Advertisements
Chapter 27 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   27 / 31

78K to 81K   out of 91.1K words

fa tana asibiti…”

“What happened?”

Ya tambaya da alamar damuwa a fuskarsa. Papa ya ɗan busa iska cikin takaici yana kallon Mahaifin Yasmine dake basu wurin zama. Wani kallon ƙasƙasci PAPA yama duka parlourn cikin tsananin fushi ya ce.

“Bani da abin zama a nan!”

Sai ya nuna IBRAHEEM da yatsa.

“Na zo daukarsa ne.”

A hankali IBRAHEEM ya sauke numfashi tare da furta.

“Bazan koma ba.”

Nan take idanun PAPA suka sake yin ja.
“Saboda ita?!” Ya fada yana nuna YASMINE cikin tsawa.

“Saboda rayuwata.” Ibraheem ya furta yana jin wani abu na taso masa game da wannan kutsen da suka masa.

Sheik Auwal ne ke kallon su gaba ɗaya cikin nutsuwa irin ta manyan malamai kafin daga bisani ya ce.

“Mr. Deefer…”

PAPA ya juya yana kallon sa, shi kuma ya dan fesar da wani numfashi kana ya ɗora da faɗin.

“Ɗanku mutum ne babba. Kuma idan ya zaɓi addininsa da rayuwarsa… bai kamata ku tsane shi ba.”

“You know nothing!”

Papa ya katse shi cikin tsawa tare da juyawa yana kallon IBRAHEEM yace.

“Zan ga kuma inda addinin da kake ikarin gaskiya ne zai kaika....”.

“Wasu sirrukan ba a ɓoye su don a kare duniya... Amma ana iya ɓoye su ne don a kare zuciya guda ɗaya daga rushewa.”

Dum gaban Papa ya faɗi, saboda jin wannan kalmar data taɓa kamanceceniyar da aka taɓa faɗa masa shekarun baya, “Zan kawo ƙarshen komai dole...” ya fadi daga haka ya juya yana barin wurin bodyguard nashi na rufa masa baya suka fice.

Ambassador Khabeer ne ya sauƙe ajiyar zuciya tare da kallon Sheik Auwal Albani yace.

“Ni dai magana ɗaya zan yi. Idan wannan yaron har ya iya barin dukiya saboda addini… toh ina tabbatar muku bazai cutar da yarinya ta ba.”

YASMINE ta runtse idanunta hawaye na cika mata su .Sai dattijon ya juya yana kallon Ambassador tare da masa godiya. Ba komai yace yana sake nanata masa kalmar.

“Aure kam za’a daura shi In sha ALLAHU.”

“NEVER!” Gaba ɗaya haka suka jiyo muryan PAPA daya dawo ɗaukan jar sandarsa daya manta.

IBRAHEEM ne ya ɗan taka gaba yana kallon mahaifinsa ido cikin ido ya ce.

“Ko duniya zata ƙi ni…” ya furta cikin kwanciyar hankali. “…bazan sake barin YASMINE ba.”

