Author : ummu maryam Category : Complete Novels
idaba yaga tayi tsale ta tashi, tana ganin shi ta hada rai batare
data ce komai ba ta bar gurin
"Tawa..please wait..am sorry.." Bata saurareshiba ta shigaba da tafiyanta shikuma
sai binta yake yana kiranta Amman ko juyawa batayiba ta shige cikin restaurant.
Duk ya mance da mutane wurin, har cikin restaurant zai bita wata gingimemiyar mata
ta tareshi
"Oga what do you want?" Da alaman mai wurin ce, kallon cikin restaurant yayi yana
cewa
"I want to buy food"
"Go inside costumer" ta fada mashi, yana shiga ya ga tawa zaune bayan wani canter
sai goge hawaye take, kallon koina yayi yaga ba kowa yakarasa inda take, ahankali
yace
"Habibty am so sorry.. In dukana zakiyi kiji sauki please hit me..Amman wannan
silent mood is killing me.." bai karasa ba tawa ta goge hawayenta sannan ta mike,
gabanta ya tare
"Amman kilan da akwai wani abu dake damunki...cos dan abinda nayi maki bai isa ya
saki hakaba.." Maganan shi kara batwa tawa rai yayi ta bi ta gefen shi ta fita.
Salem tsayawa yayi aka jera mashi abinci, har lokacin bai bar kallon kofan da tawa
ta fitaba.
Hada fuska yayi ya tsaki tsoki sannan yace
"Fuck you" yana kaiwa Nan ya bar restaurant din ya koma gida.
❤
Yau alhamis aka fara shagalin biki gidansu ameera, ba laifi family sun hallara, don
gidansu cike yake da mutanen arziki don yawancinsu don mom ameera sukazo, su ameera
kam ta kara fayyau don ba karamin gyara akayi mataba, duk Wanda ya ganta sai yakara
kallon ta don yanda take sheki. Suma ameera shasu suke gidan anty Sadiya don yan
mata banda girgiza ukwu babu abinda sukeyi.
❤
Tundaga wannan ranan bai kara zuwa gidan ko restaurant dinba Amman badon bayason
ganintaba don kullum da tunanin ta yake kwana yake tashi.
Abdul ba karamin fada yake shaba kuma shi baisan hawaba bai san sauka ba Amman
kanshi Salem ke sauke fushinshi.
Yau Thursday kuma gobe zai tafi yola gani yake in bai samu ganintaba da akwai
matsala. Saida ya tabbatar sun tashi daga restaurant sannan ya wuce gidansu, yau
bai tsaya tura wani ba yashiga da kanshi, sallama yayi a tsakar gidan Amman babu
Wanda ya amsa mashi cos gidan irin kato gidan hayan nan ne, direct bakin kofansu ya
nufa yadan kwankwasa don bayason yayi magana ta gane shine .
Tawa dake zaune kusa da mami agajiye take, kanta bisa cinyan mami take ko dan
kwalli babu, gashinta daure baya Amman da gani bata taba shafa mashi relaxer ba.
Tana jin anyi knocking batayi tunanin komai ba tace
"Shigo" don a tunanin ta yaran neighbors dinsune.
Salem najin tace shigo ya yaye labulen sannan yayi sallam. Mami Dan murmushi tayi
sannan ta amsa mashi, durkusawa yayi ya gaida mami, tawa hada rai tayi wuri ya samu
ya zauna, ji yayi mami ta fara fada da yarensu, nan take tawa ta mike ta durkusa ta
gaidashi sannan ta bashi ruwan sha, banda kallon ta babu abinda Salem ke yi, don
yaune rana ta farko daya ganta babu dankwali kanta, kara ganin kyaunta yayi, mami
mikewa tayi ta shiga kurya, itama tawa bayan ta tabi, ta dauki Dan gyale ta yafa,
sannan ta kara fitowa, ajiye cup ruwan yayi ya kalleta
"Please tawa I need to talk to you.." Kanta kasa don wani irin kunyanshi takeji
"Am listening" ahankali yakara cewa
"Please can we go outside?" Batace komaiba ta mike shima yamike suka fita, cikin
tsakar gidan in babu dakin kowa suka tsaya har lokacin fuskan tawa babu faraa.
