Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
_Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_
_ƊAN ƊANO daga alƙalamin AMMEY LAYLERH ✍️✍🏼_
*FOR YOU HAFSAT MUHAMMAD ALIYU, AMMIN SA'EED.... UBANGIJI YA ƘARA MIKI LAFIYA DA KWANCIYAR HANKALI... *
_YOTAWANMU GABA ƊAYA WANNAN LITTAN TUN DAGA FARKONSA HAR ƘARSHENSA NAKU NE KYAUTA...._
*✯ 🌠YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION {YOTA}💫*
The Writer's of
*KAREN BANA*
*JALAAL AREEF*
*ƘAUNA BIYU*
*MIKIYA*
*TA DABAN*
*SO DAN RAYUWA*
*DUNIYARMU*
*RAMIN KURA*
*ƘARSHEN ƘADDARA*
*AND ONGOING DUHU na dukan DUHU*
Page 1
_Trailer out now_
ꨄYa musulunta ata sanadiyyar soyayyarta, ya yarda ya ɗauki kasadar rabuwa da ahalinsa dama duk wani makusanci nashi duk ata dalilin zazzafar soyayyar da yake ganin zata kaishi ga wata mafita ce ta daban. Sai da tafiya tai tafiya tafiyan da yay nisan da babu komawa baya a cikinta, bayan da ya riga ya mata wani kalan nisan zango na ninƙaya a cikin duniyar sonta, Ya fuskanci ashe ita ɗin fanko ce na ashanar aci bal bal. Wacce bata da amfani a cikin tashi Rayuwar dama DUNIYARSA baki ɗaya, tunda shi ɗin ya kasance DUHU ne, yayin da yake ganin itace tsananin da zata kai shi ga hasken da yake kwadayin samu, sedai ashe ita ce hasalin DUHUN na DUKAN duhu ɗin ma gaba daya. Se dai kuma wannan ƙwadaitakar daya riga da yay a addinin da ba nasa ba, saboda ya romon addinin Musulincin daya riga da ya gama kwankwaɗa ya sanya shi jin yanzu ne ma wasan se soma, don kuwa Ya gama fuskantar *YASMINE DUHU ce na DUKAN DUHU* A cikin rayuwarsa dama Duniyarsa baki ɗaya. Wannan wacce iriyar kaɗdarace me zafi data haɗa tafiyar da kuma take maban banta a gare su? Shin kai me karatu ya zaka tsammaci wannan karin magana ta DUHU na DUKAN duhu?.....
ꨄ_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦°
♡ "Papaah!!!"
Ya faɗi cikin muryan shogoɓa da sakalci yana karyar da wuyansa gefe har farar fuskarsan na dakunewa.
"Johseph?"
Mr jef deefer daya kasance mahaifi ga Joseph ɗin shima ya furta, Yana kallon yaron nashi cike da tsantsar son da yake jin kaff duniyar babu mai masa kalansa. tsaiwarsa ya gyare tare da ɗan karkatan da hulan daya kasance me zubi da irin malafar nan yay, cikin harshen English ya furta. "Yeah Johseph har yanzu kai ƙaramin yaro ne, ba ko ina ya kamata ace naka barinka kana shiga ba, dole driver ne zai kaika" wani kalan sake ɓata ransa yay yana komawa da baya tare da faɗawa ɗaya daga cikin saman 1str ɗin da suka zagaye parlour'n, yana kaiwa zaune tare da jingina da jikin kujeran.
Zama papan yay daga gefensa yana shafa sumarsa like woni baby'n goye nan. "To shikenan na yarda zaka fita ba guard's Amma nima fa ina da sharaɗi akan hakan" ba tare dayay tunanin wanda sharaɗi bane ya furta."Ohh papa problem" daƙuwa papan ya masa da dariya a fuskanshi "Na barka jeka dawo zamuyi magana akan Deepika" cike da zumuɗi ya miƙe harda ƴar rawansa na farin cikin zayyi driving da kansa yau, ze kuma fita ba tare da guard's ko ɗaya ba, Wani tsallen farin ciki ya buga daidai da papan na cilla mishi trow pillows ɗin dake zagaye da lafayayyar kujeran da suka zagaya parlour'n. Da ɗan gudunsa ya bar parlour'n yana riƙe kunnuwansa alamun ya tuba.
