Author : ummu maryam Category : Complete Novels
tambayeshi ahankali, gyara kwanciyan shi yayi sannan yace
"Will you do anything I want?" Cikin kuka tace
"Eh..." Dan murmushi yayi
"Will you let me make lo...."
"Please stop.."
"But you say you will do what ever I want..."
"Banda irin wannan maganan..."
"OK..naji...remember its my wedding..."
"Sai Anjuma... Zanyi bacci" Salem lumshe idanuwa yayi yana tunanin ta kwance next
to him,
"To shikenan.. Let me call my wify...sai da safe"
"Na fasa baccin.." Tafada da sauri, dariya Salem yayi sosai.
"Jealousy....keda na dinga binki ina rokonki ki fadamin inda kike kinata jamin
aji...to gashi yanzu ajin ya tsinke na samu wata...".
" wallahi ka bar cemin ajina ya tsinke... ".
" karya nayi?...wai kaman ni ki tsaya kina jamin aji... Nida mata suke kashe Kansu
saboda..anyway kiyi murna da bake zan auraba..don na rantse inke na aura saina
dauki mataki kanki for playing with my heart... "
"I said am sorry..."
"Is not enough..." Shuru sukayi Salem najin wani irin dadi cikin ranshi.
"Nidai ka yafemin...I will not run away again..." Dan murmushi yayi
"Kima gudu I will be right behind you.." Yafada cikin ranshi
"Wai habibty wannan number mami ce?"
"Eh..."
"Hmmm...ki turo account in sa maki kudi ki sayi waya...for the sake of
friendship..."
"Banso...."
"To shikenan... Ai bazan kara rokonki kan komaiba cos you are stubborn..." Shuru
tayi batace komai ba yacigaba dacewa
"Kuma zanyi Maganin stubbornness dinki...when the time is right..." Yafada kasan
makoshinshi, su biyu shuru sukayi suna sauraron breathing din junan su, ahankali
Salem yace
"Habibty kinsan kasan da zanyi honeymoon dina?..." Cikin whisper tace
"No"
"Instabul...INA gida on the mountain view...daga nan zai in wuce Hollywood chan ma
ina da gida kuma in kina wurin duk american actors and actress zaki gansu...sai
kumaBeverly hills California ..in short zan 12 countries for my honeymoon...." Tawa
shuru tayi tana tunanin yanzu inda ummanshi da mami sun amince da daita zaayi
wannan yawon ganin duniyan, wasu hawayene ya kara zubo mata, ahankali Salem yace
"Habibty kinyi shuru... Ko jealous din ne...and habibty kinsan in matata ta haihu
indai inagida ni zan dinga chanza diapers.. I want to be the perfect hubby..." Ita
dai tawa shuru tayi batace kala ba, karaf taji su mami sun dawo sai Neman ta ake a
falo, da sauri tace
"Sir I have to go...su mami sun dawo..."
"OK...good night... Love you" bata amsa mashi ba ta katse wayan tana goge
hawayenta.
Tana fita falo taga mami na kuka yayanta sai rarrashin ta take, nan take hankali ta
ya tashi, da sauri ta karasa inda mami take ta durkusa gabanta
"Mami...menene?.. Why are you crying?" Mami bata amsa ba tacigaba da kuka, mami
kallon yayanta tayi tana cewa
"Nasan kilan ya samu labarin ni da yata suna garin nan...yanzu anty in ya koremu
ina zani da yarinyan nan... Ban Iya komawa Kano...." Tafada cikin kuka sosai,
itadai tawa har lokacin batasan abinda mami ke cewaba,
"Haba.. Kinsan koma meye he's your father... Kawai kiyi hakuri gobe muje muji kiran
dayake yi maki...kuma ai ba ke kadai ya kiraba... Dukkan mu ya kira...."
"anty stop saying that.. Kinsan wannan yaron don ni da yata zaayi shi...I think the
best option shine in koma garin mijina..."
