Advertisements
Chapter 44 Reading ZAKISAN KONI WAYE by ummu maryam BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ZAKISAN KONI WAYE by ummu maryam

Author :  ummu maryam Category :  Complete Novels

Chapter   44 / 44

129K to 130.5K   out of 130.5K words

bata fada mashi yayi bata good night ya tafi ya
kwanta, itama kwanciya tayi.

Har ten maran na kara ciwo ahankali amma bata dauki ciwon serious ba saboda daman
in zatayi period tana irin wannan ciwon.
Fitsari tajeyi taga wani abu kaman mucus mai hade da jini, da sauri ta fito ta tada
Vicky da ke kwance gefen gadon ta fada mata abinda ta gani, safa ta dauko ta
umarceta data kwanta ba musu ta kwanta, dubata tayi ta fada mata she's in labor,
tawa mamaki take wai ashe daman haka haihuwa keda sauki?, nace you must be joking,

Around 4am abun ya zama gaskiya don banda yarfe hannuwa babu abinda take har
lokacin baa sanar dasu Umma da Salem ba, kuka tafarayi tana yarfe hannuwa da zafin
ya bari Sai ta goge hawayenta, chan Sai ta fara kuka, Vicky sai danne mata waist
take, karfe biyar taji contractions din ya zama unbelievable
"Wayyo ki kira salem...mutuwa zanyi...." Ta dinka maimaitawa Vicky da turanci,
Vicky kiran number Umma tayi sai na Salem ta sanar dasu halin da ake ciki, tawa
durkusawa tayi gaban gado ta dora kanta ta fara bacci, ko minti biyu bata yiba ta
farka ta fara kuka sosai, lokaci daya Salem da Umma suka shigo, tawa Sai zufa take
kaman babu ac a dakin, duk hankalin Salem ya tashi, Umma sannu ta dingayi mata amma
babu bakin amsawa Sai kuka,
"Please a kaita wurin haihuwn..." Inji Umma,
"Stand..." Vicky ta umarceta ahankali, da sauri tawa ta girgiza kanta tana cewa
"Ban Iya tsayawa...." Tafada cikin kuka
"Wayyo bayana...Mara ta
.." Ta dinga maimaitawa,
"Baby sorry..." Inji Salem dake magana kaman shi ke labour, Salem ne ya daga ta
tsaye Sai ihu take, duk yanda Umma ke hana ihu Sai tace
"Wayyo Ku barni inyi kona ji sauki....Dan Allah Ku kiramin mami..." Da kyar suka
isa mini hospital Ta shiga tana tafiya da kyar don data daga kafa daya Sai tayi
minti biyar bata daga dayanba, Salem yaso daukanta amma doc ya hana wai the more
she walks the better

Ba karamin wahala tasha ba don duk hankalin su ya tashi mussanman Salem don cewa ya
dingayi ayi mata cs kawai don wahalan yayi mata yawa, har kuka sai da yayi don Umma
hanashi shiga tayi kuma daga baya ya barjin kukanta Sai ya fara tunanin kilan ma
mutuwa tayi, buga kofan ya farayi da karfi yana cewa
"Umma meyasa Tawakaltu ta bar kuka?...Umma in mutuwa tayi Ku fadamin...." Da kyar
Abba ya jashi daga wurin, kaman mahaukaci ya koma, alwallah yayi ya tafi masjid ya
dinga sallah nafila.

