Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
tsaye gabanta ya sunkuyar da kansa, wanda shi ne ya kawo mata rahoton. “Madame… he’s changing.”
“SHUT UP!”
Ta daka masa tsawa har ya yi shiru.
Numfashinta ke fita da ƙarfi.
“Wata yarinyar musulma zata tarwatsa min rayuwar ɗana?!”
Ta fizgi wayarta da sauri.
“Get Deepika here. NOW.”
Cikin ƙasa da awa ɗaya sai ga isowar
Deepika dake can wani babban clubhouse. Sanye cikin wani dogon red gown mai matuƙar kyau. Amma yau ko makeup ɗinta bai iya ɓoye irin tashin hankalin dake cikin idanunta ba, sabo da tun kan ta iso har mutane sun tsegunta mata abinda ya faru. Domin ita ma ta fara noticing canjin John. Yana guje mata ba kamar baya da sukan zauna har da dariya ba, ko kiranshi tayi da zarar yaga number ɗinta ne baya ɗagawa. Lokacin da ta shiga ɗakin Madame Victoria… tsaye ta tarar da ita jikin window.
“Mom…”
Deepika ta kira cikin sanyin murya.
Madame Victoria ta juya a hankali.
“Your fiancé is slipping away.”
Kalmar ta sauka kai tsaye cikin zuciyar Deepika. “What do you mean?” Ta tambaya, Madame Victoria ta matso kusa da ita. “That Muslim girl.” Nan take fuskar Deepika ta canza. “Yasmine?”
Madame Victoria ta ɗaga kanta da take jin kamar ze rabe. “He’s changing because of her.” Kafin Deepika ta yi magana… Sai ƙofar ɗakin ta buɗe suna ɗaga kai sukayi tozali da John dake tsaye sanye cikin black shirt. Fuskarsa cike da gajiya. Amma idanunsa sun sauya. Idonsa ya sauka akan Deepika.
Sai ya ɗauke kai. “John…” Deepika ta kira sunansa tana murmushin forced smile. Amma bai amsa murmushin ba.
Madame Victoria ta ɗan haɗe hannu.
“Good. You’re here.” John ya kalleta ba tare da motsi ba. “I’m busy.” yayi maganar yana kokarin barin wurin tayi saurin fisgoshi tana me furta.
“Busy doing what?” ta faɗa da tsauri. “Watching Muslim sermons?” Ya faɗi don shi be wani iya ɓoye ɓoye ba
Wani irin shiru ne ya sauka a wurin,
Deepika ta zuba masa ido cikin tashin hankali. Sai John ya ɗan lumshe mata idanunsa kafin ya furta a hankali.
“Yes.” Cak!!! Deepika ta tsaya tamkar mutum-mutumi. Madame Victoria kuwa ta matse baki sosai. “What did you just say?” John ya kalleta kai tsaye yace.
“I said yes.”Ya ɗan ja wani numfashi.
“And I’m tired of pretending.”
Daddy'n India dake shigowa parlour ɗin ya tsaya cak shima, “What is going on here?” Sai John ya juya a hankali yana kallon Daddyn tare da mahaifinsa yace.
“For the first time in my life…”
Ya furta cikin wata murya mai nauyin gaske. “I finally feel like I’m searching for something real.”Madame Victoria ta girgiza kai cikin rashin yarda ta shiga furta. “No… no… this is insanity.”
Sai John ya ɗan yi murmushi marar
Sautu yace. “Maybe.” Ya ɗan dafe ƙirjinsa. “But every time I hear about Islam…” Ya haɗiye wani abu mai nauyi.
“My heart becomes quiet.”
Kukan Deepika ne ya katse komai.
“STOP IT!!” Ta fashe da kuka sosai.
“If this is about that girl then I can change! I can do anything you want John!” Amma John ko kallo bata ishe shi ba. “No…” Ta girgiza kai hawaye na zuba. “No no no… don’t look at me like that…” Sai ta ƙarasa gabansa ta riƙe shirt ɗinsa da ƙarfi. “You’re mine!”
Ta faɗa tana kuka da dukan kirjinsa.
“We were supposed to get married!”
John ya runtse idanunsa cikin ciwo.
