Advertisements
Chapter 7 Reading ZAKISAN KONI WAYE by ummu maryam BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ZAKISAN KONI WAYE by ummu maryam

Author :  ummu maryam Category :  Complete Novels

Chapter   7 / 44

18K to 21K   out of 130.5K words

kara" kai Tawa ta gyadawa mami
"Kwanta in cigaba dayi maki tausan" ba musu tawa ta kwanta tayi rubda ciki, acikin
ranta tana tunanin
"Da ganin wannan mutumin ba mugubane..wai oromi...shi dole sai yayi yarenmu" mami
sai ganin tawa tayi tadan yi murmushi
"Kini?" Mami ta tambayeta, girgiza kanta tayi sannan tace
"Ba komai"


Salem kam yana zaune yana video call da agent dinshi yana nuna mashi yanda gidan
yake, daya kalli yanayin gidan sai yayi murmushi don babu abinda yakeyi mashi dadi
irin ya tuna ameera zai kai gidan.
"Gaskiya kunyi kokari tunda with in sati daya har kunyi rufi"
"Yes sir...Amman inason in tambayeka" agent din yafada
"Am listening" Salem ya amsa mashi sannan agent din yacigaba dacewa
"Sir a toilet din water system zaa saka? Ko ayishi pit toilet"
"Wane irin water system.. Kawai pit...sannan tunda an kusa gamawa inason..
Forget kawai" yafada kaman Wanda ya tuna wani abu.
Yanzu rabonshi da ganin tawa sati daya kuma shikadai yasan irin kokarin da yake,
don so kawai yake ya kara sakata ido koda saudaya ne, kullum in yakira Khalid babu
abinda yake kara gaya mashi illah kar ya kuskura ya cemata komai, kawai with time
zai mance ta Amman ya lura hakan ba mai yuwa bane
Around 4pm aka chanza mashi fuska ya fita shi kadai, don restaurant din da tawa ke
aiki kusa yake da gidan shi.
Bayan ya isawurin yayi parking wani wuri sai ya taka da kafa zuwa restaurant din.
Daga nesa ya hangi tawa tana amsan kudi daga hannun wani mutum, hannu tasa cikin
apron din dake jikin ta ta fiddo chanji tabawa mutumin tare da Dan runtsunawa.
Kallon tayi, sanye take cikin lace Wanda kudin ta bazaifi 3k ba sai dan hijjab
Wanda bai wuce kuguntaba,batayiba kwalliyaba Amman fuskanta babu laifi, Dan kara
matsawa yayi kusa da wurin , kallon yanda bakinta ke magana ahankali yayi da alaman
waka take ji, ahankali ya zo kusa daita, daga kan datayi sai sukayi ido hudu,
murmushi ta sakar mashi shima ya mayar mata martani, da sauri ta mike tare da saka
hannunta cikin hijjab dinta ta fiddo earpiece sannan tace
"Lah..ina wuni" ta gaidashi
"Oremi ya kike?" Dan daria tayi sannan tace
"Baka mance ba kenan.." Shima daria yayi
"Ya zaayi in mance"
"Inawuni" takara kara cewa wannan Karin har da dan runtsunawa
"Lafiya lau..ya aiki?"
"Alhamdulillah ..zauna " tafada tana nuna mashi inda ta tashi, cikin zolaya yace
"In zauna?..in mai wurin tazo ta tadani fa?" Cikin daria tace
"Sha kuruminka..batanan tayi tafiya" wurin data tashi ya zauna, tawa ta ajiye
Wayanta kusa dashi ta shiga cikin inda suke ajiye abincinsu na sayarwa, Salem
kallon wayan yayi yaga techno ce Wanda ko 1k bazai iya sayanta ba, earpiece din
yadan dauka ya saka cikin kunneshi yaji anacewa
"Dani dake mun dace" da sauri yacire earpiece din daga kunnenshi don kara wayan
zata Iya kashe mashi kunne, baijin wakan hausa Amman wakan tayi mashi dadi,
"Dani dake mun dace kam" ya maimaita cikin ranshi, bai ankaraba yaji tace
"Malam bisimillah" sai lokacin ya dawo hankalinshi, daga kai yayi sukayi ido hudu
sai yaji tsigan jikinshi na tashi at the same time gabanshi ya fadi, itama tawa Dan
daga kirjinta tayi, kuma tayi saurin dauke hannunta, sai yayi karfin halin cewa
"Oremi sunana ba Malam ba..sunana..." Ahankali tace
"Sorry.. Meye sunan ka?" Dan shuru yayi yana tunanin yayi mata karyan sunan shi sai
kuma yayi tunanin kar karyan yayi yawa
"Sunana Salem"
"Oga sa..."
"Meye oga kuma...gaskiya banason sunan."
"To sorry...sir Salem" gabanshi faruwa yayi don tunanin ko tasan shi waye yayi, don
yasan dukkan maaikatanshi haka suke ce mashi
"Meye kuma sir Salem?" Yayi karfIn halin cemata, Dan murmushi tayi kafin tace
"Ai bazan iya kiran sunanka direct ba.."
"Nima ki kirani da oremi mana" zatayi magana yace
"Please"
"OK..OK..OK...naji oremi kazo kaci abinci" ido Salem ya gwalo
"Ai ba abinci nazo ciba..bani da ko sisi" Dan daria tayi
"Kar ka damu zan saka kudin da kudina..so please kazo kaci" kallon environment din
yayi, tunda aka haifeshi bai taba cin abinci a public place ba sannan yasan ko ruwa
yayi gigin sha sai ya amayar da dukkan abinci dayaci don shi asalima kyaman wajen
yake
"Na koshi" Marairacewa tayi
"Please fa kaci..kaga last time ka rokeni nashiga taxi dinka to nima ina rokonka
kaci abinci" shidai yasan yarinya nan is perfect for him
"In na gaya mik gaskiya zaki yarda?" Kai ta daga mashi alaman eh sannan yace
"Azumi nake" Dan hararan zolaya tayi mashi sannan tace
"To shikenan" abinci ta maida sannan ta dawo ta dauki kujera ta zauna Dan nesa
dashi, kallonta yayi sannan yace
"Oremi wani taimako nakeso kiyi min"
"Ok...oremi"
"Ance nan Kano da akwai saukin kaya shine nakeson ki taimakamin ki rakani kasuwa
inason zan siyawa kanwata kayan boarding school" shuru tawa tayi kaman mai yin
tunani sannan tace
"Ok...Amman zan gayawa mami in ta yarda zan rakaka"
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: G ❤
ZAKISAN KONI WAYE

