Advertisements
Chapter 5 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   5 / 31

12K to 15K   out of 91.1K words

ta katse nutsuwar daƙin.... “Sir! Mun rasa daidaiton altitude na Flight JX-27...” wani daga cikin jami’an ya faɗa cikin tashin hankali. Shugaban kula da zirga-zirgar jiragen sama ya mike tsaye da gaggawa. “Wane jirgi ne?” kai tsaye tambayar daya cilla musu kenan.
“Na Captain John, sir… daga Murtala Muhammed International Airport zuwa Florida!” Wani irin shiru mai nauyi ne ya ratsa ɗakin na ƴan dakiku, Kafin shugaban ya ɗaga wayar gaggawa yana magana da cikin muryan kamar bada umarni yake ta nanata kalaman....
“Emergency protocol activated! Notify all units! We have a critical situation in the air!” take kuma a lokaci guda aka aika da saƙon gaggawa zuwa sauran hukumomi ciki har da Federal Aviation Administration. “Flight JX-271 is experiencing severe instability… possible system failure!” daga inda suke Allon radarsu yake nuna jirginsu John dake sake karkata daga hanyarsa, yana kuma gudu sama da kima. “Try to reach Captain John NOW!” wannan shugaban ya sake faɗi da dan karfi.
“Sir, mun kasa samun cikakken response… siginar na yankewa ne...!”
Hannun wasu ma’aikata na rawa yayin da suke ƙoƙarin daidaita sadarwa.
“Mayday signal detected!” wani ya yi ihu, ɗakin ya cika da tashin hankali.
Shugaban ya runtse ido na ɗan lokaci da ƙarfin bala'i sannan ya buɗe da ƙarfin.
“Prepare emergency landing clearance. Ko da menene… dole ne mu sauƙar da wannan jirgi lafiya!.....

