Author : ummu maryam Category : Complete Novels
cewa
yayi
"Sao yanzu ka gandama kenan..." Khalid Dariya kawai yayi,
"Sai ayi bincike kan family dinsu kafin muje ayi maganan aure..." Inji his
excellency,
_One week later_
Duk binciken daya kamata su dad sunyi kuma babu Wanda bai shaidan halin Khalid ba,
asalima cewa akayi yafi sauran brothers dinshi mutunci, ( hmmm daman bincike baisa
agane dukkan halin mutum.. Sai ka zauna dashi)
Abangaren Khalid kam suma anyi bincike amma sun gano yarinyan ta taba aure,
"Yanzu son yarinyan data taba aure zaka aura as a first wife?.." Shine tambayan da
mom dinshi tayi mashi, ahankali Khalid yace
"Mom..ita nakeso....kuma duk karyan mutane ne...bata taba aureba...."
"AI ba hanaka zanyi ba tunda ba haramun bane...am happy zakayi aure" Tafada cikin
jin dadi.
Bayan sati daya uncles din Khalid da wasu manyan mutane sukaje gidan su Ameera
Neman aurenta, kuma da kayan saka rana sukazo, Dad dadi sosai yaji don yasan yanzu
yarshi zatayi aure, anci ansha Sannan aka sa sati 8 that's two months.
Tunda daga ranan aka dauko mai koyawa Ameera abinci da sauran aikace2 gida. Ana
sauran 7 weeks Khalid ya shigo Kano, ba karamin kyau yayiba, itama tayi kyau sosai
saboda gyaran jikin da anty Sadiya ta fara yi mata, kasa daina kallon ta yayi,
kanta kasa Sai wasa take da fingers,
"Babyna haduwanki bai faduwa..." Yafada yana murmushi, itama murmushi tayi,
"Do you have any special events in mind?.." Ya tambayeta, ahankali ta girgiza mashi
kai
"So ki yarda in sa ashirya all the events?.." Ya sake tambayan ta, ahankali ta daga
mashi kai, kallon ta yayi
"Baby wannan kunyan fah?...tunda nazo baki daga kai kika kalleni ba...what have I
done wrong.." Ya tambayeta kaman zaiyi kuka
"Nothing..."
"Then pls look at me..." Yafada cikin whisper, daga kanta tayi suka hada ido, ido
daya ya kashe mata, tayi murmushi tare da dauke kanta,
"Angel INA kikeso mu zauna?... I have two duplexes in abuja....two in yola Sai one
a banana island lagos..." Ameera shuru tayi bata ce komai ba don babu abinda take
tunawa kaman ya kusa ganin nakedness dinta,
"Angel say something.."
"Duk inda kakeso..." Ta fada mashi
"Ko in sayi gida nan Kano?..." Kallon tayi ta saki murmushi, Dariya yayi
"Baki idaba yarinya... You want to be close to mommy..." Ya fada yana dariya, Itama
Dariya tayi don ya gano ta,
"Ai bance mu zauna nan bako..." Ta fada cikin shagwaba, Dariya ya karayi yana cewa
"sayi gida nan mu dinga sauka in Mun zo Kano..." Daga kai tayi ta harareshi
"Ga gidanmu?..." Baice komai ba ya sa hannu cikin aljihunshi ya dauko wani small
jewelry box, ya bude, wani white ring ne mai dauke da diamond stone samanshi,
hannun ta ya kama ya sa mata Sannan ya Kara dauko wani envelope ya saka cikin palm
dinta, kallon zoben tayi ta saki murmushi cos ba karamin kyau yayi wa hannun ta ba.
Sun dade suna hira batare data bude envelope dinba, sallama yayi mata ya kuma
shaida mata yanzu saidai su dinga waya cos he will be very busy saboda wedding
arrangements.
Tana komawa sama taga credit card ne da pin number kiranshi tayi ta tambayeshi ATM
din na meye ya shaida mata ta zari any amount da take bukata for her friends anko.
Duk yanmatan dake yiwa Ameera habaici saida suka dawo suka bata hakuri don ta dama
dasu, batayi masu wulakanci ba aka shiga harkoki dasu, zeenat kam bataji dadi
abinda Ameera tayiwa sultan ba amma she takes everything in good faith.
Ba karamin gyara Ameera take shaba don abubuwan is to much, jikin ta ya kara kyau
fiye da yanda kuke tunani, kullum cikin waya suke da Khalid.