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215





*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 27

Paid book

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡

Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

♡♡♡♡

ꨄ Wani irin shiru mai nauyi ne ya ratsa parlourn bayan kalmar “NEVER!” ɗin da Papa ya furta. Ga Idanunsa dake cike da fushi sosai, hannunsa riƙe da sandar da ke rawa saboda tsananin tashin ɓacin rai. “Ba zai faru ba!” ya sake maimaitawa cikin ƙarfi. “Wannan auren ba zai taɓa faruwa ba matuƙar ina raye!” Ibraheem ya tsaya a wuri ɗaya, fuskarsa a nutse kamar komai baya damunsa a zahiri. Sheikh Auwal ne ya matso gaba a hankali cikin natsuwa yace. “Mr. Jeef Deefer…” ya faɗa cikin sanyin murya kafin ya ɗora da faɗin “Fushi ba zai magance komai ba. Wannan lamari na zuciya ne da kuma addini…” da hannu Papa ya katse shi cikin tsawa.“Ni ban tambaye ka ba!”
Ibraheem ya ɗan ɗaga ido, ya kalli mahaifinsa cikin nutsuwa ya furta.
“Papa…” Kalmar ta sa Papa ya tsaya cak na ɗan lokaci amma sai ya ƙara fusata.
“Kar ka sake kirana Papa!” ya faɗa a mugun tsawacen daya saka wani irin shiru ɗin ke wurin tsaf. Ibraheem ya sauke kai a hankali, sannan ya ce cikin murya mai nutsuwa. “Ko ka yarda ko ba ka yarda ba… ni na riga na zaɓa.”
Ya ɗaga kai ya kalli Yasmine ahankali tare da fara taka wa zuwa gabanta yace.
“Ina son ta. Kuma zan aure ta.”
Daidai lokaci da Jelly ta fashe da kuka wacce shigowar ta kenan a karo na biyu tana furta. “Joseph No! John A ahhh…Mommah tana asibiti saboda wannan abun!” Tun kafin ya sama zarafin magana cikin fushi Papa ya sake ce.
“Idan ka auri yarinyar nan… ka sani ka riga ka raba kanka da ni har gaban abada.” Fuuuu yaja hannun jelly suka bar wurin a mugun fusace yana dafe ƙirjinsa dake kamar zai ɓalle masa ko zuciyarsa ta fashe ƙirjin ya fito. Bayan wucewar sune Ambassador Khabeer ya kalla Sheik Albani yace ya ya kawo shaidu bayan an fito daga sallan zuhr kawai a daura auren. Hakan kuwa akayi yazo da wasu abokansa uku shima nan da shaidunsa aka hadu bayan idar da Sallah ga masallacin a cike yake taf liman yace kar kowa ya watse akwai ƊAURIN AUREN da za'a gudanar. Waliyyin da ambassador Khabeer ya tsayar ne a matsayin na YASMINE ya kalla Ibraheem yace. “Shin ka yarda?, ka kuma yi imanin amsar wannan auren, da zuciya ɗaya bada wata manufa ba?...”

“Idan hakan ne zai sa na tsaya kan gaskiya… to na yarda.”Wani irin shiru mai nauyi Masallacin ya yi tsit…
Sai ƙarar iska kaɗan da ke ratsawa a tsakanin mutane da kuma numfashin juna. Sheikh Auwal ya kalla Ibraheem cikin nutsuwa yana me ambatar.

“ALHAMDULILLAH!…”

Nam kowa ya sake nutsuwa Ibraheem ya sauke kai, hannunsa na rawa kaɗan amma zuciyarsa cike da imani. Sheikh ɗin ya kalli Wiliyyin Yasmine.
“Waliyyi ya ba da izini?” Waliyyin Yasmine ya yi shiru na ɗan lokaci… sannan ya sauke wani numfashi yana mai furta.

“To ALHAMDULILLAH a fara…”

Sauƙe wani nutsatstsen numfashi Ibraheem yayi yana jin samun nutsuwan abinda ya jima da toƙare ƙirjinsa na komawa ya kwanta. A wani irin natse Sheik albani dake matsayin waliyyin ANGO ya Isa gaban Waliyyin Yasmine cikin kamala da dattaku da kuma jin nutsuwar aikata abinda zuciyan sa ke umar tansa daya aikata ya furta. "NI SHIEKH MUHD AUWAL a matsayina na waliyyin ango ina mai nemawa Yaro na *IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL * Auren ƴarka _*HAUWA KABEER USMAN MAINA*_ a bisa sadaki Naira dubu Hamsin"
Wata irin Ajiyan zuciya da numfashi me ɗumi Ibraheem ya sake sauƙewa.
Shi kansa Daddy'n Yasmine ɗin wani daɗi yaji yana rufe shi har cikin ranshi da zuciyan sa, faɗar irin farin ciki da nutsuwar daya tsinta kam kamar wani ɓata baki ne ma.

Wani irin kwantaccen farin cikin gaske ne ke zagaye da kyakkyawar fuskar Ibraheem yana amsa addua tare da godiya ga ALLAH da shi ne kawai ya shirya wannan Auren. Ɗaurin auren aka fara gabatarwa cikin nutsuwa da haiba. Haka aka ɗaura Auren HAUWA KHABEEER USMAN MAINA tare da IBRAHEEM IBRAHIMUL KHALEEL akan sadaki dubu Hamsin. Zuciyarsa ce yaji kamar ana narka masa ita da tsananin farin ciki. “ALHAMDULILLAH…”
ya faɗa a zuciyarsa dake cike da fata da kuma burin zuwan wannan rana.

