Advertisements
Chapter 8 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   8 / 31

21K to 24K   out of 91.1K words

titi zuwa titi, daga unguwa zuwa wata unguwar amma babu Yasmine babu alamarta, lokacin har takwas na dare ya gota, don haka driver ɗin ya ɗan leƙa ta madubi yana cewa... “Boss… mun riga mun zagaya kusan ko’ina a wannan yankin fa…” ɗan risinar da idonsa kawai John yayi, yana jin wani irin gajiya a cikin zuciyarsa, yana jin kamar ya sare amma kuma cikin yaƙini ya sake ce dashi “Keep driving…” haka har suka isa wani titi mai ɗan shiru da hasken fitila ɗaya kawai ke kyalli. Se wasu zirarin mutane kaɗan kawai dake wucewa. Ahankali motar ta ratsa titin,
John ya sake jingina da kujeran motar yayi shiru idanunsa har sun fara nuna gajiya… har yana jin kamar ya yardan ma zuciyarsa cewa watakila ba zai same ta ba a daren nan. Amma wani ɓangaren na daga cikin zuciyar ma sake ƙarfafashi akan kada ya sare, domin dama shi can ba mai sarewan bane. Shi kuwa Mecheal da hannunsa suna soma gajiya da driving ɗin ne ya ɗan sake kallarsa a ɗan tsorace yace...

“Sir… should we head back home?”

Yayi maganar yana ɗan rage gudun motar, amma shiru John bai bashi amsa ba sai ma sake maida kansa woje da yayi amma ba sosai yake duba yanayin wajen ba, don shi kansa ya fara gajiyan, se kawai taurin zuciya irin nashi, motar nasu har ta ɗan gitta wani gefen titi…
inda wata yarinya ke tsaye da dogon hijjaba har ƙasa a jijinta,inda tun da ya fito se yanzun yaga me kalan wannan abin, kuma sak irin na Trouble nashi Ash.. don haka ya dakatar da Mecheal yana buɗe motar ya fita hanzarce amma yana fitan abin mamaki ya nema yarinyar ya rasa ta ɓace masa, daga can inda yasmine ta ke kuwa ta ɗago kanta a hankali tana waiwayar bayanta,
Idanunta cike da wani irin yanayin da ita kanta taji kamar ita ma tana jin cewa wani abu ya wuce kusa da ita me muhimmancin da bata san ko miye shi ba, don haka yar tsuka kawai taja tana faɗawa motar ƙawarta dake jiranta...
Shi kuwa John wani kalan lumshe idonsa yayi yana jin kamar tabbas ita ne ya gani, gangar jikinsa na bashi cikakken tabbaci akan hakan,amma hanya ta raba su, duk da cewa sun yi kusa da juna fiye da yadda suka taɓa tunani ba tare da sanin junan su ba. Haka motar John ta ci gaba da tafiya cikin nutsuwa, tamkar wanda aka zabura ya furta... “Stop the car…” wanda ya saka driver ɗin ya taka birki yana ambatar “Boss What happen?” Riƙe kansa kawai John yayi yana jin kamar ze rabe masa guda biyu, da ƙyar ya iya ce dashi. “I don’t know… just—wait.” Shiru ne kawai ya mamaye motar, kafin John ya buɗe ƙofar motar ya fito. Kai tsaye sassanyar iskan daren ta bugi fuskarsa, tsai kawai yayi a gefen titin yana kallon hanyoyi daban daban.
Zuciyarsa naci gaba dan bugawa kamar tana ƙoƙarin gaya masa wani abu
amma bai gane ba, ya juya bayansa kenan motar data fito daga wancan titin ta wuce a guje tamkar walƙiya, motar kawai ya dawo ya zaune tare da furta
“Let’s go…” kawai motar taci gaba da tafiya. Sake kwanciya John yayi a jikin kujeran motar ya lumshe idonsa,
yana jin wani irin raɗaɗi a cikin zuciyarsa ba tare da ya san dalili ba. Haka suka koma gida bayan sun jima a wurin da hasalin haɗuwarsu na farko ya fara, hakan ma don ƙiran da Papa'nsa ya dinga masa ne tare da Madame Victoria dole suka dawo gidan ba don yaso ba, daren ranar nan haka John ya gansa be runtsa ba, saboda zuciyarsa ita kawai take muradi, idanunsa cike suke da ɗaukin sake ganinta,haka zuciyar John taƙi hutawa a daren ranar, a cikin ransa yana ayyana ko da bai san sunanta ba yana son sake ganin wannan kyakkyawar fuskar, Saboda fuskar ta ƙi barin zuciyarsa....

