Advertisements
Chapter 18 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   18 / 31

51K to 54K   out of 91.1K words

sake zubo mata.

“Me yasa…?” ta furta.

Daidai lokacin da driver nata ya gama daidai tsaiwar motarsa a parking car na gidan. Kowa babu a parlourn don haka drectly ta wuce ɓangarenta kai tsaye, anan parlourn ta zube tana cilli da takalmanta ta jefa jakanta saman kujera tare da riƙe kanta "Damm it" ta faɗa tana miƙewa tsaye ta ƙarasa bedroom nata, himar dake jikinta ta fara zarewa.
Tana ƙarasawa jikin mirror tana kallar kanta da fuskarta, gaba ɗaya se taga kamar ba ita bace a jikin hoton madubin. Wata iska ta fesar tana faɗawa toilet, bata wani dauki lokaci me tsayi ba ta fito tana jikinta da towel.
Sauri sauri ta shirya kanta cikin farar shirt da wandon Jeans ɗin da be gama kai ƙwaurin ta ba tana ɗaukar wata oversized hoodie ta ɗaura saboda sanyin da aka soma kaɗawa na bajewar hadarin da yay, tana shirin tayar da sallah aka yi knocking doorhandle nata ne ya sa ta juya ta kalli ƙofan, izinin shigowa ta bada Baba azumi ce me aikin da ita kaɗai ta yarda ta shigar mata se kuwa jikarta jimmala, wacce ita kuma taje kauye ne. sai da ta gaishe ta kafin ta tambayeta ko za'a kawo mata abinci nan sama ne?, murmushin daya bama Baba azumi mamaki ta kakalo.

" No Baba azumi zan fito yanzun, Dada yana nan ne?" dake in taso tana ƙiransa Dada ɗin.

" Ah ah sun fita tare da Mamyn ma amma basu ma dade da fitan ba"

Kanta kawai ta gyaɗa mata tana cewa. "Okay kije ina zuwa, a sama min hot chocolote pls kafin na fito"

Ɗan risinar da kai tayi tace.

"Toh sai kin Fito" ta faɗa tana fita a ɗakin tare da rufo mata ƙofan, ita kuma ta koma jingine da jikin gado ta rufe hannuwanta da fuskarta. Ta jima sosai kafin ta saƙƙo zuwa parlourn, babu kowa a parlourn lokacin da take saƙƙowar, ita Baba azumi na kitchen tana haɗa mata hot chocolote ɗin data buƙata, ita kuma Husna yau wata exams ce da ita me zafi shi yasa bata dawo zata kwana a school. kujera ta ja a dining ta zauna tana daura ƙafafunta duka biyun a kan kujeran ta tanƙwashe, tana ɗaukan sandwich ɗaya ta kai baki tana maida hankalinta gaba ɗaya kan abinda ake haskawa, kan wani ɗan ta'addan da yake nemar gagarar duniyar koma ace ya gagara. "*CODE BLACK⁉️*" ta sake maimaita sunan da taji ya wani irin yankar mata da gaba, Waye shi?, ko kuwa wacce kalar ƙungiyace da take nemar gagarar duniyar baki ɗaya?. Kamar idan zata iya tunawa wannan shi ne karo na biyu data ga ƙasar _Nerovia_ ƙarƙashin jagorancin *Noctra city*, gaba ɗaya ko media ka shiga a wannan lokacin labarin dake trending kenan, *EMPEROR RAEL (TARIQ)* A duk lokacin ma'aunan mizanin kimiyya zasu kwalkwala abinda yake basu kenan, wato *EMPEROR RAEL (TARIQ)*. Daga ƙasan zuciyarta take jin kamar zata taɓa sanin mahin hinin labarin, kodai haɗa alaƙar wani abu ko wani nata wanda ya ze danganceta a cikin labarin ɗin. Maganar da Baba azumi ke mata ne ya saka ta ɗan nisawa tana dawo da nutsuwarta gare ta, "NAGODE" ta furta lokacin da take amsar hot chocolote ɗin, ba kawai Baba azumin kalmar Nagode ɗin da yasmine ɗin ta furta mata ta daka ba, harda iyayenta dake daf da shigowa amma basu kai ga shigowanba. Domin kuwa wannan kalma ba kalma bace me sauƙi wajen furtawa a wurin Yasmine. A natse cikin ƙaunarta me zurfi Daddy ɗaya riga Mamy isowa parlourn ya ɗan shafa saman kanta, fuskarsa ƙawace da kyakkyawan murmushi. “Ma sha ALLAH haka nake son ganin farin cikin Baby narh kuma Shalelena fiye da komi dake cikin wannan duniyar, ɗan rausayar dakanta tayi tana wani langoɓewa tace. “Thanks u Daah! nd I love U so much...Mamy barkanku da dawowa...” ta rufe zancen nata da da musu sannu da zuwa ɗin. Da kallo kawai Mamyn ta bisu a ranta tana ayyana me hali dai baya taɓa denawa, amma tunda dai yanzun tana iya lankwasata shi yasa abin yazo mata da sauki, kuma baya magana ko wannan faɗan nasa. Ƙiran daya shigo mata wayar tane ya sakata miƙewa tana nufar sama da hot chocolote nata. Ba me yawa ba tayi wayan ta kashe tana ɗaukan headphone ta saka a kunnenta tayi connecting da laptop nata, taci gaba da kallon Film ɗin da take na Kaddara 4. Bayan ta gama kallon kwanciya tayi cikin yanayi na kwanciyar hankali tana jin wani abu me daɗi na ratsata ilahirin jikinta idanunta a lumshe. Santala
santalan ƙafafunta saman doguwar kujerar da take kwance ta yi hugging na matashin Kujerar irin tightly ɗin nan. Ɗan jujjuyawa take yi tana jin ƙaunar John na ci gaba da ratsa ko ina na jikinta Ta juya hagu haka kuma ta juya dama. Amma kalmarsa guda ɗayar nan ce kawai ke bibiyarta.

