Author : ummu maryam Category : Complete Novels
da dukanta har Allah yabawa dad saa ya amsheta daga hannun
mommy.
Salem kam yana fita yana rawan sanyi don sam bai wanka da ruwan sanyi balle abinda
ameera ta zuba mashi direct daga cikin fridge yake, bayan shi wani irin zafi yake
yimashi kaman ansa mashi garwashin wuta, Salem yana tafiya yana tunanin abinda
yafaru, yau dashi talakkane da ya hadiyi zuciya ya mutu don bakin ciki, yana zuwa
inda ya ajiye motanshi yabude ya shiga, zama yayi yana tunanin abinda zaiyiwa
ameera da zai huce don alokacin gani yake koda zaa yankata gabanshi bazai tausaya
mataba
"She called me a bastard...non entity... Ta zagi uwata..oh gossh..me zan wa family
dinki?...wane irin fansa zan dauka kanki?...I will deal with you and am going to
enjoy every bit of it...you and your hopeless father are going to eat your
vomit..you will beg for mercy.." Maganan tsohon ya dawo mashi
"Karshen rashi kunyaki da rashin tarbiyanki yazo...filthy bitch" Haka shi kada ya
dinga surutu, yafi hour daya zaune wurin yana tunanin, ringing wayanshi ya farayi
ya dauko wata costurmise phone Wanda baifi guda goma a duniyab ya amsa wayan, daga
chan bangaren Abdul yace
"Sir are you alright? "
"Yes..just ka nemo min the best doctor kafin in dawo gidan..." Cikin tension Abdul
yace
"Sir are alright?... What's wrong with you sir?" Ahankali Salem yace
"Am ok...just get me a doctor" Abdul zai sake magana ya katse wayan.
Still Salem zaune yayi wurin yana tunani, don har lokacin bai san abinyiba amman
yasan ko me zaiyi ba abu bane mai kyau.
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun" ya dinga maimaitawa don ji yake kaman
zuciyanshi zai bude kirjinshi abinka da mai zuciya.
Sai bayan sallan magrub ya koma gidan yana tuki yana tunani, yana zuwa gida ya
tadda Abdul zaune da wani mutum a falo, Abdul na ganin shi yayi saurin mikewa yana
cewa
"Sir me ya sameka?"
"Nothing" ya amsa masa atakaice, Abdul kallon yanda fararen idanuwanshi suka koma
ja yayi sannan yace
"Sir something is wrong..."
"I said am fine!!!!" Ya daka mashi tsawa sannan ya kwantar da murya yace
"Where is the Doctor?"
"Gashi nan" ya nuna mashi wanda ke zaune,
"Follow me" ya umarshi doctor, yayi hanyar bedroom dinshi, yana juyawa Abdul yaga
bayan riganshi da jirwaye,Abdul yasan wani abune ya sameshi Amman baisan meye ba
kuma yasan duk abinda ya sameshi shine sanadi don shine ya bashi shawaran suyi
abinda yakeyi. Duk sai yaji ya tsani kanshi, yasan in har wani abu ya sami Salem
shi zaayi holding responsible, ahankali yace
"Sir am sorry.." Juyawa Salem yayi ya kalleshi
"For what?" Shuru yayi baisan abinda zai ce ba.
Suna zuwa bedroom dinshi yacire rikanshi ya kwanta kan gado tare dayin rub da ciki
sannan yace
"Doc dubamin bayana da akwai wani ciwone?" Dukawa doc yayi tafara observing bayan
shi
"Sir da akwai abinda ya sami bayan ka ne?" Ya tambayi Salem, kai Salem ya daga
mashi sannan yace
"Eh...dazu nazo wucewa mistakingly wani ya zubamin juice ajiki...kuma naji wurin
yana yimin zafi" kara kallon wurin doc yayi sannan yace
"Sir bayan ka ba ciwo...Amman inajin juice din da aka zuba maka yana da wani Abu
ciki shiyasa kake jin zafi ...zan rubuta maka magani yanzu" kai kawai Salem ya
daga mashi, cikin ranshi yana cewa
"Har wani abu lta zuba ciki don ta illatani...daga cewa ina sonta" yana cikin
tunani wayanshi ya fara ringing, yana dubawa yaga Khalid ne, saida yace.
