Advertisements
Chapter 2 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   2 / 31

3K to 6K   out of 91.1K words

will always hold a place in my heart ♥️ _
_but you no longer belong in my gurl _ more thant I accepted Mee_"
Baki ɗaya suka saki baki suna kallonshi cikin yanayi na ɗan tsoro. Papa ne ya sake sipping hannuwansa ya ɗago kan Johseph ɗin tare da furta.
"John what the problems?"
Kansa ya girgiza se kuma ya kamo hannun papa'n yana ɗorawa saitin Heart nashi tare da furta. "Nan ciwo kawai papah nan" yay maganan yana sake tura hannun paah cikin buɗaɗɗiyar rigarsa data buɗe kusan rabinta. Tashi tsaye madame Victoria Osteen tay tare da tafa hannuwanta tana furta "Ohhhh Lord I pray for.. Jesus jesu hoooooh John hooooh john, darling don me zakabar ƙanƙanin yaro kamar John fita shi kaɗai? Amma dai ai kasan bana barin shi koda yin driving ne ko? Bare fita shi dayan sa! Oh Jesus......
Mr jef deefer da madame Victoria Osteen ta ƙira da darling ne ya ɗago kanshi yana dubanta cikin faɗa ² da yarensu ya furta. "Amma dai ai kinsan baki fini son john ba ko?" Ihu tamay a ka ta dibilbele may baki take zuba masifanta. Domin kowa yasan madame Victoria Osteen bala'ice ita kanta, shi yasa kowa na gidan ke tsoronta fiye da kowa. Gata ƙaƙƙarfa mace tsananin riƙo da addinin ta ya sanya addininta na christian bata wani babban muƙami gareta a church, da di da ƙari gasu masu shegun kuɗi ne su gaba da baya wannan shi ne ya sake kankarota da sake babban matsayi.


*YASMINE*
Tun da suka ɗauki hanya ta nutse a cikin kujerar motan tare da lafewa luff tana jin yadda bugun zuciyarta ke ta faman kai kawo har zuwa yanzun kuwa, hakan ya sanya bama tasan sun kawo katafaren dogon ginin gidan masu ba har saida driver ɗin ta ya mata magana tare da ɗan bubbuga gilashin motar kana ta firgigit ta dawo daga duniyar data lula. Fitowa tay ta fara tafiya cikin nutsuwar da tafi kama da jin kai da taƙama musamman yanda jikinta ke girgizar daukan hankalin me kallonta. Da wata maid service ta haɗu a gaban ƙofar parlour'n shiga gidan tana shanyar kayan data wanke na masu gidan. Shijab ɗin jikinta ta wurga mata saman fuska tare da dogon wandon uniforms ɗin Islamiyyar jikin nata. Kasancewar rigar irin duguwar nan ce har kusan gwiwar ta, Duk inda ta wuce sannu da dawowa ma'aikatan gidan ke mata amma bata kula kowa. Da mahaifinta Ambassador Kabeer Usman ta fara cin karo. Hakan ya sanya a guje tayi kansa tana faɗawa jikinsa tare da fashewa da kuka. "Ohh god waye kuma daga dawowan Ambasa baby zai taɓa min ita?" Fitowan Mahaifiyarta lowyer Khadijah Haroon ne ya sanyata haɗiye maganarta makut tana takurewa jikin mahaifin nata. Cikin muryan No nonsense ba tare data kalli ko inda take ba ta furta. "Oya get out of the here" sum sum ta miƙe tana yin sama se wani tattaro rigan jikinta take. Kai tsaye toilet ta shige tana sakar ma kanta shower, Bata fi 20 minute da shiga ba se gata ta fito ɗaure da fari ƙal ɗin towel me ɗan girma a jikinta.
Anutsenta tazauna gaban mirror kan stool, blow drying gashin kanta tayi tai parking nashi a ƙasan ƙeyarta, ta ɗauki wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta feffesa ma gashin, sannan tashiga shafe shafen lotion masu sanya fata tayi laushi. Kafin ta feshe jikinta da tarin turarikanta, bayan ta mulke jikinta da Shu'umar humrarta. Cikin clothes na kayanta ta shige, wasu haɗaɗɗun simple ciffon riga da wando taciro tasaka nude, there’s no way idan ka kalleta baza kaso ɗauke Idonka daga kanta ba don wani masifar ƙyaun da kayan suka mata ko nace ta musu. Don kuwa tabbas YASMINE me ƙyau ce, idan nace ƙyau ina nufin maƙura ƙarshe.
Sake fitowa cikin parlour'n tay loƙacin an jima da idar da sallar maghriba. Ƙamshinta kawai da take fitarwa me yawa ne ya janyo hankalin duk wani dake zaune a parlour'n, ciki kuwa harda Omer da babu jimawa ya zo gidan ɗa ga yayan Hajiya Khadijah Haroon Mahaifiyar yasmine. Zama tay cike da gadara dajin kan daya kasance jininta ƙafarta ta ɗauka ta ɗora ɗaya kan daya, tana jan fruits table ɗin dake gaban daddy'nta. Tsawa Mafaiyarta da take ƙiranta da Maama t.a buga mata kan cewar bata iya gaida mutane bane? Kana maza tayi hanzarin maida fruits table ɗin data janye daga mahaifin nata. Hannun Ambassador Kabeer ya ɗagama Maama tare da girgiza mata kai alaman ta kyale mishi yarinya haka nan tayi abinda ranta yake so.

