Advertisements
Chapter 27 Reading ZAKISAN KONI WAYE by ummu maryam BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

ZAKISAN KONI WAYE by ummu maryam

Author :  ummu maryam Category :  Complete Novels

Chapter   27 / 44

78K to 81K   out of 130.5K words

tayiwa tawa magana, fitowa
tayi ta shiga bedroom dinta.
Tawa kama tana jira ta saka Vail din jallabiya dake jikin ta bude kofa tafito,
gaban ta Sai faduwa take, Salem na ganin ta ya kwalo idanuwa cos ko kadan bai
ganeta, ahankali ta karaso wurin shi tana girgiza ta durkusa ta gaidashi, kasa
amsawa yayi Sai kura mata ido kawai yayi, ahankali ta daga kanta ta kalleshi tana
yi mashi murmushi, muryan shi na rawa yace
"Habibty kece?... " cikin zolaya tace
"Yes of course..." Tafada tana zama gaban shi anan kasa.
"You are my own rihanna" dariya kawai tayi
"Bari in kawo maka abun sha..." San bata fuska yayi
"Just sit let me watch you" ya umarceta,irin zaman da aka koya mata tayi Salem
banda kallon ta babu abinda yake, kallon kafanta yayi yaga sunyi sumul
"Hmmm.." Kawai yace under his breath, kallon shi tayi eye balls to eye balls Sannan
tace
"Meye..." Yanda take magana tamkar ba yarinyan daya ganin last few months tana
saida abinci gefen hanyaba
"Don't underestimate people.." Ya fada cikin ranshi
"I missed you..." Ya fada cikin whisper kara dacewa
"I can't wait for the next 4 weeks..." Gaban tawa Dan faduwa yayi amma sai ta sakar
mashi wani shuumin murmushi, Dan dukar da kanshi yayi kusa daita
"Princess.. Are you flirting with me?..." Dan kallon shi tayi ya kashe mata ido
daya, Dan kauda kanta tayi
"Yasu first love da Abba?"
"Suna lafiya.."
"Habibty.. Me kike ci?.. You look ravishing..."
"Thank you.."
"Princess..." Ya kirata sounding so lustrous
"Naam.." Ta amsa batare data kalleshi ba
"Me kika kirani dazun?..." Dasauri ta rufe fuskanta kaman wata mai jin kunya
"Am waiting.. Call me that in front of me..." Ya kara fada mata, fuskanta rufe tace
"My...sugar..." Salem Dan dariya yayi
"Habibty.. Wait until you have tasted me..." Tawa Dan turo baki tayi
"Zaka farako?..."
"Kedai kika fara..." Dan hira suka cigaba dayi, kaman an chunkuleta tace
"Baby...da akwai abinda ban Sani game da kaiba?.." Salem tsaya kallon yanda take
fidda magana kaman bataso yayi for a moment Sannan yace
"Why are asking love?.." Ahankali tace
"naji ana cewa da kyar mutum yasan 10 to 30% na halin maza..ni kuma am thinking I
know you..." Kura mata ido yayi yana tunanin abinda tace, shidai yasan bashi da
wani secret saidai case dinshi da Aisha, kuma yana ganin ko ta Sani nan gaba bazai
zama case ba
"Honey kayi shuru.. Ko da akwai abinda ya kamata in Sani..." Tafada tana kama
mashi hannu, da sauri ya dawo hayyacin shi, rike hannun ta yayi da two hands
dinshi, kaman ya fada mata gaskiyan abinda ke faruwa yayi kuma ya fada mata ko yau
yana iya sakinta kuma ya tabbatar mata bai taba komai da itaba amma this moment is
precious, he don't want to ruin it, kallon eye balls dinta data maida kaman na
maijin bacci yayi Sannan ya saki murmushi
"Habibty.. Bani da secret.. You know komai about me...sai dai ina Abu guda daya..."
Da sauri ta zaro idanuwa Sannan tace
"Please what?.." Tafada gaban ta na Dan faduwa don, yatsan shi yasa yafara shafa
tafin hannun in a circular form Sannan yace
"I think I can last 4 to 5 hours in bed.. " zare hannun ta tayi tadan kauda kanta
gefe tana Dan murmushi,
"I don't want you to be surprise.. So prepare well for me..." Tawa shuru tayi don
tasan karyake, amma cikin ranta tasan yana hiding wani secret,
"Hmmm...I just want to know everything about you... Banason Sai bayan aure in gane
wani Abu Mara kyau game da kai..."
"Haba habibty saikace ina yankan kanu?... To tell me abinda kike gani zai tada maki
hankali.."
"Nidai I don't know.. Amma am telling you..it won't be okay..." Sai kuma tayi shuru
don tasan irin tempern ta..tasan she's respective amma she don't take bullshit
"Habibty relax.." Yafada in reassuring tune don yasan zai saki ameera batare
datasan anyiba.
"Habibty.. Wacce zatayi planning traditional wedding zata zo nan around 5pm
yau...zata kawo pictures Sai ki zabi irin kayan da kike bukata" Dan turo baki tayi
"Is it necessary?.. Kawai duk abinda ka zaba is OK by me..." Dan bakinta ya rike
"No...just choose.. Kinsan its your time.. Inason komai yazama yanda kike so..."
Dan rike hannun shi tayi daga bakinta
"OK.." Hannun ta ya cigaba da murzawa kaman yana shafa kwai
"An kawo kayan da ladies zasu saka?.." Ya tambayeta
"Eh..naji su dija nata kiran friends dinsu suzo su amshi ashobi..kasan ni bani da
friends" Dan dariya yayi
"Daman banason mata mai tarin kawaye..suna leading ko misleading mutum..amma akano
baki da friend ko daya..." Shuru tayi kaman tana tunani
"Sai guda daya itama wurin aiki muke haduwa..mami bata yarda inje gidansu..."
"Sai ki bada address dinta a tura mata invitation.."
"OK..." Shuru yadan biyo baya Sannan yace
"Habibty mu shiga cikin gari mana?..." Ido ta kwalo
"Bansan koina ba..besides wannan Matan bata barina fita ko ina.."
"No..problem...da karfe nawa zaayi pics din?" Ya tambayeta har lokacin hannun ta
cikin nashi
"Wai dole ne?.."
"Yes love... I want to show you to the world.. I want people to know some delay is
a blessings.." Daga kai tayi takara sakar mashi wani lustful smile
"This smile is killing me.." Yafada kasan makoshinshi, wani takara sakar mashi
Sannan ta mike
"Where to.." Ya tambayeta yana lumshe idanuwa
"Ruwa zan kawo maka...maganan da mukayi yanzu ya isa ya saka jin dry throat.." Dan
Jan hannun ta yayi ta kusa fadawa kanshi, da sauri ta zari hannun ta ta taka cikin
kasaita ta duka ta bude fridge, Salem gyara zama yayi yana kallon yanda take tafiya
komai nata na shaking, juice ta dauko ta saka kan tray dake kan fridge Sannan ta
shiga kitchen ta dauko cup ta kawo mashi, tamkar mirror ya maidata don ko blinking
baiyi.

