Advertisements
Chapter 26 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   26 / 31

75K to 78K   out of 91.1K words

IBRAHEEMUL KHALEEL ɗin?”

“Babban malamin masallacin kasar da na musulunta.”

Madame Victoria ta dafe baki ta sake furta kalmar.

“…Shikenan.”

Ta furta cikin rauni kamar wacce ke tsoron a kwace mata wani abunda yake kamar ba nata ba. IBRAHEEM ya ɗago yana kallonta cike da Tuhuma yace.

“Meyasa kuke tsoro ne…?”

“AM AMM KA GA SOON BA KOMAI BA FA NE DA MA.... DA MA......”

“DAMA BAMASON KA RINKA ZUWA IRE IREN ƘASASHEN NAN NE SABODA YAKIN DAKE FARUWA DASU HAKA.....”

Madame Victoria ta yi saurin fanshe mijin nata, wanda wani kallon ban yarda daku ba kawai John ya jefesu dashi yana shigewarsa stairs nashi...

*INDIA*

Cikin katafaren gidan Lady Rebecca dake India kuwa. Tun da suka dawo ake ta shirye shirye bikin auren Deepika da JOHN. Don sun ce aure ne babu fashi tabbas duk inda ya tafi ma zai dawo ya tarar da an daura masa aure da Deepika ɗin, yanzu haka sun kammala duk sauran shirye shiryensu dake India suna jiran visa nasu ya fito su taho Nigeria don dama alkawari su kayi duk sanda auren Deepika ya tashi da John sun gama zaman India kenan.

Wayar Deepika dake gefe da ita ne ta soma ringing. Da murmushi Deepika ta ɗauka don ganin wanda ke kiranta, sai dai murmushin nata ya ɓace ne nan take sakamakon abinda aka faɗa mata daga cikin wayar daya saka ta mikewa tsaye a firgice tana furta kalmar.

“WHAT?!”

Cikin tsananin firgici Lady Rebecca ta juyo da sauri ga Deepika din tana jefa mata tambayar.

“Deepika meke faruwa?!”

Deepika ta kalli mahaifiyar nata da idanunta da suke cike da tsoro ta furta.

“JOHN ne! …”

Ta haɗiye wani yawu ta ɗora da fadin.
“…YA MUSULUNTA .” Wani irin shiru ne ya mamaye Wajen “MUSULUMCI?…”
Lady Rebecca ta sake furtawa a hankali don ji tayi kamar bata ji daidai ba.
Deepika ta girgiza kai hawaye na taruwa a idanun ta tana me sake furta.

“Not John…”

Ta furta cikin rawar murya. “Yana kiran kansa IBRAHEEMUL KHALEEL.” Nan take fuskar Lady Rebecca ta sauya cike da tsananin tashin hankali ta matsa kusa da Deepika tana rike kafaɗarta ta girgizata tace.

“Me... Ki.... ka... ce?!”

A dai-dai lokacin da Daddyn Deepika ke shigowa parlour ɗin.

“Rebecca me ke faruwa ne?”


Shi din ma kalmar IBRAHEEMUL KHALEEL ɗin kawai data ambata masa ne ya saka wani irin firgici ya bayyana akan fuskarsa yana ja da baya tare da furta.

“No…”

Ya ci gaba da furta kalmar No din yana girgiza kai. “This can’t be happening…”
Lady Rebecca ta kalli mijinta cikin rawar murya. “Ka tuna abinda Sheikh ɗin nan yace shekarun baya da suka wuce…?”Nan take ya juya yana mata kallon tsoro. “Kar ki sake ambaton wannan maganar!” Deepika ta zaro ido tana kallon su da furta. “Wait… what’s going on?!” Sai dai babu wanda ya bata amsa saboda dukkaninsu sun san wannan sunan ba ƙaramin suna bane me haɗari tattare da sake fasuwarsa cikin ahalinsu....