"No!" Yayanta ta daga mata tsawa, sannan ta sausauta murya tafara cewa
"Ai kina zuwa wajena tun ba yauba...kuma baitaba kirankiba sai ka yanzu...for the
past 19 years oba bai nuna yanason ganimki ba sai yanzu..in kika ki zuwa kin kara
disrespecting dinshi so kawai gobe muje..." Sai lokacin tawa tagane kakanta ne
yakeson ganin mami, ba mamiba har ita gabanta faduwa take, don bata taba ganin shi,
hannun ta tasa ta gogewa mami hawayenta tana cewa
"Stop crying"
❤
Ameera sabon holewa ake don tun rananda Salem ya bargida tasa guard dinshi yayi
mata shopping din kayan dadi take shagalin ta, baa kara hura wuta gidanba don dama
tun gida Abinci bai dametaba barta kawai da kayan lashe2, Yanzu kullum tana waya da
gida kuma ko kadan batayi gigin fada masu abinda ke faruwa ba, kullum mom na fada
mata ta turo mata pictures din gidanta sai tace zata turo, ko yanzu waya suke da
mom tana cewa
" mom har yanzu baki turo min number zeenat ba..."
"Oh sorry habibty... Bari in kira Hajiyan ta ta fada mata ta kiraki yanzu nan..."
"Yau wa mom nagode.." Dadi mom taji don halin ameera nada Dana yanzu ba daya bane
cos yanzu tana kwantar da hankali suyi hira
"Habibty ki gaida mijinki....kuma insha Allah anty Sadiya tana nan tafe..." Dan
baki ameera ta tabe don wani haushin anty takeji
"To mom..." Sallama sukayi sannan ta ajiye wayan ta dauki sauran snickers data ci
ta rage ta cigaba daci tana korawa da juice.
Bayan kaman minti ashirin wayanta yafara ringing, da sauri ta dauki wayan tana
dubawa ta gane zeenat ce don dukda bata haddace digits dinta ba tasan last number,
da sauri tayi picking tana cewa
"Shegiya kawas...I miss you die..." Daga chan bangaren zeenat sai jumping take tana
cewa
"Babe yaushe kuka shigo kasan?" Ameera kallon gidan da take ciki tayi sannan tace
"Shekaranjiya..."
"Wayyo Allah na...ya amarci...please babe yan mi tori...."
"Ke wallahi banzace...kina nufin..."
"Yes ina nufin ki fadamin yanda first night dinki ya kasance..." Ameera shuru tayi
tana tunanin abincewa
"Please babe inajinki..next week iyayen hameed zasuzo...very soon zanyi joining
league naku..." Nan take jikin ameera yayi sanyi don ita hameed ya nacewa amma ta
nuna ba ajinta bane shi, babu irin wulakanci da bata yi mashi ba, karfin hali tayi
sannan tace
"Woww...am happy for you...." Da sauri zeenat ta katse ta dacewa
"Forget... Sis ni kawai tell me...first night da zafi kaman yanda ake cewa?" Ameera
shuru tayi hawaye na taruwa idanuwanta, kaman yafadawa zeenat matsala ta takeji
amma tasan muddin ta fadawa zeenat tamkar ta fadawa iyayenta ne kuma tasan ko
iyayenta sunyi kadan su kwace ta daga hannun Salem.
"Babe..inajinki... Wallahi jikinna har rawa yake...hameed cewa yayi a Hilton
zamuyi honeymoon... Allah sai wani irin doki yake..ni har tsoro yake bani..."
Ameera goge hawayn daya gangaro mata tayi cikin sanyi murya tace
"babe mu bar wannan maganan sai wata rana..." Da sauri zeenat tace
"This voice is unlike yours...kodai sir Salem yayi maki raga2...ko kuma ince ya
koya maki manners of talking.. " ita dai ameera batace komaiba zeenat tacigaba
dacewa
"Anyway tunda bakison fadamin... Send me your international photos don na sanki da
selfie..." Ahankali ameera tace
"Banyi photo ba..."
"Wallahi kinyi karya...keda koda shop rite muka shiga sai kinyi selfie balle
Spain?...please send me jare..."