Sai bayan magrub ta haifi danta namiji, alokacin bata San inda hankalin ta yake ba
don batasan sanda aka karata ba saboda girman dan, duk gidan babu Wanda ya sha ko
ruwa saboda tashin hankali, Umma ce ta kira Abba ta sanardashi, Salem dake kwance
kasan carpet din Abba najin Abba yace alhamdulillah, ya mike da gudu yayi waje Abba
ya bi bayanshi. Yana zuwa bakin wurin yaji kukan jariri,wani irin ajiyan zuciya
yayi ya shiga wurin kasancewan Umma ta tafi dauko kayan jariri, ko kallon dan banyi
ba ya je wurin Matan da Vicky keyiwa stitching, Sai ajiyan zuciya don ko kuka bata
iyayi. Hannu ta ya rike ta bude idanuwanta da suka koma ja ya fara cewa
"Baby am sorry for putting you through such pain...baki kara haihuwa...if we need
more kids we will get a surrogate mother... Amma baki kara wannan wahalan...." Bai
idaba yaji kukan Dan kaman yana cewa daddy baka yi min magana ba, sakin hannun tawa
yayi ya koma wajen Dan, gani yayi dan kaman Dan wata uku cos girman dan yayi yawa,
"Masha Allah..." Ya fada yana duba sex din yaron, kallon doc dake daman aikinta
yayi
"What did he weigh?..." Ya tambayeta
"4.5kg..." Ta amsa mashi
"That's why ka wahalal min da mata" ya fada yana daukan Dan.

Jamaa haka ko wacce uwa take wahala kan Dan da ta Haifa amma ka tashi ba ka ganin
grima ko darajansu...to Ku Sani duk abinda da yayiwa mahaifanshi zaa yi mashi..so
be obedient respective. Allah kasa mu rabu da iyayenmu lafiya.

Kuyi hakuri, mun kusa gamawa don anyi resuming school.
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤❤
💚💜💜💙💚💛
ZAKISAN KONI WAYE
❤❤



®zuwairat(ummu Maryam)


8⃣4⃣



* *Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*

Murna wurin Ameera tamkar ita ta haihu ana fada masu suka kama hanyan family house
din Salem kasancewan tunda cikinta ya shiga wata na biyar ta bar ciwo, yanzu garau
take, ga haske data kara.

Tawa kam banda bacci babu abinda takeyi, Salem bakinshi bai rufuwa don call kawai
yake.
Atakaice ranar suna akayi shagalin fiye da tunanin mai karatu da yaci sunan dad
amma ana kiranshi da gidado,

Bangaren Ameera kam Ahankali ta ciga watan haihuwan ta, ranar haihuwa kam taci
kwakwa ta haifi danta namiji , suma na karamin shagali akayi ba ranar suna shima
dan sunan governor aka bashi ana kiranshi da lamido.

Ahankali lokaci ke tafiya aminci na kara karuwa tsakanin family din Salem dana
Ameera, yaran hinde biyu ke yiwa Ameera aiki, dukkan su basu tunawa da abinda ya
taba faruwa tsakanin Salem da Ameera, Kuma har yanzu mutane da dama basu San Salem
ya taba aure Ameera ba.
Bayan shekara biyu kowanne Family ya kara samun karawan kuma still duk maza.
Yanzu su Khalid sun koma abuja don nan ya gida sabon company.

Salem kam arziki karuwa kawai yake haka soyayyar da yake yiwa matanshi. Dukkan su
sun maida zuwa abroad tamkar bathroom.

Admission suka samarmasu a university of abuja inda Ameera take karantan medicine
ita kuma Tawakaltu tana Karanta business administration, abun mamaki shine yanda
shakuwa ta mussanman ke shiga tsakanin gidado da lamido, most of the time suna tare
gashi school daya suke the same class, har ya kaiga suyi sati daya gidan Salem suyi
daya gidan Khalid. Kuma ko wanne da kamannin ubanshi don mostly daddys junior Salem
da Khalid ke kiran first born dinsu.

Agurguje cikin shekara goma tawa ta haifi yara six four boys Sai two girls amma
kowanne da na da mai kula dashi ko ita don sam bayason a takurawa matanshi don har
yanzu halinshi na nan babu abinda ya fasa. Tawakaltu business take na kayan kitchen
da na gida gaba daya. Ko gobe zaa daurawa yarka aure in ka zo wurin ta zaka samu
duk abubuwan da kake buka,.