®zuwairat(ummu maryam)

1⃣7⃣

Kallon ta yayi for a moment sannan yace
"To in mami ta kifa?"
"Shikenan.. Bazan rakaka ba"
"Allah yasa ta yarda"
"Ameen" shuru yayi yana tunanin abinda zai ce mata don bayan son tafiya yanzu
shikuma ba gwanin fira da mata bane,
"To in mami ta yarda nan zanzo sai mu tafi?" Kai ta girgiza mashi
"Aa..sai kazo gidansu mutafi.."
"Ya zaayi in gane mami ta yarda..ko nan zanzo amsan amsata.." Kai ta kara girgiza
mashi
"Gaskiya kar kakara yuwa nan tunda madam gobe zata dawo..kawai kazo gidanmu muyi
list kar mu shiga kasuwa mu rasa abinda zamu siya..."
"To shikenan" mikewa yayi
"Ni zan tafi" daga zaune ta danyi waving dinshi tare dacewa
"Bye.." Kura mata ido yayi
"Ko in tsaya in ajiye ki?"
"Aa nagode"
"Please.." Yafada cikin muryan yan mata, daria tayi
"No..nima dana baka abinci kinci kayi"
"Bhaki yarda ina azumiba kenan"
"Wane irin azumi akeyi ranar laraba?" Shuru yayi baisan abin cewaba, yafara takawa
yana cewa
"Shikenan.. Sai nazo" waving dinshi takarayi sannan ta maida earpiece dinta cikin
kunnenta.

Salem yana tafiya yana tunanin halin tawa...wai shi zata siyawa abinci... Dan
murmushi yayi sannan yace
"You are kind and generous.." Haka ya koma gida yana tunanin inama bahaushiya ce da
yanda yake jin kaunanta acikin ranshi ajiye karyan identity dinshi zaiyi ya aureta
cikin sati daya koda kowa batasonshi, Amman in ya tuna yarenta sai hankalinshi ya
tashi don yasan da kyar ummanshi zata yarda,dan abbanshi kam bashi da matsala don
da akwaishi da understanding saidai ko kadan baya son abinda zai batawa first love
dinshi rai.