"Amma daddy'nta sau nawa zamuyi ta maimaita magana ɗaya kan Ambasajo eheeee? Yasmine fa har yanzu ba yarinyar goye bace gidan wani zata je. Don me ina kallon kusa kurai a cikin rayuwanta tana aikatawa amma da nayi yunƙurin gyarawa kace na dena kona bari? Haba Impossible wllh wannan bame yiyuwa bane bama dole na gyara rayuwar yarinyana da kaina wllh, don duk wata uwa data kasance ta gari ga ƴaƴanta dole zataso ganin ɗan ta cikin kyakykyawar nasaba ba wai a bauɗe irin Ambasajo ba!!!" Daga haka fuuuuu ta bar wurin bayan ta cillama yasmine wani mugun kallon zamu haɗe ne.....

*John*

A..........

_Washhh Hannuna ciwoooo!_
_To ya kuke ganin ko kuke tunanin wasan ze fara?, Nasan wasu zasu fara tunanin...... Ehhhhh ya neeeeee to koma dai miye mu haɗe a page na gaba lol 😄😍🥰 don jin yacce zata kaya_

_Anan ina son mu sani cewar komai na rayuwar ɗan Adam na tafiya ne bisa tsari da kuma ƙudurar ubangiji, komai kaga ya faru da bawa dama tun fil azal hakan na cikin rubutun kundin ƙaddararsa yake, Wala ƘADDARA me ƙyau ko akasin hakan, Se dai masu iya magana sukan ce ita ƘADDARA abace mara tabbas, nan take takan iya sanjawa. Ita kuma yarda da ƙaddarar kanta me kyau ko mara kyau na ɗaya daga cikin cikakken Imanin ko wanne bawa!.... A cikin Rayuwar ko wanne bawa kuma bai zama lallai ace saika amfana da wanda yake tare dakai ba, saboda wasu loƙutan ma ban banta akan sha wannan fama na kusa da kai da kake ma kallon Inuwar ka, ko Allon jinginarka, Tashin farko kwatsam se kaga kaine zaka kyautatawa na kusa da kai, Se kuma kaga sama ta ka wani shi ne zai shigo cikin rayuwarkan daga nesa ya zamo shi ne Haskenka ba wannan wanda kake ma kallon shi ne hasken naka na, bayan ka daɗe da linƙaya a cikin DUHU na DUKAN duhu'n. Duk da kasancewar tunaninsu iri ɗaya ne haka zalika Ma'amalar su iri ɗaya ce, duk da hakan bazai hana su saɓama junan suba wata rana, Amma da sun yi Haƙuri da juriya a cikin zaman takewarsun ta yau da kullum su duka se su tashi a ƙarƙashin Inuwar ita wannan Hasken Farin watan_

_Se dai kash.....