Tunda ya fito kuma ya maida fuskan nan me ɗauke da kyakykyawan murmushin nan yana medata tamkar maɗaukar zunubi.
Cikin yanayi na kamewa yake takunsa cikin ƙarfin jiki da kuma izza, don kuwa duk wanda yasan Joseph yake kuma rayuwa dashi to kuwa tabbas yasan irin izzar da yake da. ♡
Hannunsa dake ɗauke da tsadaddar wayansa ƙirar iPhone x ce riƙe a hannunsa yana kamar duba woni abu ne me muhimmanci, haka ya ringa ratsa wuraren gidan daya kasance wani irin tsararre haɗaɗɗe kuma. Tun kamin ya ƙara sa isowa Micheal yay hanzarin isa Parking car na gidan,kai tsaye wata shahararriyar mota ƙirar zamani ash color da ta gaji da haɗuwa yay hanzarin fiddota compound na gidan. wacce kallo ɗaya zaka mata kai da kanka ka fidda ƙiyasin maƙudan kuɗaɗen data lasa kafin a mallaketa. Dan The car ɗin is so majestic, so elegant, so classy, so luxurious. ♡ Yana ƙoƙarin shiga mazaunin driver sit cikin wannan daƙilallar muryan ya cira masa hannunsa ɗaya tare da furta. "Uhmmm... uhmmmm" yana kuma bashi hannu alamun ya bashi car key na motarn. Cikin ɗari ɗari da tsoro da kuma rawan jiki Micheal ɗin ya furta "Amma Bo.....
A dake muryarsa har na ɗan tashi kaɗan ya furta "Ba buƙata" daga haka ya sanya kansa cikin haɗaɗɗar car ɗin, tare da yin reverse nata yana barin haraban gidan wanda hakan yay daidai da zazzaro idanu wojen da Micheal yay cike da ruɗin fitan da yay shi kaɗai. Don yasan wannan ɗin dokar paah ne baya taɓa barin Joseph ɗin fita shi kaɗai ɗin sa ba tare da guard's ko driver nashi ba. Kasancewarsa pilot kuma dama hakan doka ce a kansu duk wani pilot baya taɓa driving da kansa sedai a ja shi... Paah dake tsaye daga samar benen dake kallon fitan Shalelen yaron nashi yay ƴar dariya cikin sautin da zaifita sosai yay ma Micheal ɗin magana kan cewan karya damu yasan da fitan. Woni kyakykyawan numfashi ya kawo yana kuma shan zuciya irin alamar na tsira ɗin nan da ƙyar. ꨄ Shi kuwa Johseph cike da nishaɗin daya gaza ɓoyuwa har saman kyakykyawar fuskanshi kai tsaye kana iya kallar hakan. Tunda ya hau saman kwaltan yake driving motan nashi very slowly, cikin ɗan tafiya tinanin papah'nshi kan rashin barinsa fita shi ɗaya ko yay driving Kamar haka shi kaɗai. Ɗan ɓata fuska yay tamkar yana gaban mahaifin nashi ya furta
"Ahh dad I'm anger so what about me which condition I'm in I have a difficulties something that happened to me papahh, everything happen to me like a young age, ahh seriously me I'm a big like any serious good human being I'm proud for my self for that hmm may be I will show him do to really understand, but I love you Papa so much I LOVE YOU paah!!"