A can cikin sararin samaniya kuwa tuni wasu daga cikin rayukan mutane sun gama saduda da saddakarwar se dai wasu basu ba, Kowa a cikinsu zaman jiran tsammanin warabbuka suke, kowa na jiran abin da zai biyo baya ko ganin abinda hali zayyi. Idan muka shiga cikin cockpit ɗin kuwa, inda komai ke tafiya da tashin hankali a cikin cockpit na jirgin, hasken gaggawa (emergency lights) ne kawai ke kyalli. A wannan karon kam gaba ɗaya gumi ya gama jiƙe goshin Captain John yayin da hannunsa ke rike da controls da ƙarfi. “Control… this is Flight JX-271… we are losing control!” muryarsa na rawa, amma yana ƙoƙarin daurewa, sai karar ƙararrawa ta sake tashi Allon gabansa na sake nuna masa matsala mai tsanani, engine ɗaya yana rasa ƙarfi.
“Damn it… not now!” ya furta a hankali, kafin ya danna wani maɓalli yana ƙoƙarin daidaita jirgin.“Come on… come on…”Jirgin ya fara karkata gefe guda da ƙarfi.Co-pilot ɗinsa ya kalle shi cikin firgici.“Captain, we’re dropping altitude too fast!” John ya matse steering (yoke) da ƙarfi, jijiyoyin hannunsa suka fito.
“Stabilize it! Reduce thrust on engine two… NOW!” “Engine two reduced—but sir, engine one is failing completely!”
Wata ƙarar girgiza ta sake ratsa jirgin.
A wajen jirgin kuwa gajimare masu duhu ne suke sake kewaye jirgin nasu sakamakon ƙasar Florida ɗin da take daf da shirin fara zubar da ruwa ba tare da sun san hakan zata iya kasancewa, duk da cewan seda suka aika da komai na tashin nasu zuwa ga Florida ɗin tace su taho babu Matsala, su a nasu ganin har jirgin ya iso ruwan be fara sauka ba, iska mai ƙarfin data sake dukan jirgin kamar zata fasa shi gida biyu ya sake saka zuciyoyin kowa sake rugujewa,
John ya haɗiye wani abu daga cikin maƙoshinsa yana cewa. “Okay… listen to me,” ya ce da ƙarfi, yana ƙoƙarin kwantar da hankali. “We’re not going down. Not today.” Ya kunna sadarwa da control tower na Miami International Airport. “Mayday, Mayday, Mayday! This is Captain John of Flight JX-271… we have an engine failure and unstable controls. Requesting immediate landing clearance!” A can ƙasa aka amsa da sauri. “Flight JX-271, this is Miami Tower. Runway is clear. You are authorized for emergency landing!”
John ya numfasa da ƙarfi.
“Alright… this is it.”
Jirgin na rawar jiki yayin da yake saukowa a hankali.
“Flaps… now!”
“Flaps deployed!”
“Landing gear!”
“Landing gear… not responding!”
Idanunsa suka buɗe sosai. “WHAT?! Try again!” “Still not working, sir!”
Shiru na ɗan lokaci ya ratsa cockpit ɗin… sai ƙarar iska kawai, John ya lumshe ido na daƙiƙa ɗaya, sannan ya buɗe su da sabon ƙarfi. “Then we land it… manually.” Co-pilot ya kalle shi cikin tsoro, yace “Sir… that’s risky…”
John ya ɗan juya kansa kaɗan, idanunsa cike da natsuwa mai zurfi irin wacce ake samu ne kawai a lokacin da mutum ya yanke hukunci na ƙarshe. “Risky… amma dole,” ya faɗa a hankali.
“Ka yarda da ni.” Jirgin ya sake girgiza da ƙarfi, sai ƙarar iska mai razanarwa ta cika cockpit. “All instruments unstable, sir!” “Forget instruments… feel the aircraft!” John ya faɗa da ƙarfi, yana
ɗan sassauta hannunsa a kan starring yana jin yadda jirgin ke amsawa.
“Altitude?” “2,500 feet… dropping!”
“Okay… muna da kaɗan lokaci.”
Ya kunna mic cikin gaggawa. “Cabin crew brace passengers immediately!”
A can cikin jirgin, ana jin muryoyin firgici… ihu… addu’o’i. Amma a cockpit shiru ne mai nauyi da ruguza zuciya,
John ya kalli gaba… runway ɗin Miami International Airport yana bayyana cikin ruwan sama da gajimaren dake kamar soma basu hanya, “Speed is too high!” co-pilot ya faɗa. “Na sani,” John ya amsa, yana rage thrust a hankali.
“Kar mu yi overcorrection… ko mu stall.” Jirgin ya ɗan yi ƙasa da ƙarfi....
“Careful!” “I’ve got it!” Ya daidaita shi da sauri, yana gyara nose ɗin jirgin, “Listen,” John ya ce cikin ƙarfi, “Za mu yi belly landing. No landing gear… no mistakes.” Co-pilot ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya gyada kai.“…I’m with you, sir.” John ya ɗan numfasa.
“Good.” “500 feet!” Runway ya kusa sosai yanzu. Iskar waje na ƙara ƙarfi, ruwan sama na bugun gilashin cockpit.
“Hold it steady…” “300 feet!” Zuciyar su na bugawa da sauri.“200 feet…” John ya matse Starring da ƙarfi yana ɗan ɗaga nose kaɗan. “100 feet…!”Shiri na ɗan lokaci ya yi kamar ya tsaya.“NOW…” Jirgin ya bugi ƙasa da ƙarfi ba tare da ƙafafun sun sauka ba.Wuta da walƙiya suka tashi daga ƙarƙashin jirgin yayin da yake gogayya da runway. “Keep it straight!!” John ya yi ihu. Jirgin na son karkata amma ya ja shi ya dawo daidai. “Don’t lose it… don’t lose it…” ahankali gudun jirgin ke raguwa, amma har yanzu yana da ƙarfi. “Brakes not available!” “I know!”Ya ci gaba da riƙe shi da ƙarfin hali, A kuma ahankali ahankali gudun ke raguwa, kafin Jirgin ya tsaya cak.Ba motsin komai, ba ƙara sai numfashi mai nauyi a cikin cockpit. Co-pilot ya dubi John da idanu masu cike da hawaye. “We survived.” John ya jingina baya, ya rufe ido na ɗan lokaci.
“Everyone did,” ya faɗa a hankali....