_Shin shin shinnm...... Kowa yaje yayi tunani ya ƙaraci tunaninsa don duk yacce kuke zata ko tunani to wasan ba haka yake ba lol 😄💃, don nayi ma kaina alƙawarin tabbas sena gindayar daku a wannan karon ma fiye da MIKIYA, koko TA DABAN, ko kuwa dai DUNIYARMU. koma nace fiye da komai ɗin ma hhhhhhhh, ciki kuwa harda RAMIN KURA......_

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215

𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐍𝐓𝐈𝐍𝐆 𝐀𝐍𝐃 𝐒𝐇𝐀𝐑𝐈𝐍𝐆






*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 2
Paid book

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

_Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_

Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215

*YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION {YOTA}*

_NA'EEMA SULAIMAN SARAUTA_ *NIMCY LUV* har abada ƙaunarki ɗaya ce a gareni Marh, domin duk inda akaje aka zo ke ce AMMEY LAYLERH 💐.

_Special Thanks to Masoya masu bibiyana ina alfahari daku a ko ina a kowacce duniya kuke Love you all 💞💖💘💗_


ꨄ_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦_ °♡◦°♡

*John*

Yana shiga bedroom nashi sarƙar cross ɗin dake wuyansa ya zare, yana ratayeta jikin wani ɗan hanger ƙarami mai kyau dake cike da sarƙoƙi kala-kala a ajiye saman mirrorn. Zama yay a stool ɗin gaban mirror'n yanata faman yamutse fuska. kana a natse ya mike kansa tsaye yana nufar bathroom. Yana shiga babu jimawa aka fara knocking kofar bedroom nashi, amma sai ya sha re yana ci gaba da abinda yake da uzirinsa. Ya ɗauki tsahon lokaci a bayin kafin farar ƙafarsa dake nan fara tass ta bayyana, yana ƙarasa fitowa jikinsa sanye da bathrobe sky blue,
Hannunsa ɗaya kuma na rike da karamin towel yana tsane gashin kansa da kallo ɗaya zakai ma gashin ka fahimci yana masifar lasar manyan kudade bana wasa ba, kodan kyau da kyallin da gashin keyi domin yafi karfin a kirashi da suma. Duk abinda yake yi tana nan maƙale a ruhinsa da tunaninsa, Sam beyi tunanin ganin Madame Victoria a bedroom ɗin ba. Ɓata face nashi yayi tamkar wani yaron goye yana nufar inda take zaune daga bakin bed nashi. Zama yayi gefe da ita tare da jingina kansa da jikinta. Bayansa ta shafa a hankali inda ya waro manyan fararen idanuwansa cike da tsoro, jin ta tabo masa inda waccen babyn robar ta jefeshi. "Ouch Mah!!!" ya sake furtawa da ɗan ƙarfi jin ta sake taɓa masa wurin. Kansa ta dungure masa tana tashi ta ɗebo masa ƙananan kaya black da black ɗin speck. Closet nashi ya shige don baya taba shiryawa gaban Mommah ɗin nashi, duk lokacin data masa kutse irin haka duk kuwa da yanda take sashi gaba. Bai wani jima sosai ba se gashi ya fito cikin black ɗin shigar, inda yamay wani kalan kyau bana wasa ba wanda ya sake fito da ainihin hasken farar fatarsa me kyau da mirjewa. A gaba ta sashi suka fita zuwa entrance dinner na gidan baki ɗaya. Wanda kowa ke hallare a wurin, Mr jef deefer ne ya fara taryan yaron nashi da kayataccen murmushinsa me kyau, kafin X Eeshika itama ta sakar masa nata murmushin wacce take Ƴa ga kanwar Mommah nashi, daga nan se jelly wacce take kanwa a gareshi. Yana zama kujerar kusa da paah ɗin sa X Eeshika ta tsalloka tsilik zuwa kujerar dake kusa dashi, wacce ke pacing nashi. Kwanciya yayi jikin papanshi Mommah ce ta miƙe tana me furta. "Stand up and eat your food" Ta faɗa tana mantawa da gadon bayansa tana ɗagoshi, wata uwar ƙara ya sanya yana riƙo gadon bayan, Se wani haɗa uban zufa yake yana matse kyakykyawar fuskar nan tamkar wani yaron goye, saurin sanya hannunta tayi tana dafe bayan nasa tana furta. "Ohhhh Jesus Sorry boy sorry!" Madame Victoria ta faɗi tana tada shi zaune daidai da tallafin papah'nsa, Sannu mutanen parlourn suka shiga masa x Eashika harda guntuwar kwallarta. Jelly ce tayi saurin ƙara gudun fanka tsabar ɗaurewa karya ƙugu, "Ma'am What wrong with this john?" X Eashika ta tambaya Mommah kai tsaye. Nan madame Victoria ta sanar dasu abinda ya faru, haba nan fa suka shiga babin tsinema Hausa girl dukansu, cikin su kuwa harda masu cin alwashin duk ranar da suka haɗu da yarinyar se sun fasa mata baya itama kamar yanda ta fasama John ɗin su. Jin yanda suke zagin masa pretty ne ya sanya John miƙewa yana me furta.