“I’m sorry Deepika…” Kalmar ta kashe wani abu a zuciyar ta, ta sake shi a hankali kamar wacce aka cire wa rai.
Madame Victoria kuwa a wannan lokacin ji tayi kamar ta fasa ihun da kowa se yaji a cikin duniyar. Sai dai ihun ma ta gane cewar wuri yake samu, tun da gata yau nema take ko haukan ne ta taɓa, amma ta gaza sema jirin daya fara dibarta ahankali numfashinta na rawa. “No…” Ta furta kamar mai roƙo.
“Not my son…” Amma John ya juya ya nufi stairs nashi ba tare da ya sake kallon kowa ba, kafin ya hau ya tsaya
ba tare da ya juya ba ya furta.
“And cancel the wedding.”
Kamar walkiya kamar saukar aradu haka kowa yaji saukar kalmar John din, wanda ya saka Deepika fasa wani irin kuka mai karya zuciya. Lady Rebecca da ta tsaya bakin ƙofa kuwa sai da ta riƙe bango saboda tashin hankali. Madame Victoria kuma Idanunta suka canza gaba ɗaya. A hankali ta furta.
“That girl…”
Sai ta ɗago kanta tana bama kanta karfi da kwarin gwiwwa ta ce.
“She started a war.”
Tunda Madame Victoria ta haye samanta babu abinda take se safa da marwa cike da tashin hankali. Kafin ta fito bata yi duba da cewar dare bane ta kalla ɗaya daga cikin guards tace.
“Prepare the car.”
Ta faɗa da murya mai cike da iko da kuma izza. “Tonight… I want to see that girl.” Wani daga cikin guards ya girgiza kai. “Yes ma’am.” da sauri ta juya
“Nobody… nobody takes my son away from me…”
*AMBASSADOR KABEER HOUSE*
Tun kan sha ɗaya kowa ya wuce makwancinsa kowa ya yayi bacci amma banda ita, tana zaune saman gadon ta gaba daya abinda ya faru ne keta famar dawo mata ka ɗazu a wurin dinner meeting ɗin nan, ko tace dinner party, ita ta ganshi lokacin daya shigo da mugun ɓacin rai amma shi bai ganta ba, tayi saurin buya domin haka kawai taji bata son ya ganta a wurin. Tana tsaka da wannan tunanin ne taji anyi wani mahaukacin hong me ƙarfi, wanda ya saka ta saurin mikewa gabanta na wani irin mugun bugawa tace. "Innalillah wa'inna ilaihi raji'un ³ me ke faruwa kuma yanzun?" tayi maganar ne kuma tana mufar window na ɗakinta, abinda ta gani ba ƙaramin taɓa ta yayi ba. Wasu lafiyayyun manyan motoci ne har guda uku duka black masu ɗauke da glass tinted, Kuma gaba daya sun tsaya ne a harabar gidan nasu. Zuciyarta ta buga da ƙarfi don ita duk a tunaninta ko yan fashi ne ma.
“Ya ALLAH…”
TA faɗi tana dafe zuciyarta tana kuma ja baya a mugun tsorace, domin dama yau wuni suka yi labarin manyan barayin da har da rana tsaka ma shige duk inda suke so suke suyi fashinsu kuna su fito lafiya, saboda tsabar karancin tsaron dake tattare da kasar tamu. A kuma daidai lokacin ne
ƙofar ɗakinta ta buɗe da ƙarfi, wanda ya sakata wani irin mugun firgitan daya sakata fasa ƙara a tunaninta barayin ne suka iso. Amma ganin mahaifiyarta ce ya ɗan sanyaya mata rai sedai ita ma Mamyn fuskarta cike take da tsoro me tsanani. "Momy me ke faruwa a gidan nan ne wai?" Hannunta Mamyn ta kama tana ce mata ba lokacin taja hannunta zuwa bangarenta data ɓoye Husna. A can waje kuwa cike da isa aka budewa Madame Victoria mota ta fito tana wani huhhura hanci sama, daga inda take tsayen ta ɗaga kanta idonta ya sauka kan gidan. Sai tayi murmushi mai mara ma'ana tare da furta.
