Advertisements
Chapter 12 Reading ZAKISAN KONI WAYE by ummu maryam BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ZAKISAN KONI WAYE by ummu maryam

Author :  ummu maryam Category :  Complete Novels

Chapter   12 / 44

33K to 36K   out of 130.5K words

tafara tafiya Amman dukda haka bai bar
ingizata ba, kaman prisoner haka ta koma, tana zuwa wurin motan bata tsaya aka bude
mata ba ta bude ta shiga tana kuka
"Dakin tsaya an bude maki" inji Abdul dakeji kaman yau salla, majed har ya taho
Salem ya kalleshi yace
"Ka biyomu da wannan shaidaniyan yarinyan"
"Yes sir"
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE


®zuwairat(ummu maryam)


Suna tafiya Salem na sauraon wakan breathless na ward Shayne, magagganun Umma sai
dawo mashi suke
_"Indai nice saidai kar kayi aure har ka mutu Amman bazaka kawomin Yoruba ta
haifamani jikokiba"_ kauda kanshi gefe yayi tare da lumshe idanuwa, sannan maganan
tawa ya faraji cikin kunnenshi shi
_"Yin haka disrespect ne..nidai in mami batason abu ban yi.."_ kara maida kanshi
yayi dayan gefen
"Kardai ashe bazan auri tawaba..." Da sauri ya kauda wannan tunanin tare dacewa
"No" har saida driver yace
"Sir ka yimin magana ne?"
"Kaji sunanka abakina ne?" Shima ya amsa mashi.

Sunfi hour daya suna tafiya, kuma har lokacin ameera bata bar kuka ba, majed daya
juyo sai ya daka mata tsawa sai tayi shuru don wani irin tsoron shi takeji don ko
kamanninshi ka kalla yaisa ya baka tsoro don yafi dukkan guard din Salem tsawo da
kwari.

Suna zuwa gidan sukayi parking, aka budewa Salem kofa ya fito yana gyara button din
gaban suit dinshi, abakin gate din wasu guys ne guda biyu suna gadin wurin, suna
ganinshi suka mike tare da bude gate din, daganin katangan gidan mai tsawo kana iya
tunanin da akwai katon gidan acikin ta, Amman da an bude zaka ga tamkar kango don
ginin ciki bai da tsawo sosai, har lokacin ameera bata fito daga cikin motan ba,
Salem kallon majed yayi.
"Bring her out" yafadawa majed, ameera tana ganin yayiwa majed magana tayi saurin
fitowa tana sauri ta nufi inda Salem ke tsaye Dan har ta mutu bazata yi marmarin
wannan mutumin ya kara tabata ba, Salem na ganin ta taho ya Yajuya ya shiga ciki,
da sauri tabi bayanshi, kallon gidan tayi tana tunanin kilan wani abu zaiyi sannan
su wuce, saida suka shiga Dan falon mai dauke da ledan da labule kawai sannan ya
juya, gani yayi ameera tanayiwa wurin disgusting look, tan ganin ya juyo tayi
saurin chanza yanayin fuskanta,
"Daman baki taba janzawa cos it runs in your blood" yafa cikin ranshi sannan ya
hada giran sama Dana kasa yace
"Welcome home.." Ido ameera tazaro sabbin hawaye na zubowa daga idonta
"Duk abubuwan dazaki bukata da akwai shi cikin gidan nan..." Bai karasaba tayi
kneeling tare da rike takalmin shi
"Kinsan kina gigin tabani sai na balli buroubanki...stop touching me with you
filthy hands" da sauri ta cire hannunta ta Amman tana nan durkushe
"Dan Allah.. Dan annabi...nasan nayi laifi..Amman wannan hukuncin yayi min
yawa...wallahi I will not survive here...dan Allah ka yamemin ka maidani
gidanmu..." Kuka yaci karfinta tadan goge hawayenta ta cigaba dacewa
"Please I promise to be a good person.." Salem tsaya kallonta yayi Amman ko kadan
babu alaman tausayi a zuciyanshi ,ameera ta cigaba dacewa
"Please forgive me..."
"Ke please don't waste my time.. Yanzu kishiga kitchen..." Ya nuna mata dan akurkin
da aka gina in the name of kitchen sannan yacigaba dacewa
"Ki dafawa akalla almajirai ashirin abinci.. Kuma na baki hour daya..in ba haka ba
in hada ki da guards dina.." Yana kaiwa nan ya juya zai tafi..da sauri ta kara rike
kafanshi
"Wallahi ban iya girkiba...ban taba girkiba...wayyo na shiga uku..nidai ka maidani
gidanmu.." Ta fada tana kuka kaman ranta zai fita don har juwa take gani don yunwa.
"Baki iya girkiba kike kiran kanki mace?..dalla ki sakarmin kafa kar itakaki...."
"Wallahi ka kashe ni...Amman ban zama wannan gidan"
"Haka kikace?..then wait...majed" ya kira da karfi, ameera na ganin majed tayi
saurin sakin kafanshi, daria Salem yayi hannunshi cikin aljihunshi
"Bakince kina son mutuwaba...da kin bari kin ga aiki da cikawa...kuma wallahi na
kashe banza...now ki shiga kitchen before I count three.." Tana shesheka tafara
cewa
"Please zanyi..Amman Dan Allah.. Kubani abinci.. Wallahi rabona da abinci tun
shekarajiya..." Daria Salem yayi
"In kin dafa kici" yajuya yafara tafiya, cikin kuka sosai tace
"I beg you in the name of Allah..ka bani abinci ...please am dying" tabe baki yayi
ya fice daga wurin.