Ana sauran sati four biki aka kawo lefenta, fadin kyau da yawan kayan is a waste of
time and strength just imagine lefen yayan governor, kuma civilised one don mom din
Khalid wise woman ce ta gidan karshe, akwati 18 aka kawo 12 lv sai 6 gucci
traveling bag da mota daya sai kujeran makka 3, mom kam abun tsoro ya bata dad baki
har kunne saboda jin dadi, duk Wanda ya zo ganin lefen Sai ya koma da baki bude,
aranan Ameera da Khalid suna waya take shaida mashi kayan sunyi yawa, cewa yayi bai
ma gansuba Kuma ta dauka duk yawan kayan can never be compired to her beauty.
Abangaren Salem kam duk ya damu ba don komai ba sai yanda Khalid yaki amsan komai
daga hannun shi, duk abinda ya bashi Sai ya ki amsa yana cewa bayason rai Ameera ya
baci, ko yanzu suna zaune da tawa tawa suna kallo shi kuma yana waya da Khalid,
"Guy gaskiya abubuwan da kakeyi is touching me... Ya zakayi min haka...we grow up
together... Amma zakayi aure ka ki amince wa da komai daga gareni..." Inji Salem
daga chan bangaren Khalid yace
"Just understand....banason abinda zaisa Ameera bacin rai...remember she almost
dump me because of you..." Gyara zama Salem yayi Sannan yace
"Yanzu guy mace zata rabamu da kai kenan?..."
"Haba wake maganan rabuwa...it's just for the main time..." Inji Khalid,
"Ba komai...we will be coming back next week..." Inji Salem yana rike hannun tawa,
da sauri Khalid yace
"I beg you in the precious names of Allah... Don't come back now... Wait until five
weeks for now..." Ido Salem ya zaro
"Hope this is not what am thinking?..."
"Yes it is... In ka dawo su first lady da first love zasuyi mamakin rashin ganin ka
a wedding dina...so pls just wait till after my wedding..."
"Yanzu Khalid are you saying I should not be present at your wedding?.." Ya
tambayeshi afusace, ahankali Khalid yace
"am sorry but yes...." Salem bai Kara cewa komai na ya katse wayanshi tare da
mikewa daga inda yake zaune kusa da Tawakaltu, da sauri ta bi bayan shi,
"What's wrong?..." Ta tambayeshi,
"Nothing..." Ya fada mata atakaice, rike mashi hannun tayi ya fixge
"I said nothing!...." Ya daka mata tsawa, da sauri ta ja baya, tana kallon shi,
gaba yayi tabi bayan shi Ahankali, afusace ya juyo ya kalleta fuskan shi Sam babu
walwala
"See just go back...right now am upset and I don't want to be disturbed..." Kuka
tafarayi tana cewa
"So am disturbing you?...to shikenan... Let me keep my distance..." Tafada tana
juyawa Ahankali tare da dafa maranta, Salem tsaya kallon ta yayi har ta zaunasai
yaji bai kyauta ba cos ba ita tayi mashi laifi ba amma he's taking it on her,
komawa yayi wajenta,
"Princess am sorry... Kawai rainane a bace...kiyi hakuri kinji?"... Kai ta daga
mashi, hannu yasa ya goge mata hawayenta tare da jawota jikinshi.
Ahankali lokacin ke tafiya inda Khalid ya kawowa Ameera list na events da zasuyi
for a whole week, kuma ko wanne rana nada dress code, ana sauran two weeks Ameera
ta rabawa friends dinta iv. Yanmatan kam shirye suke don sunji abun nayine.
Gyaran da anty Sadiya takewa Ameera yafi na wancan lokacin cos ta samu enough time
and money, Sannan lefen da aka kawo ya Kara nunawa cewa ba anyhow mutum zata aura
ba haka yasa kullum da abinda take bata, Sannan yanzu ba laifi Ameera ta iya at
least not less than 15 variety of food
Duk Wanda yaga pre wedding pics dinsu Sai yace Ameera da Khalid sis and bro ne
saboda yanayin hasken su da pointed noise,guys Sai zolayan Khalid suke suna cewa ya
fi abokinshi iya zabe, cikin ranshi kam saidai yace bakusan shi ya fara aurenta ba.
Yau sauran ten days saurin aure, da yamma around 5pm wani moving van ya shigo
gidan, mom fitowa tayi tana kallon katon van din Sai mamaki van din take don sai
gobe kayan Ameera suke isowa, driver ya fito daga cikin van tare da yaranshi,
kallon mom dake ta mamaki yayi Sannan yace
"Sakone daga sultan..." Baki mom ta bude da aka fara sauke kayan, complete set ne
na kujera da da gado, exactly irin na zeenat, mom komawa ciki tayi ta fadawa Ameera
abinda dake faruwa, kiran sultan tayi amma baiyi picking ba..