★...

A washe garin ranar se wajajen sha ɗaya ya fito daga ɓangarensa, yana fitowa Mommah nashi kallo ɗaya ta amsa tasan bai yi bacci ba daren jiya, don haka ta ƙira ye shi kai tsaye ta zaunar dashi a gefenta, tana shafa fuskarsa da se faman kawar da ita yake. “My love what happens???, me ya sa baka yi bacci ba jiya gaya nan ina kallon hakan a idanunka!” hannunta ya ɗauke daga fuskan yana matsawa jikin Grandfather nashi Patriarch. A tare yaci abinci da kakan nasa wanda kusan shi yake bashi da kan sa ma, X-Eashika ta matsa kusa dashi tana ɗora kanta saman kafaɗar John ɗin, Madame Victoria ta daka tsawa tana cewa ta ƙyale shi, ko bata ga baya da lafiya bane, Deepika ce ta faɗa fuska tana isa ga John tana ƙoƙarin kama hannunsa ya mata tsawa yana miƙewa a fusace fuuuu ya fita daga parlourn, inda gaba ɗaya suka bishi da kallo cike da zullumin ko me ke damunsa tsakanin jiya da yau ɗin?, amma babu wanda ya tanka sema kowa miƙewa da suka fara ɗaya bayan ɗaya suna barin wurin, ya rage daga Papa se Patriarch..

John kuwa yana fita Mecheal ya taso ya buɗe masa mota, zuciyarsa cike da tsantsar munafincin ko me ke damun Boss ɗin haka?, yau ma zaga garin suka yi, inda sake komawarsu wurin kai tsaye ya bama Mecheal ɗin hasken kodai Hausa gal ɗin nan John ɗin ke nema yasa su cinye ta ɗanya?, kai tsaye ya labe a bayan mota ya ƙira Madame Victoria yake sanar da ita duk abinda ya faru, tin daga fitarsu na jiya har zuwa yanzun har dama ƙarin gishiri a zancen nasa, kai tsaye hankalin Madame Victoria ya tashi amma kuma sanin halin Joseph ɗin ya sa bata yi yunƙurin komai a lokacin ba, har suka sake dawowa gida. Kai tsaye ya haye sama cike da zafin zuciyar rashin nasarar samunta da yau ma basu yi ba, tun da ya shige kuma babu wanda yayi gigin zuwa inda yake har ita kanta Victoria ɗin, se can ta shiga kai miahi dinner da yaki saƙƙowa yayi, don bata taɓa barin su Deepika ko X-Eashika wani shigar masa ɗaki,gudun ma kar wata ta rinjayi ra'ayinsa a cikinsu. Ahankali ta zauna a gefen gadonsa da yake kwance da kayan shan iska ta ɗora hannunta saman goshinsa, tare da masa adda'a irin tasu kana cikin tausasa murya tace dashi, in dai akan maganar wannan Hausa gal ɗin ce ya bar maganar a hannunta, duk inda take a faɗin lagos se ta saka an nemo mata ita, ita da kanta ta saka an hukun tata ba sai ya wahal da kansa ba, wanda ita tayi hakan ne da biyu don bata son taga kowacce mace ta rabe shi bayan ita, kamar yadda bata son taga shi ma ya raɓa ko wacce macece. Wani duba ya mata jin wai zata sa a hukuntata, hukuncin me to?, yayi maganar da zuciyar yana kawar da zancen hakan, duk da yayi mamakin yadda bata manta zancen ba, kuma ma har tasan itan yake nema kai tsaye, da kyar ya yarda yaci abinda ƙarfe biyar na cika ya sake fita a gidan, zuciyarsa babu daɗi daga shi se wani kakkauran wando na jeans iya gwiwwarsa, se guntuwar shirt mara hannu, se ƙatotuwar sarƙar Cross ɗin sa daya sanja me hoton kwandalar dake jikinsa da me hoton tauraro, ko gashin kan yau sama sama ya gyara sa fuskar nan a turɓune murtik kamar hadarin daya ƙunshi ruwa yaki ya fashe, directly wani lafiyayyen mall ya nufa saboda duk kayan kwalam nasa ya karar dasu,kuma Mommah me bi bata kula ba, don haka zuciyarsa kawai ta bashi shawaran ƙara ya saya kawai, don yadda kwana biyun nan ba wani cin abincin kirki yaje ba se dangin su biscuit chocolote ɗin yasa shi bin umarnin zuciyar, suka yada zango a shagon suka fara siyayyar Mecheal na tura masa basket na kayansa da yaje jida kamar wanda ke shirin buɗe ɗan ƙaramin shago, daga ƙarshe ma Mecheal ya bari yaci gaba da zaɓa masa manyan biscuit ɗin masu lafiya da tsada, samun kansa yayi da fara zaga mall ɗin kamar me neman wani abu, har idonsa ya sauƙa akan best chocolate nashi ta Ferrero Rocher, wacce tun da suka shigo ita yake ta nema, ya miƙa hannunsa kenan da niyar ɗauka,wani hannun ma daban ya kawo da niyar ɗauka,hakan yasa kusan lokaci guda hannunsa ya ɗoru akan chocolate ɗin har yatsun hannun nasu na ɗan haɗuwa, ɗagowa yayi da nufin ganin waye kai tsaye idanunsu suka sarƙe cikin na juna, Cak numfashin John ya tsaya, yana tunanin anya kuwa ita ce?, ba gizo idonsa ke masa ba, anya kuwa ita ce yarinyar da akan ya dinga yawo cikin dare yana zaga anguwannin da suka yi kusa da inda suka haɗu?... Ita kuwa yasmine da kai tsaye bata gane shi ba ne ta ɗan kallesa kawai tare da cewa...