“So… this is where she lives…”
Gaba ɗaya gidan ya cika da ruɗani
Servants na gudu…guards na fita waje…
Ambassador Kabeer ya fito cikin gaggawa yana tambayar “Wane ne a wannan lokacin?!” ya faɗa cikin murya mai cike da iko daidai lokacin da da kofar ke buɗewa. Madame Victoria Osteen ta bayyana cikin takunta ɗaya bayan ɗaya mai cike da izza da kuma
iko…kamar wacce ta mallaki duniya.
Taja ta tsaya a tsakiyar parlour tana ƙare masa kallo kafin idonta kai tsaye ya sauƙa akan Yasmine da fitowar su kenan da Mamy. Wani irin shiru mai nauyi ne ya dan ratsa parlourn kafin ta ɗan karkata kai ta murmusa tana me furta.
“So… you are the girl.”
YASMINE kuwa ganin da wacce idon ta suka mata tozali ne ya saka zuciyarta bugawa… amma kuma hakan be nuna ta tsorata ko a fuska ba, sema dubanta da tayi ba tare da tsoro ko shakkun komai ba tace. "Me ya kawo ki gidanmu? ko a tunaninki nan ɗin ma kin zo ne kiyi baraza wa ahalina tunda kin kasa ja da ɗan da kike ikirarin cewar naki ne?..."
“Kin san ko wace ni ce, Kana ina son ki sani nazo gida gaban iyayen ki ne domin su farga da wuri, ba sai sun rasa ki suzo suna kukan rashi ba?”
Ɗan gyara hannunta data nade a kirjinta Yasmine tayi, ta re da ɗan murmusa kaɗan mai ɗauke da raini tace. “Wacce take tunanin duniya mallakarta ce… wacce girman kai da izza suke hana mata gane gaskiya.... Sai kuma ta ɗan dakata.
“Sai dai kuma ki sani kin makaro!, domin wannan zuciyar a yanzun ma ta sama kwarin gwiwwarta na ci gaba da ƙaunar abinda take so, ina son ki sa a ranki cewar nie Yasmine diya ga ambassador so na shayar dake mamallakin da zata ko tsammaninki bai taba baki ba right?..."
Wani irin shegen shiru ne ya hade wurin Servants ɗin dake tsaitsaye suka kalli juna. Ambassador ya ɗan motsa
amma ya tsaya be ce komai ba, don yaga
yarsa tana tsaye da ƙarfinta.
Ahankali Madame Victoria ta matsa kusa sosai da Yasmine har numfashinsu na haɗuwa tace.
“Ki saurara sosai…”
Ta faɗa cike da ikon dake dauke da mugun gargadi tace.
“Ki nisance ɗana.”
Wani kallo Yasmine ta mata tare da cewa, “Ko idan aka ki nisantar nashi me zai faru?” ta jefa mata tambayar kai tsaye, wanda ya saka Madame Victoria ta ɗan yi dariya irin ta shegun da suka jima a duniya tace.
“Zaki lalace tabbas.” ta dan dakata tare da sake kallonta da idanunta masu kama dana mashaya tace.
“Zan lalata rayuwarki… zan sa ki nemi mutuwa… amma ki rasa wannan kadan kenan idan har baki nisanci dana ba.”
Husna ta dafe bakinta da duka hannuwanta, Mummy ta matsa kusa da Yasmine amma Yasmine din ta ɗaga mata hannu, alamar kowa ya tsaya.
Sai ta matsa gaba kaɗan idanunta da su kayi ja ta ta zubama Madame Victoria tace.
“Ki zo ki lalata nin na ga ni.”
ta faɗa a hankali tana fesar da wani abu me kama da bacin rai taci gaba da cewa.
“Se dai ki sani… ni ba irin yaran da kuke tsoratarwa bane.” Wani irin shiru ya sake sauka a wurin. Madame Victoria kuwa mutuwar tsaye a wurin tayi tana kallonta kamar me na zartar halaye ko dabi'unta. Kafin a hankali ta janye tana dan sakin murmushi tare da tafa hannayenta tace.
“Good…”
ta faɗa tana sake tafa hannayen nata.
“Ina son ƙalubale.”
Daga haka ta juya ta fara tafiya, seda takai har baƙin kofar fita ta ta dan dakata. Ba tare data juyowa ba se dan kada hannunta da tayi suka bada wani sautun ɓass kana tace.
