Author : ummu maryam Category : Complete Novels
abinci dukda ya kuduri aniyan ya kusa gaya mata koshi
WAYE don yanzu hutunshi sauran sati uku ta kare,
"Daman ana samu mace mai hali, kyau , sanin ya kamata?...ko dai kina da wani halin
da ban saniba?..you have all the qualities.. You have the perfect shape perfect
body... " ya fadawa kanshi, zama yayi yana tunanin yanda zaiyi ya dinga sa tawa
dafa mashi abinci batare datasan shi takewa ba, yafi minti goma yana tunani sannan
ya saki dan kasaitaccen murmushi, wayanshi ya dauka yaga 6:15am, number tawa yayi
dialing yana cewa Allah yasa bani zan tadaki daga bacci ba, bayan ringing uku ta
dauka da sallama, dajin muryan ta kasan ta dade da tashi kuma jiya kusan 1 na dare
suna hira awaya, gaidashi tayi kaman yanda ta saba shima ya amsa sannan yace
"Princess kinsa me yafaru dasafen nan?"
"No sir"
"Dazun naje daukao uban gidana daga Aminu Kano airport...shine yake fadamin yana
Neman wacce zata dinga yi mashi abinci.. Ya dinga bata 15k kullum tana siyan kayan
sannan ta rike sauran...kuma yace zai bada 200k ta sayi kayan aiki" saida ya kai
aya sannan tawa tadan saki daria
"Amman ifemi you are very funny.. Ka taba ganin inda mutum yaci abinci 5k arana
balle 15k?" Dan murmushi yayi don yasan da akwai elegant restaurant dake abroad,
zama daya sai yaci 3000$
"Ai mutumin yana da naira...kuma na fada mashi nasan wata yarinya data iya abinci
sosai" tawa shuru tayi for a moment sannan tace
"Gaskiya bazan iyaba..tsoro nakeji...kuma nasan da kyar mami ta amince"
"Tsoron me?"
"Kar mutumin ya zama dan yankan kai" daria Salem yayi
"Kina tsoron kar mutumin ya yanke maki beautiful head dinki...well relax..ban dan
occult bane sannan babu ruwanki dashi cos ni Zan amso kudin sannan ni zan kai mashi
abinci so kinga babu ruwanki dashi..."
"Hmmm gaskiya mami bazata yarda ba...kuma ko ta yarda ina tsoron kar inyi
disappointing dinka cos kilan baya cin anyhow food"
"Don't worry about that.. You are a wonderful cook..kawai talk to mami yanzu
nan..inta amince ki kirani sai in amso kudin"
"So soon?"
"Yes mana...bayason son cin abinci anyhow.. Kuma kema kin huta da wannan katuwar
madam din nan" daria tayi
"OK...let me talk to her"
"Good.. Call me inta amince.. Kuma please ki nace har sai ta yarda" daria ta karayi
sannan ta katse wayan ta.
"Indai ba cikin wahala take sonkiba ai ta amince" yafawa kanshi yana dailing number
Abdul, bayan yayi picking yace
"Call me the makeup artist" sannan ya katse wayan shi.