“Ohhh… I’m sorry,” ta faɗa a hankali tana janye hannunta daga kan chocolote in, shi kuwa John gaza ko wanne irin motsi yayi jin daddaɗar muryanta ta ratsa har tsakar kansa, ko yanzun ma tana sanye da niƙab nata,wanda ta dage shi ne don ganin wanda ya rigata ɗaukar cutie chocolate nata, John da yake kallonta kamar wanda ya samu abin da ya rasa wani faffaɗan murmushin da kai tsaye baka isa gani daga fuskarsa cikin sauƙi ba na kufce masa a bazatan ganintan da yayi, godiya yama Mommah a cikin ransa don yasan ƙarfin adda'an data mishi ce yasa har ya haɗu da ita cikin sauƙi haka...

“My Trouble…”

ya faɗa a hankali yana ci gaba da kallon ta wanda hakan ya saka yasmine ɗan ɗage gira ɗaya “Excuse me zan iya ɗauka?” tayi maganar dana sake kai hannunta kan chocolote ɗin da yayi hanzarin ɗaukewa, idanunsa naci gaba da kallonta kai tsaye.
“Babyn roba…” ya sake faɗa da murya mai laushi kamar yana gwada yadda kalmar ke fita ne a bakinsa. Cak ta dagata domin wannan karon kai tsaye tasan da ita yake kenan, don haka da alamar mamaki tana haɗe ranta ta ce...

“Do I know you?” ta tambaya, wanda ya saka John saurin zagawa yana girgiza mata kai kaɗan, murmushinsa har lokacin bai gushe ba yace “Not yet…” ya faɗa tare da sake matsota ya sake furta.

“Amma na jima ina nemanki, har daren jiya ma” Kai tsaye kalmarsa ta tsaya mata a zuciyarta ta wai ya jima yana nemanta, kafin ta kalleshi kamar tana ƙoƙarin tuna wani abu tace...
“Nie kuma?, nemana fa really?” ta yi maganar mamakinsa har lokacin bai bar ran ta ba. Taku biyu ya sake yi gabanta har yana ƙoƙarin haɗe tazarar dake tsakaninsu tayi hanzarin yin baya, ne damu ba sema kai tsaye da yace mata.