Wurin masu gadin gate yaje
"Kun ga wancan ta cikin gidan?"
"Yes sir" sukace da sauri, Salem ya cigaba dacewa
"On no account zaku barta ta fita, sannan ban yarda kuyi magana daitaba..karta
aikeku..I repeat ban yarda ta fita ba...do I make myself clear?"
"Yes sir"
"Good.." Cikin mota ya shiga ya dauko 1k yabawa daya daga cikin masu gadin yace
"Wane irin abinci ake saidawa nan wurin?"
"Sir da akwai Dan wake..awara, taliya da mai da yaji, soyayyen dankalin Hausa. ."
bai karasaba Salem ya katseshi dacewa
"What ever...ka saya mata talaiya na 200.."
"OK..sir" Salem shiga mota yayi escort dinshi suka shiga suka bar wajen.
Ameera kaman ta hadiyi zuciya ta mutu , yanzu tasan Salem uwarta zaici don da tayi
tunanin abin wasa ne kuma gani take ko sati bazata yi cikin gidan nan da raiba.


Umma Salem ce zaune Sam fuskanta babu walwala, daka ganta kasan babu farin cikin
tattare da itako kadan, yau rabon da ranta ya kirata tun ranar Friday, gashi yau
lahadi.
"Wannan shine kashi na farko da dana ya iya kwana biyu bai ji murya ta ba...all
because of a girl...a Yoruba for that matter... Dole in san ko wacce irin yarinya
ce..sannan dole ta fadamin da bakin ta" tafada tana daukan wayan ta, wata number da
aka rubuta hjy ummi kano tayi dialing, few seconds later akayi picking, daga chan
bangaren akace
"Hajiya ta ta kaina ya kike ya kwana biyu?" Ahankali Umma tace
"Alhamdulillah..ya yan gidan.."
"Lafiya lau suke...ranan asabar akayi wannan auren..wallahi duk garin sunyi tunanin
Salem ne..."
"Manta da wannan ba shi bane Amman ina cikin matsala..." Da saurin matan tace
"Hajiya wane matsala kuma?" Ajiyan zuciya Umma tayi sannan tafara cewa
"Hajiya ummi narasa Dana..."
"Subhanallahi! Hajiya meke faruwa ne?"
"Ranar Friday Salem yazo nan da maganan auren wata beyerebiya dan nace Aa shine
Salem yajuya min baya...can you imagine that?...Salem da bai iya hour uku baiji
murya taba yayi kwana biyu bai nemeniba..."
"Hajiya beyerebiya fa kika ce.. Ai an gama dashi...ai babu masu asiri
kamansu...Amman Salem baiyiba..ga yara nan birjit cikin family sai ya kwaso wani
abi waishi Yoruba?.. Gaskiya da akwai matsala babba...yanzu meye abinyi?" Shuru
Umma tayi na Dan lokaci sannan ta fara cewa
"Shine dalilin dayasa na kiraki..inasin ki sa guys su dauko min yarinyan.. Nan Kano
take..."
"Yanzu Hajiya har sai an dauko maki ita? Kawai agama ...."
"Please stop... Ni bawani abu zanyi mataba..kawai zan roketane ta kunce asirin
datayiwa Dana..kuma kar ki bari a tabata..kawai akawomin ita" ahankali Matan tace.
"Yasunan ta"
"Naji yace Tawakaltu..."
"Kin San sunan unguwarsu?"
"No..Amman shi Salem yana Kano...so guys din subishi zaiyi leading dinsu wajen ta."
"To madallah..zakiji daga gareni zuwa gobe" tafada ranta baisoba ..don ita kawai a
fidda tawa daga way.
Umma wata kawanta tasake kira ta gaya mata abinda ke faruwa sannan ta fada mata
tasa guys su dinga duba shiga da fitan Salem in case zaizo da wata yarinya. Hmmm
masu kudi ko kadan wasu basu san kaddaraba.