Around six sukaje Emirates garden sukayi pics, na farko suka English waer jean da
t shirt agaban na Salem an rubuta her prince, agaban nata an rubuta his princess,
ta tsaya gabanshi ya saka hannun shi cikin aljihun wandonta suna kallon juna,ba
karamin kyau sukayi ba.
Nabiyu sun saka kayan Fulani Salem ya rike sanda itakuma rike da kwarya nan ma ba
karamin kyau sukayi ba, na uku ya saka shadda fari kal dinkin babban riga amma ba
mai zurfi ba, na hudu ta saka gown blue Sai shi yasha blue suit Sai na karshe sun
saka kayan Yoruba, Sai around 8 aka gama pics don duk chanzawa da zasuyi Sai an
gyara mata fuska suna kan hanyan dawowa ta kalleshi
"Wai kai kayi hiring wayan nan mutanen dasuka dauke mu photo?" Dan girgiza mata kai
yayi
"No.. Wani abokina ne...har kayan da muka saka da directors dinshi shi ya dau
nauyi.."
"He's nice.." Murmushi kawai yayi Sannan ya kalli drive dake driving dinsu yace
"Take us to the best restaurant in town.."
Atakaice basu dawo gidaba Sai around 10pm har bakin kofan part da take ya rakata
saida ya juya yaga babu kowa Sannan yayi saurin hugging dinta , kafin tayi wani Abu
har ya hada bakinshi da naya, passionate kiss yayi mata sannan yace
"Good night...make sure you dream of me.."