"The person I need.." Sannan yayi picking, daga dayan bangaren Khalid yace
"Driver what's up..." Salem shuru yayi baice mashi komai ba, Khalid yacigaba dacewa
"Na yanka mana ticket din zuwa kallon kwallon man united...ko taxi driving bazai
barka kajeba.." Salem dan murmushi karfin hali yayi sannan yace
"Bazanje...." Bai karasaba Khalid ya katseshi dacewa
"Kan uban nan...dan taxi driving sai ka ruguza mana aladanmu da muka saba..."
Ahankali Salem yace
"Ba laifinka bane..." Khalid kara katseshi yayi
"Guy ya akayi naji muryan ka kasa...kodai yan matan Kano sun cima uwane?"
"Ba kadanba" Salem ya amsa mashi, wani irin daria rainin hankali Khalid yafara yi
yana cewa
"Me sukayi maka" yafada har lokacin bai bar daria ba, ahankali Salem yafada mashi
abinda yafaru, shima Khalid ranshi yayi mugun bashi, Salem yacigaba dacewa
"Kuma abin haushi shine har yanzu bansan abinda zanyiwa yarinyan nan in
huceba...don nayi tunani har nagaji.." Shuru Khalid yayi na dan lokaci sannan yace
"Guy ko insa ayi kidnapping dinta muci mata uwa..." Kai Salem ya girgiza kafin yace
"Mom da brother dinta are nice.. Kawai inason abinda zanyi in bata mata da dad
dinta..." Shuru suka sakeyi kafin Khalid yace
"Kaima matsala gareka...yanzu wake ta wani true love.. Kawai kasamu mace mai kyau
ciki da waje ka aura, ka biya mata bukatunta da rana itakuma ta biya maka bukatanka
da dare..that's life now... Amman true love no longer exists,..." Bai gamaba Salem
yace
"Best kasan I want a woman that can sacrifice her self for me.. Nasan there is a
woman out there for me..."
"Kana nufin bazaka yi giving up ba kenan... Ko sai ansumu yarinyan da ta watsa
maka acid a handsome face dinka zaka hakura....." Tsoki Salem yaja kafin yace
"Dalla yimin shuru...kawai ka gayamin abinda zai yiwa yarinyan nan I huce"
"Nace muyi kidnapping dinta kaki...to bari inda a dauko maka ita kayi raping..."
Wani dogon tsoki yayi sannan yace
"Amman bestie baka da hankali..ai ko ina mazinaci bazan kusanci wannan yarinyan ba
balle kasan ba halinabane..kawai inason in gan yarinyan nan under my control... I
want her to beg for my mercy... Wallahi guy yarinyan sam batayiba....killan shiyasa
Allah ya turani gidan don in koya mata hankali" shuru suka danyi sannan Khalid yace
"Yanzu meye abinyi?"
"I don't know.."
"To marry her...tunda kanason ta zauna karkashinka...sai kayi yanda ka gandama
daita.." Salem bai karasa jin abinda Khalid zaice ba ya kashe wayanshi.
Bayan hour daya Abdul ya kawo mashi magaggunan da akayi mashi prescribing, still
Abdul tambayan shi yayi abinda yafaru Amman still Salem ce mashi yayi bakomai.
Tundaga wannan ranan Salem ya rufe fita, daga bedroom sai masjid, kullum cikin
tunanin abinda zaiyiwa ameera yake Amman still bai samu solution ba daga baya ya
bawa kanshi hakurin ya kyaleta Allah ya hadata da daidai daita tunda shi ba abinda
yazoyi ba kenan.
Bayan sati daya da faruwan abun Wanda yayi daidai da satinsu uku a garin Kano,
Salem yasa Abdul ya kira mashi makeup artist ya gyara mashi fuska.
