Author : ummu maryam Category : Complete Novels
inda ameera ta jefeshiba.
Salem kam mamaki yake, Amman baisan abinda ya sami tsohon ba Amman tunani yake
killan hajiyan gidance ta yimashi wani abu sam baiyi tunanin ameera ba.
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: 💜💛💙💚♥
ZAKISAN KONI WAYE
💚💙💜💛♥
®zuwairat(ummu maryam)
🔟
"Dan Allah Malam kayi hakuri" yagayawa maigadin lokacin daya karasa bakin gate ,
"Bakomai" ya amsa mashi.
Salem fita yayi jiki ba kwari amman bai fidda niyyanshi na san ganintaba,
"I will not give up" ya fadawa kansa, yana fita ya hangi Abdul tsaye jikin motan,
yana ganin Salem yagane basu daidaitaba, takawa Abdul yayi ya karasa wurin Salem
dake tafiya kaman Wanda kwai ya fashewa aciki.
"Sir how far" Abdul ya tambayeshi, ahankali Salem yace
"Ban gantaba"
"No yawa...zamu dawo gobe" ya cewa Salem, daga mashi kai Salem yayi, Abdul yayi
mamaki chanjin yanayin Salem cos tunda suka baro abuja sukazo Kano baitaba bin
yarinya gidansu ba ,kawai daya sauke yarinya zai nuna yanasonta amman dasun
disgashi bai kara takansu amman wannan karin gashi yazo gidan yarinya kuma bai samu
ganintaba Amman ya yarda su dawo.
Bakin mota suka isa Abdul yayi saurin bude mashi baya ya zauna,sannan shi yazoma ya
zauna driver seat suka bar wajen.
Har suka bar wajen bai bar tunanin abinda yafaruba, kuma shi bai tabajin yanason
ganin mace sau biyu kaman yanda yakeson ganintaba
"Ohhh..I don't even know her name" yadawa kanshi ahankali,
"Sir kayimin magana ne?" Abdul yajuyo tare da tambayanshi, kai kawai Salem ya
girgiza mashi.
Ahaka suka isah gida babu mai cewa komai. look
Wacegari tunda wuri akayi mashi chanjin fuskata sannan aka kawo masu lunch daga
cilantro Indian restaurant. Suna gamawa suka kama hanya gidansu ameera, still yau
ma Abdul ne ke tukin motan, suna zuwa yayi parking inda yayi jiya Salem ya fito
yana aduan Allah yasa ya samu ganinta.
Bakin gate yaje yayi knocking, still tsohon jiya ya bude mashi, yana ganin Salem
yanayin fuskanshi ya sauya
"Malam kai kuma..."
"Ina wuni" Salem ya gaiceshi, mitumin irin mutanen nan ne masu son yara masu
girmama manyansu, ahankali yace
"Lafiya lau..." Kafin ya kara magana Salem yayi saurin cewa
"Baba dan Allah kayi hakuri ka kiramin yarinya nan.." Mutumin shuru yayi yana
tunanin wai meyasa wannan dan arzikin yake zuwa Neman wannan shaidaniyan yarinyan,
kaman yacewa Salem ka bar yarinyan nan bata da halin kirki Amman sai yayi shuru don
ba abinda aka kawoshi yi bane
"Malam so kake in rasa hanyar bawa yarana abinci?" Girgiza mashi kai Salem yayi
"To indai bakason in rasa aikina kar kara aikena kiran yarinyan nan" Dan jinginawa
Salem yayi da gate din sannan yace
"Baba...nawa ne albashinka?" Kallonshi mutumin ya danyi sannan yace
"Dubu hamsin" Dan murmushi Salem yayi kafin yace
"To in na biyaka albashinka na wata hudu zaka ..." Bai karasaba mutumin ya zaro ido
tare dacewa
"Ban ganeba " yafada yana kallon Salem
"Ina na baka 200k zaka kiramin ita?" Washe hakori mitumin yayi
"Ai sai in kawo maka kanta ma" dariya Salem yayi don furucinshi,Salem komawa yayi
wurin Abdul yaamshi wrapper na dubu2 guda biyu, kallonshi Abdul yayi
"Sir in kabashi wannan kudin baka ganin zaka nuna identify dinka?"