“YOU.”

Ta rufe idanunta da ƙarfi tana ambatar.

“Ya ALLAH!…”

Kafin ta sake wani juyin a kusan karo na babu adadi.

“Ka fitar da shi daga raina…”

Amma zuciyarta ta ƙi yarda....

_IKOYI high-brow area..._

Anguwar tayi wani irin shirun dake bama duk wani mazaunin dake cikin anguwar ko nace mension ɗin tsaro,da sanya nutsuwa najin cewar ehhh lallai yana cikin kwanciyar hankali, komai anguwar ta haɗa tun daga kan daraja, Tsaro. Abin dai gwanin birgewa musamman ma manyan gidajen dake
tsaye kamar manyan ganuwar mulki, gaba ɗaya kuɗi,hutu,jin daɗi na rayuwa,wadata, kwanciyar hankali sune suka haɗa ƙarfi da ƙarfe suna ma mutanen dake cikin estate ɗin taron dangi tsabar gata.

*JOHN*

Drectly bedroom nashi ya wuce bayan awannin daya ɗiba zaune a parlourn. Yana mayar da ƙofan ya rufe harda saka key ya jingina da jikin ƙofar yana sauƙe wata zazzafar ajiyan zuciya, Ahankali ya ɗaura hannunshi kan heart ɗin sa da duk wani motsi na bugun da zuciyar zatayi tana bugawa ne tare da yasmine, hannun daya dage zuciyar ya kafe da ido jikinshi namai wani iri tuno wannan kalmar ta *Then learn to leave* ɗin da ta furta masa. Sosai kalmar ke wani kalan dukansa ba da wasa ba. Idanunsa ya Lumshe dafe da Heart nashibya kai kwance saman bed ɗin daya gama jin komai da komai. Hannunsa duka biyun ya saka yana taro ƙeyarsa dasu, ya zaman komai nasa na kallon sama ƙafafuwan sa kuma na a ƙasa yana zubawa Pop tarts lafiyayyun fararen Idanuwansa da yake jin kamar an sauya musu ƙarfin ganinsu.... A haka wani ɗan bacci yazo yay gaba dashi, daga nan be saka farkawaba har seda hasken ranar daya dallare idonsa kana ya motsa, sakamakon raba curtains da yayi biyu wanda hakan shi ya bama ranar damar haskesa son ranta ita ma, har kuma lokacin hannun na dafe da heart nashi. Ahankali ya zubo ƙafafunsa ƙasa yana saka hannuwansa biyu ya ɓangare yana yin baya kaɗan idanunsa su ɗan tafi suma luuuu wanda baccin be gama sakin su ba. A natse ya faɗa bathroom yayi taking shower ya fito yana nufar gaban makeken glass na window'nsa yana kallon waje. Hannunsa ɗaya cikin dark Gucci jogger pants dake jikinsa, Wanda yabi dogon figure nashi me tambarin Gucci dake jikin dogon wandon nasa, ya ƙara wani modern flair to the look not as casual as he wanted to look, fitted balanciaga hoodie ne a jikinsa charcoal grey colour, taushin cotton ɗin making him feel comfortable yet sophisticated.
Ƙafafunsa zube cikin slipper's masu taushi na Versace's. Knocking doorhandle ɗin da akayi a bakin ƙofa sau biyu ne ya sa shi juyowa yana barin jikin glass ɗin, ya zauna a gefen gado yana bada izinin shigowa, da sallama Mecheal ya shigo Room ɗin yana sanye da kaya na shan iska tamkar dai me gidan nasa. Zama yay Kan kujerar dake facing data Boss ɗin nashi, kafin ya shiga wasu ƴan latse latse yay tare da tura may Ipad ɗin gabansa yana me furta...