Gidan Salem a zoo road yake , kuma duk Wanda yasan zoo road yasan hanyarta busy
road ne, saboda da akwai masu business kala2 a wurin , bayan sun fito, basu dade
da barin gidaba wani dan almajiri yazo tsallake titi garin Salem ya kaushe mashi
mistakenly ya Dan gogi wata murano, da sauri yayi parking don bawa mai motan hakuri
shima mai motan parking tayi tafito, Salem da Abdul na fitowa, Salem ya gane Ashe
mai motan ameera ce, da sauri ameera ta dubi motan bayan motanta da Salem ya goga,
wani irin ashar ta saki sannan ta daga kai ta kalli Wanda ya goge motanta, tana
ganin Salem ne tanufeshi gadan2, tana zuwa gabanshi ta sharara mashi wani wawan
mari, nan take ya dafa cheeks dinshi, cikin zafin nama Abdul yazo wucewa da sauri
Salem ya rikeshi da hannu daya still hannunshi daya rike da cheeks dinshi,
Ameera kallon Abdul tayi sannan tace
"Oh kana son tabani?..please bring it on...da saina koya maka hankali..." Sannan ta
juya wurin Salem da har lokacin bai saki kuncinshiba tace
"Kai kuma ka bar bina kuma motata da kayi scratching saiya sayi uwarka da ubanka"
Salem tsayawa yayi kaman bara lakka, muryan wata yarinyan ya tsinta tanacewa
"Ke Allah ya wadar halinki..." Bata idaba ameera tace
"Daga ke harshi kunci uban da ya haifeku banzaye matsiyata..." Yarinyan ta sake
cewa
"Kece matsiyaciya tunda har zaki iya daga hannu ki mari Wanda ya girmeki saboda
wannan motan..." Salem ji yayi wata tace
"Tawa..amebo watin concern you"
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE
❤
®zuwairat(ummu maryam)
1⃣3⃣
Yarinyan da aka kira da Tawa ta kalli Salem taga kaman da jini hancinshi, bata ce
komai ba ta nufi wani chemist dake kusa da wurin, Salem na kallonta ta cire kudi
cikin apron din dake jikin ta don da alaman abinci suke saidawa awajen, ba da
dadewaba ta dawo rike da cotton wool, tana zuwa ta mikewa Abdul, ahankali Abdul
yace
"Me zanyi dashi?" Yarinyan nuna Salem tayi da yatsa kafin tace
"Habo yake.." Sai lokacin Abdul ya lura da jinin dake hancin Salem, da sauri Abdul
ya amshi cotton wool din yafara goge mashi hanci, har lokacin Salem bai dawo daidai
ba, don tunda uwar da ta haifeshi baa taba taba mashi lafiyan jikiba, sannan daga
nursery school zuwa secondary school Turkish international school yayi kuma ko
kadan baa dukan yara, amman shine yau Mace ta mareshi yau, duk da yasan yana da
saukin zuciya yasan he can't let this go.
Itakam ameera tana ganin yafara habo ta dauki motanta ta bar wurin Amman fa har
lokacin bata bar zaginshi ba.
Abdul yafara Goge mashi hanci, shima sai lokacin Salem yasan yana nasal bleeding,
cikin ran Abdul kam ji yake in shi aka mara zai fi mashi sauki sau dubu, don
zuciyanshi tafasa yake kuma abinda yafi bashi haushi shine yanda Salem ya hanashi
ya Koya mata hankali, Salem ya ji wata babban mace nacewa
"Tawa..na my money you use buy cotton wool?" Ahankali tajuya wurin matan sannan
tace
"Zan biya ki cikin kudin da zaki bani anjuma " Mata da ganintaba mutunci kuma da
alama ita Tawa takewa aiki
"Ai dole ki biyani..makulmaciya...ko wa ya kiraki oho..oya wuce ki bawa mutane
abinci" nafa wayanda suke aiki tare suka fara yi mata dariya, itakam juyawa tayi
wurin Salem sannan tace
"Oga sorry..Allah zai sak maka...kuma insha Allah kaima watarana Allah zai baka
motan daya fi nata..." Salem tsaya kallonta yayi sannan yace
"Thank you"
"Bakomai..." Ta juya ta tafi tana cewa
"Daman masu kudi basu ganin talaka as anything... Allah zai saka mana".
