya fara ringing cos waya ce, dan murmushi
yayi kasancewan yasan mai kiran don wakan sweet mother ne kawai ke tashi daga
agogon hannunshi, ahankali ya yi picking tare dacewa
"good evening first love... " bai karasaba naji wata irin sweet mature female voice
tana cewa
"son ka rainani ko?.. " da sauri yace
"first love kiyi hakuri..." matan ta katseshi da cewa
"keep quiet silly child...kullum am sorry.. Yanzu where are you?" Salem kan kujera
ya zauna yana shafa kanshi irin na mara gaskiya sannan yace
"first love ina ABUJA.. "
" me ka gayamin da safe? "" matan ta tambayeshi, ahankali yace
" umma cewa nayi zanzo yola yau... "
"to yanzu a yola kake? " matan ta sake tambayanshi, dan girgisza kanshi yayi
sannan yace
"no... Umma sai karfe eight na tashi daga off... "
"yimin shuru makaryaci... Nasanj dalilin dayasa bakason zuwa...don't worry zansa
abbanka ya zaba maka mata cikin family ko cikin yayan friends dinshi.... " sanin
halin ummanshi yasa shi saurin cewa
"wayyo Allah first love kiyi hakuri na kusa kawo mata...please don't talk to
abbah.. " ahankali matan tafara cewa
"love why are you treating me like this?... Ko don ka san you are my only
son?...sisters dinka suna chan gidan mazajensu kai kuma bazaka kawo min
yarinyaba?... "
"first love give me a little more time... Inshort ki bani maximum of five months...
In ban kawo mataba ki auramin kuturuwa..." darian ummanshi ya katseshi , shima
murmushi yayi
"habibi ka maidani kakanka ko.."
"no first love am serious.. Kibani wata biyar kawai...kinji please "
"naji..amman let your five months be five months.." da sauri yace
"yes umma" dan hira sukayi for about 20 minutes sannan sukayi sallama. Dan ajiyan
zuciya ya saki sannan yace
"atleast zan dan huta da fadan mom na wata biyar... " relaxing yayi yana lumshe ido
ahankali yana tunanin ya Allah kabani mata and she will be the luckiest girl.
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: 💛💙♥💚💜
ZAKISAN KONI WAYE
💜💚💛♥💙
®zuwairat(ummu maryam)

3⃣

Su mimi suna ganin ya fita suka kalli junansu sannan suka fara kallon dakin, komai
na dakin golden color ne, wani irin makeken gado ne a tsakiyan dakin wanda ke
kamada baa kwanvciya samanshi don komai very neat, mimi dan matsawa tayi kusa da
dressing mirror taga kayan shafa kaman da mace don ko a mata sai masu hali zasu iya
siyan irin kayan shafanshi cos ko su da suke yayan minister basu da yawan kayan
shafanshi, perfume kam tamkar nan ake saidasu, itakam fina wani kiofa da aka
rubuta my wardrobe ta bude sai taga dakine amman abin mamaki duk girman wurin
suturanshi ne shake da wurin, suit sunfi kala dari da hamsin kuma dukkansu
designer ne like wise takalma ma basu irguwa suma yawancinsu daga companin prada
ne, juyawa tayi ta kalli inda yake ajiye agogo da glass suma sunfi kala 40 suma
designer, itama mimi dakin tabi fina, itama tana shiga ta bude baki
" the guy is beyond our expectations.." fina juyawa tayi ta kalli mimi tare dacewa
"ni tunda nake zuwa shopping abroad ban taba ganin boutique dake dauke da yawan
designer clothes waje daya kaman na slim ba... Kalli vallantino pijamas.. Babe mu
ajiye fadamu waje daya mu dangwali arziki..wallahi this guy is loaded " murmushi
mimi tayi tana tunanin ai ko a ta hudu tana iyan ajiye pride dinta ta aureshi,
itama fina tunanin da take kenan don salem ya fi duk yanda take tunani, wata
koface suka gani mai cikin wardrobe room din, ahankali mimi ta bude wurin, wani
irin wagegen bathroom suka gani,
"shidai slim komai nashi extra large.." inji fina.

Girman bathroom din abin mamakine don wani katon swimming pool ne wurin sai wata
plasma a tsakiyan ceiling din. Daga gefe kuma wani mirror ne wanda shake yake da
bath perfume kala2 sai shower gel suma kala2 , daga dayan gefen kuma wani rank ne
mai dauke da towel manya da kanana.

Wata kofa suka bi sai gasu a bedroom, wani fridge duka bude sai ga exotic wine
amman ba mai giyaba, daya suka dauka tare da cup guda biyu, kan wani mini dinning
mai dauke da kujera biyu suka kioma suka zauna suna shan wine din kiowacce tana
tunanin yanda zatayi slim ya zama mallakinta.

Shidai salem dan tsohon shugaban kasane amman baya cikin yara masu dogara da
arzikin iyayensu don yanzu shine shugaban NGO na Africa gabaki daya, shine babba
agidansu sai kannenshi biyu mata wanda yansu suna gidan mazajensu.
Salem yana da kirki sosai don duk shekara sai ya biya mutane dari kudin hajj sannan
yana da kungiyan tallafawa talakawa a garuruwan arewa sanna duk begger daya cikaro
da slim kaman yanda friends suke ce mashi saboda yanayin jikinshi ya warke ko da a
gidansu talaucin duniya ta kare. Shidai Salem yana daga cikin the most eligible
bachelor da muke dasu a duniya don yan

1 / 44