*YASMINE *

A gefe guda kuma gaba daya yinin yau
YASMINE ta yi sane cikin faduwar gaban haka kawai, Ko yanzun ma tsaye take bakin window ɗinta tana kallon ruwan dake sauka kaɗan ƙadan.
Zuciyarta cike take da rashin nutsuwa tun kwanakin nan bama iyaka yau ɗin ba. Wani irin faɗuwar gaba take ji kamar akwai wani abu da yake shirin canza rayuwarta gaba ɗaya, wayarta data soma ringing ne ya saka ta saurin kallo, tana ganin sunan wanda ke kiran taji numfashinta ya kusa tsayawa. Hannunta na rawa ta daga wayar tare da mannata da kunnenta. Wani shiru ne ya ratsa tsakanin wayar, kafin daga bisani ta ji muryarsa mai cime da nutsuwa ya furta mata kalmar.

“Assalamu alaikum, Yas_mine…”

Wani irin bugun zuciyar YASMINE tayi
saboda wannan…ba muryar JOHN ɗin data sani bane.

_Hhhhhhh to ai shikenan jama'a a gimtse haka nan._

_Shin kuna ganin cewar YASMINE kuwa ko za ta iya karɓar sabon IBRAHEEM din daya dawo mata a madadin JOHN?_

_Ko mene ne sirrin dake tattare da sunan IBRAHEEMUL_ KHALEEL?.. Kome yasa kowa ke firgita da jin sunan Saudi Arabia kawai bayan sunan kuma sunan
IBRAHIMUL_KHALEEL ɗin…?_

_Ko kuwa sirrin da ke tattare da sunan IBRAHEEMUL KHALEEL ɗin shi zai fara rusa komai?_

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215








*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 26

Paid book

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡

Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

♡♡♡♡

Wani irin sake yankewa ya fadi gaban YASMINE yayi lokacin da muryarsa ta sake ratsata ta cikin wayar a karo na biyu. “Assalamu alaikum, Yas_mine…”
Numfashinta ne ya ɗan tsaya na wasu sakanni kafin daga bisani cikin rawar murya ta amsa. “Wa… alaikumus salam…” Sai dai zuciyarta gaba ɗaya ta shiga wani irin ruɗani saboda wannan ba JOHN ɗin data sani bane. Wannan muryar cike take da wata irin nutsuwa da sanyin da take ji har cikin ranta.
A hankali ta lumshe idanunta tana riƙe wayar sosai a kunnen ta furta “John…?”
Shiru ya ɗan ratsa tsakanin wayar kafin daga bisani ta sake jin muryarsa cikin taushin da ya taba zuciyarta ya ce.

“Not John…” Ya furta a hankali.
“IBRAHEEMUL KHALEEL.”

Wani irin faɗuwar gaba YASMINE ta ji sai dai ba tsoron sunan tayi ba kamar sauran mutane… zuciyarta ce kawai ta shiga bugawa da sauri saboda yadda take jin canjin dake cikin muryarsa.
“Ka… ka dawo Nigeria…?” “Na dawo.”
Ya amsa cikin nutsuwa wani shiru ne ya sake ratsa tsakaninsu kafin daga bisani ya furta. “Ina son ganinki.” Nan take zuciyar YASMINE ta sake bugawa da ƙarfi. Tun kafin ta samu damar magana ya sake cewa. “Please…” Wannan kalmar tasa ce ta karya mata zuciya gaba ɗaya saboda bata taɓa jin JOHN yana roƙon kowa ba. A hankali ta haɗiye wani yawu kafin daga bisani ta furta, “Ina… ina gida.” “Zan zo.” Daga haka ya kashe wayar. YASMINE ta sauke wayar daga kunnenta a hankali zuciyarta na wani irin bugawa, don har yanzu bata gama yarda cewa JOHN ya musulunta ba. “To wai… me yake faruwa ne…?” Ta furta a hankali tana dafe ƙirjinta.
★..