“Let the game begin.”
Ta saka kai tana ficewa zuwa inda
Motocinta ke fake ta shige suka bar gidan cike da wani irin mugun kudiri a cikin rai da ruhinta.
Suna barin wurin Mamy ta isa ga YASMINE cike da wani irin tashin hankali tace. "YASMINE me kike yi haka?, faɗa faɗanma kuma da Christian, ina kika san wannan matar wacce da gani bata san ko miye imani ba, and Waye dan nata da take ta ikirari a kansa?"
"JOSEPH" furta a fisge tace. "Kwarai da gaske matuka na kamu da mayen SO da KAUNARSA Mamy...."
Numfashin Mamy ne ya kusa fita da ƙarfi amma tayi hanzarin tare shi, tana bin Yasmine ɗin da kallon baki da hankali?, ba kuma kisan abinda kike shirin aikatawa ba, ta bude baki kenan za tayi magana Daddy ya daga mata hannu yana dubar Yasmine ɗin da Husna yace kowa yaje ɗakinsa...
♡
JOHN dake zaune cikin motar daya dakko ya fito bayan yaga fitar mahaifiyar nasa ne ya sauƙe wani nannauyan numfashi, domin tun daga lokacin da yaga mahaifiyar nasa a wurin aikin Yasmine ɗin ya saka mata bi diddigi. Yaji komai Yes… yana saurare, wani ɗan rufe idonsa yayi amma kuma daya tuna da irin maganganun Yasmine ɗin da yaji ta faɗi har besan lokacin da kyakkyawan murmushi ya bayyana a fuskarsa.
Ya wani dafe kirjinsa yana me furta.
"Just because you love someone, doesn't mean they feel loved by you.
You know love is an action. Love is a verb.
It's not enough to just say it.
If you really love someone.
You'll do the work to make.
Sure that they feel it from you too...."
Ya kai ƙarshen maganar yana wani lafewa jikin kujerar motar....
*BY AMMEY LAYLERH ✍️
08104493215
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 21
Paid book
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
♡♡♡♡
ꨄ
Cikin one week kawai sega Yasmine da John sun fara sabawa, duk da ba wata magana me zurfi ce ke haɗa su ba, gashi kuma yana shirye shiryen komawa bakin aikin sane, kuma har tsayin wannan lokacin be nuna mahaifiyarsa komai dange da gidan su Yasmine ɗin da taje ba. Yau tun farar safiya aka tashi da hadari amma ALLAH be kadarta ruwan ba se yanzun da yamma take list, har kamar ma ana gaf da kiran Sallah, se dai a zahiri kuma lokacin bai kara soba, dan da ƴar sauran tafiya ma.
Ruwa ake kamar da bakin ƙwarya wanda ruwan yau shi ya hana John fita ko ina, yana bedroom nashi bai yana tunanin ta yadda ya kamata ace ma ya ɓulloma lamarin. Ƙarar da wayarsa ta dauka ne ta dakatar dashi dole daga duniyar tunanin daya lula, wani kasaitaccen murmushi ne ya kubce masa ganin ko waye me kiran, yau shi ne karo na biyun data taɓa kiransa ita da kanta, tun bayan da sukayi exchange number. “Yas-mine!?…” ya ƙira sunanta cikin murya mai laushi. Daga can bangaren Yasmine kuwa, seda ta ɗan fesar da wani numfashi me dumi tace.
“John… ina kan titi. Motana ta tsaya driver ya tafi zai nemo mai gyara amma ya daɗe bai dawo ba. Ga ruwa, ga uban duhu… I'm scared,” ta faɗa cikin murya shagwaɓa mai ɗauke da tsoro. Ahankali ya tashi zaune daga kishingidar da yayi cikin taushin murya yace. “Wani titi kike?” ya tambayata kai tsaye yana mikewa, kwatancen inda take ta masa ya fita dake ruwa ake yasa kowa yana ɗaka a lafe babu wanda yaga fitan John ɗin. Cikin mintuna talatin da biyar, ya iso wajen duk da iska mai ƙarfi da ruwan da ke hana gani sosai. Wanda garin ya fi farko duhu mai nauyi tsabar ruwan da ake tsalawa. Da ƙyar ya hango motar nata, Ta buɗe masa ƙofa ya shiga.