❤
Ameera batayi bacci ba har garin Allah waye, tana ganin hasken wayewan gari ta
rarrafa ta koma cikin dakin ta kwanta kasan carpet tana tuna daddy, nan hawaye ya
fara zubo mata, mom ta kara tunowa ya kara fashewa da kuka,ba karamin sauro ya
cijeta ba, don duk jikinta kaikayi yake mata,, bata dade da kwantawa ba taji
anacewa
"Salamun alaikum" banza tayi bata amsa ba, saida aka maimaita kusan sau uku sannan
ta mike jiki ba kwari don azaban yunwa da takeji, ahankali ta fito waje, wata mata
ta gani kaman aljana saboda muninta
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!" Tafada da karfi tare da komawa cikin dakin,
matan wace green teeth dinta tayi sannan tace
"Ke dawo..nice hinde..ni..." Ameera bata saurareta ba ta dinga kwala ihu, matan
binta tayi daki, ameera kamewa tayi waje daya tana kallon ta don kayan jikin ta
wulik don dirty, Matan tacigaba dacewa
"Nice akace in dinga koya maki abinci..." Ameera kuka ta kara fashewa dashi tana
kalle2 inda zata samu abinda zata jefawa matan, bata ga komaiba ta cire takalmin
kafanta ta jefawa matan
"Ki tafi...mahaukaciya kawai..ubanwa zaici abin hannunki...dirty, disgusting
creature" Matan Dan scratching gashin kanta tayi kaman mai lice aka
"To shikenan.. Tunda baki son in koya maki" tafada tana daria kaman na morons,
juyawa tayi ta fita, da sauri ta ameera ta mike ta bi bayan ta, har matan ta kai
bakin gate tayi saurin cewa
"Kin iya dafa abinci?" Da sauri hinde tace
"Sosai" ameera tana ganin hakoranta ta sartar da yawu sannan tace
"Kina Iya tsayawa daga nesa ki koya min?"
"Eh" ameera kallon ta tayi tana tunanin bata da zabi don tasan in bata ci abinci ba
tana iya mutuwa, nuna mata itacen tayi
"To ki huta wuta" ameera ta umarceta, da sauri hinde ta dawo ta dauko murhu ta saka
itace, ameera sai kallon ta take, tana gamawa tace
"Ina ashana?"
"Tsaya inda kike indauko maki" tafada tana shiga cikin kitchen dinta , cikin kayan
ta duba ta dauko sashana ta wullawa hinde, babu bata lokaci wuta ya kama
"Kawo tukunya in Dora" hinde ta fada mata
"Ubanwa zaki dafawa abinci?.. Dan matsa baya ki gani" ta fadawa hinde, matsawa baya
tayi daga inda wuta yake,ameera kitchen ta koma ta dauko tukunya,
"Me zan fara sawa cikin tukunyan?" Dan takowa hinde ta farayi
"Dalla tsaya inda kike ki fada min abinyi" ameera ta daka mata tsawa, daga nesa
Matan ta tsaya tana gaya mata steps din da zata bi, cikin kankanin lokaci abinci ya
dahu, ameera kitchen ta shiga ta dauki kwano ta zuba ta fara ci, kaman wacce bata
taba cin abinci ba , haka ta dinga ci ,dukda dadin abinci bai kai Wanda ta saba ci
ba, tana ci tana zagin Salem, hinde ta nan daga tsaye, ameera ko kallon inda take
batayiba har saida ta koshi sannan ta kalleta
"Ke ki tafi mana" ta fada mata,
"To" hinde ta amsa mata kuma daga gani ranta ya biya, Amman ameera bata kalleta ba,
kuma abinci na da yawa. Sauran abinci ta kai kitchen sannan ta nemi sabulun wanka
da soso, sabulun wanki ta gani, sabon kuka tafara, idanuwanta sunyi mugun kumburi,
ahaka tayi wanka da sabulun wankin, mai cocobutter ta dauka, tabude Amman ta maida
ta rufe don warinshi ma takeji.
❤
Umma Salem zaune tana waya, ji nayi tana cewa
"Kina nufin baa taba bude office dinshi ba?"
"Eh..guys din cewa sukayi kwata2 babu alaman shi akano don cewa sukayi duk binciken
da akayi ya nuna cewa tunda shi ba boyeyyen mutum bane zamanshi a Kano ma bazai
boyeba.." Matan ta fada mata daga chan bangaren, shuru Umma tayi kaman mai tunanin
wani Abu,
"To me hakan yake nufi kenan?"
"Gaskiya inajin bai Kano"
"To shikenan, but please keep on finding him cos nasan yan Kano,..tunda nasan
bayayi min karya"
"To hajiyata..da akwai daya daga cikin yarona Wanda yake aboki da wani bodyguard
din Salem, zansa shi ya kirashi muji in suna Kano..."
"Ok ..haka ma yayi..make the call right away".