Kan hanya Salem wani dake south Africa ya gaya mashi ya turo mashi number shugaban
mtn.
Suna isagida number na shigowa,
Kiran mutumin yayi suka gaisa sannan Salem yace.
"I need a help?"
"Anything for big guys like you" Salem tabe baki yayi sannan yafara cewa
"Da akwai wata yarinya dakeso kuyiwa kyautan 25m.." Dasauri mutumin yace
"Wa zaiyi kyautan?"
"Ni zanyi Amman da sunanku..."
"That's a good business...so tell me what I should do"
"There is a house in maitama"
Yabashi address din gidan sannan ya cigaba dacewa
" I want your people to paint it yellow.. Before next week then call me on this
line its my direct line and I will tell you what to do next.."
"OK..I will call them right" ji yayi wayanshi na ringing yana dubawa yaga tawa,
katse wayan Dan Mtn din yayi batare da sunyi ban kwana ba sannan yayi picking
"Princess of Yoruba land how are you.."
"Good morning sir"
"Morning ma...har kin tashi?"
"Eh wallahi.. Har nazo wajen aiki..."
"Tunda dazu nake son kiranki in baki wata labari" da sauri tace
"Please wane labari?"
"Wani abokina ne ya kirani dazun yacemin Mtn sun bashi million ashirin da biyar da
katon gida" tawa daria tayi
"Congratulations to him in ba karya yayi makaba...please let's say something
important.. Yaushe zaka dawo"
"Yanzu habibty maganan abokina ba abun important bane?.."
"No sir bahaka bane..kawai gane nayi kamar karya.."
"Love nine makaryaci?..."
"Ohhh..ifemi...yau kana jin fada..ba da kai nakeba...kaman abokinka karya yayi
maka...Amman sorry if you are angry" Salem ceje lebe yayi yana daria ahankali
"Nima ba fushi nayiba..Amman da gaske ne..Mtn suna bawa masu luck kyauta"
"Naji...yaushe zaka dawo?"
"Yau... ina hanya..me zaki ajiye min tunda kin isheni da tambayan" daria jin dadi
tawa tayi
"Na meye wannan darian?" Salem ya tambayeta
"Haka nan..yanzu me kakeso in ajiye maka?" Karaf Salem yace
"Kanki..."
"Zaka farako...bari in kashe wayata..."
"Sorry.. Sorry habibty karki kashe..bani da kudin kiranki..kiyi min tuwon shinkafa
da miya...kina iyawa?" Daria tayi
"Sosai kam"
"Kina da kudi?" Ahankali tawa tace
"Ranar da akiyi bikin Dan President madam ta bamu bonus din 1k zai isheni tunda da
kai da mami kawai zanyiwa..."
"Har kin bar aiki ki koma gida ki daga tuwon shinkafa da miya?"
"Kwarai kuwa"
"To shikenan... I love you"
"Love you more"
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE


®zuwairat(ummu maryam)