Salem kallon Abdul dake ta goge mashi hanci yayi yace
" take me to the hospital " kai kawai ya daga mashi don kunyan hada ido da Salem
yake,
Cikin mota suka koma Abdul yafara tuki shi kuma Salem har lokacin hannunshi rike da
cotton wool a hancinshi cos jinin ba bar zuba ba, Abdul dan kallonshi yayi
"Sir ka kwantar da kanka baya kadan" babu musu ya kwantar da kanshi baya.
Free hand dinshi yasaka cikin aljihunshi ya dauko wayanshi, wata number da aka
rubuta Nigeria head of NGO yayi dialling, cikin kankanin lokaci akayi picking tare
dacewa
"Sir..good afternoon.. How is your holidays"
"Fine" kawai Salem ya amsa atakaice sannan yacigaba dacewa
"Ka turo min Pictures da details na yan northern NGO"
"Sir yaushe kake bukatanshi?"
"Right now" yana kaiwa nan ya katse wayan shi, tare da lumshe idanuwanshi,
"Allah nasan kanason in koyawa yarinyan nan hankali... Don nasan haduwata da ita ba
coincidence bane destiny ne" yafada cikin ranshi.
Suna zuwa hospital aka nubashi doc yace abinda ya sameshi ya zo mashi unexpected ne
shiyasa yake bleeding, ice block aka sa agaban goshinshi for a moment jinin ya
tsaya sannan suka bashi magunguna.
Suna kan hanyan dawowa emails suka shigo mashi, bai budeba har suka isa gida. Suna
zuwa gida ya dauki makeup remover ya goge fuskanshi nan ya kara ganin hannun ameera
kwance kan fuskanshi, wayan shi ya dauka ya dauki photon fuskanshi ya turawa Khalid
nan take Khalid ya kirashi
"Guy meye wannan?"
"Same yarinyan nan ta mareni..."
"What... Karshen mari kenan... She really have to be taught an unforgettable
lessons.. If you are not doing anything kawai ka barni in sa aiyi maganinta.."
Ahankali Salem yace
"I have a plan... Zanbi shawaran ka..." Nan ya kwace abinda yayi niyyan yi ya
gayawa Khalid, shewa kawai Khalid yayi yana cewa
"Best ko shaidan zai jinjina maka.."
"Ai friend nasan ba haka nan Allah yake ta hada ni daita ba...yanason in koyamata
rayuwa..and am not let him down.." Cikin daria Khalid yace
"Yanzu zaka hakura da taxi driving ko?" Shuru Salem yayi for a moment kafin yace
"No.." Cikin zolaya Khalid ya kara cewa
"Haba ango gashi zakayi aure?" Salem katse wayan shi yayi ya dauki iPad dinshi ya
ya bude emails dinshi.
Nan ya ga emails da shugaban NGO na Nigeria ya tura mashi,hotuna ya fara kallon don
tantance dad ameera, yana cikin dubawa yaga alh umar Adam gezawa
"Yes wannan shine Wanda na ganin gidan su wannan shaidaniyan yarinyan" yafada wa
kanshi, budewa yayi yafara karanta details dinshi, Ashe shine head na Kano zone,
" mere state head shine yarka take yanda ta gandama kaman yar Aliko dangote..let's
see what happens... " wayanshi ya dauka ya kara kiran head na Nigeria, mutumin na
picking yace mashi
"Terminate umar Adam gezawa's appointment... In yayi complain ka bashi details din
da zansa secretary dina ta turo maka...ka gaya mashi ina Kano Kuma gidana nada GPS
so yayi searching location dina..am sure motnashi yana da navigation"
"Yes sir " kawai mutum ya fada sannan Salem yayi hanging off.