Yay maganan yana wani lumshe kyawawan fararen idanunsa da kwayar cikin su ta kasance gold colour. Wani kalan jan birki yay ƙoƙarin yi amma ina hakan na neman gagaransa kasancewar an daɗe ba'a haɗu ba, don ba a barinsa yin driving da kansa koda kuwa zuwa ƙofar gida ne. A wani irin zuciye yajuya kan motar yana tsaida ita, amma duk da hakan seda car ɗin ta bugi matashiyar buduryar dake sanye cikin shijab kalan ash colour har ƙass.Farar ƙafarsa dake cikin baƙin takalminsa me shegen ƙyau ce ta fara bayyana, kafin blue dogon wandon outpit ɗin dake jikinsa. A kuma zafafe ya fito don baiga hurimin ubanda ya kawo ta saman kwaltan haka ba.
Ita kuwa wacce aka bige ɗin kamar ba zata juyo ba, sai kuma zuciyarta ta bata shawarar juyawa taga wane shahararran ƙwallan mara imanine da mutuncin ne haka .da ya nemi kaɗe ta. Idasa fitowar yay yana ƙarasowa har inda take duƙe da jikin motor ɗin. A gabanta ya tsaya yana hucin ɓacin rai shegen tsayinsa harna ƙaruwa yana ganin tsayin kansa da nata ba ɗaya ba, duk da kasancewar a duƙen take har yanzun kuwa. ♡ Soft fararen hannuwansa masu aji ya sanya kai tsaye yana kai hannun da nufin wurgar da ita daga jikin motar nashi. Se kuma aka sami akasi hannunsa kawai ya sauka saman shimar nata yana cilli dashi. Wani kalan waro manyan idanunta tay ganin an fusge dogon shimar ɗin dake jikin ta, saur̃in sáke ƙanƙame Alqur'anin dake rungume a hannunta tay, Zuciyarta na wani kalan tafasan ɓacin rai har tana jin yadda bugun ta ke fita fatt² haka da mugun ƙarfin gaske. Se kuma gaba ɗayanta ta juyo a fusace kai tsaye tana ɗauke wannan kyakykyawar fuskan nashi da wani lafiyayyen mari ta ɓangaren dama kana again ta sake juyowa ta kuma wanke shi da woni ta ɓangaren hagu....
♡
"Shin kai babu zuciyn a ƙirjinka ne hala!? kokuwa kana tunani da zuciyar takane bada ƙwaƙwalwa ba?.Amma kaikam duk ahalunka babu masu imani kuma bakusan menene daraja da muhimmancin ƴa mace ba?" Matashiyar budurwarn ta faɗi fuskanta ɗauke da mugun ɓacin rai, Kana ta bishi da kallo tun daga sama har ƙasa, wasu shegun riga da wando ne a jikinsa outpit kalan koɗaɗɗun nan masu ya ga² Se kuma sarƙan Cross na diamond ɗin dake saƙale a wuyansa, se bariman warin diamond ɗayan dake manne a kunnensa, se wani shegen kalan ɗan iskan askin dake kansa irin me kibiyar nan, ta ƙasa kuma ya tari gashin kan nasa ya tufke shi. iyaka su kaɗai sun isa tabbatar maka da cewan Ehhh lallai wannan ɗin ba musulmi bane Christian ne. Da wani kalan wulaƙantaccen kallo ta bishi kana taci gaba da furta. "Koda yake alamu sun gama nuna cewar musulumcinma kai baka da!, don da dukkan alamu arziƙinsa ma baka samu ba bare kuma har aje ga sanin daraja ɗan Adam. Amma duk da haka Kai mutum ne wadda ko acikin Christian ɗin ma kai baka da daraja daga kallonka na tabbata haka, duk iskancin da irinku masu addininku suke dashi basa taɓa wulaƙanta ɗan Adam irin haka"
A nutse ya janye idanuwansa daga kallonta yana rasa ma ta inda wanna ƴar filic ɗin yarinyarn ta sama kwarin gwiwan yi may maganganu har haka? Duk da kasancewar motsin da bakinta kaɗai keyi ne ya tabbatar may da cewan masifa take may bawai don yasan abinda take cewan ba kuwa.