Ameera kam count down kawai take, don har ranar auren Salem tasani kuma yanzu
alhamdulillah ta fidda shi daga cikin ranta kawai gurinta kawai gida, yanzu suna
shiri sosai da babban yar hinde zainabu don har hiran da bata taba yi da aminiyar
zeenat ba tanayi da Zainabu don har yanzu bata fada mata gaskiya alamarin ba,
kullum cikin kallon film suke wani lokacin har yar gala2 suke, yanzu ameera ba
rabuwa da Salem ne matsalan taba Sai rabuwa da hinde da mutane ta don har cikin
jininta take jinsu, adua take Allah ya bata ikon kula dasu in ta bar gidan, kuma
har Allah 2 take ta koma gida don ta nemi yafiyan mutanen data zalunta especially
masu yimasu aiki. Tasan Salem yashiga hakkinta amma she can't give him all the
blame,
"Ni abinda ke daure min kai shine dalilin dayasa yaki sallama ta tunda ya sami
Matan aure.." Tafadawa Zainabu da ke zaune kusa daita tana wanke2 itakuma tana
dauraya
"Hmmm..wayasani...kilan so yake ya barki Ku zauna tare.." Bata idaba ameera ta ja
tsaki
"Wa zai hada miji da mayu?... Ai ko yace in zauna dashi bazan zauna..kawai Allah ya
hadani da mai sona...."
"Yarinyan dazai aura mayyace?"
"Yo yarbawa ai masafane...ko a lahira bana fatan Allah ya hadani ni dasu wani harka
balle miji..."
"Hmmm da gaskiyanki..amma in da akwai rabo tsakanin Ku fa?"
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE


®zuwairat(ummu Maryam)



5⃣6⃣


"Rabo!.. Tab Allah ya rabumu da mummunar kaddara..." Tafada tana Dan mikewa tsaye,
"Daman bakison shi..amma in kana son mutum duk yanda yake zaka zauna tare dashi.."
"Ni gaskiya ya fita raina.. Kinga ranar dana kirashi..zagi ya dingayi...gaskiya
mutumin bashi da kirki..."
"Aike kika yarda damanki tun farko..." Ameera dai shuru tayi batace komaiba don
tasan gaskiya Zainabu ta fada
"Amma kin San me?" Ahankali ameera ta girgiza mata kai
"Allah zsai saka maki..saboda ya wulakanta aure..kuma aure ba abun wasa bane..don
haka nasan tabbas Allah bazai barshi hakaba..." Still ameera batace komaiba ta
tsaya tana goge ruwan hannunta ga zanin dake jikin ta
"Allah yasa Matan taci mashi uwar..." Dariya ameera tafarayi tana cewa
"Kai na ji dadin wannan aduan.. Inama ina kusa inga yanda zatayi mashi..."
"Kikasan ikon Allah?... Kedai Allah ya zaba mana abinda yafi alkhairi.."
"Ameen.. Amma da kika ce banason shi..ke ba kinason mijinki ba amma kika rabu dashi
saboda extra banana da yake baki?" Zainabu tattara plates din tayi tana cewa
"Inason shi mana.. Amma ban Iya zama dashi.." Dan shuumin murmushi ameera tayi
kafin tace
"Amma tsakanin ki da Allah da akwai lokacin da kike jin dadin abinda yake yi
maki.."
"Ina dadi kullum ana cikin fama maki ciwo.. Wallahi Sam babu dadi..." Ameera
dariya tayi
"Ni shiyasa hankali na kwance don ina cikin Leda ta.." Dariya Zainabu tayi
"Ai kinji dadi..in wani na mijin ne bai kyaleki haka nan..." Tafada tana kai plates
cikin kitchen, su hinde kam anachan an kurawa TV ido kaman her life depends on it.