Washe gari kuma aka tashi da walima,na maza daban na mata ma haka, wacce tuni Mamy ta sanar ma da yan uwa da dangi se gashi har sun cika gidan, ALLAH Sarki Ya Omer lokacin da zancen auren ke isa gareshi seda wata hajijiya ta kusa zubar dashi, amma yayi ta maza ya maze. Haka Mahaifiyar Mamy ta iso itama tun a ranar kusan komai a gaggauce aka ma Yasmine ɗin, bayan ta ƙare mata tasss din taki auren jikan ta ta auri sabon tubar da bata da cikakken tabbaci akansa. Toshe kunnuwanta kawai tayi sema kokarin maida hankalinta kan party ɗin da suka hada ita da friend nata da tayi. Kwana uku ran na huɗun aka karasa kimtsata da yamma aka mikata hadadden tsararren gidanta dake cikin anguwar Kabuga Jan bulo,kada kuso ganin yadda yan uwa suke zuba santin gidan Yasmine ɗin, duk da kasancewarsa ba wani tsararre ma amma kuma komai bisa tsari yake shi yasa ma gidan ya musu kyau sosai, wanda tuni komai na ciki an sauya an zuba mata nata sabo gwanin burgewa,bayan ƴan rakiyar amarya sun fara tafiya duka da yake dama ba wasu mutane ne na daban ba yan uwane kawai se makwabtansu. Manyan kawayenta biyu aka bar mata suka zaune tare da ita har dare, tara da rabi dadi IBRAHEEM ya shigo gidan shi da ɗan gidan Sheik Albani me suna Usman. Bayan ya sake musu nasiha ya debi ƙawayen Amarya ya wuce dasu, aka bar iyaka ango da amaryarsa kawai masu fata da burin suga sun mallaki juna.

*AUJARA JIGAWA STATE*

A wani irin mugun firgice matar dake bacci ta farka bakinta yana jeranta duk adda'ar da yazo bakinta.

"A'uzhubillahi minashshaiɗanir rajiiym.. Laa ilaaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn
Allahumma inni as’aluka sakinah fil qalb, wa rahat fid-dunya wal-akhirah!! Allahumma inni a’udhu bika minal-hammi wal-hazan!!!....”

Yanayin yadda ta farka da ɗin ne ya saka gumi keto mata duk uban sanyin dake cikin ƙayataccen bedroom nata.
Da sauri Magidanciciyar matar da shigowarta kenan bedroom ɗin ta nufo inda take fuskarsa cike da damuwa tana tambayarta "JANNEERH LAFIYANKI?...” Kirjinta ta dafe tana dago manyan idanun ta da yanayin su suke kamar na mai jin bacci ta kalla Mahaifiyar nata data zauna daf da ita rike da kafadunta. Kanta take ɗan girgiza mata idanunta kamar an soye mata su se wani irin uban zugin da suke mata ta girgiza kai, tana haɗiye wayun da take da tabbacin babu su da kyar ta makoshinta tana kallon Mahaifiyar nata
tana ƙirƙirar wani murmushi saboda ta ganin yadda hankalin Ummien nata ya tashi ta sake girgiza mata kai alamar babu komai. Ahankali Mahaifiyar nata tayj ajiyar zuciya tana kallon yarinyar nata cike da ƙauna tana riko hannunta ta sake jefa mata tambayar "What happened Dear?" Ɗan jim wacce aka ƙira da jannerh tayi tana tunanin abunda za ta faɗa ma Ummien nata, ce mata za tayi mafarkin namiji tayi?, ko kuwa zata ce mata na mafarkinta ta gani tare da wata macen a daren yau cike da Duhu da kuma Haske duk a cakuɗe dasu. A hankali ta lumshe idanunta kawai tace "mafarki nayi" Wacce aka ƙira da ummein ce ta sake yin ajiyar zuciya kafin tace "Ok! Ai kinyi adda'ah ko?, IN SHA ALLAHU nothing will happen" JANNEERH ɗin tace "IN SHA ALLAH" Mahaifiyar nata na kamo kanta tana ɗorawa kan Kirjinta wani irin tausayin ƴar nata na cika ta tana karanta mata.