Kallonta yake daga sama har ƙasa ta cikin eye glasess ɗin dake sanye a idonsa, ba tare da yama nuna alamar ya fahimta yaren da take maganar da shiba, ko nuna yama ji zafin marin data may ba ya raɓata zai wuce abinsa, saurin sake shan gabansa tay ganin kamar duk bayajin hausarn da tay maganan dashi, hakan ne ya sanya kai tsaye ta juye harshe zuwa English ta furta "To dan ma kaji Wllh² baka buge banza ba!, tun da kai baka da cikakken imani da kuma tausayi to kuwa wllh se na nuna maka hasalin yadda ake mutum ta mace da kuma darajantata!"
Wani kalan ɗan ware mata manyan idanunsa yay tare da ambatar "what? Hhhhh this girl is very stubborn and stopid shutter. stopid girl wannan wani kalan shashancine kodai ke baki da class ne? ko da yake naga ke mahaukaciyane ok you are deaf"
Yay maganan yana zare eye glasses ɗin dake sanye a cikin idonsa, Daidai da loƙacin da niƙab ɗin dake sakaye da fuskanta iska me ƙarfin dake kaɗawa ta yayeshi sama, daga saman kyakykyawan farar fuskarta, wani irin bugawa dummmm gabansa yay.
Don haɗewan da idanuwasu sukai wuri guda,Wanda wani kalan launinsu da hasken kwalliyar halittar da idanuwanta suka yi may tozali. Haka yaga gilmawar fararen idanuwan ta tamkar hasken farar zinariya mai ɗauke da tambarin Alkuki acikin ragayar fitilar kwai. Wani kalan ɗan dukan kansa yay yana tsurama kyawawan laɓɓanta da kai tsaye yake iya tantace kalan laushinsu. A mugun fusace ta sake fidda zara zaran yatsun ta biyar da ALLAH ya halatta mata ta sake ɗauke kyakykyawar fuskan shi da wani kalan arnen bahagon mari me gigita duniyar wanda aka yima shi.
A kuma daidai loƙacin ne bodyguard nashi da madame Victoria Osteen ta balbalesu da masifan barin shi fitan da yay shi kaɗai. Domin ba ƙaramin Mahaukacin S0 take ma Johseph ɗin ba, Ba tare da yasan da wanzuwar su wurin ba kattin arnan majiya ƙarfin kawai suka ma matashiyar budurwarn ƙawanya aka tamkar zasu cinye ta ɗan ya, Da wani irin mugun kallon baku da hankali ya shiga binsu dashi ɗaya bayan ɗayan.
Se kuma ko wannensu ya shiga yin baya da baya a mugun tsorace don sune kawai suka san ainihin ko wanene Johseph ɗin.
Ita kuwa wani irin nauyi ƙahon zuciyarta ya mata tamkar za ta faso ƙirjina ta fito haka taji ƙirjinta ya danne.A karo na biyu a kuma kausashe ta sake furta. "Kar ka yadda ko a rashin sani ne wannan ƙazamin hannun naka ya sake yinƙurin taɓa koda hijjabin jiki nane balle hannuwana Malam" tai maganar tana ƙara sa fusgo numfashinta da ƙyar da suke kokawa da juna wajen barazanar barin jikinta da yake shirin yi wajen fita baki ɗaya.
Wani kalan taɓune fuska yayi yana tsurama kyawawan laɓɓanta ido. Wanda suka yi matuƙar burgeshi sosai wajen yadda take balbala bala'in masifan, hakan ya sanya ba tare da tunanin komai ba ko dede ze aikata ko akasin hakan babu zata babu tsammani kawai taji sauƙar lisp nashi saman nata. A wani irin daskare ta tsaya chak da shirin tafiyan da take ƙoƙarin yi tamkar wacce akayi freezing nata. dan ko iya juyowa ba tayi ba balle tay tunanin meke faruwa da ita, Wani kalan rumtse idanunta tayi for the moment tana sauraran bugun zuciyarta, sharrr kuma hawayen tashin hankali suka wanke samar kyakkyawar fuskarta na tsantsan tashin hankali.