Cikin ƙasar Florida kuwa, tuni labari ya gama karede ƙasar cewar jirgin daya taso daga Lagos zuwa Florida ɗin is bad….. kan kace me ne labarin har ya fara gama fita, irin su hidan talabijin na Florida sun katse shirye-shiryensu...
“BREAKING NEWS!”
“An emergency situation involving an international flight approaching Florida…” Hoton jirgi a cikin hadari ya bayyana a screen, mutane a gidajensu tare da su aka kalla komai cikin tashin hankali.... A filin jirgin sama na Miami International Airport motocin gaggawa sun fara jera ambulance, fire service, police duk sun shirya. Wani jami’i ya faɗa da ƙarfi, “Prepare for emergency landing!” gaba ɗaya ƙasar na kallon jirgin ko sai sauƙa lafiya… ko kuwa zai zama labarin ƙarshene?.


A lokacin da jirgin yayi kamar wata fisga daidai zai sauka ƙasa cikin sauri
Fasinjoji wasu suka riƙe kujerunsu da tsoro, wasu na runtse ido cike da tashin hankalin da basu taɓa shiga, saurin ya fara raguwa har seda jirgin ya sauƙa akan diga digansa yana tsayawa da kansa, wani shiru na mamaye ilahirin jirgin. Fuskan First Officer cike da fara'a ya zube a kujera yana me furta
“we survived Finally....” John ya kalli gaban jirgin yadda ruwan saman ke zuba a gilashin cockpit ɗin, Ya wani lumshe ido na ɗan lokaci, yana sakin wata ijiyar zuciya me kyau tare da furta....

“Welcome back to earth.”

Yana ci gaba da kallon ruwan saman yanda yake zuba a hankali… ga hasken motoci na walƙiya a ko’ina a
filin jirgi. Har dama tarin Ambulance… ƴan jarida… jami’an tsaro duk sun cika wajen. Kafin da a aka buɗe ƙofar jirgin
fasinjoji suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya… wasu suna kuka, wasu suna godiya. “Thank you! Thank you!” wasu na cewa “God bless the pilot!”
Suna kiran suna guda ɗaya…
JOHN shi ne ƙarshen fitowa haka ya fito sanye da uniform ɗinsa mai tsabta duk da abin da ya faru, amma kayan na nan fesss, Ruwan sama naci gaba da sauƙa a kansa, amma bai damu ba, gefe guda ka ƙaran ƙaran cameras suka juya gare,wani irin numfashi John ya fesar me ɗan zafi, lokacin da wata ƴar jarida ke cilla masa tambayoyi. Cikin wani irin zallar izzar da yake da yaci gaba da takawansa, A hankali yana janye idanunsa da ga kallon su cike da basarwa alamar ƴan izzar na kusa kenan. Wata daga cikin yar jaridar ce ta sake matsa kusa dashi, tare da furta...
“Captain John! How did you manage to land under such conditions?!” ko kallo bata isheshi ba ya drectly yana nufar wata mayyar Black jeeb ɗin da aka buɗe masa ya shige, aka jata da mugun gudu suna barin airport ɗin baki ɗaya....


*Hhhhhhh mun sha da kyar,don ALLAH zuciyoyin su waye suka girgiza suma bayan ta AMMEY LAYLERH,da kuma passinger's namu?.......*

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215





*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 5
Paid book

Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215


*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

_Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_

ꨄ Drectly babban Hilton Blue Lagoon motar ta nufa, ga shirun daren daya sake nisanta yanayin se hasken streetline ɗin daken kyalli, A natse aka faka motar a gaban Hilton Miami Airport Blue Lagoon ɗin dake ɗauke da hayaniya tamkar ba dare ba, Ahankali
ya fito daga motar fuskar sa babu wani abu me kama da annuri, se kawai gajiya da wani abinda ke damunsa a zuciya, kai tsaye a reception har an riga an tanajar musu komai. Ɗaya daga cikin ma'aikatan reception ɗin ya furta...

“Good evening, Captain John… your room is ready.”