Mikewa yayi yana cewa
"Am going to enjoy this" bathroom yashiga ya dauro alwallah sannan ya fito falo,
yana shiga Abdul dake zaune yasha jinin jikinshi , ahankali Abdul ya daga kai ya
kalli fuskan Salem, yaga gefen fuskanshi jajur kauda kanshi yayi, kallon shi Salem
yayi
"Alh Abdul let's go to masjid" yayi maganan kaman babu abinda ke damunshi,
Kallonshi Abdul yayi
"Sir am very sorry.. Ni na kawo silly idea dake jamaka wulakanci...dan Allah in
ranka bazai baciba mu bar wannan hunting..." Karasaba Salem ya katseshi dacewa
"Tausayamin kake?..to for your information banason self pity sannan bani bane abin
tausayi..wannan shegiyar yarinyan ce abin tausayi...kuma kaga wannan quest din
yanzu muka farata don ya koyamin abubuwa da dama and most especially ya koyamin ba
duk abu mai kyalli keda kyauba wato not all that glitter is gold..ka ga tafiya ta
masjid" ya fita ya bar Abdul nan zaune, yana fita Abdul yabi bayan shi da sauri.
❤❤
"Mami kin san abinda ya faru wajen aikina yau?" Tawa ta tambayi mamanta, Matan
girgiza kanta tayi sannan tace
"Ya zaayi in sani tunda ba wurin aikimki nakeba" Matan ta amsa mata da yarensu
itakuma tawa tana magana da hausa kasancewan tanajin yarensu Amman bata Iya yinshi
itakuma Maman bata Iya hausaba sosai, tawa ta cigaba dacewa
"Mami wata yarinyce ta mari wani babban mutum a gaban restaurant dinmu..wai dan ya
dan gogi motanta da taxi dinshi... Wallahi mami mutum saida jini ya fita a
hancinshi... Ni kuma nayita zagin yarinyan...." Da sauri mami ta katseta dacewa
"Kini...meye ruwan ki ?..kinason ki ja manako?" Dan turo baki tayi
"Mami mutum zai girme brother tajudeen fa..."
"Ina ruwanki koya girmi babanki...please karki jamana matsala... Kinga ta abinci
muke ..." Ahankali tawa tace
"Yes mami.. Gobe zan saya maki inhaler ki don madam ta cire daribiyu cikin kudin
aikina don na sayawa mitumin da aka Mara cotton wool... Kuma mami cotton wool din
ashirin na tsaya Amman Dan zalunci ta cire min Dari biyu" ahankali Matan tace
"Naji Allah ya saka maki..Amman karki kara shiga abinda ba ruwanki"
"Yes mami" tafada sannan ta mike ta sauke abinci dake kan stove cikin Dan karamin
tukunya ta zubawa mami sannan ta dauki mafici tana hurawa mami suna labari kaman
yanda suka saba.
❤❤
Aranar da ameera ta mari Salem taje office din babanta take bashi labarin abinda
yafaru da kuma yanda ta maka mashi mari, dad dinta jinjina mata yayi yana cewa
"That's daddy's angel" wuri ta samu ta zauna acikin daya daga cikin wasu relaxing
sofa dake office din dad, sannan ta kurawa photo Salem da dad dinta dake manne
jikin bango. Da alaman Salem baisan ana daukanshi photon ba Amman still he's
looking breathtaking. Kurawa photo ido tayi tana tunanin
"Wannan mijin mai rabone" tafada tana lumshe idanuwanta
[10/8, 12:06 AM] Fadila S. Takko: ❤
ZAKISAN KONI WAYE
❤
®zuwairat(ummu maryam)
1⃣4⃣
Sai tunani take tana cewa
"Duk wacce Allah ya zaba amatsayin matan wannan bawan Allah ta huta...imagine being
married to the most handsome and the richest guy in africa...kam kome kakeso a
hannunka..ka hau the latest car...ka saka the latest version of clothes and kaci
abinci daga the best cook in Nigeria sannan ka zauna in the best house Kuma ka
maida kasashen waje kaman zuwa toilet..." Tana cikin tunanin wata zuciya tace mata
"Ameera ki farka daga mafarkin da kike...don sam baki da chance... Kilan bazaki
taba ganin shi ba har ki mutu" bakinta ta tabe tare da gyara kwaciyanta, sai dab da
magrub suka koma gida, motan dad dinta gaba nata bayan nashi.