"Momma I can't eat anything now, i want to sleep, because am feeling sleeping". Ya bata amsa can ƙasan maƙoshinsa kuma ya faɗi hakan ne bawai don hakan yake ba, A ahh kawai dai ze basu wuri ne bazai iya zama ana zagar masa love tashi ba. Duk da kallo suka bishi suna son masa magana suna kuma tsoron masan ya sauƙe musu ruwan Bala'insa da ya iya buhu², don shi tamkar fire and Ice haka yake, yanzu za'a kalleshi cikin nishaɗi yanzun kuma za'a kalleshi cikin mugun tsare gida da ɓacin ran da idan ka ganshi a lokacin zama kayi tunanin cewar be taɓa sanin wata aba wai dariya bane. Don haka kowa yayi gim da bakinsa yana tsoron masa magana.

_Great place a wonderful mension_

Mension ne babba da ko a cikin Cristian suke ji dashi, domin kuwa shi ne lamba ɗaya wanda sunansa ya zage baki ɗaya katafanin garin Lagos ɗin harma da kewayenta, sunan POWER kun san me ma'anar sunan yake nufi, kalmar POWER kalmace dake tattarene da karfin iko, Isa, Izza, taƙama. ★ *Mr jef deefer* shi ne ƙatoton arne lamba ɗaya da suke ji dashi. Baya da Imani ko kaɗan, haka Kuma baya da tausayi ko rangwame bare yafiya. Idan kanason ganin murmushi ko dariyarsa to ka tabbatar yana tare da zuciyarsa ne gaba ɗaya wato John. Wani irin mahaukacin So uwa da ubansa suke masa, Wanda samm samm hankali baze Iya ɗauka ba. Mahaifinsa Mr jef deefer Wani irin shimfideden iko yake gudanarwa, sedai samm baya taɓa yarda da maci Amana ko kaɗan. Idan kuwa har ya kama mutum da cin amanarsa yana gindile masa yan yatsu biyu ne, ma'ana babbar yatsar mutum da kuma yar ƙurinsa wannan shi ne hukuncin wanda ya kama da laifin cin amanarsa. A tsarin mension ɗin nasu kuwa. Wani irin katafaren mension ne mai matuƙar kyau da tsaruwa, Wanda ya gama gajiya da haɗuwa iyaka haɗuwa kam gidan nan ya haɗu, kai da ganin ginin gidan kasan masu rayuwa a cikin sa sedai wani babban ƙusa daga gomnati ko dai wani babban ɗan kasuwa ne, gate ɗin gidan kawai abin a tsaya a kalla ne, bangaren uku ne a cikin gidan ga wani dan ma dai dai cin pool a tsakar harabar gidan, daga gefen hagu katafaren parking space ne mai dauke da ƙaton rumfa gefe guda kuma ga wasu fittatun manyan motonci nan babu kalan da babu, tin daga kan su *Mercedes-Benz* *McLaren solus GT.* *Roll-Royce boat Tail* *land cruiser * Kai ganan dai su motocin babu kalan da babu, su kansu kawai abun kallo ne. daga gefen dama kuma shuke shuken plowers ne in different colors awajen masu matuƙar kyau da ban sha'awa. daga ɗan gefen parking space ɗin kuwa, wani Katafaren wajen hutawa ne dake zagaye da glass. wajen ɗauke yake da wasu ƙayatattun sofa set ɗaya launin sky blue, a tsaƙiyar kujerun kuma wani haɗaɗɗen sofa table ne mai ɗan girma a wajen, daga gefe guda kuma ga wani irin deep fridge ƙawace da wajen, Wanda suke ɗauke da lemukan sha da barasa, haɗuwa kam gidan ya gama tsaruwa tabbas.....