"Ai nasan bazai gaya masuba"
"Are you sure?... Don banason a gane ka"
"Don't worry..I will make sure of that" ya juya yakoma wurin mutumin,
Mika mashi kudin yayi kafin yace
"Amman yazama sirri tsakanin mu" washe hokara mutumin yayi
"Nikam wa zan gayawa ... Da ganin ka asan mai naira ne kai dan ko kadan kirarka
bata kama dana talaka" shikam Salem banda daria babu abinda yake yi, bude mashi
gate din yayi
"Shigo" ya fadawa Salem, yana daria yashiga ya zauna inda ya zauna jiya, sauri ya
maida gate din sannan yayi hanyan falo dagudu.
Abinka da Wanda ya saba da hutu yayi relaxing kaman gidanshi yake zaune.
Shika mutumin yana shigan falo ya hangi ameera zaune kan dinning ita kadai,daga ita
sai bump short sai shimi Mara kauri, sallama yayi Amman ameera bata daga kaiba
balle ta kalleshi ko kuma ta amsa mashi sallaman, ahankali ya kara matsawa kusa
daita tare da karfin gwaiwan 200k dake aljihunshi, sallam yakara yi sai lokacin
ameera ta daga kanta fuskanta kaman wacce akayi wa albishir da jahannama
"Ya akayi you disgusting creature.." Ahankali yace
"Hajiya wani ne yace in kira..." Wani irin dirty look ta yi mashi kafin tace
" koma waye ya kirani..in kuma bashi da number ta yasan inda dare yayi mashi"
tafada tare da maida hankalinta kan abinda take ci, juyawa yayi ya fita.
Salem da yayi balancing kan kujera yana lumshe lulu eyes dinshi ya mike zaune
yana jiran yaji abinda tsohon zai ce.
"Alh yace ka kirata...$" tsohon ya fadawa Salem,
"Baba ka bani number ta mana " ido tsohon ya zaro kafin yace
"Alh INA zan samu number ta...gaskiya babu mai number ta cikin maaikatan gidan nan"
shuru Salem yayi yana tunanin me zaiyi don gani yake in bai sata a ido ba bacci
zai gagareshi
"Baba dan Allah kace mata tabaka number ta" dan murmushi tsohon yayi yana tunanin
wannan bawan Allah bai san wancan yar iskan yarinyan ba, don yasan ko duniya zasu
taru a kanta bazata bashi number ba Amman bayan son yi mashi gardama
"To " kawai ya amsa wa Salem sannan ya koma.
Ya shiga falo da sallam, ran ameera in yayi dubu to duka sun baci, bata daga kaiba
Amman tana tunanin abinda zata yimashi yaji dadi
"Hajiya yace ki bashi numberki" yafada babu tsoro a muryanshi don gani yake tunda
yana da 200k cash daidai yake da uban kowa, ameera daga kanta tayi kafin tace
"You creepy being me nayi maka...jiya ka hanani kallon program dina yau kuma ka
hanani Cin abincina...any way number yace ka amsar mashi ko?"
" eh " ya amsa mata, mikewa tayi daga kan dinning sannan tace
"Ka jirani" tafada mashi kaman wani abun kirki, saman bene ta hau, direct dakinta
ta shiga ta dauko pepper spray wato turare mai yaji ta zauko, hannunta daya rike da
turaren dayan kuma rike da takarda, tana zuwa tayi kaman zata bashi takardan, yana
miko mata hannun ta fesa mashi turaren direct cikin idonshi, da gudu yafara tsale2
yana ihu
"Wayyo idona!!..idona! ..idona...na shiga uku na lalace...ta kashemin
ido...wayyo..idona" ihu kawai yake, ameera kallon hanyan stairs tayi don kar mom
ta ji muryan shi taci uwarta , shikam mai gadin ya rasa hanyar fita don idonshi
basu buduwa, da sauri ameera ta fara Ingizashi har suka fita waje.