"Good morning Boss"

Da ka ya amsa shi yana sake yin relax saman gadon daya daddafe gefe da gefensa kamar wanda ciwon naƙuda ya kama. Ganin ba zai tanka shi ba ne ya saka miƙewa. Breakfast ɗin da ya ajje masa don ya damu da yaga be fito ba shi ne ya biyo shi har nan ɗin dashi, idonsa a lumshen da suke be buɗe ba har ya kammala jera masa a kan table glass ɗin dake dap da gadon ya fita, ya jima a hakan kafin ya buɗe idon ya kalla break ɗin idan da yiyuwar ya iya ci se ya ga. A natse yayi break ɗin kana ya miƙe yana goge bakinsa da tishu ya fita suka bar gidan. Tun daga nesa ta hango shi tsaye yau ɗin ma jingine da jikin motarsa, waya ƙare a kunnensa alamar he is making a phone call, 3 quarter ne baƙi a jikinsa with gray polo idonsa lumshe yana ci gaba da amsar wayar. Yasmine ta sake ɗago idanunta a hankali tana ci gaba da kallonsa kai tsaye cikin idanu… kallon da ya haɗa kauna, tsoro, da kuma rashin tabbaci akan abinda zuciya ta riga data kamu da son sa babu zata ko tsammaninta. Ahankali ya fara jin bugun zuciyarsa na sanjawa zuwa na matakin kai da kai ɗin da yake ji duk lokacin data bayyana a wuri, don haka ya zare wayar daga kunnensa yana katse ƙiran idonsa a kanta daga tsayen da take. “My unknown beloved!” ya furta a saman laɓɓansa da motsawarsu kawai ta gani amma ta fahimci sunan daya ambata ɗin.Yasmine ta wani kallesa kafin ta fara taku ta iso har inda yake idanunta na taruwa da wani abun da bata san ko me ye shi ba tace.
“John… ka san me? duk yadda nake ƙoƙarin ɓoye komai amma se gashi zuciyata tana ƙoƙarin yaudarata akan hakan.” Jin wannan kalmar ya saka John matsawa kusa kaɗan, idonsa cike da tambaya da tsananin ƙaunar da yake hangowa tashi cikin idanunta.

“Then don’t hide it… please, Yasmine. Tell me the truth.”

Ta lumshe ido na ɗan lokaci tana amsar bugun da zuciyarta take.m kamar tana yaƙi da wani abu a ranta… sannan ta buɗe su, hawaye na taruwa a gefen idonta. “Ina son ka fita a rayuwana!, ka barni haka nan na rayu cikin salama da aminci ba da azabtar wa irin haka ba.”

Shiru ne ya ratsa wurin kafin ya kalleta zuciyarsa naci gaba da bugawa, ahankali murya cike da raunin da ake son tallafa zuwa kwarin gwiwa yace.

“Ina son ki Yasmine!, zan kuma ci gaba da SO da ƘAUNARKI har ƙarshen abada.. ba zan taɓa rabuwan da kika ce inyi dake My world....”

A hankali ta ɗago idanunta tana zuba masa manyan fararen idanunta tas a kan shi, kaɗan ya yi saurin ɗauke nasa idanun saboda abin da ya kalla daga cikinsu ba masu sauki bane. Don haka shi ma ya zuba mata nasa idanun har na kusan second goma ya ɗauka yana kallonta, yana kuma hukuntata da idanunshi kafin daga baya ya buɗe bakinsa kamar baya son yin magana yace. “You know I love you too.” kanta take ɗan girgiza masa.