John kuwa kai tsaye balcony na gidan yayi shigewansa phone náshi tare dashi, Akan wata doguwar Royal Caribbean chier yakai zaune, yana taune gefen lips náshi da tsarin halittarsu yake pink. gaba ɗaya tunaninta ne yake neman fasa kansa,kodan be taɓa jin hakan dangane da kowacce mace bene oho. Amma dai abinda kawai ya sani seya mallaketa kota yayane. Gaba ɗaya lissafinsa cikin lokaci ƙanƙani ya nemi daya kwance, dukkan wani motsi da zayyi ƙamshin turarenta kawai yakeji daya shaƙa yana sake hargitsa tunaninsa, ya sani tabbas shi masoyin ƙamshi ne but a rayuwarsa bai taɓa jin asalin ƙamshin daya taɓa masa ba bayan nashi ƙamshin se yau daya shaƙa nata. Tsaye ya miƙe yana riƙe da ƙugunsa ya fara aikin safa da marwa, yana ma rasa ta ina tunanin wannan Baby'n robar ke kutso masa kai?. Da misalin ƙarfe 9:44 ya lallaɓa ya fito zuwa compound na gidan.
Kai tsaye bayan ya baro ɓangaren sa parking space ɗin dake gidan ya nufa, dake daidai lokacin babu kowa shi ya bashi damar shigewa cikin motar nashi, yana tada ta ya fice a gidan bayan ya ba get man umarnin buɗe gidan. ko lamps ɗin motar bai kunna ba gudun kada a ganshi tamkar wani ɓarowa haka ya saɗaɗa yana ficewa a gidan baki ɗaya. Yana ɗan nesa da gidan nasu ya kunna lamps na motar ya harbata saman titin. Wanda daidai lokacin garin ke haɗe wani irin hadarin da yama sama ado ta hanyar ƙawanyar daya masa da gajimare.

*Ambassadors kabeer house*

Gaba ɗaya mutanen gidan zaune suke cikin wani katafaren parlour na alfarma, Me ɗauke da wasu manya manyan sofa set guda masu numfashi wanda suka kasance masu launin blue da milk, Wanda kalan sukayi wani irin ƙawata parlour'n sosai suka sake fito da asalin kyaun sa, inda yaji komai da ake buƙata na rayuwa, wanda idan nace zan tsaya zayyana muku kyan parlour'n kaɗai ɓata ma juna time,A natse matashiyar yarinyar wacce take fara tas yanayin jikinta kuma kai tsaye na bayyana tsantsar hutu da jin daɗin da suke ciki ta ɗan saci kallar mamy'n nata tare da furta. "Aunty yasmine tana lafiya kuwa Mummy?, Har yanzun bata fito ɗinner ba. Ita da mahaifiyar nata suna sanye cikin shiga iri ɗaya na lace doguwan riga inda ita yarinyar nata a kasance fitet gown ne, ita kuma uwar normal doguwan rigawa esharp. Cakkk kuwa Abbin nasu ya dakata daga sipping coffee ɗin da yake yi, tare da dubar matashiyar yarinyar yana me furta. "Maza Husna je dubomin ko lafiyarta" yay maganan yana dire bowl ɗin dake hannunsa ya zubawa upsairs nata idanu tare da buga wani uban tagumi. Takun takarmin ta da kuma ƙamshin turarenta da baya taɓa ɓuya kawai mahaifin nata ya shaƙa ya sauƙe wata nannauyar ajiyar zuciya. Har zuwa lokacin data ƙara so cikin tsaƙiyar parlour'n ba a sake ba. "ALLAH sarki Ambasa Baby'n daddy'nta ƙaraso mana",cewar mahaifin nata, wanda ya sata ƙarowa sum sum domin bata mata kashedin mahaifiyar nata ba

2 / 31