Sai the following day Salem yabar kwara inda kudirat ta zauna dashi ta bashi advice
sosai kan in take fada mashi ya fidda zancen sex gabanshi cos karamin abune cikin
aure, alokacin da take bashi wannan shawaran cikin ranshi kam cewa yake
"Ashe?" Kamar kar su rabu da Tawakaltu don har kukan gulma tayi mashi. Salem kaman
ya dawo kwara da zama har agama wedding din yakeji don wani irin sonta da kaunarta
ke ratsa shi. Alokacin ya Riga ya baza pics dinsu a social media.

Yana cikin jet kan hanyan shi na dawowa Khalid ya kirashi yana picking yaji yana
cewa
"Nima wallahi Sai ka samomin irin wannan a gidansu..." Dariya Salem yayi
"To ni wani ya samomin?..."
"To nima zanje taxi driving.." Yafada yana dariya
"Allah ya hadaka da irin wannan shaidaniyan yarinyan ta gurguri buroubanka..."
Yafada yana dariya, Khalid ma dariya yayi
"Na ma mance da ita...ka rabu daita?"
"Aa..."
"What are you waiting for..."
"Time.. So nake insa akai mata wedding video dina ta kalla taga abinda tayi
missing..."
"Ka kyaleta haka nan... Komai ya wuce.. Haba"
"Ai komai ya wuce.. Da ban yafe mataba zan bata enough money for her up keep?..
Kawai dai.." Da sauri Khalid yace
"Kodai ka fara sonta..."
"No way...am in love already.. No free space a zuciyata..ni kama tuna min in nayi
aure da maganan sakinta cos ina Iya mancewa saboda abubuwa..."
"Da gaske dai sakinta zakayi...ni kama bani takardar sakin in kai mata ko Allah
yasa tayi min Sai in aureta cos the devil you know is better than the angel you
don't know..." Dariya Salem yayi
"Ai yarinyan tayi...she's beyond beautiful amma she's nothing compared to my
baby.." Shima Khalid dariya yayi
"Gaskiya ai your madam karshe ce..." Ahankali Salem yace
"In fada maka gaskiya wannan shekiyar yarinyan tafita kyau.. Kaman aljana take don
kyau amma Sam bata da kyau hali..." Ihu Khalid yayi Sannan yace
"Guy...tayi min kawai... Kawai ka saketa yanzu....please kasan I always have
something for beautiful ladies..." Dariya Salem ya karayi
"Wannan balarabiyar fa?...ko ka fasa..."
"Manta da wannan.. Kawai ka saketa yanzu..."
"Nayi alkawarin Sai nayi aure zan saketa...kuma am a man of my word" Shuru yadan
biyo baya kafin Salem yace
"Har yanzu bansan irin party da zaayi ba..." Shuumin dariya Khalid yayi farayi
Sannan yace
"Zan hada mana cool party har da bikini party zaayi..." Dariya sosai Salem ya
dingayi har da rike ciki
"Su waye zasu saka bikini?.." Ya tambayeshi yana dariya
"Ladies.. Har da matanka..." Yanda yayi maganan yasa Salem kara fashewa da dariya
"Amma baka da hankali..."
Kunji min Dan iska...bakasan ana bikini party ba?...kawai ayi bikini party a Lagos
beach Sai kuwuce... "
"Duk iskanci na ai ban kaikaba...tunda ni har yanzu ina cikin Leda..." Dariya raina
hankali Khalid yakarayi
"Weirdo...Virginia..virgin at 37...nima virgin ne..." Shima Salem daria ya dingayi
yana cewa
"Dalla get out of my phone" yafada yana girgiza kai Sannan ya kashe wayan shi yana
dariya.