"Baya bari photo... " tafada kuma dakaji maganan kasan karya take, shuru zeenat
tayi for a moment sannan tace
"Babe you are sounding weird... Ko dai wani abu na damunki?.." Ameera kallon wani
katon lizard dake jikin bango dan nesa daita tayi da sauri ta mike daga gurin tana
cewa
" babe zan kiraki..."
"Ya dawo ne?" Zeenat ta tambayeta
"Eh kawai tace sannan ta katse wayanta.
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE
❤
®zuwairat(ummu maryam)
4⃣5⃣
Daki ta shige da gudu ta rufe tana maida numfashi, arayuwa babu abinda take tsoro
kaman lizard, lekawa tayi ta window taga yana gurin zaune ko matsawa batayiba,
kurya ta koma don gani take yana iya binta, kwantawa tayi ta fara kuka.
"Wallahi nagaji da zama gidan nan...am feed up..." Tafada a tsiwace.
Aranan bata kara fitaba, daga baya ta kira zeenat suka shigaba da hiransu.
❤
Su Abba sunyi niyyan baro palace yau Sunday amma OBJ yace subari har sai sun ga
zuwansu ameenatu, to kawai Abba yace mashi.
Abangaren su mami kam tun wayewan gari ta kara shiga sabon tashin sense, gani take
korarta daga garin oba zaiyi, da wuri suka kama hanyan kwara daga Ilorin da mom sai
yaranta uku tare da tawa da mami don haka aka ce masu kowa ya zo da family dinshi,
daman mijin mom baya kasan. Femi ya dinga tukin mota sai kallon tawa datayi takumi,
dayayi tuki kadan daya daga kai ya kalli tawa, acikin zuciyanshi yana mugun son
tawa amma yasan Sam aladansu babu zancen auren zumunci, mami da mom suna baya sit
din karshe sai kuka take mom na rarrashin ta.
Da wuri suka isa palace, da kyar mom ta fito da mami dake tsoron palace kaman ba
gidan ubantaba, itama tawa jiki ba kwari ta fito, ahankali femi ya karasa wurin ta
"sis you look pale...what's the problem?" Ahankali ta juyo ta kalleshi sannan tayi
forming murmushi karya
"Nothing... Kawai kukan mami ke tadamin hankali" hannu ya dora kan kafadanta
"Don't worry.. Everything will be alright..." Kai kawai ta gyada mashi.
Cikin palace suka shiga kowa ya nufi inda oba da mutanen sa ke zama, daidai lokacin
da Abba da su OBJ suka iso, mami da sauran yanuwan ta suka shiga dukkan su sai
kallon ta suke kaman ba yar uwansu ba, itakam mami sai mamakin abinda Yusuf
sulaiman Abba Salem yake palace din babanta, don tasan shine baban Salem, itakam
tawa batasan Abba Salem ba. Daga nesa oba ya kurawa mami ido, Abba da obj gaisawa
sukayi da oba sannan suka zauna, mami sam bata daga kai ba, dukkan yaran kwanatawa
kasa sukayi sauka gaida oba sannan suka zauna, Abba sai tunanin anya Salem na iya
wannan kwanciya kasan, da juyawa yayi ya hangi yarinyan dake kusa da mami nan ya
gane itace yarinyan data sacewa danshi zuciya
"She's adorable..." yafada cikin ranshi.
Ji yayi oba nace addua sannan ya fara cewa
"Alhamdulillah..nasan dukkan Ku kuna mamakin abinda yasa na taraku duka wurin
nan..." Shuru yayi sannan yacigaba dacewa
"Kunsan am not a king with many words... Kaman yanda kuka Sani ameenatu bata cikin
yarana saboda abinda ta aikata...Wanda nasan dukkanku nan kunsani..." Shuru ya kuma
yi a wannan lokacin zucyan mami kaman ya fito don yanda take harvawa, ahankali oba
yacigaba dacewa
"To kaman yanda nayi announcing na cireta daga cikin yayana...ta ci darajan wayan
nan Nigeria legends din ..." Ya fada yan nuna Abba da OBJ da wani abu na yan
sarauta dake hannun shi
"Ni oba sadiku ayodele na maida ameenatu cikin yarana!..." Aikam gabaki daya family
kwantawa sukayi kasa suna nuna godiyansu, mami sabon babi kuka ta bude tayi
kneeling ta rarrafa har gaban oba ta rungume kafafunshi tana kuka tana cewa
"Pami am sorry... Am sorry...." Bata karasa ba ya jawota ya rungume ta..