Salem dake zaune ya hangeta daga nesa ta wani turo tsohon waje kuma kaman walkiya
takoma ciki tare da rufe kofan falon. Har lokacin tsohon baibar ihunba
"Shikenan idona basu gani..." Da sauri Salem ya taso yazo wurin tsohon, shikam
tsohon kokarin bude idonshi yake amman daya bude sai ya kara fashewa da ihu, cikin
hanzari Salem ya karasa wurin tsohon
"Baba lafia... Me yasameka..." Cikin kuka tsohon yace
"Alh ka tafi...." Salem rikeshi yayi
"Kayi hakuri...laifina ne... Bari intafi da kai hospital.." Tsohon da har lokacin
bai bar kukaba saboda azaban da yakeji cikin idonshi yace
"Ba laifinka bane dana..kwadayina yajamin...kawai ka tafi..." Hankalin Salem yayi
mugun tashi cos tunda aka haifeshi bai taba ganin babban mutum yana zubda hawaye
hakaba.
"Ko kadan baka da laifi baba..." Bai karasaba tsohon yace
"kai kawai ka tafi ...inkuma kudin ka kake so sai in baka..."
"Aa kar kabani Amman dan Allah ka amsamin tambayata...waya zuba maka wani abu cikin
ido?" Tsohon yadan yi kokarin bude idonshi, duk da azaban dayake ji yayi halin maza
ya barsu bude
"Subhanallahi... Please baba ka bari in kaika hospital kar idonka ya sami matsala"
yafada lokacin da yaga yanda idon tsohon suka koma ja sosai, kai tsohon ya girgiza
mashi tare dacewa
"Ka tafi dan son annabi" Salem bai kara cewa komaiba ya tafi.
Mommy su ameera kam bata San abinda ke faruwaba cos tana dakinta tana bacci shikuma
sarkin rahoto affan yana dakinshi yana video game.
Salem na fita Abdul ya bude mashi kofan mota, yanayin shi ya nuna babu nasara
"Sir halan yauma baka samu ganintaba"Abdul ya tambayeshi, shuru Salem yayi for a
moment kafin yace
" eh bangantaba..Amman am not coming back... Ina tunanin da akwai abinda ke faruwa
cikin gidan da bai kamataba ...they is something weird about the family "
"OK sir" Kawai ya amsa mashi don bayason yiwa oganshi shishigi.
Salem kam tunanin tsohon yake, don gani yake kaman da kar idon tsohon su dawo
daidai, aranan bai samu sukunin kirkiba don daya tuna yanda idon tsohon yakoma sai
tsigan jikinshi ya tashi.
Around 9pm yakira Khalid yabashi labarin abinda yafaru, Khalid cewa yayi
"Slim kana tunanin yarinyan ce ta zuba mashi wani abu a ido?" Salem dake kwance
daure da towel yace
"That's what am thinking don na tabbatar ita ce ta ingizo tsohon" dariya Khalid
yayi kafin yace
"Taxi driver kodai inzo Kano ka kaini gidansu yarinya mu dan koyawa dukkan gidansu
respect?" Salem tsoki yayi tare da katse wayanshi
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: 💛♥💙💚💜
ZAKISAN KONI WAYE
❤
®zuwairat(ummu maryam)
1⃣1⃣
Aranan Salem baiyi dinner ba don tunani kawai yake, amman abinda ya bashi mamaki
shine yanda zuciyanshi bai daina son zuwa gidanba,
"Ya Allah... Why is my heart forcing me to a bad place?" Ya tambayi kanshi, Haka ya
kwana da tunani iri2 cikin zuciyanshi.
Wacegari bai fitaba, Abdul ya tambayeshi ko lafia bazasu fitaba? Amman ko juyawa
baiyiba balle ya bashi amsa.
Atakaice saida sukayi kwana uku basu fitaba, abin takaici Shine acikin kwana ukun
zuciyan Salem bai daina shaawan komawa gidanba, yayi2 amman ina ya kasan don anashi
tunanin ko baije dan yarinyan ba ya kamata ya koma saboda tsohon da ya jawa
wulakanci.