2⃣8⃣

Ameera na zaune tana kuka wanda aka aika ya sayo abinci ya kawo cikin bakin Leda,
daga kai tayi ta kalleshi da red eyes dinta
"Ubanmeye wannan?" Bai amsa mata ba ya juya abun shi
"Dan uwarka ba da kai nakeba?" Mutumin juyowa yayi yana kallon ikon Allah
"Me nayi maki kike zagina?" Da sauri ta girgiza mashi kai
"Kayi hakuri...Dan Allah" tafada tana kuka,
"Banza karuwa.. Ai Maganin Ku kenan.." Wani sabon bakin ciki ne ya tur nuketa
"Wallahi ba karuwa bace ni...Dan Allah Ku barni in tafi ko nawa kukeso zan Baku"
wani irin dariya rainin hankali yayi
"Yarinya baki da abun badawa" daga chan waje dayan yace
"Magana kake daita ko?...har ka mance abinda sir yace?" Da sauri ya bar wajen ya
koma bakin gate.

Ameera tana ji tana gani aka maida gate aka rufe, tayi kuka ta gaji, ahankali ta
dauko ledan ta buda taga taliyace da mai da yaji, sabon kuka ta fara
"Allah yaisa tsakanina da kai...wallahi bazan taba yafe makaba..mugu macuci" tafada
tana deban abinci, don tasan in har bata ciba tana iya mutuwa,tana ci ta tsinewa
Salem, cinye abinci tayi tas, ta mike tafita, kitchen ta shiga taga duk an ajiye
kayan abinci Amman babu wani abun fast food cikin su, wasu yan container ta bude
taga da tashi da su daddawa,
"Amman duk ubanda ya sayi kayan nan matsiyaci ne...da Wanda ya saya.. Da Wanda ya
saida...Allah sai ya tsine maku.." Tafada tana kuka, wani katon tulu tagani ta bude
taga cike yake da ruwa, cikin kayan ta dauki wani cup ta dibi ruwan, tana sha tana
kuka, komawa tayi cikin ta kwanta kanta nayi mata mugun ciwo, bata dade da
kwanciyaba bacci yayi gaba daita.
Baa dade ba Abdul ya kara dawowa ya ajiye mata kayan sawanta da aka mance baa ajiye
ba, yana ganin tana bacci ya ajiye ahankali batare daya tada taba.



Da yamma Salem ya hau jet ya koma Kano , ko tuna ameera bayayi hankalinshi kwance
don gani yake one mission is accomplished, sai zancen tawa kawai ne gabanshi da
kuma yanda zaiyi ya shawo kan ummanshi.

Around 4pm tawa tayi wanka ta shirya , mami sai kallon ta take ba tare data ce
komaiba, saida ta gama sannan tace
"Mami inason insayo kayan miya inyi maki tuwon shinkafa da miya" mami kallon mamaki
tayi mata
"Yaushe muka taba tuwon shinkafa nan gidan?" tawa tsuru2 tayi
"Ai mami tunda yau ina gida, so nake in yi maki ki ji dadi" mami kallon tuhuma tayi
mata
"Ai kinsan bai dameniba..dawo kawai ki zauna" jikin tawa sanyi yayi don bata Iya
gayawa mami cewa Salem zata dafawa don tana Iya cin ubanta,
"To mami bari in sayo kayan sai in yiwa kaina"
"Tawa...ina kikeson zuwa?"
"Wallahi mami kayan miya da shinkafa tuwo zan sayo.." Mami kura mata ido tayi na
dan lokaci sannan tace
"To kar ki dade...banson gantali...kullum kina yawo..yau dake ranar hutunki basai
ki hutaba?...Aa kinfison gantali" tawa daukan gyalenta tayi
"Mami ba gantali zan niba...yanzu nan zan dawo" ta fice, tana hanya ta kira Salem,
ta gaya mashi karyan data yiwa mami, banda daria babu abinda suke, data tambayeshi
inda suke sai yace basu kusa zuwaba don kilan sai dare zai iso. Alhalin lokacin
yana kwance kan gado yana hutawanshi.

Tawa bata dadeba ta dawo da yan kayanta m, cikin hour daya da rabi ta hada hadadden
tuwon shinkafa da miyan ganye.