"please am sorry.. Wallahi bazan gigin kara tabakiba..until it's halal..please da
akwai abinda nakeson fada maki..can I continue?" Dan harara kasan ido tayi mashi
sannan ta daga mashi kai, Salem yayi shuru tare da danyi ajiya zuciya sannan yafara
cewa
"Tawakaltu.. Zan fada maki abinda ban taba fadawa kowacce ya mace ba..I love you! I
love you so much...u are special.. I love you with all my heart... Please abinda
nayi maki is unfair.. Forgive me" tawa shuru tayi tana jin wani irin dadi kasan
ranta, ahankali tace
"Ya wuce..Amman promise me..." Da sauri Salem yace
"Anything for you" tacigaba dacewa
"Bazaka Kara zuwa gidanmu da dareba" Dan daria Salem yayi
"I promise" itama murmushi tayi
"Kayi hakuri I over reacted."
"No problem.. I love it.. Baki fada min how you feel about me ba" tawa shuru tayi
kanta kasa sai murmushi take
"Please say something...you are my second love..." Gani yayi ta hade rai , daria
yayi
"You are jealous ko...don't worry Ummata is my first love" sai lokacin tawa ta saki
ranta.
"I love you too" ta fada ahankali, dadi kaman ya kashe shi
"I promise you won't regret it.." Hira suka sha kaman babu abindaya taba hadasu,
daga karshen suka amso dinki sannan ya sanar daita zaiyi tafiya.
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE
❤
®zuwairat(Ummu maryam).
2⃣3⃣
Aranan Salem da kyar suka rabu da tawa don dayazo tafiya sai ta marairace tace
"Please don't go" sai ya kara gyara tsayuwa su cigaba da hiransu, har bayan magrub
suna tare, kallon gari yayi yace
"Habibty kalli dare yayi.." Dan turo baki tayi
"To ka tafi " tafada Amman badan ranta yasoba, daria yayi sannan yayi mata bakwana
ya tafi.
Yana zuwa gida ya bawa Abdul dinki daya amso, hankali Abdul kwantawa yayi don yaga
yanayin shi yayi kyau.
"Ka ajiye wannan kayan bayan boot din taxi din da zaku kai shaidaniyan yarinyan nan
abuja"
Yafadawa Abdul
"OK sir " Abdul ya amsa mashi sannan ya mike ya ajiye kayan bayan mota. Salem yaso
yaga sanda zaisa guards dinshi su fixgi ameera daga cikin jet dinshi su turata
cikin taxi din data tsana suyi Abuja daita, yaso ya tsaya da hannunshi cikin
aljihunshi yana kallon reaction dinta
"Bai bace ba..." Ya fadawa kanshi lokacin dayake Alwalla.
Aranan kwana yayi waya da abin kaunanshi, sai wajen 1 am yaji muryan mami tana yiwa
tawa fada, dukda baijin abinda take cewa yasan fadawa tajeyiwa tawa ta kwanta. Ba
kara bata lokaci ba ya kashe wayan tare da busa mata kiss.
Jiyake inama yana da right kanta, da babu abinda zai hanashi romancing dinta har
sai ya tabbatar ta gamsu dashi sannan shima ya gamsu, kwantawa yayi tare da rungume
pillow
"Love is sweet.. Love is wonderful.. I love you my heart desire..I can't imagine
life without you"
Karfe 11 na safe jet dinshi ya iso kano, cikin nutsuwa ya shirya cikin wasu
tsadaddun farar shadda, banda kam shi babu abinda ke tashi.
Umarnin yanda gobe zai kasance ya bawa Abdul da majid sannan ya hau jet pilot
dinshi yayi gaba dashi.