Ana sauran nine days daurin aure governor na Kano ya amshe dukkan hotel da quest
house saboda baki kuma baban Khalid babban abokinshi ne.
Tun sauran 8 days gayu suka shika garin kano, duk inda kika ratsa handsome guys
kake gani daman Khalid yafi Salem hulda da guys kuma yafi shi shiga social life.
Umman da abban Salem Sai kiranshi suke suna why bai dawo ba har zaayi bikin
amininshi, karya kawai yayi masu kan he's seriously sick, ammi kam cewa take
"Kuyi adua ya gane hanyar gidansu tunda ya auro mayu...kilan tana chan tana
zukeshi...."
Yau aka fara events, inda kunshi aka fara dashi, cikin katon hall dukkan yanmata ne
kawai Sai tsantsara masu hyena decor ake. Ga kidi yana tashi.
The following day akayi kauyawa party a gezawa gidan granny din Ameera, shigan
original yan kauye akayi, Khalid kam kasa daina kallon Ameera she was looking extra
stunning.
Sai Fulani night inda ango da amarya tare da friends sukayi shigan Fulani, followed
by Arabian nights Sai mothers night, yawancin Matan governor sun hallaci wannan
taron.
Sai picnics,
Atakaice ranar Friday akayi daurin auren Ameera da Khalid kan sadakin dubu Dari,
daurin auren ya samu manyan mutanen kasa, abinka da dan governor, Khalid kam
bakinshi bai rufuwa saboda
Farin ciki, bayan daurin aure aka wuce reception inda amarya ta sha silver flowy
gown daga companin varsace. Khalid ma ya sanyan suit silver mai dan sheki kaman an
zuba mashi ruwa.
😳😳😳😳 surprised?....don't be...am full of surprises💃🤣
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE.
❤
®zuwairat(ummu Maryam)
8⃣0⃣
*My Habeeba I don't know how to show my appreciation... But I want you to know I
love you, Allah ya bar kauna...* 💋💋💋
Ba karamin party akayi wurin reception, dama ga Ameera sarauniyar rawa kuma Khalid
sarkin rawa, rawa sukasha har na tashin hankali, Khalid komawa gefe yayi yana
kallon yanda matarshi take dansewa, daga baya iyaye tafiya sukayi suka bar yanmata
da samari suka shiga da party, wani crazy beat aka saka mai instrumental, fili yan
mata suka bawa samari suka shiga da rawa kaman hauka har da kwantawa kasa don dadin
dancing, suna cikin haka wata siririyar budurwa ta shigo mai shegen kyau kamar ita
tayi kanta, da ka ganta ka ga Khalid saidai ita tafishi kyau kasancewan ta mace, ga
hujen hanci rawa ta farayi ta nufo inda Khalid ke tsaye suna rawa, juyowa Khalid
yayi ya wangalo idanuwa tare da rungume yarinyan
"Baby ya akayi kika dawo?...bana fada maki kar kizoba?..." Ya tambayeta, marairace
fuska tayi tana cewa
"Kun hanani zuwa na yaya Salem Sannan kuma ashe kar inzo naka?...AI bani kadai ke
karatu abroad ba..." Khalid girgiza kai kawai yayi ya kama hannun ta yayi
introducing Ameera as his wife, yarinyan kissing Ameera tayi a cheeks dinta tana
cewa
"Yaya dole ka mutu kanta... Wannan kyau haka?..." Ameera da Khalid Dariya suka,
yarinyan wurin mc taje ta fada mashi ya fadawa mutane duka su zauna zata danse da
yayan ta, aikam kowa komawa yayi ya zauna ya rage daga yarinyan Sai Khalid cikin
katon filin, nan akasaka masu wani sabon waka suka fara rawa kaman mahaukata, banda
Dariya babu abinda Ameera da sauran mutane suke, Ameera har da rike ciki saboda
Dariya. Atakaice Sai twelve na dare aka tashi aka maida ameera gidansu cos the
following day zaa kaita yola, adaren mom ta zaunar daita tayi mata nasiha ba kadan
ba, har kuka Ameera ta farayi saboda yanda mom take magana. Sai wajen 3am ta
kwanta, wacegari da wuri mom ta tadata tayi sallan Sannan takara yimata nasiha kan
zamantakewa Daga nan ta koma dakinta Zainabu ta hada mata ruwan wanka mai dauke da
turare, tayi wanka ta fito ta tadda anty Sadiya ta fiddo mata wasu blue lace masu
shegen kyau da tsada, dinkin skirt da riga, skirt din har Jan kasa yake, ba karamin
kyau tayiba, kwalliya wance aka biya donyi mata kwalliya tayi kyau sosai, mom ta
kawo mata tea my kauri da kwai amma ta girgiza mata kai, zare mata ido mom tayi
"Mom na koshi..." Ta fada kaman zatayi kuka,
"Ubanme kike CI da safen nan zakice kin koshi?...come on amsa..." Ta daka mata