Salem kiran ummanshi yayi
"First love Good evening" sai da ta gandama sannan tace
"Evening.. Yanzu Salem Dan nace kar ka auri Yoruba shine ka yadani...yanzu ka nuna
min tafini matsayi kenan ko?" Ahankali Salem yace
"Umma babu wacce zata taba kaiki matsayi balle ta fiki...amma Umma it hurt me Ashe
you don't trust my choice.. Am 35 am old enough to make my decisions..."
"Shut up there..." Tafada tare da zaginshi da fillanci sannan ta cigaba dacewa
"Habibi..kazo zan baka yarinyan da bazaka yi Dana saniba..."
"Umma please.. I love tawa..." Kat ta katse wayan ta. Salem ya kwanta yana tunanin
abinda zaiyi next.

Ameera tana farkawa daga bacci ta fito waje, ji tayi ana kiraye2 sallan asar don
rana yayi nisa sosai, wani irin matsiyacin ciwon kai take har lokacin, bakin gate
taje ta tsaya ta kwankwansa
"Dan Allah Ku bude min ..." Wani irin daria masu gadi sukayi
"Ke wuce ki koma inda sir ya ajiyeki..baa bamu umarnin mu bude maki gate ba..."
"Dan Allah Ku taimakamin.. Wallahi yunwa nakeji" banza sukayi daita, fara buga
kofan tayi, tana bugawa tana kuka, still banza sukayi daita, kallon gidan tayi yaga
wani dutsi ta dauka tafara bugun kofan da karfi, duk yan kauyen dake area din suna
jin bugun da take, tana kuka tana cewa
"Jamaa Ku tai makeni..kasheni zasuyi" kunsan yan kauye da iyayi, nan take suka cika
kofan gidan, suna cewa
"Ku bude mata mana ko Ku yan yankan kanu ne?" Ameera najin abinda suke cewa ta
cigaba da kuka sosai, tana
"Ku taimaka min..yankani zasuyi" wata tsohuwa cikin yan kauyen tace
"Daman daga ganin wannan gidan bana arziki bane.. Gida da tsawo kaman husumiyan
babila?..to Ku budeta ko musa matasan mu su suburbudeku yanzu nan" masu gadi najin
ance zaa suburbudesu suka fara cewa
"Aa bar mu kirawo Wanda ya kawomu gadinta" daya daga cikin su ya kira agent din
daya basu aiki ya sanar dashi abinda ke faruwa, shikuma agent ya kira Salem,
Har lokacin Salem bai mike zaune ba, yana ganin kira agent yayi tsoki
"What did he want" ya fada sannan yayi picking tare da cewa
"What?" Ahankali agent ya fada mashi abinda ke faruwa
"Send me the number of the security men" yafada tare da katse wayan shi, ko minti
biyu baa yiba number ta shigo mashi, kiran number yayi, ana picking yaji hayaniya
sosai
"Hello" a tsawace Salem yace
"Put the phone on speak.. I want to talk to those idiots"
"Yes sir" mutumin yace sannan Salem yaji suna cewa
"Jamaaku saurara..Wanda ya kawota zaiyi maku magana" nan take sukayi tsit kaman
ruwa ya cinye su, Salem yace
"Kuma jina?" Abinka da China phone maganan kaman saurin yayi ta
"Wannan yarinyan dake cikin wurin matatace... Maza takebi shiyasa na kawota wurin
nace kar abarta ta fita...yanzu dana barta ta fita zata koma karuwanci..."
"Subhanallahi!!" Yaji suna ta maimaitawa, Salem sai dariya zuci yake, yacigaba
dacewa
"Yanzu kun ga laifina?" Duka su kace
"Aa" sai yaji wata tace
"yazamuyi mugane gaskiyar ka?" Baki Salem ya tabe sannan yace
"Abudawa mata uku daga cikin Ku su shiga su gani..babu kayan abinci da babu..in
yankata zaayi zan saya mata kayan abinci?..Kuma nasan da anbude zatayi kokarin
guduwa don ta koma karuwancinta kuma inkun barta ta fita alhaki kanku " yafada
kaman zai tuntsure da daria.