" yanzu nan insha Allah "Umma ta katse wayan tare da kara kiran kawanta dake abuja
ta jadadda mata akara tsaro wurin duba gidan Salem. Don yanzu babu abinda take so
kaman tasa tawa a idonta
❤
"Tawa wace irin abinci zaki dafawa mutum a 15k kuma kullum?" Mami ta tambayi tawa
"Mami nidai ban saniba...cewa wannan mutum dake zuwa wurina yace mutumin mai kudi
ne" mami shuru tayi tana tunanin maganan tawa
"Hmmm..kina ganin da gaske yake?"
"Eh mami don bai cika karyaba..ko yanzu ma cewa yayi inki yarda zai koma gidan
mutumin ya amso kudin"
"Kuma yace babu inda zakishi zai kawo kudi yazo ya amshi abinci?"
"Yes mami..ni kawai indafa abinci shine nawa"
"To kina gani zaki Iya dafa kalolin abinda zai gansar da mutumin?"
"Insha Allah"
"To shikenan.." Bata idaba tawa ta mike ta dauki wayanta ta kira
Salem tana tsale tana cewa
"Ifemi.ta yarda" karaf sai kunnen mami, don tunda take kirnashi ifemi mamiba
tabajiba
"Tawa me kika kirashi?" Tawa dauke wayan tayi daga kunnenta Amman bata tuna ta
kashe wayan ba don yanda jikin ta ke rawa
"Mami...ba..komai..," tafada kaman zatayi kuka, duk abinda suke cewa a kunnen Salem
"Tawa Hausa kike cewa ifemi.. Tawa..."
"Mami sorry" mami bata sauraretaba ta nufeta
"Tawa Hausa kike cewa ifemi" kunnenta takama da karfi, daga chan bangaren Salem
yaji ihun tawa sai hakuri take bawa mami, ji yayi ranshi yayi mugun baci
"If you don't want it the easy way...we will do it the hard way" yafadawa kanshi,
har lokacin bai bar jin ihun tawa ba, yaji mami tana gayawa neighbors dasuka shigo
ceton tawa da hausanta Mara fita
"Wai wannan yarinyan Hausa take so..bata ganin abinda suke yiwa Matan su?..yau aure
gobe babu" hakuri aka dinga bata, tawa share hawayenta tayi
"Mami I love him.." Salem dake jinsu ya lumshe idanuwa kwalla na taruwa idonshi,
mami kunnen tawa takara kamawa, banda ihu babu abinda takeyi, sai ka rantse yankata
akeyi kuma kunnenta kawai mami ke kamawa.
A lokacin anayiwa Salem Chanjin fuska, ture artist din yayi ya mike ya koma daki ya
kwanta, har lokacin wayan bai katseba, yaji tawa nacewa
"Mami he's not a bad person" mami kara kama kunnenta tayi da karfi sosai, wannan
Karin da karfi tarike don da kar aka kwace kunnen tawa daga hannunta, Salem kaman
yashake mami yakeji, daga baya wayan ta katse, dagani kudinta ne ya kare.
Salem kwantawa yayi yana juye2.
Bayan kaman minti talatin ya kirata bata dagaba, kara kiranta yayi, saida ya kusa
tsinkewa sannan tayi picking, muryan ta chan kasa tayi mashi magana, pretending
yayi kaman baisan abinda yafaruba
"Princess na amso kudin inzo mutafi?" Ahankali tace
"Ka bari saida yamma kaina ke ciwo"
"Ayya sorry.. In sayo maki magani?"
"Aa"
"OK..I love you" bata amsa ba ta katse wayan ta.
Da yamma yazo gidan, yau mami bata yi mashi faraa ba.