Bayan an chanja mashi fuskah ya fita, shiryawa Abdul yayi Amman sai Salem yace
mashi ya zauna gida tunda ba nesa zashiba, Abdul baisoba tunda yasan Salem bai gane
gari da zai fita shi kadaiba amman ko kadan bayason yiwa Salem gardama, yana fita
direct gidansu ameera ya nufa. Karfe hudu da rabi yaisa gidan, parking yayi sannan
ya fito.
Knocking yayi kaman yanda ya saba,tsohon ya dan bude kofa ta yanda zai ga mai
knocking
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun" Salem ya fada lokacin dayaga yanda idon tsohon
ya kara ja yana ruwa kaman zai tsiyaye,
"Baba am so sorry... " tsohon Wanda run randa ameera ta fesa mashi pepper spray ya
bar gani sosai Amman yanajin muryan Salem ya gane shine
"Haba dan nan..." Salem ya katseshi dacewa
"Bari zan kaika hospital yanzu nan.." Tsohon ya katseshi dacewa
"Aa...kar ka kara sakani cikin matsala... Wlh Hajiya karama tace zata hallakani in
har ka kara zuwa bada appointment ba" shuru Salem yayi kaman mai tunani sannan yace
"To Amman ka budemin in shiga, bazan saka ka kirataba , zan shiga da kaina..kuma
nayi maka alkawarin in na fito zamu tafi tare kuma zan baka kudin da zaka iya fara
Sana'a". Shuru tsohon ya bude kofan, Salem nashiga ya hangi wani cute handsome boy
yana kwallo kan dan field din dake gidan, yaron yana ganin Salem ya tsaya yana
kallonshi, ajiye ball dinshi yayi ya ya nufo Salem, yana zuwa gurin Salem yace.
" good evening " murmushi Salem yayi don yaron ya burgeshi
"Evening.. How are you"
"Am fine thank you sir..who are you looking for.. Don in daddy ne yana abuja amma
anjuma zai dawo cos yana hanya...and in mom kake nema tana falo inkuma anty kake
nema tana dakinta tana rawa" dariya ne ya kufcewa Salem sannan yace
"Anty nake nema.."
"OK...bari in kirata" yafada sannan ya kama hanyan falonsu, yana shiga falo ya
hangi mom Amman baice mata komaiba yanufi upstairs, bakin kofan dakin ameera da
wakan beautiful liars na Beyonce ke tashi ya tsaya tare dayin knocking
"Come in" ta fada, affan shiga dakin yayi
"Anty wani na nemanki" ya fada mata, hada giran sama Dana kasan tayi
"Waye?" Ta tambayeshi
"Nima ban sanshiba" dan matsawa tayi bakin window ta cos ana ganin komai na
compound din, wani ta gani tsaye jikin motanta, juyawa tayi ta kalli affan kafin
tace
"Go and tell him to fuck off.." Affan bata fuska yayi
"Anty ba mommy tace ki bar Koran..." Bai karasaba ta turashi waje tana cewa
"Je ka gayamashi ban zuwa" tana kaiwa nan ta maida kofanta ta rufe.
Affan sauka kasan yayi tare da zuwa wajen mommy
"Mom kin ga wani ya aikeni kiran anty ameera Amman tace inje in gayamashi bata zuwa
ko?" Matan ajiye remote control dake hannuta tayi kafin ta mike, direct dakin
ameera ta tafi don Matan bata da matsalan ko kuma ince gurin daya wuce ameera tayi
aure ba Dan komaiba illah don ganin hakan yana Iya kawo chanji a rayuwan ameera,
tana bude kofan ameera dake zaune sanye Da bump short tare da half vest tayi saurin
mikewa ,
"Wai bake ake dema ba?" Tafada fuskanta daure, da Sauri ameera tace
"Nice"
"Then why are you not dressed.." Bata gamaba ameera ta yi saurin bude wardrobe tare
da dauko wasu pink gown da dan karamin Vail blue, Matan tafita tanacewa
"Kiyi sauri ki fito kar ranki yayi mugun baci" .