“Hasbiyallahu la ilaha illa huwa, ‘alaihi tawakkaltu, wa huwa rabbul arshil
Azeeem.” cike da tsananin tausayi irin na uwa akan ƴaƴanta, bayan ƙaddarar aure, cikin year's ɗin nan kuma gaba ɗaya mafarkai take yawan yi marasa kan gado, wacce har zuwa yau ta gaza basu takamammiyar amsa akan irin mafarkin da take yawan yi ɗin. Mahaifinta MALAM MUHAMMAD ALIYU BAITA babu irin adda'an da bai mata ba, ita kanta tsaye take akan diga diganta amma ALLAH be kawo makarin abun ba. Duk da kasancewarta babbar malamar musuluncin da gaba ɗaya jihar ta ke ji da ita, kasancewarta gwana wajan lashe musabaƙar Alkur'ani ta ƙasa da ƙasa, ita kuma ta ƙara jawo kima da martabar jiharsu ta gasar duk shekarar da akeyi ta kasar Madina. Malamar dake sake nutsur da matan aure akan darajar da kuma martabar dake cikin aure duk da kasancewarta budurwa bame auren ba. Wacce kaddarar auren kuma ta hau kan tane sakamakon addinin da mazajen auren ke ganin kamar ya mata yawa, suna ganin ta yaya ne zasu iya fara fuskantar MALAMA HAFSAT da maganar aure?, wannan dalili yasa kowa ke gudun aurenta don gani suke kamar ta jima da wuce a jinsu, su kansu manyan makamai da Ustazan da zuciyoyinsu suke cike da ƙaunarta tsoron fuskantarta suke, saboda tsananin kwarjininta,Addini da haiba da kamalar da ubangiji ya mata, tana son AURE, tana son ta budi ido wata ran ta ganta a dakin MIJINTA koda na kara ne, sai dai mutane na ganin kamar wasa ne.

Sake shafo kanta ummey tayi cike da kwantar mata da hankali kamar kullum cike da hikima ta shiga faɗin.

“Ƙaddara ba ta tambayar ra’ayinka…
tana aiwatar da hukuncinta ne kawai,
duk kuwa gudun da za kayi ta yi to kuwa ƙaddara tana nan tana jiranka ne a inda zaka tsaya. Wani laifin ba naka bane ƙaddara ce ta shirya komai tun kafin a haife ka!, domin ita ƙaddara tana da hanyoyi masu ban tsoro…
amma a ƙarshe, tana kai ka mutum inda ya dace ne. Ina son ki dauka cewar ba duk wanda ya zo rayuwarka ne ya zo da gangan ba… wasu ƙaddara ce ta turo su domin su sauya ka har abada, abu guda nake son ki saka a ranki shi ne *WANNAN MA ZAI WUCE!*....” Idanunta taf da ruwan hawaye take gyadama Ummien nata kanta tana sake yarda da duk maganganunta, tabbas ta sani cewar.

_Kullum kowanne ɗan Adam yana rayuwa ne a yadda ƙaddara ta zaɓa masa, domin duk nunfashinka guda ɗaya yana sake kusantar dakai ne ga tarin ƙaddarorin dake nan suna jiranka.
Shi yasa a koda yaushe ake son ɗan adam ya kasance cikin bautawa ALLAH, ya kuma yi masa biyayya ya yawaita aiyukan alkhairi a rayuwarsa, adda'a da kusanta kai ga ALLAH ne kawai kan sassauta kaifin ƙaddara amma ba iya gudunka ko saurin kane ze fansheka daga cikin kaddarar data zabi rayuwa da kai irin haka ba._

Wata ajiyar zuciya me nauyi ta sauƙe bayan fitar Ummien nata ta sake to feta da adda'a. Zaune ta tashi a tsakiyar gadon tana dafe setin zuciyarta ita kadai ta shiga tambayar kanta da kanta cewar.

'Me yasa nake jin wani abu mai kama da ƙaguwa a raina! amma kuma ban san abin da nake nema ba?, Zuciyata na kuka da sunan da ban iya tuna shi ba…
amma na san yana da muhimmanci a cikin rayuwata tun da har ya kasance ina mafarkin sa babu dare babu rana.
Na rayu cikin kunci da zamewa abar zargi ga wasu zukatan, yayin da a koda yaushe murmushi na kawai suke gani wanda nake ara na yafama kai na na ƙarfin hali da kuma tawakkali da mika lamura ga ALLAH… amma gashi ayau a cikin jikina ina jin kewar abin da ban ma san ko me ye shi ba' Tsaye ta Mike tana a bayyane tana mai furta.