Tun bayan shigewar IBRAHEEM ɗakinsa Mr. Jeff Deefer ya kasa zaune ya kasa tsaye ko na minti guda. Sai faman kai kawo cikin parlourn yake tamkar wanda aka ce masa hankalinsa zai bar jikinsa, Madame Victoria kuwa gaba ɗaya idanunta sun yi wani irin zurfin sanya ɓacin rai, tana maƙale wurin mijin nata. “Jeff…” ta kira cikin rawar murya, sai dai ya dakatar da ita da hannu cikin tsananin fushi.

“Na ce kar ki sake min wannan maganar!” ya furta a tsawace.

“Wannan yaron bai san abinda yake kunnawa kansa ba!”

Jelly dake zaune gefe tana kallonsu cikin ruɗani ta kasa jurewa tace.
“Papa… me yasa kuke tsoron sunan nan haka ne?” Nan take parlour ɗin yayi tsit.
Mr. Jeff Deefer ya tsaya cak har numfashinsa ya ɗan tsaya shima kafin daga bisani ya juya ya kalli Jelly da idanunsa da suka kaɗa suka yi ja.

“Saboda wannan sunan…” Ya fara cikin murya mai nauyi.“…yana da alaƙa da mutumin daya taɓa rusa rayuwar mutane da yawa.” Wani irin faɗuwar gaba Madame Victoria ta ji. “Jeff stop please…” Ta furta cikin tsoro sai dai ya girgiza kai. “A’a Victoria! Lokaci yayi da zamu fara fuskantar gaskiya.” don haka
ya juya yana kallon staircase ɗin da yake jin kamar motsin wani abu.

“Na rantse bazan bari ya sake komawa kusa da waɗannan mutanen ba.”

A dai-dai lokacin kuma wayar Papa ta soma ringing wanda yake masa maganar da yake yi yana daukar wayar da sauri, sai dai abinda aka faɗa masa ne ya saka idanunsa buɗewa sosai cikin firgici. “What?!” Madame Victoria ta miƙe da sauri. “Me ya faru?” take tambayarsa cike da wani sabon tsoro da rikicin. Sauƙe wayar a hankali yayi yana kallonta. “…John ya cire sunan DEEFER daga duk wani social account nasa.”

“What?!”

“He changed everything to IBRAHEEMUL KHALEEL.”

Wani irin shiru ne ya mamaye parlour ɗin. Jelly ta zaro ido, Madame Victoria kuwa ta dafe baki. Shi kuwa Mr. Jeff Deefer cikin wani irin fushi ya sake ɗaukar wayarsa yana saka ƙiran wata No. “Freeze every single account belonging to him.”

“Sir?”

Aka so katse shi daga cikin wayar.

“I said EVERYTHING!”

Ya daka musu tsawa yana ci gaba da bada umarnin.

“Credit cards, company access, shares, properties… komai!”

Madame Victoria ta kalleshi cike da mamaki da tsoro ta ce.

“Jeff no!”

Sai dai ko kallonta bai yi ba ya ce.

“Daga yau ba JOHN DEEFER bane shi.”
A kuma dai-dai lokacin Wayar IBRAHEEM dake gefensa ta soma vibrating babu ƙaƙƙautawa.
ACCOUNT BLOCKED,ACCESS DENIED
OWNERSHIP REMOVED. Haka Saƙonnin suka cigaba da shigowa, amma sam sam a fuskarsa bai nuna ko ɗigon tashin hankali ba. Sai ma ahankalin da yaja idanunsa ya lumshe kawai yana ci gaba da jan tasbahar dake hannunsa yana jan numfashi. “ALHAMDULILLAH…”
Ya furta cikin nutsuwa kamar wanda dama tun farko ya shirya rasa komai saboda addininsa. Wayarsa ce ta sake haskawa da wani sabon saƙon.
_YOU HAVE BEEN REMOVED AS CEO OF DEEFER EMPIRE._ Wani ɗan murmushi ne kawai ya bayyana akan lips ɗinsa. Daidai kuma lokacin ƙofar ɗakin nasa ta buɗe da ƙarfi, Mr. Jeff Deefer ne ya shigo cikin tsananin fushi.