Bangaren su Abba komai yayi ready, sun sayi kayan list din a aka basu kuma komai
saida suka linkashi.
Ana sauran sati biyu traditional wedding Umma da su ilham da shuwa da yanuwan Umma
Sai tareda kawayenta uku sukaje kwara, wani irinhospitality suka bawa su Umma, su
shuwa kam kaman su maida Tawakaltu ciki saboda yanda suka nuna so da kauna kanta,
tasha kyautan kayan mussanman wajen shuwa, don katon bag ta bata cike da perfumes
da kayan shafa, Umma hakuri tabawa Tawakaltu kan maganan data fada mata kuma ta
nuna just n dadinta da son gaskiya da Tawakaltu ta nunawa Salem dukda batasan koshi
WAYE ba
"He tells me everything" tafada sannan tayi bata alkawarin bazata samu matsala a
gidan Salem ba muddin ta zama mai biyayya, Sai a wannan lokacin mami ta Dan samu
kwanciyan hankali amma har lokacin hankalin ta bai kwanta dukaba cos ta lura da
irin kallon da ammi takewa Tawakaltu. Shuwa ido tayiwa tawa alaman mukebe, ahankali
tawa ta mike ta bi bayanta tafada mata da akwai magani cikin kayan data kawo mata,
ta dinga sha da madara. Bayan asar suka tashi tafiya kasancewan da jet din salem
sukazo Yaran ilham cewa sukayi su abarsu wajen antyn uncle Salem.

Bakin jet su mami da mutanen gidan suka rakasu, ammi Dan matsawa tayi kusa da
Tawakaltu Sannan ta kwantar da murya tace
"Munji Ku baayi maku kishiya ..to mu danmu Sai ya jera Matan nan hudu..babu gudu
babu ja da baya don wannan yayiwa mace daya yawa..." Tafada yanda babu mai jinta
Sai tawa, nan fa jikin tawa yayi sanyi.
Mami ta lura da tana fadawa tawa magana same with Umma saida suka hau jet Sannan
Umma ta tambayeta abinda ta fadawa tawa maimaita mata abinda tace tayi, Umma batace
komaiba Sai daya daga cikin friends din Umma tace
"Maganan ki gaskiya ce...don su basu yarda da akara masu kishiya...kaman ba
musulumai ba" still Umma shuru tayi don har cikin ranta tanason danta ya auri
cikakkan bafulatana. ilham kam cewa tayi
"Yanda bana fatan ayimin kishiya bazan yiwa ko wacce mace fatan kishiya ba...."
Bata idaba ammi tace
"Wai Nafisa meyasa yaran ki basu rufe baki in manya suna magana?... Ko Dan Allah
bai bakisuba da yawa yasa baki basu tarbiya ba?...to wallahi duk yar kutumar
burouban data kara sakamin baki cikin magana Sai na cire mata hakora...mussanman ke
mai kama da aljanu" tafada tana nuna shuwa da yatsa, Umma dai batace komaiba don
abinda ke damunta daman. Shuwa kallon ilham tayi sannan tace
"Anty wallahi Matan yaya kaman rihanna..don tafi kyau a kasa kan cikin waya.."
Daria ilham tayi don tsaki ammi ya hanata cewa kala cos cikin yaran Umma tafisu
tsoro cos bata da rikici kaman Salem da shuwa.