“Sorry, Yas-mine!… ruwan ya tsananta sosai. Are you okay ma?” ya tambaya da damuwa a fuskarsa wacce so ya gama cinyewa, “I’m fine… yanzu da ka zo,” ta amsa tana kallonsa da wata nutsuwar da haka kawai taji tana jin ya kamata. Ɗan murmushi kawai yayi yace.
“Mu tafi na sauke ki gida”
Ta gyada kai suka fito ya cire jacket ɗinsa ya rufe mata kai da shi saboda ruwan ga kuma sanyin sa garin ya dauka, Suka nufi motarsa.Duhun wurin da ruwan da ke sauka ya sa Yasmine ta matso kusa da shi sosai saboda tsoro.
John ya fahimci hakan, sai ya ɗan tsaya ya ɗauke ta a hankali ya kai ta cikin mota duk da bata so ba. Suna shiga suka rufe ƙofar dukansu sun jike, amma John bai damu da hakan ba hankalinsa gaba ɗaya yana kan yadda zata ji lafiya.
Ya kunna motar amma gani ya yi ba zai iya tuƙi da kyau ba saboda tsananin ruwan. “Zan tsaya nan kaɗan… sai ruwan ya lafa,” ya faɗa yana ajiye motar a gefe duba da cewar shi pilot ne, kuma a dokance duk pilot baya taɓa tuka mota, Idan kuma aka kama shi da laifin hakan hukunci ne me tsanani a kansa. A hankali ruwan dake jikinsu ya fara ratsa su yana haifar musu da wani mugun sanyi, “Yasmine…” ya kira a hankali yana sake miƙa mata jaket ɗinsa dake gaban motar ajje. Ta sake amsa ta rungume jikinta da shi, shiru ya ratsa tsakaninsu. Duhun wajen, sautin ruwan, da ƙarar iska duk sun haɗu sun ba yanayin wani irin nauyi.
“I’m scared,” ta faɗa ahankali kuma ƙasa ƙasa, “Ba komai… ina nan,” ya bata amsa da nutsuwa. Ta jingina kaɗan kusa da shi not ba dan saboda wani abu ba, sai don ta samu kwanciyar hankali.
John ya kame kansa sosai, yana ƙoƙarin ya kiyaye nisan da ya dace, bai so ya wuce iyaka ba domin ita ce da kanta ta dokan ta masa iyakokin. Yanayin wurin ya sake ɗaukar shiru duk da cinkoso irin na garin Lagos, sun jima sosai a wurin kafin ya tada motar su tafi, har cikin gidan ya shigar da motarsa ya sauke ta ya rakata har kofar shiga kana ta ɗaga masa hannu tana masa bye bye ta shige shi kuma ya juya ya tafi. Washegari Joseph ya tashi da mummunan zazzafan zazzabin da iyayen suka san tabbas ya bari ruwan sama ya dake shi kenan?, hankali tashe suka yi asibiti dashi don ko wanne irin kuzari baya da, shi kansa yasan illar da dukan ruwan ke masa amma kuma ya fita din cikin ruwan. Kwanansa biyu a asibiti kana suka dawo gida, yaki ma kowa magana duk kuwa da uban tambayar da ake masa. Wani ne daga cikin guads din gidan ke sanar ma da Mademe Victoria ai ranar fita yayi a mota, shi kuma ya bi bayansa ba tare daya bari ya gan shi ba, don ba motar gidan ma ya bi bayansa ba a napep ne. Daga nan ya bata wayarsa ta fara kallon hotunan da aka ɗauke su cikin motar, da lokacin da yake cire jacket na jikin sa ya rufa mata, da lokacin daya dauketa din nan tayi saurin dago ido a tsorace tana kallonsa. Wani yawu Madame Victoria ta hadiye da taji ya mata wani shegen daci a makoshi.
Bangaren Yasmine kuwa… lokacin da yake suke isa gidansu ta ce banda kiranta, banda kuma tura message ko mata magana WhatsApp. Amma kuma kwana biyun da bata gan shi ba duk se taji