“Last night… I was out there,” ya nuna kansa kaɗan. “Trying to find you… I didn’t even know your name.” wani kalan shiru ne ya ratsa wurin kwakwalwarta na son tuno mata ko shi ɗin waye, zuciyarta ce ta ɗan buga kai tsaye ta gane shi kam yanzun, musamman da se a lokacin da masa kallon tsaf, ga wannan shegiyar sarƙar Cross ɗin nasa nan se rito take a jikinsa.
“Strange…” ta furta da ɗan ƙarfi tana ja baya fuskarta sanjawa zuwa tsuketa da tayi, tana haɗa duk abubuwan da suka faru a ranar a cikin ranta. “Wait…” ta faɗa a hankali tana sake matsawa da kyau tana kallonsa, kafin a wani kalan fusace tace... “Don’t tell me…” se kuma ta ɗan yi dariya kaɗan amma dariyar ba ta da sauƙi a gare shi, “You’re that guy from last day…?” ɗan murmushi kawai yayi yana harɗe hannuwansa a ƙirji ya ce da ita. “Maybe…” ya faɗa a hankali wanda ya saka yasmine ɗan girgiza kanta, kafin kuma ta warto Ferrero Rocher ɗin daga shelf ɗin da take da ƙarfi kaɗan. “Unbelievable…” ta furta tare da sake kallonsa amma wannan karon idanunta cike suke da ɗan rashin kunya da ƙarfin hali irin na farko.
“Toh yanzun ma ka biyo ni har nan ɗin kenan don ka maimaita irin na ranar ko?, tayi maganar da hausa wanda gaba ɗaya be gane me take nufi ba, don ba directly ya iya hausa a cukurkude irin haka ba, kaɗan kaɗan ya iya kawai,
amma ta sake ɗaga masa hannu ta dakatar da shi da cewa. “No, no… don’t even start.” kafin ta sake matsawa kusa da dashi ta nuna shi da yatsa tace. “Listen, mister… ban san ko kai waye ba, kuma honestly ban damu ba.” tayi maganar da ihu, wanda ya jayo hankalin mutanen har wasu na ɗan juya suna kallon su kaɗan, amma ita ko kaɗan bata damu ba seka ci gaba da nuna shi da tayi tana ci gaba da faɗin.
“Ka dena bin bayana,” ta faɗa kai tsaye.
“Because if I catch you doing that again”
ta ɗan karkata kai tana kallonsa da ƙanƙanin murmushi mai haɗe da gargadi “ ka sani zan iya sake marin ka a karo na biyu And trust me… I don’t miss.” tun da ta fara maganar John ya tsaya yana kallonta… mamaki da ɗan dariya na haɗuwa a fuskarsa duk lokaci guda. Ta juya zata tafi amma ta sake juyowa da sauri tace “Seriously. Stay away.” Ta fara tafiya cikin ƙarfin hali kamar yadda ta saba daga hakan ta ɓace cikin mutane....

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215




*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 8
Paid book

Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215


*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

_Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_

♡♡♡♡

ꨄ John tun da ta ɓace a cikin mutanen ya tsaya a wurin kamar wanda aka dasa, idanunsa na bin bayanta har ta ɓace cikin cunkoson mutanen mall ɗin. Wani irin shiru ne ya mamaye shi na wasu daƙiƙu.ya saki wani ɗan ƙaramin dariya mai sanyi. “Still the same…” ya furta a hankali yana girgiza kai.
Mecheal da ke tsaye daga nesa yana kallon duk abinda ke faruwa ya matso kusa da shi yana ɗan ɗaga gira.
“Boss…?” ya kira shi da yanayin tambaya. Amma John ko kallonsa bai yi ba… har yanzu idanunsa suna kallon inda ta bi kamar yana tsammanin zata sake bayyanane. “Did you see her?” ya tambaya a hankali. Mecheal ya ɗan rikice tare da furta. “Which one, sir?”
A hankali John ya juya ya kalleshi… idanunsa cike da wani irin haske da Mecheal bai taɓa gani a cikinsu ba.
“My trouble…” ya faɗa kamar wanda yake magana da kansa. Kafin ya ja wani gauran numfashi ya ce… “Find her.”
Cak Mecheal ya ƙame tare da buɗe baki kafin yayi kunɗunbalar cewa.