"I miss you.. My stubborn princess..." Cikin kuka mami tayi daria, ahankali shima
yace
"Am sorry my princess... Mulki yasani son hana abinda Allah ya hada..." Mami tana
rungume da jikin tsohon ta ta girgiza kai
"No..pami..." Da sauri oba yace where is my granddaughter, mami Dan janyewa tayi ta
kira tawa, ahankali ta karasa wurin tayi kneeling gaban oba, abun hannun shi yadan
dora bisakanta ya dinga jero adduoi dukkan yan palace na amsawa da ameen. Abba
kallon natsuwan tawa kawai yake acikin zuciyanshi yana
"Alhamdulillah Dana yayi dace...Allah yasa kinada hali na gari" shikam OBJ har Dan
guntun hawaye ya goge, oba kallon yara da jikokinshi dake kwance kasa yayi
"Bani zaku gaidaba..Ku gaida wayan nan" yafada yana nuna Abba da OBJ, dukkan su
juyawa sukayi daga kwance suka fuskanci inda Abba da OBJ suke sukayi masu godiya.
Bayan kaman hour daya Abba da OBJ suka hau jet aka sauke OBJ a osun sannan Abba
yayi hanyar yola.
Murna a family dinsu mami kaman anyi aure don gidan shika yayi da family, gasu
masu hali da naira mami da tawa ne kadai suka fita daban cikin su, saukin ma kayan
da mom tasa aka dayawa tawa sai man da take shafawa, don ba laifi skin dinta ya
danfi da kyau da haske.
Aranan aka sauke su mami da tawa acikin wani 4 bedroom apartment dake cikin palace
din, sannan aka bawa mami maidens biyu don su dinga yi mata hidima, mami cewa tayi
bata bukatan su amma oba yace dole princess saida maiden. Kuma ranar oba ya sanar
dasu cewa ranar asabar mai zuwa zaayi bikin maidawa mami da tawa kayan sarauta.
Abba yana isa gida Salem ya rungume shi babu kunya ya dinga jera mashi kisses a
hannu
"Kai baka da kunya ko?..." Abba yafada yana daria, shima Salem daria ya dingayi
yana cewa
"Am too excited.. Thanks"
"Ai naga yarinyan... She is so adorable... Gaskiya ka iya zabi..." Salem rufe
fuskanshi yayi yana daria
"Abba you mean you saw Tawakaltu?..." Yafada cikin exaggeration,
"Eh mana...yanzu suna palace"
"Thank you so much Abba..."
"Son don't thank me, ka kaiwa obasonjo gaisuwa don ya taimaka sosai..."
"Hmmm..he has always been a wonderful person.. " ya fada yana budewa Abba kofan
side dinshi. Abba zama yayi Salem ya nufi fridge ya dauko mashi fresh cow milk da
ruwa, ruwan ya fara zuba mashi yasha sannan ya zuba mashi milk din ya mika mashi,
Salem komawa yayi a zauna yana kallon Abba ya kasa daina murmushi
"Yanzu Abba next week zamu kwara?" Abba Dan kurban milk din yayi sannan yace
"Bafa wannan week dinba sarkin zumudi...I said next week Saturday..." Salem daria
yayi
"To Abba... Da wa zamu?"