tsawa, kuka ta farayi, anty Sadiya ta amshi tea din ta fara rarrashin ta tana bata
da kanta tana sha har tasha rabi, lifaya aka sa mata mai shegen kyau aka rufe mata
kai da hulan, wurin su dad aka kaita sukayi mata nasiha aka kaita wurin mom ta
karayimata, kuka ta farayi sosai, hahhh su Ameera anyi hankali, ita kanta tasan Sai
yanzu tayi aure. Motocin daukan amarya ne suka fara shigowa gidan, nan su anty
Sadiya sukazo daukanta, kiri2 Ameera tace bata zuwa tana kuka kaman ba itace suke
dirty dance da Khalid ba jiya. Da kyar aka banbareta daga jikin mom aka kaita kasa
Sai ihu take kaman wacce zaa kai lahira, wayanta dake hannun Zainabu Sai ringing
take, amma kuka ya hanata amsan wayan, har aka kaita bakin wani white range Rover
bata bar kuka ba. Affan na gefen ta yana kuka shima kaman ranshi zai fita, anty
Sadiya koreshi tayi yace shima zashi raka anty, dole anty Sadiya ta amince suka
shiga cikin mota tare. Motoci 20 aka kawo daukan amarya, kowacce mota mutum biyu
baya Sai daya gaba. A haka yanmatan suka shige motocin akayi hanyan Adamawa.
Har suka isa Ameera bata daina kukaba, affan Sai rarrashin ta yake kaman wani
babba, wani kasaitaccen unguwa suka shiga, duk unguwan babu mutane Sai manyan
gidaje, bakin wani katon gate sukayi horn mai gadi ya wangale gate aka fara shiga
da cars, dukkan motocin shiga sukayi kuma da akwai extra space da zaa Iya ajiye
wasu motoci da suka fi yawan wayan nan, fadi haduwan gidan is a waste of time don
gidan ya hadu Sannan tsarin zamani. Anty Sadiya fitowa tayi ta kama Ameera dake
kuka har lokacin suka shiga cikin wani makeken falo. Nan yanmatan da manyan suka
fara guda don wurin ba karamin haduwa yayi ba, daya daga cikin bedroom aka kai
Ameera basu dade da zuwa ba aka fara shigowa da manyan kula na abinci kala2_
atakaice Sai wacegari akayi walima Sannan aka maida su anty Sadiya da sauran mutane
Kano, Ameera kam idanuwanta basu buduwa saboda
Kukan data sha sam bata wannan zumudin da ta dingayi lokacin aurenta da Salem, har
cikin ranta take tsoron abinda zai biyo baya, Jitayi kaman ana motsi inda take da
sauri ta kame waje daya don girma gidan tsoroyake bata, around 5pm Khalid ya shigo
da Sallama amsawa tayi amma bakajinta saboda yanda muryanta ya dashe, Ahankali
Khalid ya ya karasa wurin ta ya zauna kasa yana kallon swollen face dinta, shuru
yayi ya cigaba da kallon ta for a while Sannan yace
"Baby ji yanda idanuwanki suka kumbura saboda kuka...please stop it already..."
Yafada yana goge mata hawayenta, murmushin karfin hali tayi shima ya saki murmushi
yana kama hannun ta, "muje kici abinci,.." Ya fada mata, ahankali ta Girgiza mashi
kai, marairace fuska yayi
"Please... " yafada yana mikar daita tsaye, bata kara cewa komai ba ta bishi zuwa
wani kasaitaccen dinning table na mutum biyu kadai, Ameera Sai shessheka take,
kallon ta yayi
"Tell me what you want and i will do it for you..." Ya fada cikin natsuwa,
"Nothing.. Am just missing home.." Tafada Ahankali, murmushi yayi
"Tun yanzu?... Anyway don't worry.. Ko gobe kikeson zuwa gida ina iya kaiki in
maidoki...am not among those that makes their wives stay away from their
families... Am a civilise man...you will know me better..." Shuru tayi tana
sauraron shi yacigaba dacewa
"And if you are scared because of first night don't be...I won't do anything you
don't like..." Yafada yana serving dinta, feeding dinta yayi amma ba sosai taci
abinci ba, mikar daita yayi
"Angel muje in nuna maki gidanmu kafin magrub ta gabato, ba musu ta mike ya kama
hannun ta suka shiga zagaya gidan ita kanta can't believe itace matan gidan cos it
is far beyond her expectations, har gym ke da akwai Sannan da kawai underground
kuma acikin underground da akwai swimming pool inda zakayi swimming batare da kaji
tsoron wani zai ganka ba, suna tsaye jiki pool din hannun ta cikin nashi ya juyar
daita tare da rike shoulder dinta ahankali Sannan yace
" nan zamu dinga pool parties dinmu ni dake tunda naga you are a good dancer..."