Ko hour daya baiyiba naga jet ya sauka ciki wani makeken gida, komai na gida
exotic, dukkan masu aikin gidan waje suka fito suna
"Alh Salem..alh Salem" Daka gan yanda sukeyi kasan da akwai so da kauna tsakanin
su, dukan mazan musabaha sukayi sannan suka gaisa da Matan, gidane gari guda kaman
bazaa mutuba, daga kai nayi nayi naga wata gareran mata my shegen kyau don da gani
ita ta haifi Salem, sanye take cikin wasu expensive Arabian gown, daka ganta kaga
bafulatan gaske don har tsagansu gareta, da gudu Salem ya nufe zai rungume ta Amman
ta daga mashi hannu ya tsaya chak gabanta, cheek dinta na dama ta nunawa Salem,
ahankali ya duka yayi kissing wajen, na hagu ta nuna mashi ya kara dukawa yayi
kissing wajen sannan ta nuna mashi goshinta shima yayi kiss a wurin sannan ta bude
mashi hannuwa ya fada jikinta
"Umma I miss you so much.." Keyanshi ta buga
"Karya kake" shafa keyanshi yayi yana yi kaman saiyi kukan shawagba, Matan tsayawa
tayi tana kurawa danta ido, banda so da kauna babu abinda ke fita idonta.
"Son ka rame kayi baki..me ke damunka?" Tafada lokacin tana sakale da hannunshi
sunyi hanyan wani makeken apartment.
"Umma aikine"
"Ko wa kake wa wannan wahalan oho..kai ba mata ba balle yara Amman you are working
your ass off" daria Salem yayi
"Ai first love ko bani da iyali ba gaku..."
"Yimin shuru tunda sanin kankane babu mai bukatan kudin ka.." Salem daria ya kara
yi cikin zolaya yace
"Amman kinsan am richer than dad.." Kara dukan shi tayi adaidai lokacin da suka
wani irin babban falo,
"Ai kudin ban gan amfaninsu ba tunda babu maici" Umma ta fada mashi,hannunta cikin
nashi ta kaishi kan wani golden dinning Wanda yake daukan mutane shabiyu, abinci ne
jere kala2, in ka kalli kan dinning din sai kayi tunanin President ake tarba.
With out wasting of time ya zauna don tunda suka samu matsala da tawa ya rage cin
abinci, Umma da kanta tayi mashi serving favorite, ya nade hannu riganshi yafara
cin abinci kaman yayi wata baici abinci ba, daya daga kai sai su hada ido da
ummanshi, banda kallon danta babu abinda take, shima dasu hada ido sai ya sakar
mata murmushi. Saida yayi nat sannan yayi relaxing kan kujeran dinning
"Umma ina Abba?" Daria tayi
"Jairi..sai yanzu ka tuna da babanka?...anyway ya tafi rukanshi Amman bada dadewaba
zai dawo"
"Abbah da rugah.."
"Oya je kayi relaxing kafin lokacin sallah yayi"
"Umma barni kawai in zauna nan..na kwanta yanzu bacci zanyi kuma its not good for
my health.."
"Dalla rufemin baki...go an have some rest." Ba musu ya mike yana balla button din
wuyan riganshi. Fita yayi daga side dinta ya koma nashi personal part, Wanda baa
budewa sai in zai dawo abude a gyaramashi.
Bayan sallan jumaa Abba ya dawo, side dinshi Salem ya wuce bayan ya dawo daga
masjid, gaisawa sukayi cikin so da kauna, kasa ya zauna gefen abbanshi
"Ya Kano?" Abba ya tambayeshi
"Abba Kano lafiya lau..."
"Ya abinda kaje nema?..da nasara ko har yanzu baka gama shiriritanba?" Salem shuru
yayi yana shafa keyanshi
"Baka amsa minba" Abba ya kara cewa
"Abba.. Na samu nasara..Amman ban saniba ko zan samu goyon bayan Ku.."
"Me zai hana...tunda shekara nawa muje jiran kayi aure..." Salem shuru yayi yana
tunanin ta yanda zai fara gayawa Abba abinda ke zuciyanshi
"Meyasa kake ganin bazamu baka goyan bayaba?" Abba ya tambayeshi, ahankali Salem
yafara cewa
"Abba ba yarenmu..."