"Aa... Ban gane da wa zamuba.. Ga uncles dinka sannan ga friends irin su OBJ"
ahankali Salem yace
"Abba kana ganin su uncle bazasu nuna tribalism ba kuwa?.." Abba ajiye cup dinshi
yayi sannan yace
"Kaji zancen banza...tribalism na marasa ilimine...ai in mutum yana da ilimi yasan
komai na Allah ne...kuma kasan su uncle dinka sunfi civilize saboda sun zauna
wurare daban2" Dan ajiyan zuciya Salem yayi yana tunanin yanzu babu wani obstacles
gabanshi dazai hanashi auren Tawakaltu, yana cikin tunani ummanshi ta shigo, Abba
bude mata hannu yayi ya fada jikinshi ya sumbaceta a goshi, Salem relaxing yayi kan
sofa yana kallon iyayenshi cikin shaawa da jindadi
"Umma ina nan fa..." Yafada yana daria, Umma juyowa tayi ta kalleshi tana murmushi,
zama tayi gefen mijin ta tana cewa
"Alh ka dawo lafiya?"
"Alhamdulillah.."
"Ya OBJ?" tambayeshi kasancewan batasan asalin dalilin dayasa Abba zuwa kwara ba,
suna nan zaune Abba ya fada mata komai gameda tafiyan da yayi, Umma shuru tayi don
har cikin ranta batason danta ya auri wata yare sannan kuma har ga Allah bata ga
aibun Tawakaltu ba ko kadan ita kawai alada ke batason jikokinta suyi exchanging
amma who is she to separate what Allah have joined, shuru datayi yasa Salem kallon
Abba da zara2 idanuwanshi sannan ya mike ahankali da niyyan tafiya part dinshi, sai
lokacin Umma ta dawo hankalinta
"Son ina zaka kuma?" Ahankali ya juyo ya kalleta
"I want to go..." Cikin sanyin murya Umma tace
"Habibi dawo ka zauna" ahankali ya tako zuwa gaban Umma ya durkusa, Abba sai kallon
su yake, Salem dafa gwaiwan Umma yayi
"Umma nasan har yanzu baki son Tawakaltu..." Dasauri Umma ta rufe mashi baki
"Habibi stop saying that... Batawa ke banisoba...its just the language.. Tawa is a
lovely girl... Amma habibi I give you my 100% support... You have my blessings..."
Da sauri ya mike ya rungume Umma
"Thanks so much...insha Allah ba zamuyi regretting ba..." Umma pointed noise mai
kama da nata taja
"Allah yasa Ummas habibi.."
"Argggg... " yafada yana shafa inda Umma ta rike mashi hanci. Haka suka cigaba dari
hiransu cikin jindadi, amma fa har lokacin Umma bata bar tunanin Yoruba daughter
in-law dintaba...ko ya abun zai kasance?.. Oho....
_One week later_
Kowa na inda yake don ameera kam bata da friends sai lizard don tamkar sunsan tana
tsoron su, most of the time tana daki, abun takaici tunda Salem yace kar akara
barin hinde ta shigo bata kara shigowa ba, sai tayi kusan hour 10 tana waya da
friends and family.
Salem kam ya koma aiki amma komai nashi ya koma shiririta don banda waya da
princess tawa babu abinda yakeyi kullum saiya sata tayi mashi kuka hankalinshi yake
kwantawa, don kullum cikin zolayanta da sabon amaryanshi yake, he's tormenting her
to death and he's enjoying every part of it.
Abangaren tawa kam jiya akayi party basu right place dinsu a kwara, mutane da dama
sunzo don har da yan nta da AIT, yanzu sabon rayuwa suke ciki don wata babban
fashion artist CE mai dauko designer and qualitative dress ta kawo masu dresses,
duk Wanda yaga tawa yasan she's royalty don da akwai bead sakale agaban goshint,
sannan da akwai bead a kafafunta biyu kaman leglace sai daya a hannun ta na dama,
jikin ta yayi mugun kyau amma kuma ta rame sosai don yanda Salem ke tada mata
hankali don har cemata yake in yasan inda take zai kawo mata matanshi su gaisa.