Da sauri ameera ta saka kayanta don bata tsoron mutuwa yanda take tsoron mommy ba
kaman in dad dinta bayanan.
Tana zuwa kasa ta kalli affan tace
"Go and tell him tana zuwa" da sauri affan ya fita waje yana tsale2, Salem na ganin
shi yayi tunanin same old story ne Amman sai yaji yaron yace
"Sir gata nan zuwa"
"Thanks" Salem yace mashi, yaron yacigaba dacewa
"Da tace you should fuck off....sai na gayawa mom" daria Salem yayi
"Stop using that f**k word..babu kyau ga yara "
"OK sir" yaron yace sannan ya juya da niyyan tafiya amman sai yakara juyowa sannan
yace
"Sir kana dan kama da wani dake cikin photo din dad dina dake office dinshi" Salem
dan shuru yayi sannan ya girgiza mashi kai
"Gaskiya bani bane... Shiyasa kake kirana sir?"
"No sir...wata antymu mai suna Mrs adeoye tace indai mutum ya girmemu mu dinga
kiran su da sir ko mam"
"Good boy..keep it up"
"Yes sir" yafada kafin yabar wurin da gudu ya koma kan field.
Ameera kam da sauri tafito kaman wata mutuniyar kirki, har zata wuce mom takira
"Haka zaki tafi hannu rabbana?..dalla wuce kitchen ki dauki drink ki kaiwa bakonki,
ameera kaman ta hadiyi zuciya ta mutu don bakin ciki gashi babu daman gardama mom
ta suburbudeta,
Kitchen ta shiga ta dauki juice da ruwa tare da cup ta ajiye kan tray, har ta fito
sai wani mugun tunani ya fado mata cikin rai ta kara komawa cikin kitchen ta dauki
cup din ta zuba barkono sannan ta zuba juice saman shi tare da rufewa da saucer ta
fito.
Salem da har lokacin yake jingine jikin motanta ya hangota ta taho, haka nan sai ya
tsinci kanshi da faduwan gaba, kura mata ido yayi yana tunanin Allah yasa ba wannan
yarinyan ke muguwarba
" Allah yasa su biyu ne..." Yafada Cikin zuciyanshi, kara daga kai yayi ya kalli
yanda take tafiya kaman tana runway show, tamkar tana modeling cos duk step dinta
is marvelous, fuskanta ya kalla yaga tamkar anyi mata albishir da mutuwan Wanda
tafiso aduniya, tafiya da takeyi a ahankali ya bashi daman kallon kafanta don gown
dake jikinta bai kai kasaba, wasu silver ankle lace ya gani kafanta sannan da
ganin fingers dinta fixing tayi, bai ankaraba yaji kaman daga sama ance
"Malan wane bashi naci wurin ka ban biyaba?" Sai lokacin Salem ya dawo hayyacinsa,
kallonta ya sake yi
"Kiyi...." Bai karasaba tace
"Kaman kaine taxi driver din da ya daukomu last week ko.." Ahankali Salem yace
"Nine...." Still bai karasaba ta kara katseshi da wani irin daria rainin hankali
tana cewa
"Halan aiki kake nema...don gaskiya gidan nan babu vacancy" Dan murmushi karfin
halin Salem yayi before saying
"Ba aiki nake nema ba...wajen ki nazo" kallonshi tayi from head to toe sannan ta
kalli kanta sannan tace
"Ina jinka...low classer" still murmushi Salem ya sake yi
"Na ganki kuma kinyi..."
"Wow..what a courage.. Dan Allah Malam ka kalleni...ko ban shafawata kana Iya
saye?.." Salem zaiyi maganan tadaga mashi hannu tare dacewa
"Shut your pit toilet am not don talking.." Gira daya Salem ya daga don tunda yake
bai tabajin zagin daya tsotsa mashi rai kaman wannan ba
"For your information.. I don't mingle with low life pest..bana harka da non
entity.. Bana magana da mutane that a from gutta... Bana harka da mutane da basu da
hope don da ganinka you look hopeless...and ina warning dinka ...."