Tawa tana zuwa gidan ta gayawa mami abinda Salem tace mata, mami rufe ido tayi tace
"Aa..babu inda zaki.."
"Mami dan Allah" cikin fada mami tace
"Aa..wai baki da tsoro ne?..baki tsoron a kashe min ke?..."da sauri tawa tafara
girgiza kanta tana cewa
" mami da ganinshi ba mugu bane..."
"Dalla rufemin baki..mugu lamba gareshi?..." Mami ta daka mata tsawa. Wiwi tawa ta
fashe da kuka, tana cewa
"Mami wallahi nasan ba mugu bane... Kuma nayi mashi alkawarin zan rakashi...haka
nan sai ya dinga ganina makaryaciya?" Mami bude baki tayi tana ganin ikon rabbi.
"Meye abun kuka...anya Tawa kasuwa zaki rakashi?" Cikin kuka tace
"Wallahi mami.. Kasuwa zan rakashi... Kuma baisan garin ba yace in rakashi" tafada
har lokacin bata bar kukaba, mami zuba mata ido tayi na dan lokaci sannan tace.
"Toyin tsakanin ki da Allah meye sakaninki da mutumin?" Da sauri tawa tace
"Mami babu komai.."
"Babu komai.. Amman daga nace baki rakashi kasuwa shine kike
kuka?...tawa...tawa..sau nawa na kiraki?" Da sauri tace
"sau biyu" don tasan dukda mami ba lafiyayya bace bata daukan rainin hankali, mami
ta sake cewa
"Zan kara tambayan ki..meye tsakanin ki da mutumin?" Cikin kuka tawa ta sake cewa
"Mami bakom...." Mami ta katseta dacewa
"Tawa kar kisa raina ya baci...ki gayamin gaskiya abinda ke tsakanin ki da wannan
mutumin?" Tawa shuru tayi tana kuka, gani tayi mami ta mike, ta fara cewa
"Wallahi mami nima ban saniba...Amman duk sanda na tunashi gabana na faduwa..."
Tayi shuru, mami ta kara cewa
"Inajinki..kuma ki gayamin gaskiya banason karya.." Tawa Dan share hawayenta tayi
sannan tacigaba dacewa
"Kuma mami inayawa tunanin shi.. Sannan ina son in ganshi kullum" baki mami ta bude
"Tawa..Ashe soyayya kike zuwa yi?...don kin gan bani da lafiyan dazan yi aiki in
nema mana abinci shine kike fita kina abinda kika gandama?.." Tawa sabon kuka
tafara tana cewa
"Mami ni ba soyayya nake.."
"Rufemin baki..wato ke bakisan sonshi kikeba?...yanzu wane yareneshi?" Ahankali
tace
"Mami bahaushene" baki mami takara budewa
"Tawa Hausa...Hausa kikeso?.. Hausan da abu kadan sun saki Matan su?...baki ganin
wasila da akayi bikinta wata uku dasuka har an saketa?..to ita bahaushiya ma kenan
balleke wata yaren..."
"Mami ni ba soyayya nake dashi ba"
"Matsalarki...nidai bazan hanakiba tunda ban taba ganin ki da waniba..Amman kibi a
hankali.." Still itadai tawa nacewa tayi kan ba sonshi take ba, abinda bata saniba
shine abinda babba yagani zaune to ko yaro zai hau mountain bazai ganshiba. Goge
hawayenta tayi sannan tace
"Mami kin yarda in rakashi kasuwa?" Mami dan hararanta tayi sannan ta bude
hannuwanta
"Zo" tawa rarrafawa tayi gurin mami, mami ta rungume ta sannan tace
"Ifemi..kinsan inasonki...banason abinda zai saki cikin bakinciki..hausawa basu
rike aure..." Cikin shagwaba tawa ta katseta dacewa
"Nifa ba sonshi nakeba.."
"Ai shikenan..zanga abinda zai biyo baya.. Kwanta inyi maki tausa" tawa kwantawa
tayi mami tafara yimata tausa, chan kuma Tawa ta karacewa
"Mami kin amince in rakashi kasuwan?" Dan daria mami tayi
"Na yarda" tawa lumshe ido tayi cikin ranta tana aduan Allah yasa sir Salem yazo
gobe.