“Ka taɓa jin cewa zuciya na iya canza mutum…?”

Kai tsaye itace kalmar data ratsa cikin kunnuwansa, wani ɗan murmushi yayi mara ƙarfi.

“Ban taɓa yarda da hakan ba… sai da na haɗu dake.”

Yasmine ta lumshe idanunta, zuciyarta na bugawa da sauri.

“Idan haka ne… ka shirya ka bi gaskiya… ko da zata raba ka da kowa da komai?”

John ya ɗan yi shiru… kamar yana yaƙi da kansa, kamar kuma ya tafi nazari da fashin baki akan maganar nata ne.

“Gaskiya…? Wacce gaskiya…?”

Ta kalle shi da idanu masu cike da wani haske na daban.

“Musuluncin da kake gudu daga gare shi… shi ne kawai zai baka salama.”

Wani irin shiru yayi maganar ta bugi zuciyarsa kai tsaye.

“Musulunci…?” Ya sake furta kalmar a hankalin daya saka Yasmine gyaɗa masa kai.

“Ba don ni ba… ba don kowa ba… sai don kai da zuciyarka.”

JOHN ya juya baya…yana kallon sararin sama. A karo na farko… zuciyarsa ta girgiza. Ba don saboda soyayya ba…
amma saboda son gano gaskiyar dake cikin zancen nata...

“Ina son ka fahimta, John ba zan aure ka ba!”

Kalmar data saka John tsayawa cak kenan kamar an watsa masa ruwan sanyi, ko wanne akayi freezing nashi.

“Saboda me? Saboda addini? wannan ne kawai?”

Ta ɗaga murya kaɗan cike da mamakin maganarsa ta wai Addinin ce kawai?.

“Wannan ne kawai ɗin ka ce? Ka kuwa san me kake magana kuwa?”

Ya matso kusa da ita yana daidaita tsaiwarsa.

“Eh! Ina magana ne akan mu! Akan soyayyar da kike ƙoƙarin guduwa daga gare ta!”

Ta yi wata ƴar dariya mai ɗaci.

“Soyayya?”

Ta faɗa kafin ta nuna shi da yatsa, “Ka kira wannan soyayya amma baka gane komai akanta ba!”

“To ki gaya min!” ya faɗa da ƙarfi, “Me nake rashin fahimta?!”. Ta taka zuwa gabansa, zuciyarta na tafarfasa.
“Ina ce maka addinina ba wasa bane! Ba abu bane da zan ajje gefe saboda zuciyata ta motsa ba!”

“Ni kuma ina ce miki zuciya ba abin da za a kashe bane saboda tsoro!”

Wani ɗan cizar laɓɓanta tayi

“Ba tsoro bane imani ne!”

“To me ya sa kike ji kamar idan kika zaɓe ni, kin aikata laifi?”

Ta ɗaga murya sosai yanzun kam tace.

“Saboda a wurina haka yake tamkar laifin domin kuwa ƙatoton zunubi ne nake shirin aikatawa idan har na yarda zuciyana ta rinjayi ra'ayina!”

Wani shiru ne ya ratsa wurin kowannensu cike da fargaban rashin tabbaci, amma fushin su bai ragu ba.
Sai ya kalleta da wani irin zafi a idanunsa. “Don haka… duk wannan da muka gina, kina iya jefar da shi saboda abin da kika riga kika yanke?”
Ta matsa kusa da shi, murya na rawa amma cike da tsauri. “Ba abin da na yanke bane hanyar rayuwata ce!”

“Kuma ni fa? Ni ba na cikin wannan rayuwar taki?” ya jefa mata da tambayar kai tsaye.

Ta ɗan ja baya kamar kalmar ta motsa mata zuciya, amma ta ƙi sassautawa.
“Saboda tawa rayuwar tana da iyaka, ba ko ina ake shiga aji daɗin da ake nufin samu ba!” Ya yi dariya mai ciwo.

“Ko kuma kawai baki son in shiga ɗin ne ba?” Ta kalleshi kai tsaye, idonta cike da hawaye amma murya nata ta tsaya daram. “Ko da ina son ka… to ka sani ba zan taɓa karya abin da nake yi wa ALLAH ba saboda kai.”