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE
❤
®zuwairat(ummu maryam)
3⃣0⃣
Falonsu yazauna kanshi kasa, mami amsa gaisuwan shi tayi babu yabo babu fallasa,
daki ta shige, baa dade ba tawa ta fito, daganin idanuwanta kasan tasha kuka, tana
kallon shi ta sakar mashi murmushi karfin hali, kura mata ido yayi
"Tawa ciwon kai din ne yasa idanuwanki kumburi?" Ahankali ta daga mashi kai hawaye
na taruwa idanuwa ta,
"Sorry.. Inje in sayo maki magani?" Girgiza mashi kai tayi tana goge hawayen dake
sauko mata, hannu yasa cikin aljihunshi ya dauko 300k
"Gasu, yace tunda farkone ki sayi duk abinda kike bukata..sauran ki ajiye" daga red
eyes dinta tayi ta kalli kudin
"Ka ajiye su..muje kasuwa tare" ta fada a hankali, maida kudin yayi ita kuma ta
mike tashiga ciki dakin, yana zaune yanajin mami sai fada take Amman baijin abinda
take cewa, bayan kaman minti goma ta fito cikin skirt da riga na atampa da gyale,
mikewa yayi tabi bayan shi.
Bayan sun shiga mota ya kalleta
"Am sorry for all the pains..you won't regret it" kallon shi tayi tadan wayance.
"ban ganeba?" Bai kara cewa komaiba ba ya tada motan, ita ta nuna mashi hanya har
suka shiga jifatu,abinda ya bashi mamaki shine yanda ta wartsake kaman ba itaba,
Kayan kitchen suka siya, babu yawa sai shegen tsada
"Ifemi wannan food warmer yayi tsada da yawa..just 1 for 40k?" Daria Salem yayi
"Ai godi am mutumin bayason kayan banza..shiyasa ya baki enough money.. Kinsan har
extra 100k yabani in case kudin zasuyi kadan..." Tawa tsayawa tayi tana kallon shi,
kura mashi ido tayi sosai..don yau ne rana ta farko data nutsu ta kalleshi sosai
"Wannan kallon fa?" Ya tambayeta, Amman still bata daina kallon fuskanshi ba,
ahankali ta daga hannu zata shafa a fuskanshi, kauda kanshi yayi tare da rike mata
hannu
"Wai meye?" Ya kara tambayanta, ahankali tace
"Sir da akwai wani abu afuskanka..." Da sauri ya kauda kanshi gefe daya, don sai
lokacin ya tuna bai bar makeup artist dinshi yayi mashi blending din kayan sosaiba,
har lokacin bai saki hannunta ba
"Ciwon kan ke saki ganin biji biji?" Itakuma har lokacin bata daina kallon shi ba
"Serious da akwai wani abu a fuskanka...bari in nuna maka" tafada tana kai dayan
hannunta kan fuskansh, daria ya farayi tare da kara dauke fuskanshi yana tunanin
"Wannan yarinyan tana son tonamin asiri yau" kara rike dayan hannunta yayi,
hannuwanta biyu cikin hannunshi, still kura mashi ido tayi
"Habibty kurajene suka fito min na shafa magani" yayi mata karya yana aduan Allah
yasa ta yarda don yasan Yoruba da smartness, mutanen dake wucewa ta inda suke sai
kallon yanda ya kama mata hannuwa suke, da sauri ta zame hannunta
"Muyi sauri mu gama, kaga lokacin dinner na gabatowa" ta fada tana kallon uban
kayan kitchen din da suka saya
"To..sauran fridge da gas cooker" yafada yana nufan wurin wani katon gas cooker mai
kai shida, bin bayanshi tayi tana cewa
"Kam...ina zan ajiye wannan gas din ...kawai mu sayi stove mai kai biyu" bai kara
cewa komaiba suka sayi stove, wurin fridge ya nufa
" me zamuyi da fridge kuma?"
"Ai kina bukata don ki dinga saka ingredients da spices..kinga ba sai kin dinga
yawon Shiga kasuwa kullum ba" wani foreign cool room ya nufa, tawa baki ta bude
"Gaskiya wannan yayi girma..kawai ka sayi wancan" ta nuna mashi wani medium sized
freezer " haka suka dinga sayan kaya har Salem ya kashe over 400k Amman tawa bata
saniba.