Bangaren Salem kam kaman ana huramashi son tawa don kullum daita yake kwana yake
tashi, cikin kwana biyun da bai gantaba kaman ya mutu hakan yasa yayi niyyan zuwa
gidansu, tunawa yayi da dazun ankirashi angama gidan ameera, Dan mikewa yayi yakoma
bakin window abinda zai yi next, wasu haddadun Porsche Cayenne dake parking tsakar
gidanshi ya kalla yayi murmushi tare da shafa sajenshi dake sheki kaman ana shafa
masu relaxer.

Da sauri yashiga wanka yana cewa
"Bari inje ingan ikon Allah" bai dau lokaci ba ya fito daure da towel, gaban mirror
ya tsaya ya fesa turare sun kala goma jikinshi sannan ya dauki wata armani tuxedo
shirt ya saka da wando shi. Nan take yafito kaman ba taxi driver da yan mata ke
ciwa uwaba. Yana fita falon koina ya bade da kamshin turare shi masu tsadan gaske,
Abdul juyawa yayi dasauri yana cewa.
"Sir ina zamu?" Mukullin motan ya mikawa Abdul sannan yace
"G,R,A sultan road" Abdul baki ya bude zaiyi magana Salem ya hade giran kasa dana
sama, shuru yayi ya dauki car keys ya fita da sauri ya budewa Salem gidan baya ya
zauna sannan shima yashiga suka bar gidan Abdul sai tunanin yau Salem yayi
switching copporate mode.

Daidai gidansu ameera Abdul yayi horning, maigadin na budewa Salem ya tuna da
alkawarin da yayi wa tsohon, nan take ya fiddo check book dinshi ya rubuta mashi
check na 3m ya bawa Abdul
"In ka shiga ciki ka kiramin uban yarinyan ka bawa wancan tsohon wannan check din"
ya fadawa Abdul lokacin dayake parking a farfayiyan gidan.