Bayan sun gama dinner wayan dad yayi ringing, yana ganin mai kira ya gwalo
idanuwanshi tare dacewa
"Allah ya sa lafia.." Yafada yana picking wayanshi
"Hello sir..good evening.." Shuru dad yayi yana sauraron abinda oganshi yake cewawa
sannan yace
"Sir ban bude emails dinava " mutum magana yayi kafin dad yace
"OK sir ..bari in duba emails din" sannan ya kashe wayan.
Ameera ya kira ta dauko mashi laptop dinshi, emails dinshi yafara dubawa, nanfa
yaga takardan sallama
"inna lillahi waina ilaihi rajuun..." Ya fara maimaitawa da karfi, mom da ameera
sai affan suka nufeshi da tension,
"Lafiya?" Ko wannensu ke tambayanshi.. Amman
"Inna lillahi.." Kawai yake ta maimaitawa... Da kyar ya samu cewa
An koreshi daga aikinshi, ko waccensu salati ta saki, ameera kam hannu ta dora bisa
kai tana kuka. Mom kam neman hawaye tayi tarasa, shikam affan kallonsu kawai yake
dukda yasan rashin aiki matsalane, hannu dad na rawa ya dauki wayanshi yayi dialing
number oganshi, bayan ringing kaman biyar ya amsa
"Me nayi kuka yimin haka...meye laifina?...ple..." Bai gamaba mutum ya katseshi
dacewa
"Calm down.. Sir Salem ne ya bada umarni...kuma yace yana kano..so zansa secretary
dina ya turo maka details sai kayi amfani da car navigation ka nemi gidan shi..."
Da sauri dad ameera yace
"My car don't have a navigation... "
"OK don't worry.. Bari in kirashi..in ya bada address dinshi zan baka sai ka
sameshi"
"Thank you... Thank you.." Kawai dad ameera keta maimaitawa ayayinda zufa ke ta
keto mashi.
❤❤
Salem kam bayan sallan ishai ya zauna yana jiran abinda zai biyo baya, bai Dade da
zamaba wayanshi yafa ringing, yana dubawa yaga Nigeria head ne ke kiran shi, ajiye
wayan yayi bhai dagaba, saida yayi mashi kusan 3 miss call sannan ya daga tare
dacewa
"Ya akayi kuma?" Ahankali mutum yace
"Sir..wannan alh umar Adam din yace motan shi baida navigation.. So sir in babu
stress ka dan bani address dinka..." Bai karasaba Salem ya katseshi dacewa
"Listen to me...bani da lokacin raba address dina...in bashi da navigation then ya
samo ma kanshi sabon aiki...and tell him zan bar Kano jibi..in har na bar Kano kar
ya nemeni..." Kas ya katse wayan shi yana murmushi mugunta..Abdul dake zaune a
falon yanajin abinda Salem ke cewa yasan ba abu arziki bane.
Abangaren dad ameera kam oganshi na gaya mashi yanda sukayi da Salem ya dora hannu
bisa kai yanacewa
"Ina zan samu kudin siyan mota mai navigation... OK bari inkira kB mai motoci.."
Yafada kaman wani Mara hankali, kiran kB yayi bayan ya daga yake gaya mashi ko suna
da babban mota mai navigation, mutum yace da akwai, dad ameera ya tambayeshi nawa,
kB yace 70millions,baki dad ameera ya bude kafin yace
"KB in na kawo jeep dina dana Hajiya sai murano ameera nawa zaka saya?" Daga dayan
bangaren kB yace
"Gaskiya alh..tunda Kaine zan sayi jeep dinka dana hajiya million 12 each sannan na
ameera million 2..."
"Haba kB wurinkafa nasayi nawa dana Hajiya million 20 each..."
"To alh ai kasuwane..." dad yaga ko an sayi dukkan motaccin gidan bazai saya mashi
motan da yake bukata ba,
"To kB don Allah alfarma nake nema...zan baka million 1 ka aramin motan...gobe
kawai zanyi amfani