Daga nan kasuwa suka shiga suka sayi kayan abinci Da manyan dry fish, suna dawowa
gida yan unguwa da neighbors suka bude baki, wata yarinya cewa tayi
"Tawa kodai aure zakiyi baki gaya mana ba?" Dariya tawa tayi
"Duka nawa nake da zanyi aure" kallon mamaki Salem yayi mata batare dayace komaiba.
Suna shiga da kaya ciki mami ta mike tsaye tana mamakin yawan kayan, saida suka
gama kai kayan tawa ta rako Salem waje, har ya shiga cikin mota, ya kalleta
"Wai cewa kike baki isa aureba?" Daria tayi
"To na isa ne?"
"Ai you are ripe for harvesting..."
"Ka fara ko?"
"To sorry.. Ni zan tafi..around 7pm wannan abokin nawa zai zo ya amshi abincina"
yafada , kallon mamaki tayi mashi
"Abincin ka kuma?"
"I mean abincin mutumin"
"OK"
"I love you" ya ce mata , Amman bata amsa mashi ba,
"Tawa.."
"Sir" ta amsa mashi,
"Ki bawa mami hakuri ta amince ta bani ke..in ba hakaba...zan daukeki inkai wata
kasar in aureki" dariya tawa tafariyi tana kallon shi sai taga Sam babu alaman wasa
a fuskanshi, juyawa tayi tana cewa
"Sai kun zo amsan abincin" yabi bayan ta da kallo
"Zaki Sani in wasa nakeyi maki" yafada tare da tada motan ya bar wajen.
Tawa na komawa gida tabawa wani yaro ya sayo mata kerosene, babu bata lokaci tafara
hada kayan fried Rice da chicken pepper soup.
Bayan sallan ishai Salem da Abdul na zaune a dinning suna kwasan garan da tawa tayi
masu, sai wayan Abdul ya fara ringing, kallon Salem yayi Salem yace
"You can receive your call if you want" Abdul picking yayi
"Guy sai yau ka tuna ni?" Abdul ya fada, daga chan bangaren akace
"Wallahi Dan uwa kayi hakuri.. Wai kana inane?"
"Me akayi kake tambayan inda nake"
"Wallahi haka nan.. Kawai inason shiga garin abujane nace tunda kaine dan abuja
bari in gaya maka" daria Abdul yayi
"Ai kusan wata na biyu bana abuja...muna tare da the boss"
"Amman gaskiya Abdul baka da mutunci.. Ashe kayi wata biyu gida Amman baka
nememuba?...to ni fadamin inda kake sai inzo" Abdul zai bude baki yayi magana yaga
Salem ya bata fuska
"Kayi hakuri kasan I can't disclose the boss's address" daria dayan guy din yayi
"Kayi gaskiya.. Amman Dan Allah da gaske ne wai oganka yana son wata yarinya
Yoruba.." Karaf sai akunnen Salem, Abdul kallon shi yayi Salem yayi mashi alaman
yace eh
"Eh..ya akayi ne?"
"Yarinya tayi saa.. Amman ba nan garin take bako"
"Ya akayi ne guy..what's happening?" Salem hannu yayi mashi ya maida wayan hands
free, Abdul maidawa yayi, guy din yacigaba dacewa
"Kana cikin mutane ne?"
"No..talk to me" Ahankali mutumin yafara cewa
"Cewa akayi mu dauketa mu kaita..." Sai kuma yayi shuru
"Ina akace Ku kai ta kuma wayace ku daukota?" Abdul ya tambayeshi, Salem kam tuni
zufa ya fara keto mashi
"Yola akace mu kaita..saidai gaskiya bansan Wanda yace mu daukota" yayi mashi
karya, zaiyi magana Salem ya kwace wayan daga hannunshi, afusace yafara cewa
"In wani abu ya sami..fingers din dake hannunta.. Daku, da uwayenku, ubanku.. In
short your entire family will pay dearly.." Bai ida magana ba aka katse wayan.
Salem wurgar da wayan Abdul yayi
"Waye wannan?" Salem ya tambaye Abdul
"Wani abokina ne" bai kara cewa komaiba ya dauki wayan shi number shugaban police
gabaki daya yakira ya fada mashi yana son ayi guiding wata yarinya akano, sannan
yanason akama wasu yara,
"Yes sir " kawai mutumin yace mashi sannan ya katse wayan.