“Ka rasa komai!”

Ya furta yana nuna shi da yatsa ta da sake ɗorawa da “Everything all!”
Cikin nutsuwa IBRAHEEM ya ɗaga kansa yana kallon sa ba tare da shakka ko tunanin komai ba yace.

“ALLAH yana tare da ni”

Wannan kalmar tasa ce ta ƙara fusata PAPA har besan Lokacin da sake furta. “Ka haukace ne?!” ya daka masa tsawa.
A hankali IBRAHEEM ya miƙe tsaye yana kallon mahaifin nasa.

“Ina son yin aure.”

Nan take Papa ya tsaya cak yana binsa da wani irin kallon mamaki.

“Da wa?”

Cikin kwanciyar hankali IBRAHEEM ya furta.

“YAS-MINE.”

Wata irin zabura Papa yayi tamkar wanda aka caka wa wuƙa cikin ihu ya furta.

“NEVER!!”

“Na fi son ganin mutuwarka akan ka aureta, akan sabuwar masifa da bala'in da kake kokarin sake kunno mana bayan shekaru!” Wani irin shiru ne ya mamaye ɗakin kafin amma duk da zafin kalaman be saka fuskar IBRAHEEM nuna tsoro ba. Sai ma sake sauke idanunsa da yay cikin nutsuwa kafin daga bisani ya furta.

“Ina sonta saboda ALLAH.”

Wani irin tsit ne ya mamaye ɗakin bayan furucin IBRAHEEM, Ko motsin numfashi ba’a jin sa sosai saboda yadda kalamansa suka tsaya cak cikin zuciyar kowa.

“Ina sonta saboda ALLAH.”

Kalmar ta sake masa amsa kuwwa cikin kunnuwan MR. JEFF DEEFER tamkar ana maimaita masa ita sau dubu. Idanunsa kuwa tuni sun sake yin ja saboda tsananin fushi da kuma wani irin tsoro da yake ƙoƙarin ɓoyewa.
“Ka haukace Ibrahim!” ya sake faɗa cikin tsawa. “Ka rasa komai amma har yanzu baka gane abinda ka janyo mana ba?!”Duk wannan abin kuwa da yake tunanin yanayi ne don ya razana IBRAHEEM ɗin amma bai motsa ba. Sai ma tsayen da yayi cikin nutsuwa kamar dutse, hannunsa riƙe da tasbaharsa yana kallon mahaifin nasa cikin idanuwan da suka rasa girman kai na duniya amma suna dauke da wani kalan kamewa da kwarjin da girma irin na musulunci daya bashi. “A duk rayuwata…” ya faɗa cikin nutsuwan murya. “…ban taɓa jin nutsuwa kamar lokacin da na san ALLAH ba.”
Papa ya girgiza kai cikin takaici.
“Saboda wata yarinya zaka jefar da rayuwarka?” A hankali IBRAHEEM ya ɗan girgiza kansa, “Ba saboda ita kaɗai ba…” ya furta. “…saboda gaskiyar da na gani.” Madame Victoria dake bakin ƙofa ta kasa jurewa ta fara kuka a hankali.
“John please…” ta furta cikin rawar murya. “Ka dawo mana yadda kake…”
Wani irin rauni ne ya ratsa fuskar IBRAHEEM kafin daga bisani ya sauke idanunsa ƙasa. “Sunana ba John bane kuma, Mom.”Wata irin faɗuwar gaba Madame Victoria taji har sai da ta dafe bango. “Ni IBRAHEEMUL KHALEEL ne.....” Da wata irin tsawa Mahaifin nasa ya dube se cikin kallon tsana ya nuna masa hanya yana furta....


“OUT”

A wani irin tsawacen daya sake rudar da Madame Victoria tayi wurin Mijin nata tana riko hannun sa tana bashi hakuri akan kada ya kori JOHN daga gidan.