Kansa kawai ya ɗan jinjina ba tare da ko tsaya amsa gaisuwan daya kawo masa ba, key card na room ɗin kawai ya amsa yana nufar room nashi, yana shiga ɗakin ƙofar ta koma ta rufe da ƙaramar ƙara, shiru babu motsin komai a room ɗin se A/Cn dake kaɗawa a hankali kaɗai. A tsaƙiyan ɗakin John ya tsaya na ɗan lokaci, tamkar wanda bai san me zai yi ba, p-carp nashi kawai ya zare daga kansa yana jefa ta saman gado yana jan wani numfashi mai nauyi… kafin ya kai zauna gefen gadon hannunsa riƙe kansa da yake jin na sara masa sosai,Wata iska me zafi ya fesar yana me ambatar kalmar. “Ohh Jesus..” saboda yadda abinda ya faru a jirgin ne kawai ke dawowa a kansa, tun daga kan muryoyi, gargaɗi, firgicin da mutane suka shiga dama sauran crew ɗin su. Tsaye ya miƙe ahankali ya isa bakin window, yana kallar ainihin tsakiyan birnin Florida ta hasken fitilun Miami suna kyalli kamar komai yana tafiya lafiya… ya jima tsaye a wurin kafin ya dawo gefen gadon ya zauna, se da ya ɗan sake diban lokaci kana ya faɗa bathroom yayo wanka ya fito, kayansa ya sanja kawai zuwa na bacci ya rufe ido, amma baccin ya ƙi zuwa, don daya rufe idon yaje jin kamar har yanzu yana cikin cockpit ɗin ne, ga zuciyarsa dake bugawa da sauri ba sassauci ko sauƙin hakan dangane da lamarin, a ɗan wahalce ya juya gefe ɗaya, nan ɗin ma babu sauki ,don haka ya sake juyawa ɗayan gefen shima hakan babu afuwa.
Daga ƙarshe ma sai buɗen idonsa yayi cikin duhun ɗakin, ga gajiyan dake ci gaba da ratsa ilahirin jikinsa, zuciyarsa babu nutsuwar komai, haka dare ya ci gaba da tafiya ba tare da John ya sama runtsawa ba, daga ƙarshe ma yadda yaga daren ranar haka safiyar ta iske shi amma idanunsa a lumshe kuma se dab da farkon fara ƙiraye ƙirayen sallan subhi ya rufe idonsa da ƙarfin daya saka komai nashi mutuwa. 8:00 Hasken ranar da ya shiga ɗakin na Hilton Miami Airport Blue Lagoon ne ya saka John
buɗe idonsa a ɗan firgice, numfashinsa ya ɗan yi nauyi. Kafin ya tashi zaune da sauri yana jin haushin kansa daya farka yanzun,saboda baccin da bai sama ba a daren jiyan, wani yamutse fuska yayi tare da furta kalmar…

“Damn it…”

A bayyane yana saukowa daga gadon da ƙarfi kai tsaye ya nufi window… direcly hasken rana ya kutso ta cikin labulen glass na ɗakin yana sauka a fuskar John. Sai ya buɗe idonsa da kyau yana amsar iskar dake kaɗawo daga sama tana sauƙa a kyakkyawar fuskarsa, tafin hannunsa ya ware yana cusa su cikin gashin kansa ya soma yamutsawa, tare da dafe glass door ɗin da hannunsa ɗaya ya matse shi sosai har jijiyoyin hannunsa suka fito. Yana daga tsayen da yake ya ji kamar yanzun ne komai ke ƙoƙarin shirin sake faruwa,
Muryar “Mayday” da kuma lokacin da hannunsa ya sauƙa kan control yana
matse shi da ƙarfu, da kalmar...

“Control… we are losing”

Wani toshe ƙofofin kunnuwansa yayi yana me furta...

“STOP IT!”

Ya wani faɗi a tsawace yana janyewa daga jikin window'n ɗin kamar wanda ake ja da shocking ,tafiya ya fara cikin ɗakin gaba da baya kamar zakin da aka kulle a cikin keji ya kasa fita, hannunsa yakai ya ɗauki wayarsa ya kulketa yana yin jifa da ita saman gado da ɗan ƙarfi. Domin baya son magana da kowa, haka baya son jin komai!, Kafin ya taka ya nufi bathroom. Shower kawai ya buɗe ya sakar ma kansa, take kuwa ruwan ya soma zuba da sauti mai ƙarfi yana dukan fuskansa da jikinsa,hannuwansa duka biyun ya saka yana jingina da sink, yana kallon kansa a mirror da Idanunsa da suka ɗan yi ja. Fuskar sa ta canza ba ba kamar John ɗin farkon da muka fara gani bane, wannan ɗin ya rikiɗe zuwa wani John ɗin na daban, haƙoransa ya matse da ƙarfi yana taune gefen lips nashi, kafin cikin wani ƙaƙƙarfan sautu ya ce....