Da sauri Abdul yafito ya nufi balcony dinsu ameera, knocking yayi affan ya bude
mashi koda, kallon yaron yayi sannan yace
"Kaje ja kagayawa dad dinka sir Salem na sallama..." Bai gamaba dad ameera dake
kallon CNN ya mike da sauri yana
"Da gaske ne sir Salem a gidana?" Kai Abdul ya daga mashi, da sauri ameera dake
zaune ta mike ta hau upstairs da gudu, dad ameera bangaje Abdul yayi ya nufi inda
motan Salem ke tsaye, Salem dake kallon abinda ke faruwa ya kauda kanshi tare da
yin daria na yan second sannan ya kara daure fuskanshi kaman bashi bane, da gudu
dad ameera ya karasa gurin motan Salem yana cewa.
"Sir yau kaine a gidana?...ka shigo ciki mana" Dan girgiza kai Salem yayi
"Aa nan ma ya isa...." Da sauri dad ameera ya kara katseshi
"Sir please ka shigo mana...sai ka tsaya waje kaman wani bako...please come in"
yafada yana budewa Salem mota, ahankali Salem ya fito da cikin mota, dad ameera
gaba yana yimashi jagora shikuma Salem na biye dashi yana tuna irin zagin da ameera
ta yimashi da kuma irin maganan da dad ameera yayi mashi.
Ameera kam tanajin ance sir Salem ta Haura sama, direct dakinta ta tafi ,hannunta
na rawa ta dauko makeup kit dinta tafara shafawa , cikin sauri ta gama shafawa
sannan ta dauki wani dogonhijj ta sumbula sasnnan ta dauki turare ta kusa karar
daita jikinta sanna ta nufidownstairs tana tafiya kaman kazan da kwai ta fashema
aciki.
Salem na shiga falo ya gaisa da mom sannan sukayi shaking hannu da affan, wuri ya
samu ya zauna, bai ankaraba yaji ance
"Ina wuni" cikin wata irin sanyi murya, Salem daga kai yayi yaga ameera, sai ka
rantse ba itaba don durkusshe take gabanshi kanta kasa kaman wata salaha, inda bai
taba ganintaba zai rantse mutuniyan kirkice
"Haka kuke zaluntan samari in sun zo neman aurenku...sai dagabaya kalanku ta
gaskiya ta baiyyana" ya fada azuciyashi a zahari yace
"Lafiya" ahankali ameera ta mike ta nufi hanyan kitchen, dad ameera kam kaman anyi
mashi albishir da aljanna, Salem mikewa yayi yana cewa
"Mommy sai anjuma..." Zatayi magana dad yayi sauri
"Sir ka tsaya kaci abinci"
"Aa nagode" yafada har ya kai bakin koda, dad binsu yayi shikam Abdul kallon ikon
Allah kawai yake , suna fita Salem ya juya ya kalli dad
"Daman nazo inji in kuna bukatan wani abu don next week nakeson a daura aure..."
Baki dad ameera ya bude zaiyi magana Salem yayi saurin cewa
"Oh sorry kace baka bukatan ko sisi...Amman abinda ke nan shine daga nan Spain nayi
so ranar asabar by 4 zan turo private jet akaita airport na Lagos sai ta sameni
chan...inyaso in tazo zan kaita shopping to make up for the rashin lefe...hope
hakan yayi" dad ameera banda daga mashi kai babu abinda yakeyi
"Yanzu sir ranar asabar mai zuwa zaayi daurin auren kenan.."
"Eh...ko da matsala?.." Da sauri dad ameera ya girgiza mashi kai
"Aa wallahi....sir yanzu yaushe zan fara zuwa aiki" Salem shuru yayi yana tunanin
yanason ya wahalal da ameera da dad dinta Amman yasan da zaran ya hanashi aikinshi
zai dau alhalin mom da affan, hannu yasa cikin aljihunshi ya dauki wayanshi yakira
Nigeria head ya bashi umarnin ya maidawa umar Adam aikinshi. Murna wurin dad baa
magana, kofa aka bude ameera tafito tana tafiya kaman batason taka kasa, dad ameera
barin wurin yayi, shikam Abdul kurawa ameera ido yayi yagane itace yarinyan data
mari Salem, jin hiran da dad da Salem keyi ya tabbatar mashi rashin mutunci Salem
zaiyi.
Kallon ameera Abdul ya karayi sai ya tsinci kanshi da tausaya mata, don yasan halin
Salem.

Salem na ganin yafito ya juya baya ya shiga motan shi, da sauri Abdul ya shiga, sai
ji yayi tace
"Allah ya kiyaye" kallon ta yayi suka hada, da sauri ta kauda kanta tare da
sunkuyar da kanta kasa kaman mai jin kunya, acikin ranshi yace
"Monster in disguise" Abdul ya ja mota suka bar gidan, ahankali Abdul yace.
"Sir what's happening?" Murmushin gefen baki Salem yayi sannan yace
"So nake in gaya mata KONI WAYE"
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE

®zuwairat(ummu maryam)

1⃣8⃣

"Haba..alh. Wane irin aurene wannan?.. Ya zaayi mu aurar da yarmu ga wanda baa
zauna akayi magana da magabatan shiba?..gaskiya am smelling something fishy.." Mom
ta fada lokacin da dad ya fada mata yanda sukayi da Salem. Dad tabe baki yayi
"Ina ruwanki..yarinyan da baki damu daitaba? ..ai ko saida tanayi ba damuwanki
bane"
"Ya zaayi kace ban damu daitaba..ai ko bakomai ni na haifeta..kawai halin da takeyi
ke banso Amman ba wai banason yataba.." Dad banza yayi daita ya fiddo wayanshi
yafara kiran yan gidan radio station ayi mashi sanarwan bikin yarshi, sannan ya
kira yan gidan TV ya gaya masu ayi mashi sanarwa. Mom baki ta bude tana kallon shi,
yana gama wayan ya mike zai fita mom tayi saurin tare gabanshi tana cewa
"Yanzu alh baka tunanin wannan abun ba yanda ya kamata bane?..ya zaayi auren yata
kwara daya babu wedding event.. Babu lefe....babu miji wurin daurin auren..sannan
the most annoying part of all ace yan uwa bazasu rakata gidanta don su san mazaunin
taba?..gaskiya something is wrong" dad dirty look ya watsa mata sannan yace
"Aniyanki ya biki..." Yana kaiwa nan ya fice ya nufi dakin ameera.
Ameera kam tunda tayi ido hudu da Salem tazama speechless, don kyaunshi ya wuce
yanda take tunani, cos yaune ranar farko da ta taba ganin shi atunaninta , daman
tana yawan ganishi cikin news sannan tana following dinshi a social Media, Amman
sam photo baya yi mashi adalci don a kasa yafi cikin photo kyau sau dubu.
Dad ameera yashiga ya gaya mata yanda sukayi da Salem, ko kadan ameera batayi
tunanin wani abuba, asalima farincikine cikin ranta don bata taba hawan jirgiba
Amman yanzu tata zataje Spain tare da the most handsome guy amatsayin mijinta.
Nikam nace ameera you better stop dream cos they is no chance in hell.