Bangaren Khalid suma cikin ten years sukayi four kids, three boys and a girl, kuma
sunce sun rufe saboda yanda Ameera take shan wahala in tana da ciki.
Yanzu Ameera doc ce kuma ya gina mata hospital inda take aiki.

Yaran sultan da queen Habeeba biyu, suna zaune abroad.

Zainabu ma tayi aure da yaranta uku.

Every part is happy especially mami da ta san cewa ba duka aka taru aka zama daya
don duk sanda tawa da yaranta sukaje Sai ta godewa Allah da ya hada Salem da yarta,
saidai abinda ke bata haushi shine yanda yaranta basu son zuwa Kwara.

Bayan su Lamido sun gama first degree dinsu daga Cambridge akayi masu aure, lamido
da fourth child din Salem mai suna amra Sai gidado da last born din Khalid mai suna
afra.
They all live happily ever after


To jamaa nan na kawo karshen littafina.

Na gode na kulawanku.

Mata ga shawara
Ina mai Baku shawaran abar zaman banza, wato zaman rashin aikin yi ko Sana'a, mata
da dama suna zaune gida basu da hanyan samun sisin Kansu Sai miji ya bada which is
very bad, komai miji, biki miji...anko..miji in short common gishiri Sai miji ya
saya, why?... Nasan zakuce Allah ne ya dora masu amma babu Wanda baya bukatan
taimako, kullum cikin yar murya kike don abaki kudi, at least in bai bari aiki to
kayi Sana'a ko ta cikin gidane don babu abinda ke saurin sa mace ta fita ran
mijinta kaman kullum bani, Wallahi duk yanda mijinki ke millionaire watarana dole
ya gaji da bani, watarana kiri2 zaice babu kuma babu yanda zakiyi amma the moment
kina da abinyi baki jin frustration inya hanaki.

Karki ji na fi karfin inyi kaza da kaza dole Sai kaza wallahi you are deceiving
yourself, duk yanda kike takama da kyau da akwai wacce ta damaki tasha. So mata Kar
ayi zaman hakan nan, akoyi Sana'a.

Ku kuma masu aiki a dinga taimaka wa mai gida, karkice dole Sai shi kadai zai biya
school fees fin yara alhalin kina da halin taimaka mashi, Sai kiji wasu Matan na
cewa
" ni zan taimakawa namiji?.. Allah ya sauwake....AI namiji ba Dan goyo bane..in
kashe mashi kudina watarana ya kawo min kishiya?..." Well namiji ba dan goyo bane
amma in kika yi don Allah zaki ci riba, Sannan in kika taimaka mashi da yaranki
tamkar kinyiwa kanki. Kuma kishiya in Allah ya kaddara zaayita babu Wanda yaisa ya
hana don haka a dinga taimakawa mai gida don ba karamin aiki suke ba, in kin
taimakeshi ya kwareki shi da Allah.

Allah ya sadamu da alkhairi. Sai kunji ni a sabuwa novel dina mai suna *kawarta ce
sanadi*

Amma ba yanzu ba cos Sai na gama typing zan fara turowa.


Love you all most especially you my die hard fan.
VISIT www.aihausanovels.com.ng For More Novel.

AIHAUSANOVELS is website consists of hausa novels note, the reason of launching
this site is to Entetaint, Motivate and Educate our readers.



We provided hausa novels of many type, Such Adventure, love, romance, fiction,
non-fiction, mystry, fantasy, action e.t.c from hausa Authors



We provided a new and old novels both softcopy and hardcopy from our Author with
thier permission.
AIHAUSANOVELS shafin yanar gizo ne wanda yake ?auke da littattafan hausa, dalilin
bude wannan shafin shine domin Kayatar masu karatu da kuma ilimantar da su.



Mun samar da littattafan hausa na nau'uka daban-daban, kama daga littafin,
soyayya, tatsuniya, almara, Hikayoyi, gyara kayanki (yadda mata zasu kula da kansu
a gidan mijinsu) da dai sauransu, daga Marubutan hausa.

44 / 44