"Hey!!!" ya daka mata wani razannen tsawa
"What do you think you are... Kina ganin kinada chance awurin high class
babes?..well for your information Iyakanki nan kano..shiyasa you are so
arrogant..." Clapping ameera tafarayi
"Ashe matsiyacin ya Iya speaking..kace who am I ..any way ni ba kowa bace amman
nafin uwarka da ubanka.." Nan take idon Salem ya koma ja don tunda aka haifeshi
babu Wanda ya tana kaishi makura kaman wannan yarinyan
"Sam ban gan laifinkiba....ammn you are not worth my precious time.. Sannan bani da
lokaci...da time gareni danayi maganinki koda na dan lokacine"
"Look at this bastard..uban WAYE kai!!?" Ran Salem Kara baci yayi
"Baki chanchanci kisan KONI WAYE ba.." Yana kaiwa nan ya juya ya fara tafiya,
ameera daukan juice mai yajin tayi
"Jimana" tace mashi Amman yayi banza ya shigaba da tafiyanshi, kawai baiankaraba
yaji saukan ruwa bayanshi, allah ya taimakeshi bai shiga idonshiba, tsayawa yayi
kaman dutse don tunda yake baitaba zama so humiliated kaman yauba , kasa juyawa
yayi ita kuma ameera tacigaba dacewa
"Wash up you son of a bitch" at that moment Salem jiyake yana iya shake ta ,dukkan
masu gadinsu da driver da mai wankin motansu Salem suke kallo suna magana ahankali
"What can you do?" Ta sake cewa adaidai lokacin da akayi horn a bakin gate , da
gudu mai gadi ya bude gate wata babban jeep ya shiga gidan ,affan dake kwallo ya
taho da gudu ,sai lokacin ya lura da abinda ya faru maimakon yaje wurin dad dinshi
dake fitowa daga cikin mota sai yayi cikin falonsu da gudu yana kiran mommy, daddy
ameera na fitowa ya kurawa Salem ido yana tunanin wannan kaman sir Salem amman
yasan wannan bashi bane don salem din dayasani is filthy billonare , shima Salem
yana daga kan shi ya ga mutumin ya ganeshi sai dai baisan sunanshiba amman yasan
suna haduwa a board meeting
"Waye wannan?" Dad ameera ya tambaya cikin shagwaba ameera ta fara cewa
"Dad Wai wannan low class bastard din ne yace yana sona" dad ameera dirty look ya
watsawa Salem sannan yace
"Haba dan nan ina kai ina ameeran daddy..." shi kam Salem baice komaiba yafara
tafiya, ita kuma ameera da dad dinta suka shiga falo, bai kai bakin gate ba
yafara Jin ihun ameera, Salem tafiya yake kaman kazan da ruwan sama ya doka. Saida
Yazo bakin gate ya tsinci muryan mai gadi nacewa
"Dan nan kayi hakuri..daman naso in fada maka amman nace kar inyi shishigi...Sam
yarinyan bata ganin kowa gashin arziki... Hajiya da affan kawai ke da mutunci amman
alhaj da yarinyan nan halin su iri daya ..." Salem ba idajin abinda tsohon ke cewa
ba ya fita yana rawan sanyi ga bayanshi yana yi mashi zafi saboda barkono cikin
lemon. Yana tafiya yana cewa
"ZAKISAN KONI WAYE
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE
❤
®zuwairat(ummu maryam)
1⃣2⃣
Mom ameera dukanta take kaman an aikota, duk yanda dad ke son kwatan ameera kasawa
yayi don tunda yake bai taba ganin bacin ran matanshi kaman yau ba, don kaman bai
mitanen boye ta koma, tana dukan ameera tana cewa.
"Me nayi maki kikeson sa jinina ya hau,..me nayi maki kikeson jamin zagi da shaidan
banza wurin jamaa...irin tarbiyan danayi maki kenan?..yau mai amsanki hannuna sai
Allah" haka ta shigaba