Tawa kam wacegari ta zuba ido don ganin Salem Amman baizoba, duk sai ta tsinci
kanta da bakin cikin rashin ganinshi. Ranan wajen aikinta saida suka gane wani abu
na damun ta, Amman dasun tambayeta saitace bakomai. Wacegari ma which is Friday ta
zuba ido zuwanshi Amman babu shi.
Yau asabar, dawuri tawa ta dawo daga restaurant don basu yin abinci dayawa. Tana
zaune dakin su tayi tagumi duk abin duniya ya isheta, banda tunanin Salem babu
abinda takeyi ita kanta abin tsoro yake bata don tunda take bata taba jin mutum na
yawan fado mata a raiba sai yanzu, kallon agogon wayanta tayi taga karfe 4 sannan
tace
"Allah yasa lafiya wannan sir Salem din baizoba...Allah kasashi yazo yau...inason
ganinshi.." Karaf sai kunnen mami dake dawowa daga bathroom
"Me kike cewa?" Mami ta tambayeta, da sauri tawa ta dawo hankalinta,
"Mami ba komai" mami kallon ta tayi tare da tabe bakinta sannan ta wuce cikin
kuryan dakin.


Akan hanyan dawowan Salem daga gidansu ameera ya cewa Abdul ya bi ta hanyan
restaurant din su Tawakaltu, ba masu Abdul yabi ta hanyan
"Sir wurin kaman a rufe yake.." Abdul yafada yana kallon wurin daga nesa, Salem
kallon wurin yayi, ranshi batcewa yayi don niyyan shi ya tsaya cikin motan shi ya
ganta ko yadan samu jin dadi cikin zuciyanshi. Haka suka tafi gida ranshi babu dadi
don banda tawa babu wacce yake son gani.
Kallon agogon hannunshi yayi yaga har 5pm dan guntun tsaki yaja don yasan makeup
artist dinshi bazai iya zuwa ya chanza mashi fuska ba har yaje gidansu tawa.

Wacegari which is Sunday tun 11 aka chanzawa Salem fuska, 11:30 daidai ya isa
gidansu tawa kasancewan babu nesa tsakanin tukuntawa da zoo road, ya zuwa Salem
yayi parking a inuwan wani bushiyan neem, sannan ya fita yana neman yaron dazai
aika kiranta, bai dade da tsayuwaba saiga wani almajiri yazo wucewa, kirashi Salem
yayi yace mashi yakira mashi tawa.
Tawa data gama wankin ta dana mami tare da yin wanke da gyara dakinsu cos basu zuwa
aiki ranar lahadi saboda Matan da take saidawa abinci Christian ne, tana kwance
tana sauraron sanarwan auren dan tsohon shugaban kasa dazaayi sati mai zuwa aka
aiko kiran ta, da sauri ta mike tsaye dukda ta fidda ran zuwa Salem, almajiri na
sallama ranta ya bata shine, mami dake kwance kurya tace
"tawa tani?" Maana waye?
"Mami ban saniba bari in leka in gani" ta amsawa mami tana fita daga dakin ko gyale
babu jikin ta don Allah 2 take taga mai kiran ta, sanye take da atampha wax dinkin
skirt da blouse, fuskanta ko powder babu Amman she's not looking bad, dankwali
kawai ne kanta, already almajirin ya fita, ahankali tayi sadaf2 ta taho ta tsaya
bayan kofan su

7 / 44