Su tawa na komawa gida mami ta tambayeta abinda wannan Matan ta fada mata amma tace
bakomai, duk juyin duniya taki fada mata, mami part dinta ta koma tana cewa
"Kanki..." Tawa shiga part din da take tayi tashiga bedroom ta dinga kuka, nan take
tafara Dana sanin amince wa Salem don gani take har ya auri sauran ukun kuma tasan
dole zaa nuna mata banbanci, tana cikin kuka Salem ya kirata, kin picking tayi,
saida ya bata 3 miss call Sannan ta gyara muryan ta tayi picking, tana cewa
"Hello.." Salem ya gane da akwai abinda ke damunta, tambayeta yayi da sauri abinda
ke damunta amma taki fada mashi, dasauri ya katse wayan. Nan take ranshi ya bashi
kilan su Umma suka fada mata wani Abu. Kiran Umma yayi tana picking yafara cewa
"Umma.. Dan Allah me kuka fadawa Tawakaltu?..."
"Dan ubanka ni kake fadawa wannan maganan?... Ubanme tace maka an fada mata?...."
Ammi salati ta farayi ta kwace wayan daga hannun Umma
"Shanyayye..ni na fada mata..." Ta maimaita mashi abinda tafada mata sannan ta
cigaba dacewa
"Shine Dan kilibibi har ta fada maka?...to wani auren har kayi angama...." Afusace
Salem yace
"Wallahi ammi in har kikasa wannan yarinyan ta fasa aurena... Sai na daure dukkan
yaran ki...har da wannan banzan na Sudan..." Yana kaiwa nan ya katse wayan shi.
Ammi fashewa tayi da kuka tana cewa
"Shikenan Mun rasa wannan Dan arzikin...Dan wannan maganan danayi yace Sai ya kulle
dukkan yarana...$" Umma dai batace kala ba saidai kawayen Umma ne keta salati suna
cewa Sai an tashi tsaye kanshi, shuwa kam relaxing tayi kan leather seat din cikin
jet tana murmushin jin dadi.

Abangaren ameera kam tunda aka turo mata photo din Salem da tawa ta ida fidda rai
gaba daya don ba karamin matching dinsu tagani ba, ko kadan bata aduan Allah ya
hadata da kishi da wannan don komai nata kaman ita tayiwa kanta, photo dinsu Wanda
suka sa jean da riga ta bude tana kallo, kallon hannuwan Salem dake cikin aljihun
wando tawa tayi, fuskanshi ta kalla taga irin kallon da yakewa tawa, irin kallon
nan na in bakeba Sai rijiya, tabe baki tayi tare da tsaki ta ajiye wayan, kaman an
sinkareta takara daukan wayan ta hau Facebook nan ma hotunansu ta cikaro dashi,
gani tayi ana cewa is the best African pre wedding pictures of the century, tsaki
takaraja ta ajiye wayan
"Wai meke damunki ne?..." Hinde ta tambayeta, Dan murmushin karfin hali tayi tana
cewa
"Nasan nan da kwana 21 yanzu ina gidanmu..." Tafada hawaye na taruwa idonta, dukkan
su shuru sukayi kowa yana tunani



Yau sauran 1 week traditional wedding, already anyi booking din dukkan manyan hotel
dake kwara, in short har small hotel akayi booking saboda rashin wuri, all
arrangement is in order ranan kawai ake jira, tawa kam takoyi abubuwa da yawa Wanda
in ni Zuwairat zan ce za fada maku Sai ya cinye kusan 20 pages, har traditional
dancing da party dance ta koya kuma kudirat ta fada mata ranar wedding dinta tayi
rawa sosai don is her day and she promise herself nothing is standing in her way
dukda maganan ammi bai bar yawo cikin kunnenta ba amma her sweet hubby promise daga
ita Sai ita, hmmm, yanzu final lesson dinta kan sex ne da yanda zata biyawa mijinta
desires yanda ko ya auri wata bazai ji yanda yasaba ba.

Salem na zaune compound dinshi shi kadai yana cikin jin annashuwa cos gani yake he
can't be happier, horn akayi ya maida eyes dinshi don ganin masu shigowa, mai gadi
na bude gate ya hangi white range rover na shigowa , daure fuska yayi don yasan
mima ce, mai gadin na kulle gate ya kirashi, da gudu guy din yazo wajen shi, nuna
shi yayi da Dan yatsa Sannan yace
"Wallahi kana bari karuwai suna shigo min gida Sai ka rasa aikinka...from today no
lady should enter my estate without my permission.. Am I clear?..."
"Yes sir...am sorry sir..."
"sorry my white ass...fall out" yafada yana

27 / 44