Madame Victoria ta fashe da kuka mai ciwo tana bin bayan IBRAHEEM yayin da yake fita daga ɗakin cikin nutsuwar sa. “IBRAHEEM please… don’t leave…” ta faɗa cikin rawar murya tana riƙo hannunsa. Sai dai a hankali ya sauke idanunsa yana kallon hannun mahaifiyarsa dake rawa saboda kuka. Wani irin tausayinta ne ya cika zuciyarsa amma duk da haka ya san bazai iya komawa baya ba.
“Mom…” ya furta cikin sanyin murya. “Idan na zauna zan rasa kaina ne, amma idan na tafi ALLAH bazai taɓa bari na tozar ta ba.” Wata irin kuka Madame Victoria ta sake fashewa dashi tana girgiza kai. “A’a… a’a John Ohhh Jesus! Ohh Jesus Help me with your John…” Wani ɗan rumtse idonsa yayi yana zame hannun sa a nata. A dai-dai lokacin kuma JELLY ke sakkowa daga upstairs cikin tashin hankali bayan jin ihu da hayaniya.

“Mum… What happened?” ta tambaya tambaya cikin firgici tana kallon akwatunan da already wasu guards suka fara saukowa da su daga ɗakin IBRAHEEM. Papa kuwa tsaye yake a wurin ƙamm kamar dutse fuskarsa cike da wani irin baƙin ciki da fushi da ya kasa ɓoyewa. “Ya fice daga gidan nan.” Ya ya furta a taƙaice.“What?!” jelly ta faɗa tana zaro ido tana kallon ɗan uwan nata.

“Joseph … kana nufin zaka bar komai ne saboda ita?, Saboda addininta, and Ai zaka iya aurota ka kawo ta gidan nan kowa yayi rayuwarsa yacce yaso right?”
A hankali IBRAHEEM ya ɗan taka gabanta kafin ya kalli sama ya ce.
“Wasu abubuwan na duniya idan ka barsu saboda ALLAH… ALLAH yakan baka mafi alkhairi wasu, ki dauka haka Jelly.” Wani irin tsit ne ya sake ratsa parlourn yayin da ya juya ya nufi ƙofa.
Madame Victoria kuwa ta bishi da gudu har outside cikin kuka.

“IBRAHEEM!”

Ya tsaya cak tana isa gabansa ta riƙe fuskarsa da hannayenta masu rawa.
“Ka kula da kanka…” ta furta cikin kuka, wani irin rauni ne ya bayyana a saman fuskarsa kafin daga bisani ya sunkuyar da kansa ya sumbaci hannunta cikin girmamawa. “Ki yafe min Mom amma nayi abinda ya dace ne…” Daga haka ya juya ya shiga motar da se da kyar Madame Victoria ta zaro masa key nata.
A hankali motar tasa ta fara barin katafaren gidan DEEFER mansion yayin da Madame Victoria ke tsaye tana kuka kamar zuciyarta zata tarwatse.
★
Wasu sa’o’i bayan haka... Tsaye yake gaban wani ƙaramin modern flat house dake wani unguwa mai nutsuwa a Lagos. Ba wani katafaren gida bane irin wanda ya saba rayuwa a ciki, amma wajen cike yake da salama. Agent ɗin gidan na miƙa masa key yana murmushi. “Congratulations sir.”
A hankali IBRAHEEM ya karɓa yana kallon gidan. Bedroom biyu ne kawai, sai ƙaramin parlour da kitchen… amma a karon farko cikin rayuwarsa ya ji kamar yana gida na gaskiya. Ya shiga ciki a hankali yana kallon ko’ina kafin daga bisani ya shimfiɗa prayer mat ɗinsa a ƙasa. Sujjada yayi mai tsawo.
“ALHAMDULILLAH…” Hawaye ne suka zubo masa karo na farko tun bayan fitowarsa daga gidan mahaifinsa.