"Kaji min shashancin banza..yare yana hana aurene?...da mutumin ke zuwa wata kasa
yayi aure fa?..ai wannan ba matsala bane...hope muslima ce?" Salem wani sanyi yaji
cikin ranshi, daman yasan abbanshi bashi da case
"Eh Abba"
"Wace yarece?" Ahankali ya kara cewa
"Yoruba" baki Abba ya bude
"Yan gidan abokina obasonjo kenan.. Waye babban ta?" Salem murmushi yayi
"Abba yar talaka ce..abbanta ya rasu"
"To Allah ya jikanshi..its good..haka zai baka access ka kara taimakawa talakawa
tunda ga kudin babu abinyi da su" Salem daria yayi
"Eh mana tunda kullum cikin aiki kake..at least ko yan gidan matanka ka kara
taimakawa zaka samu lada" Salem lumshe idanuwa yayi yana tunanin
"I wish such word is coming from first love mouth" yafada cikin ranshi, don
ummanshi irin Matan nan masu mulki, masu ganin uwa tafi karfi cikin decisions din
yayansu.
"Abba nagode.. You have always supported me...all ya saka maka da jannatul
Firdausi.."
"Ameen habibi..kaima Allah yasa kar kayi Dana sanin zabinka"
"Ameen the best father in the world" Abba daria yayi, ahankali Salem yafara cewa.
"Abba kana ganin Umma zata amince?"
"Kunfi kusa"
"Please Abba katayani fada mata..." Ahankali Abba yace
"Aa..kasan yanda ummanka take...tana iyacewa ni na zaba maka yarinyan... Tell her
ni kuma will be there to support you in case an samu matsala"
"Please Abba kayi min aduan kar a samu matsala.. Wallahi Abba I love her...Abba
dukan mata danayiwa magana zagina suke..wallahi Abba wata har marina tayi..."
"what! Mari kuma?"
"Yes Abba.. Abba Tawakaltu kadaice ta saurareni..har kudi take bani"
"Tawakaltu.. Its a lovely name" inji Abba, lumshe ido Salem yayi yana daria, Dan
shafa bayanshi Abba yayi
"Salem unlove" daria ya dinga yi Abba na tayashi.
Haka suka sha hiransu har lokacin sallan asar sannan sukaje tare suka dawo, suna
dawowa sukaci abinci, side din ummanshi ya wuce cos ba tare sukaci abinci ba, falon
ta ya taddata zaune wata yarinya na massaging kafanta, tana Ganin Salem ta sallami
yarinyan,
"My handsome son"
"Yes Umma"
"The richest guy in Africa"
"Yes Umma"
"The most eligible bachelor in Africa"
"Yes Umma"
"Umma's only son..."
"Umma kirarin ya isa hakanan" ya fadawa ummanshi don inda sabo yasaba da kirarin
Umma. Zama yayi kusa daita suka fara labarin duniya, hira suke Amman yarasa ta inda
zai fada mata abinda ke zuciyanshi. Ahankali ya daga kai ya kalleta
"Umma albishirinki?"
"Goro"
"Umma na samu Matan aure" da sauri Umma ta tallabo fuskanshi
"Son are serious.. Ko you are just pulling my legs"
"No Umma.. Am serious"
"Yar gidan wacece?" Ahankali Salem yace
"Yar talakawace.." Shuru Umma tadanyi sannan tace
"No problem.. There is enough money to go round" Salem murmushi yayi sannan yace
"One more thing"
"Meye kuma?" Salem shuru yayi for a moment tare da gyara zamanshi sannan yace
"She's not Fulani or Hausa.." Surprise look Umma ta watsa mashi
"Then wace yarece?"
"Yorubace..."
"What!!!!"