“Mai yasa nake jin wani abu na cin raina kamar akwai wani ɓangare na rayuwata da aka cire?, me yasa nake jin kamar akwai wani wuri da ya kamata in koma amma ban san inda yake ba?..
Ban san me yasa zuciyata ke kiran koma waye ba, amma duk lokacin da nayi mafarkinsa ina jin ƙaguwata na ƙaruwa, me yasa kuma yau nake jin kamar wani abu me kama da rauni na kokarin kama ni a kan ka? Why duk da ban san ka ba. Amma zuciyata tana jin kamar ta daɗe tana jiranka why? A Ina ka makale daka gaza isowa gareni tsayin shekarun nan?....” Sai kuma ta saka tafukan hannayenta biyu tana rufe fuskar ta, saboda ita kanta ji tayi tana jin nauyin kanta, wasu hawayen da suka zubo mata ta sharce tana cewa.

“Na tsorata da irin yadda nake buƙatar ka alhali ban san dalilin hakan ba. Akwai wani abu a cikin raina da ke motsi…kamar sirrin da ke neman fita.”

Ta sake matse jikinta wuri guda taci gaba da faɗin. “Na fara jin tsoron kaina…saboda zuciyata tana tunanin abin da kwakwalwata ta manta. Me yasa wasu lokutan nake jin kaina kamar
akwai wata rayuwar dana taɓa fuskanta a baya?, Nasan kuma hakan shima duk yana cikin jerin Ƙaddarorin dake kirana…amma ban san sunan da take kirana da shi ba...”

Ta dafe ƙirjinta da hannuwanta duka biyun…zuciyarta na bugawa da wani irin raɗaɗi mai zafin gaske, ba ta san abin da take nema ba amma sai take jin kamar ta rasa wani abu mai girma ne cikin rayuwarta. Ahankali ta mike ta faɗa toilet babu jimawa ta fito fuskarta ɗauke da damshin ruwa alamar alwala ta dauro, nan ta shiga jera nafilfulun da suka ƙarasa janta tsawon daren. Bayan ta idar ta lumshe Idanunta cikin wani irin ƙira'ar da indai kaji duk rashin imaninka sai zuciyarka ta rusuna ko bata girgiza ba, wani irin sautin laffuzane ke tashi cikin ɗakin wanda ya saka komai nutsuwa a lokacin, wasu zirarayen hawaye na biyo shatin gefen idonta dake rufen. Tana zan zaune har aka ƙira sallar subhi, bayan an idar da sallar ta faɗa toilet a gurguje ta watso ruwa ta sanja kaya ta fito cikin ƙaton himar nata, hannunta ɗauke da jakarta da tarin litattafanta ke ciki. Ɗakin mahaifiyar ta ta fara nufa ta gaida ta kamar babu abinda ya faru, ta san Baffa baya gida don ba lokacin shigowar sa bane, kamar zata wuce sauran matan Baban nata amma kuma zuciyar ba zata iya ba taje ƙofar ɗakin tsakiyarun ta ɗan ɗurkusa daga bakin ƙofar ɗakin tace. “Mama barka da asuba, mun tashi lafiya..” kamar babu kowa a dakin haka aka banzatar da ita kafin kuma daga ƙarshe kamar wacce a fusace aka amsa.
“Lafiya...” kawai da wani guntun tsaki. Haɗiye abinda ke taso mata tayi tana nufar ƙofar ɗakin Anty Amarya. Ita din ma dai a fusgen ta amsa da lafiya ɗin yaronta me Halifa daga can uwar ɗakan uwar yana cewa. “Anty Hafsa Don ALLAH gani nan” amma uwar ta katse shi a tsawace tana cewa zata fashe masa baki in bai dena shiga sabgar wannan guzumar da taki auruwa ba. Makut haka taji wucewar wani abu cikin ranta ta mike tsam tana cewa ya sameta Islamiyyar.

*IBRAHEEM *

Washe gari yana zaune daga gefen gadon yana kallon Yasmine, zuciyarsa cike fal da tarin tambayoyi amma ya hana kansa yin ta. Saboda yana tsoron amsar ƙadan yaja idanunsa a hankali ya rufe yana gaya wa kansa

“Komai zai daidaita…”

Yana kallon hakan a matsayin hawalar da tasha a daren jiya ne ya saka ta kasa tashi har zuwa yanzun, juz'i amma ɗin dake hannunsa ya koma yana ci gaba da karantawa. Fita yayi babu jimawa ya dawo musu

27 / 31