Rayuwan palace Sam baiyi mata dadi cos cousins dinta are so expose to life, cikin
yan Matan babu mai saka normal skirt da riga saidai kaga an saga skirt abaya sosai
ko kuma a gefe, datayi dressing sai su dinga cewa
"Princess toyin.. Omo Hausa" wai yar Hausa
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE
❤
®zuwairat(ummu maryam)
4⃣6⃣
Mata dake kawo kayan sawansu ne ta kaya cike da box dukkan jikonki oba su zama
saboda ya fada masu zaayi babban bako a palace,
"Duk jikokina yan mata su shirya...ranar asabar mai zuwa zamuyi bako...kuma bakon
sananne ne akasan nan...kuma nayi farin ciki daya ga family din mu worthy.. Kunsan
aladan mu dole yazo ya nuna mana wacce yakeso cikin Ku.." Oba yafada masu jiya
wajen shagalin su mami, hakan yasa Matan ta bus shike da decent kaya, irin su
jallabiya da long gowns, don oba ya bata umarnin kar ta kawo kayan banza don yasan
halin jikokinshi.
A wani katon falo a juye kayan ko wacce cikin su shida sai zaba suke, sai da suka
zaba sai daya ta juya ta kalli tima
"Wai ina toyin?" Sai lokacin tima ta lura da babu tawa awajen, ajiye kayan ta tayi
ta nufi part dinsu tawa.
Tawa na kwance kanta kan cinya mami, sai kallon yanda mami ta chanza cikin kankanin
lokaci take, daga idanuwanta tayi tana kallon mami, karaf suka hada ido, da sauri
mami ta rufe mata idanuwa da hannun ta
"Ife..wayan nan idanuwan suna bani tsoro.." Tawa daria tayi, sai kuma tayi shuru
for a moment sannan tace
"Mami" ta kira ta, Ahankali mami tana shafa kanta
"Yes love" ta amsa mata cikin so da kulawa
"Are you happy?..." Mami taji ta tambayeta, mami shuru tayi tana kallon ta,
Ahankali ta gyada mata kai
"Yes..am very happy..na dade banji irin wannan farin cikin ba" tafada tana
murmushi, tana shafa kan tawa tace
"Habibty.. A you happy?..." Tawa kara daga manyan idanuwanta tayi ta kalli mami,
shuru tayi batace komaiba , Ahankali mami takara cewa
"Love are you happy?..." Ahankali ta girgiza wa mami kai, cikin sanyin murya tace
"Why love" tawa fashewa tayi da kuka tana cewa
"Mami..sir Salem is getting married!" Da sauri mami ta daga ta ta rungume
"Don't cry...kilan hakan shiyafi alkhairi.... Koda ni na amince.. Kina Iya auren
Wanda ummanshi bata sonki?.." Da sauri ta girgizawa mami kai
"No..mami..I can't"
"Good... So ki mance dashi..ki koma school.. Nasan insha Allah kafin ki gama degree
dinki Allah zai kawo miji na gari..." Cikin kuka tace
"But mami I love him..."
"Habibty you are too young to know what love is..." Mami tafada tana shafa bayan
tawa dake kuka kaman ranta zai fita tace
"Mami.. My heart beats for him" mami dai shuru tayi tana rarrashin ta don tasan
yarta da kafiya kan abu, suna cikin hakane tima tayi sallama tashigo ,
"Mami meyasa toyin bata zo daukan kayaba?" Tafada bayan ta gaida mami,
"Oh..na mance... Habibty tashi maza kije ki dauki kaya..." Tawa mikewa tayi daga
jikin mami tare da goge hawayenta, tima batace komai ba don ta saba da ganin tana
kuka
"Mami na meye kayan?" Daria mami tayi, ta tuna mata abinda oba ya fada jiya, komawa
tayi ta kwanta
"Gaskiya mami ban zuwa...." Bata idaba mami ta katseta dacewa
"Kai...Aa ..karki yiwa oba gardama.. Kuma aladanmu dole yan Matan mu su shirya in
yar uwansu zatayi introducing Wanda