❤
Yau Friday akayi yinin biki gidansu ameera, dukda baa gayyaci mutane da yawaba bai
hana gidan shika da mutane ba, don inkazo gidan babu masakan tsinke, aranan aka
maido ameera gidansu, tasha ado cikin wani tsadadded code lace, fuskanta yasha
heavy makeup, ko rashin waya da Wanda zata aura bai dametaba, kawayenta duk suna
kusa daita sai iskancin su suke, ameera kam bata ki a dauketa yanzu akaiwa Salem
ba, cikin zuciyanta sai Allah yaisa takewa anty Sadiya saboda banda sexual desire
babu abinda ke damunta, ganitake gobe in Salem bai nemetaba zata fidda kunya ta
nemeshi
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE
❤
®zuwairat(ummu Maryam)
2⃣4⃣
Tawa sai trying number Salem take, yana ringing Amman baya dauka, duk ta tada
hankalin ta, tana wajen aiki Amman hankalinta baya wajen don gani take kaman wani
abu ya samu Salem
"Wai wani abu ke damunki naga sai tsoki kike" Zara ta tambayi tawa
"Tunda safe nake trying number sir Salem yana ringing Amman bai dauka,..Allah yasa
lafiya" tawa tafada kaman zatayi kuka, daria Zara tayi
"Har kin shirya da wanfa ya taba maki precious boobs dinki?.."
"Ohhh...Zara stop it ina maganan abin sona kina maganan boobs" daria Zara ta karayi
wanda yasa tawa kara kuluwa, tsoki taja ta bar wajen, komawa tayi waje ta zauna
tare dayin tagumi.
❤
"What's today's date?" Umma ta tambayi Salem
"18 November" Salem ya amsa mata gabanshi na faduwa,
"Today is not first April.. So what sought of joke is that?" Umma ta tambayeshi
muryan ta babu alaman wasa, ahankali Salem yace
"Umma.. Am not joking.. Am in love with a Yoruba..."
"Shut up!!!" Umma ta daka mashi tsawa, mikewa tayi tayi tsaye kanshi
"Daman haka kake ban saniba?..you look matured..but you are stupid.. Ina Fulani ina
wata yare waishi Yoruba?.. To tunda bakason samu matan aure zan samo maka..this
discussion is over.." Tana kaiwa nan tafara tafiya, tunda tafara magana Salem ya
had kanshi da kwaiwa, yanajin Umma tabar wajen ya mike da sauri ya bi bayan ta
"Umma am sorry I disappointed you...but she's the one my heart choose.. I love
her..in ban same taba zan rasa raina" afusace Umma tajuyo
"Then get ready to die..don bazan iyazama wata yare ta haifamani jikokiba..ta
koyawa jikokina aladan da ba namuba..sam hakan bazai taba yuwaba..if you are
dreaming wake up" juyawa tayi ta fara shiga bedroom Salem yakara binta da sauri
"Umma yarinyan bata ma iya yarensuba balle Ashe zata koyawa jikokinki...please Umma
support me this once...I love her..please" Umma bata saurareshiba ta shige bedroom
dinta, har lokacin Salem bai bar binta ba, abakin gado ta zauna ta dora kafa daya
kan daya, gabanta Salem yayi kneeling
"Umma ban taba so ya mace ba sai yarinyan.. Umma in har kina sona ki so Tawakaltu..
Please" har lokacin Umma bata ce komaiba sai karkada kafa take, Amman fuskanta babu
alaman amincewa
"Please first love help me..ina bin umarnin ki...ban taba yi maki gardama ba..nima
dan Allah kiyi min wannan.."