Shi kuwa John samm be san abinda ya aikata a gareta me girma bane duk da kasancewar dama samm can shiba Mutum bane ma'abocin irin hakan ko da kuwa da yake ba Musulmi ba. Amma samm hakan tsentseni yake bashi kuma da ƙazantane yake danganta hakan.
Amma se gashi yau da kansa shi Johseph Mr jef deefer ya aikata hakan ga wata? Watan ma Hausa gurl, shi ne ma sanadiyyar da har su Micheal suka janye shi daga gare ta be farga da hakan fa. Don ji yay Duniyar na juya masa yana jin tamkar shi kansa ba shi bane haka yake binsu, suna daɗa janshi ganinsa na ƙare nesa da ita har zuwa gaban Manyan motocin da suka zo dasu wajen guda biyar. Chark ya ja ya tsaya da shirin shiga car ɗin da yake yi, sakamakon sauƙar wani abu me nauyi da yaji a tsakiyar gadon bayansa. Su kuwa kattin arnan nan a 370 sukayi kanta da niyar su dagargaza ko wanne ƙashi da tsoka na jikinta. A wannan karon ma dakatar dasu yay ta hanyar ɗaga musu hannu. Cikin mugun azabar daya dirar masa lokaci guda ya juyo ga kallonta daidai tana shigewa cikin jibgegiyar car ɗin da ta taho ɗaukanta, Ba don ya soba don dole ya faɗa cikin car ɗin, yaransu najan motocin da shegen gudu na tsiya don sosai sukaji haushin hana musu raga raga da naman yarinyan da yay. Hakan yasa cikin mugun fushi ɗaya daga cikin yaran suka kira Madam Victoria Osteen tun kamin su Isa ga gidan suka sanar mata cewan wata Hausa girl ta jima John rauni.
A silo tarin motocin nasu suka lula zuwa haɗaɗɗiyar unguwar Banana Island, a katon get ɗin makeken gidansu sukayi Parking car nasu. Wani kalan mahaukacin hong suka shiga do ƙawa. Kai tsaye kutsa kansu cikin wargajejen katon get ɗin gidan sukai loƙacin da aka gama wangale musu shi. Baki ɗaya jama'ar gidan tun daga kan yaransu har manya suna kammale a ƙofar parlour'n shigowa, kasancewar Micheal yayi woya dasu kan cewar ai Johseph ɗin yayi faɗa da wata Hausa gurl ne, harma ta jimay ciwo, jin ambatar iyaka ciwon ne ya tashi duka hankalin madame itama tana tasar hankalin duk jama'ar gidan. Jin jirin tsaiwar motocin sune ya sanya su yowa Parking car ɗin dukansu barin ma jikin Madam Victoria osteen da har wani rawa² yake yi. Tun kamin ya ida fitowa ta shiga motar tana fitowa dashi kusan rungume a jikinta dukansa, duk ta cewan girman jikin da yake da amma samm ita bata gani idanunta sun rufe akan ƙaunar Shalelen ɗan nata.
A hankali a kuma nutse suke tafiya yana jingine da jikinta suke takowa zuwa cikin parlour'n. Dab da inda Papan shi yake zaune Madam Victoria ta zaunar da Johseph ɗin, itama tana zama gefensa suka sanya shi tsaƙiyansu. Sake tsumewayi yayi wuri guda jin yadda duk iyayen nashi suka bi suka ruɗe da ɗan bugun da besan ko miye ba yarin yan ta buga masa. A wani irin hankali yaji zuciyarsa tana narkewa tuno da waɗan nan mayun idon da bai taɓa ganin irin suba. A bayyane ya shiga furta.
"Meri har saash me tu ♥️_
_meri har Khushi me tu tere bina jindg_
_meri nhi kyu ki Meri jindagi hai tu ♥️😘 I love you, my sweet dreams baby_ As much ASI love you _
_I've finally accepted that it's time to let you go_
_you