Kalmar ta bugi zuciyarsa.

“Toh kenan kina zaɓar addininki a kaina?”

Ta amsa ba tare da jinkiri ba.

“Eh haka ne.”

Hannuwansa ya zuba jikin Quiter ɗin dake jikinsa yana jinjina kai a hankali, zuciyarsa na kamar zata karye.

“Na gane… to ni kuma ba zan daina son ki ba Yesmine.”

Ta juya da sauri, hawaye na zuba.

“Ka daina bi na JOHN… don ALLAH!...


*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215










*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 18

Paid book

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.


Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215


*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

♡♡♡♡

ꨄ Tsayuwar da JOHN yayi a wajen kamar wanda aka dasa shi a ƙasa ce, har motar Yasmine ta ɓace daga idanunsa bai motsa ba. Iskar sanyin da ke kaɗawa ce kawai ke bugun fuskarsa amma shi ko kaɗan bai ji komai ba.
A hankali ya sauke numfashi mai nauyi yana lumshe idanunsa.

“Why does it hurt this much…?”


Ya furta cikin muryar da ko shi kansa bai gane ta ba. Mecheal dake jingine jikin motar daga ɗan nesa ya jima yana kallonsa. Tun shekaru yana tare da JOHN amma bai taɓa ganin sa a irin wannan yanayin ba. Boss ɗin nasa wanda ko hatsarin da yake shiga a cikin jirgi bai sa shi firgita ba, amma yau se gashi mace guda ɗaya ce ta sauya komai nasa, gaba ɗaya neman birkita masa Boss ɗin nasa take yarinyar, wata zazzafan ijiyan zuciya ya fesar yana dan matsowa kadan a hankali yace.

“Boss…”

Amma JOHN bai amsa ba sai ma kawai
juyawar da yayi ya nufi motarsa cikin tafiyar kasala irin ta mutumin da zuciyarsa ta gaji da yaƙi. Bai jira Mecheal ya buɗe masa ƙofar motar ba ya buɗe shi da kansa ya shiga. Tun da suka dauki hanyar dawowa gidan babu wanda ya sake magana cikinsu. Sai ma ƙarar music mai laushin dake fita a cikin motar da Mecheal ɗin ya saka musu dan ɗebe kewa ga ogan nasa…
Amma duk da haka kalamanta ne kawai ke ci gaba da dawo masa. “Eh haka ne… na zaɓi addinina akanka.” Wani irin ɗaci ne ya zo ya masa tsai a ƙahon zuciyarsa. Yana saka gaskata a karo na farkon da ya ji an taɓa girman kansa.
Ba don ta ƙi sonsa ba sai don ta fi son wani abu a kansa.

IKOYI...

Kai tsaye Mecheal ya danna hancin motar a katafaren gidan da John ɗin ya dawo da zama, kai tsaye a fito daga cikin motar ba tare da jira ba. Ya fara tafiya cikin nutsuwa amma daga yadda ya matse jaw ɗinsa zaka fahimci cewa lallai akwai abinda ya ɓoye cikin kirjinsa. Tun kafin ya ƙara sa shiga parlourn nasa yaji kamar muryan Mammoh nashi, wacce sam tsabar yadda yake a ruɗe besa ya kula da katuwar motar ta dake harabar gidan ba. Ahankali yaja ya tsaya cak a hankali ya ɗaga idanunsa yana kallon MOTHER ɗinsa dake zaune cikin parlour ɗin, sanye da wata doguwar riga wine colour, hannunta riƙe da glass cup na tea. Duk da shekarunta… har yanzu akwai wata irin haɗuwa da kwarjini tattare da ita. Idonta ƙanƙance a kansa da furta.

“Come here.”

Numfashi ya sauke a hankali ya ƙarasa cikin parlour ɗin. “Good evening Mother.” giranta ɗaya ta dage.

“Really? Good evening?”

Ta ajje cup ɗin hannunta tana kallonsa sama da ƙasa.

“Tun safe nake trying to reach you.”
“Busy ne”

“Busy?”

Ta katse shi da wata ƴar dariya mai saukin nauyi.

“Busy doing what exactly?”

Shiru ya mata yaki magana, wanda hakan ya bata damar mikewa tsaye
tana gyara zaman silk

18 / 31