"Kai kar ka yimin maganan banza!!" Ta daka mashi tsawa
"Yazaayi dana ya auri Yoruba?..me kakeso in gayawa family?...me kakeso mutane
suce.. So kake adinga ganin mu kaman bamu isa da yaranmu ba?...to indai nice saidai
ka mutu ba mata Amman bazaka kawo min Yoruba amatsayin surukaba...this discussion
is over" Salem sunkuyar da kanshi kasa yayi, bai ankaraba yaji hawaye na zubowa
daga idanuwanshi, ahankali ya mike sannan yafara cewa
"Umma I thought you love me..but am wrong don nasan inda kinason ko mahaukaciya
nace inaso kema zaki sota..." Dan goge hawayen fuskanshi yayi sannan yacigaba
dacewa
"Umma ban taba ketara umarnin kiba...banson karanta doctor kika yi forcing dina..I
never complaint.. Banson karatu a Europe..har na samu admission a Oxford Amman kika
ce dole sai peacock still I don't complain... Umma banason rayuwa a Nigeria Amman
kika yi forcing dina na zauna...you choose friends for me...You choose everything
for me...but am not going to let you choose my life partner...no problem tunda
kinfi son family fiye dani...Amman let me make one thing crystal clear... Nobody
will stop me from marrying Tawakaltu.. I love her and she's my choice.." Yana kaiwa
nan ya fice daga cikin dakin
"Salem come back here now" Umma ta fada a tsawace , Amman bai juyawa ba yacigaba da
tafiya, hannu yasa cikin aljihunshi yafara Neman wayoyinshi Amman bai gansuba,
tsakar gidan ya tsaya ya kwallawa pilot dinshi kira sai ga guy din ya fito daga
cikin wani party da gudu
"Get your things.. We are leaving.. Kuma check if my phones are in the jet" Da
sauri guy din ya koma ciki ya shirya cikin sauri, shima Salem part din abbanshi ya
koma ya gayamashi yanda sukayi da Umma sannan ya kara dacewa
"So Abba zan wuce abuja..I will call you"
"Amman I wish you can stay more" Abba ya fada mashi, ban kwana sukayi sannan ya
fito, direct cikin jet ya wuce ya zauna sai yaga Ashe nan ya bar wayoyinshi, family
phone ya dauka sai yaga 46 miss calls. Budewa yayi yaga duka tawace ta kirashi,
lumshe idanuwa yayi wasu sabbin hawaye na taruwa idanuwanshi, pilot din tada jet
din yayi.
Umma najin antada jet ta fito da sauri, kafin ta fito waje har sun tashi sama,
ranta kara baci yayi
"Wace yarinya CE dana yakeson fifita ta kaina?..Salem always obeys me...dole in san
yarinyan" tafada sannan ta koma ciki rai bace, Abba yana kallon ta ta window, Abba
irin mutanen nan ne masu sanyi don Umma kadai ke making 80% of the family
decisions, don ko kannen Salem biyu ita ta zaba masu miji.
"Sir where are we going?" Pilot ya tambayeshi
"Abuja" ya amsa mashi har lokacin muryan shi bai dawo daidai, waya ya daga zai kira
tawa Amman yasan daya kirata zatasan da abinda ke damunshi, dole ya ajiye wayan,
baiyi 15 second da ajiyewa ba tafara ringing, dubawa yayi yaga itace, dan murmushi
yayi sannan yayi gyaran murya yayi picking
" my choice how far?", wani irin ajiyan zuciya yaji tayi
"Ya akayine?" Ya sake tambayan ta, ahankali tace
"Wallahi oremi hankalina ya tashi, tundazu inata kiranka ba amsa..so..."
"Sai kikayi tunanin na mutu..? Dariya tayi, yacigaba dacewa
" in wani abu ya sameni ya kenan" ahankali tace
"Sai in kashe kaina...I can imagine life with you.." Salem lumshe idanuwa yayi
"I love you.. And no obstacles will stand in the way of our love.." Yafada muryan
shi na rawa
"Oremi what's the problem?" Dan daria karfi hali yayi
"Haba habibty ban fi karfin oremi wajen kiba?...Gaskiya ki chanzamin suna" yafada
don ta bar maganan
"Ifemi...what's the problem..your voice is down" darian karfi hali ya karayi
"What's the meaning of ifemi" shuru tayi for a moment sannan tace
"Abin sirrine"
"Please tell me"
"I said sirri ne..har yanzu baka fada min abinda ke damunka ba" ahankali yace
"Missing dinki nake..my choice in har ban samekiba. Zan hadiye zuciya in mutu.."
"Hmmm"
"Is that all you could say...hmmm?" Daria tayi
"To me kakeso ince...anyway yasu first love da sauran yan gidan?"
"Suna lafiya..habibty anya zan