“You need to get a grip, John…”

Ya faɗama kansa da kansa da ƙarfi, yana wanke fuskansa da ruwa mai sanyi. Sanyin ruwan daya gama ratsa shi ne ya saka ji jan wata ajiyar zuciya na ɗan lokaci, sake nutsuwa yayi yana jin sanyin yana ci gaba da ratsa fatar sa da zuciyarsa. Bayan wasu mintuna ya
fito daga bathroom ɗin, ya shirya cikin sauri kamar wanda yake gudu daga wani abu, lafiyayyar jacket ɗinsa ya ɗauka yana ɗorawa saman shigar jikinsa, kai tsaye ya nufa bakin ƙofar. Se da yaja ya ɗan tsaya kafin ya kai
hannunsa kan Handledoor amma be kai ga budewa ba, se shirun da kawai yayi kafin yaja wani numfashi mai nauyi…ya buɗe ƙofar inda Corridor ɗin hotel ɗin ya bayyana inda yake nan shiru, a hankali ƙafafunsa suka soma taka carpet mai laushi sanyin safiyar ranar da kuma na na'urorin dake bayar da sanyin suma, tafiya yake ba tare da ya waiwaya ba. Kuma jin duk wani taku yake a wani mataki me nauyi, yana jin ba wai kawai yana tafiya ba ne, har ababuwan dake ransa yake son yaga yayi ƙoƙarin kawarwa, a haka har ya kawo inda lift take, da kanta Lift ɗin ta buɗe ya shiga, ƙofar ta rufe a hankali…
Reflection ɗinsa ya bayyana a cikin glass ɗin lift. Kafin ya wani kalla kansa a hankali ya wani kawar da kansa daidai lokacin da Lift ɗin ke kawo shi Ground floor. Ƙofar lift ta buɗe tana bayyana Reception ɗin Hilton Miami Airport Blue Lagoon ɗin dake cike da hasken safiyan ranar da motsin mutane masu kai da komo, ahankali ya fito yaci gaba da tafi daidai wata Receptionist na ƙarasowa har inda yake da murmushi a fuskarta take furta.

“Good morning, Captain”

Bai tsaya ba, bai kuma amsa mata ba yayi wucewarsa kai tsaye, Iskar safiyar na sake bugar fuskar sa wanda ya saka shi ɗan lumshe ido, ya furzar da wani
numfashi mai zurfi… yana ƙarasa fita daga ainihin hotel ɗin hannuwansa zube cikin aljihunsa, haka yaja ya tsaya a bakin hanya na ɗan lokaci yana kallar yadda motoci ke wucewa…wayar sace tayi vibrating ɗin da dole ya saka shi fito da wayar ya kalli screen nata ahankali,
_Airline Operations_ Fuskarsa ta ɗan canza duk da yasan hakan ba wani abun mamaki ba ne, wayar ya ɗaga inda yana kai ta kunne aka furta.

“Good morning Captain,” muryan da aka kira shi ɗin ya faɗa cikin tsari.
“We hope you got some rest.” Sai ya ɗan yi shiru Idonsa ya lumshe kaɗan kafin ya wani furta kalmar. “Not really.” aka sake yin shiru na ɗan lokaci, kafin muryar ta sake dawowa... “We need you ready. Your next flight is scheduled…”
John ya ɗan matse haƙoransa. “Next flight?” “Yes, Captain. You’ll be departing soon.” aka sake bashi tabbacin hakan, Zuciyarsa ce ta ɗan buga da ƙarfi. “Where to?” se kuma yayi shiru kawai yana jiran amsar da za'a bashi, tamkar wanda yake tantance yadda zasu faɗa masa aka furta...

“…Back to Lagos.”

Wani irin shiru ne ya ratsa tsakanin wayoyin nasu, kafin John ya juya ya kalli hotel ɗin dake bayansa. Sai kuma ya sake kallon hanyar, tare da matse wayar da ƙarfi. Komawa Lagos?…
Wannan tafiya da ta kusa zama bala’i…sake komawa cikin jirgi?, duk da dai bawai yana a tsorace bane, se dan kawai buƙatan balance ɗin da yake ko ya samu ƙwaƙwalwansa ta huta.

“Captain, are you there?”

Wannan kalmar ta

5 / 31