Kauda kanta tayi tana murmushi,
"Muje muyi sallah kafin muyi parking..." Da sauri ta kalleshi
"Ina zamu?..."
"Florida..." Mamaki ne kwance kan fuskan ta, murmushi yayi yana cewa
"Am not that poor you know..." Yafada yana daukanta in a bridal style.
Sallah sukayi Sannan suka zauna hira kaman ba amarya da ango ba, yanda Khalid keyi
yasa Ameera sakin ranta don he's very much free.
Yana Dariya yace
"You can ask me anything... I promise to be frank..." Daga kai tayi ta kalleshi
directly Sannan tace
"Why sir Salem baizo wedding dinmu ba?..." Murmushi Khalid yayi yafada mata gaskiya
bai boye mata komai ba, ahankali tace
"Gaskiya baka kyauta ba....kar yayi tunanin ni nasaka kyin hakan...kasan komai nada
sanadi kuma sir Salem shine sanadin haduwata da kai...."
"But you were really angry when you find out the truthful about us...."
"Ni ba friendship dinku ya bani haushi ba...kawai boyemin da kayi ne ya bata min
rai"
Khalid kallon ta yayi yana mamakin ashe irin su na samun mata irin Ameera?,
"Ai yanzu fushi yake dani don ko na kirashi bai dauka...." Inji Khalid
"Konice fushi zanyi..." Inji Ameera, Khalid kurawa lips dinta ido yayi Sannan yace
"You beautiful lips... Can't still believe they are mine..." Yafada sounding
naughty, murmushi kawai tayi tana kallon bakinshi, tunawa tayi wasu matan sun gama
kissing wannan red lips din,
"In kara tambayan ka wani abun?..." Ta tambayeshi ahankali, kaman hannun ta yayi
tare dayiwa hannun ta kiss,
"Anything..." Kallon shi tayi Sannan tace
"Ka taba kawo mata nan gidan?..." Ajiyan zuciya ya saki tare sa girgiza mata kai
yana massaging yatsunta,
"Ina kake kaisu?...." Ta kara tambayanshi, ahankali yace
"Ban guest House na abuja...." Murmushin karfin hali tayi
"Gidan su kake zuwa daukan su kafin ka kaisu guest house ka lalata su?..." Da sauri
ya matsa kusa daita sosai ya tallabo fuskan ta don yaji yanda maganan ke fita daga
bakinta da bitterness,
"Angel... Ban taba zuwa daukan mace ba...mostly yan Matan ke kawo Kansu....zasu
sameka office dressed almost naked...watama zatazo office dinka da after dress amma
data cire zaki ganta daga ita Sai bikini pant wata kuma rough dress... Baby am not
an angel...wasu lokutan ina resist dinsu wasu time kuma I can't... Wallahi ban taba
tsayar da yarinya nace tazo muyi zinaba...kawai the ladies are looking for
connection and we are willing to oblige...." Ameera shuru kawai tayi tana kallon
yanda yake moving bakinshi kaman tafiyan tsutsa.
"Hmmm...yanzu ni tsoro nake ji kar kayi resuming office wata ta kawo kanta..."
Rungume ta yayi
"Wallahi nayi maki alkawarin no woman except you..."
"Kasan lokacin da akace zaayi bincike kanka I was afraid kar a gano gaskiya game da
halin ka amma surprisingly Sai akace you are a nice man..." Dariya Khalid yayi
"Ai is only small boys that play games in their towns... If a girl is interested in
me then follow me to abuja...." Itadai Ameera sauraron ikon Allah kawai take don
gani take he's not telling the truth...ya zaayi mace ta mikawa namijin da ba halal
dinta ba kanta
"Yanzu baka tsoron wata cuta?..." Ameera ta tambayeshi, murmushi yayi yana cewa
"Am no fool...I don't goto woman unprotected...", Ameera shuru tayi ya jawota
jikinshi
" baby I will never cheat on you... " yafada yana reassuring dinta,