Daga chan bangaren suka zabi manyan mata guda uku mai gadi ya bude masu har lokacin
Salem bai kashe wayan shi ba. Itakam ameera batasan yanda akayi duk mutanen kofan
gidan sukayi shuru ba don batajin abinda Salem ke cewa Amman yaji ana
"Subhanallahi... Subhanallahi" tana ganin an bude kofa tayi kokarin fita , nan
Matan dake shigowa suka kamata suka maidata cikin gidan, Salem kam yanajin ihun
ameera ya tuntsure da dariya Amman bai bari sukajiba, yaji daya daga cikin Matan na
cewa
"Wallahi da gaske yake...da ganinta mutuniyar kirki bace" suka kara shakumota
sukayi ciki daita, ameera sabon ihu tafara tana cewa
"Stop touching me with your filthy.. Stinking hand.. Kar Ku kara tabani da karamin
hannunku..." Tas Salem yaji wata ta buge mata baki tare dacewa
"Kull...yara basu zagin manya nan wurin" ameera takara fashewa da ihu tana rike
bakinta, har lokacin maigadin bai cire wayan daga speaker ba, Salem yakara cewa
"Kuci mata uwa...bata da tarbiya"
"Ai mungan alaman hakan" suka amsa mashi, daya daga cikin Matan ta zagaya gidan
sannan tashiga kitchen taga lodin abinci, baki ta bude
"Amman wannan yarinyan baki da kirki... Ga kayan abinci kaman shago... Kai ko
shagon dalha bai da kayan abinci haka" ameera kam sai kuka take tana kokarin
kwacewa daga rikon daya dagacikin Matan, gashi babu bakin magana balle tayi zagin
data saba.

Matan fita sukayi mai gadin yabisu ya maida gate ya rufe har lokacin Salem bai
kashe wayanba, Matan dasuka shiga suka tabbatar masu cewa ba gidan yankan kai bane.
Salem yakara cewa
"Yanzu kun yarda da magana ta?"
"Eh..." Suka amsa mashi sannan yacigaba dacewa
"to inason Ku sami wacce ta fi kowa kazanta ta dinga zuwa koya mata abinci zan
biyata duk karshen wata" duka suka ce
"Ai indai kazama kake son ta koya mata abinci sai hinde..tafi kowa kazanta nan
unkuwan"
"To daga gobe ta dinga zuwa tana koya mata abinci" sannan yayi was masu gadin
umarnin su rage volume din wayan, bayan mutumin ya kanga wayan ga kunne Salem yace
"Ku dinga barinmace daya tana shiga gidan ...sannan ban daita ban amince Ku bar
wata ta shigaba" katse wayanshi yayi yana shuumin daria
"We're are just getting started.. Bitch" agent dinshi ya kara kira ya gaya mashi ya
saka CCTV cameras cikin koina na gidan ayi mashi recording din abubuwan dake faruwa
cikin gidan.

Aranan ameera kam rana bata kara cin abinci ba, sau uku tana shiga kitchen Amman
bata iya sarrafa kayan abinci ba, kuka tayi har daga baya hawaye suka bar zubo
mata, bayan sallan ishai ta koma ta zauna daga bakin gate inda zata dinga jin
motsin mutane, adua take mutuwa yazo ya dauketa kawai ta huta.

bayan sallan ishai Salem yaje gidan su tawa, cikin dakin su suka zauna suka sha
hiransu, banda kallon ta babu abinda yakeyi don gani yake in har iyayensu basu
yarda suyi aureba yana Iya dauketa ya maida ta wata kasan a daura masu aure don
yasan babu abinda zaace dazai hanashi auren ta saidai wani iko daga rabbi, dazai
tafi tabashi tuwon shinkafa cikin cooler, mamaki ne kwance kan fuskanshi donshi har
ya manta da maganan tuwon.
Aranan ne yasani cewa abinci basai da nama, kifi, kayan ciki etc yake dadi ba don
kashine cikin miyan Amman it's the most delicious tuwon shinkafa daya taba ci, yana
ci yana waya daita yana yi mata santi
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE"


®zuwairat(ummu maryam)

2⃣9⃣


Wacegari bayan ya dawo daga masjid ya kwanta yana tunanin abinci tawa, shidai in so
samune ta cigaba dayi mashi

12 / 44