“Sir…? Find who exactly?”

John ya ɗan yi murmushi, amma murmushin nan na nufin abu ɗaya ne ba zai bar wannan ba. “The girl in hijab!… the one that almost killed me yesterday…” ya faɗa da ɗan sarcasm.
Mecheal ya ɗan yi dariya kaɗan.

“Sir, Lagos ba ƙaramin gari bane fa…”

“Then search it.”

John ya katse shi kai tsaye ta hanyar fadin hakan. Kafin wani ɗan shiru ya gitta tsakaninsu, sai kuma ya juya ya fara tafiya zuwa exit ɗin mall ɗin yana cewa…

“I want her name… where she lives… everything.”

A ɓangaren Yasmine kuwa… Tana fita daga mall ɗin zuciyarta naci gaba da bugawa da sauri fiye da yadda ta saba.
“What happen…?” ta faɗa a hankali tana dafa ƙirjinta. Ƙawarta Aysher da ke jiranta a mota ta kalleta da mamaki kafin tace.

“Yasmine lafiya? Kina ta faman numfashi kamar wacce kika yi gudu.” Motar kawai ta shige tana gyara niƙab ɗinta. “Wani ne kawai…” ta faɗa a takaice. Ƙawarta Aysher ta ɗan yi murmushi mai ɗan raini.
“Wani ne… ko wani NE?” ta jaddada kalmar a bayyane. Ɗan hararanta Yasmine ɗin tayi tare da furta.
“Please, ki ja mota kawai muje.”
Don har zuwa yanzun hoton fuskar John kawai take gani ranar da yayi kissing lips nata a tausashe gaba daya hakan ya ƙi barin zuciyarta. Barin ma wannan munafikin murmushi nasa, Idanunsa, da yadda a yau ɗin kuma ya wani kira ta... “My Trouble…” Se kawai ta tsinta kanta da wani lumshe ido a hankali, kafin ta furta. “Ya Allah…” a bayyane daidai lokacin da suke parkin car nasu a babban get ɗin gidan su...

Aysher ɗin bata shiga ba kasancewar magrib ta kawo kai. Don haka ta buɗe motar ta fita tare da ledanta a hannun.
Zuciyarta cike da wani irin tunani da bata saba ji ba, ta jefa jakarta a kan kujerar babban parlourn gidan su, ta zauna tana kallon bango kamar wacce aka ɗaure da tunani.

“Me wannan mutumin yake nufi da ni ne wai?”

Ta faɗa a hankali a kuma bayyane, tana tuna yadda ya tsaya yana kallonta… yadda ya kira ta da suna “Babyn roba” duk da cewa ita kanta ta gargade shi. Wani mugun tsakin da yaja hankalin ƙanwarta Husna ƙanwarta da tun farkon shigowar Yayar tata take kallonta kawai. Ba tare da sanin kalmar zata kwace mata ba ta sake furta...

“Wannan mutumin matsala ne… amma me yasa nake tunaninsa haka?”

Husna gaza yin shiru tayi har seda ta. “Ambasajon Daddy lafiyanki kuwa tun da kika shigo se surutai kike?” Yi tayi kamar ta fasa ɗan ƙaramin ihu amma tana mazewa tama mike tana barma Husna ɗin dogon hijjaba nata da ledan sayayyar, ta haura sama daga ita se riga da wando Three quiter din dake jikinta pink. Da kallon tausayawa kawai Husna ɗin tabi Yayar nata dashi, don sau da dama irin haka tausayin Yayar nata kamata yake. Tana daf da hawa saman kuma ta dakata cak dan jin muryan mahaifiyarta da tayi

8 / 31