*Washegari…*

Wajajen Sha biyu IBRAHEEM ya isa gidan su yasmine tare da wani babban malamin da SHEIKH IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL WAXER ne ya hada shi dashi, get man ya musu iso bayan ya leko sun bashi sakon, har babban parlourn gidan suka isa. Ambassador yana ganin John ya gane shi, kuma Yasmine ta faɗa masa labarin musulumtar da yayi.

“Assalamu alaikum.”
Ibraheem ya fara sallama kafin ta malamin ta biyo baya, “Wa alaikumus salam…” mahaifin YASMINE ya amsa yana binsa da kallo kafin ya ce.
“Ku karaso mana.”A parlourn gidan ya zauna cikin nutsuwa. Bayan an kawo musu ruwa ne ya ɗago kansa yana kallon su Ibraheem din. Tun kafin yayi magana wannan malamin ya taryi numfashinsa ta hanyar. “Mun zo ne da magana mai muhimmanci” Ambassador Khabeer ya sake gyara zamansa yana amsawa da.

“Ina jinka.”

A hankali SHEIKH AUWAL ALBANI ya sauke numfashin. Kana a natse ya faro da basu tun daga farkon komai… yadda ya musulunta… yadda ya rasa komai saboda addininsa… yadda aka cire shi daga wurin aikinsa na pilot… da yadda ya bar gidansu gaba ɗaya. Cike da wata irin nutsuwa Malamin yake magana amma kowace kalma tasa na sauka da nauyi cikin zuciyar kowa. Domin duka har yasmine ɗin da malamin ya bukaci gani tana zaune tare da Mamy da Husner. Mahaifin YASMINE ya daɗe yana kallon John kafin daga bisani ya ce. “Saboda yarinyata ka jure duk wannan abun?”A hankali IBRAHEEM ya girgiza kai. “Saboda ALLAH ne farko… sannan saboda ina sonta da gaskiya.”
Ambassador ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin ya juya ya kalli YASMINE.

“Yasmine…”

“Na’am Daddy…”

“Kin tabbata kina sonsa?” Nan take idanun YASMINE suka cika da hawaye.
Cikin rawar murya tace. “Fiye da komai ma …” Mahaifinta ya daɗe yana kallonta kafin daga bisani murmushi mai cike da tausayi ya bayyana a fuskarsa.
“To…” ya faɗa cikin nutsuwa yana kallon IBRAHEEM. “Idan haka ne… gara a daura auren nan tun wuri.” ALLAH Sarki Mamy komai bata ce domin tashin farko taji John din ya kwanta mata a rai, tun daga kamo yadda komai nashi a natse da kuma taka tsantsan. Malamin ne ya jinjina kai ya buɗe baki kenan da niyar magana, amma amma wata irin ƙarar tsayuwar motoci ta cika harabar gidan. Kowa ya juya da sauri cikin firgici…!Wata irin ƙarar tsayuwar motocin ce ta sake cika harabar gidan gaba ɗaya tamkar an zo kama wani ɗan ta’adda. Kafin wani ya samu damar magana aka turo ƙofar parlourn da ƙarfin, Jelly ce ta fara shigowa numfashinta na fita da sauri kamar wacce tayi gudu, bayanta kuma wasu security guards ne tare da… MR. JEFF DEEFER. Nan take gaba ɗaya yanayin wajen ya canza. Ambassador Khabeer ne ya miƙe tsaye cikin mamaki.

“Mr… Deefer?”

Sai dai ko kallonsa PAPA bai yi ba sai ma Idanunsa daya mayar kan Ibraheem gaba ɗaya.

“Ka raina ni har haka ne?” Ya furta cikin wata irin murya mai nauyi.
Shiru IBRAHEEM yayi yana kallon mahaifinsa cikin nutsuwa. JELLY dake tsaye tana kallon Yayan nata idanunta duk sun kumbura saboda kuka ta girgiza kai tana ce. “Joseph … Mommy

26 / 31