Shugaban Mtn yakira
"Wai har yanzu baku gama painting gidan ba?"
"Pardon me sir..dazu da yamma aka gama..cewa nayi kar in dameka sai gobe" tsaki
Salem yaja
"Zan gayawa person in charge of my account ya turo maki 30m, sannan zan tura maka
number da zakuyiwa albishir da kayan...make sure you send the message tonight..
Gobe Ku kirata Ku fada mata ranar Thursday zaa rufe, so taje abuja ta amso kudin da
gida"
"Yes sir" kawai mutumin ke cewa sannan yace
"Sir kace 30m.. I thought 25k ka fada da farko"
"The remaining 5k is for your boys"
"Ah thanks sir..we will do it right away" Salem katse wayan yayi sannan yakira
manager ya fada mashi what to do. Salem bai kara cin abinci ba ya mike yakoma
bedroom,
"Umma what have I ever done to you... Umma please let me be happy for once.." Ya
fadawa kanshi
❤
Abangaren ameera, abinci da sukayi da hinde ta yini tana ci, har yayi sauran ta
zubdashi, around 5pm ta kara wanka, kayan jikin ta ta cire ta duba ledan da aka
ajiye mata kaya ta dauki Riga da zani, ameera dai bata taba daura zaniba balle ta
iyashi, haka ta cukuikuya shi a waist dinta , tafiya daya sai ya fadi, kurya ta
shiga don tunda tazo bata shigaba, shima gani tayi daga student foam sai leda, tana
cikin debe2 cikin gidan aka bude, agent din Salem ne da masu saka CCTV ameera ko
kallon su batayiba ta koma bayan gidan tayi zamanta tana kuka don tasan dukkan su
under Salem suke don haka babu mai taimakonta, duk Wanda ya ganta sai ya tausaya
mata, don from Saturday zuwa yau Monday ta rame sosai.
Su agent basu dade ba suka saka CCTV cameras a falon, kurya sai compound, ameera
kam bata damu tasan abinda sukeba, tanajin sun tafi takara fashewa da sabon kuka,
banda daddy babu Wanda take kira.
Yauma bakin gate ta koma bayan sallan ishai.
❤
Around 10pm Salem ne kwance sai juye2 yake,hannuwanshi biyu dafe da maranshi, da
kyar ya mike ya balli magani yasha, Amman har 10:30 bai samu sauki
"Wane irin matsala ne wannan... Why is the medicine not working..." Yana cikin
haka wayanshi yafara ringing, da kyar yayi picking kasancewan yasan mai kira
"Guy how far?" Ya fada mashi ahankali, da sauri Khalid yace
"Bestie meke damunka?" Ahankali Salem yace
"Am having abdominal pain"
"Sorry dear.. Kasha drugs dinka mana"
"Nasha..its not working" yafada yana nishi
"Guy in banda abinka ..gaka da mata Amman you are suffering your self.." Ahankali
Salem yace.
"Wace mata?"
"Wacce ka kai sambisa forest mana" shuru Salem yayi For a moment
"Wallahi mantawa nake daita...dukkan hankali na yana kan tawa"
"But you don't have tawa now..sai kayi amfani da abinda kake dashi" ahankali Salem
yace
"I don't want to use that gal...nasan in Allah yabani tawa ta isheni..kuma tawa is
not the kind of gal dazata zauna da kishiya..kawai just pray for me in sameta..don
na samu labarin Umma ta sa a dauketa and dazun da safe itama saida maminta ta
doketa because of me..am just confused"
"Am sorry you are going through a lot...I wish there is something I can do to help"
"Just help me prayer"
"I will.. About that gal..your wife in sambiza, meye ma sunan ta?"
"Ban saniba..but I think it's sameera"
" to ita sameera tunda ba zama zakayi daita ba.. I suggest you let her go" Salem da
sai cije lower lip dinshi yake saboda azaban da cikin shi keyi mashi yace
"I