Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
koma tace tana kanyi akan yasmine amma abubuwa sake taɓarɓarewa sukeyi. A hankali wasu hawayen masu raɗaɗi suka silalo mata saman kumatu, ta saka bayan hannunta tana kwace wa tace. "Kai ba uba na gari ba ne Khabeer!, kai ba irin uban daya dace tun farko a zaɓa bane domin maimakon ka tayani tarbiyan da yaran sema tufkar da nake ta ƙoƙarin tufkewace kai kuma kake min warwara daga baya ngd kwarai da gaske, amma ka sani na gama zaman aure dakai wllh, maza kayi gaggawar biyoni da takardar sak.... Ai tun kafin ta ƙarasa suka ji an fasa wata uwar ƙara da kururuwar daya saka su kallon inda ihun da ƙarar suka fito ban da Mamy kawai, a guje Husna, Daddy, Omer ɗin suka yi kan yasmine ɗin dake gangarowa daga saman bene, wacce fitowarta kenan gaba ɗaya kunnuwanta suke jiye mata waɗan nan muggwan kalaman. Idan tace hankalinta be tashi ba toma tama uwar data haife ta ƙarya, duk yadda takai da rashin kirkinta tabbas tana ƙaunar mahaifiyar nata, kawai abinda ta ɗauka abinda take mata wata ƴar takurawace da rashin son ganin rayuwarta taci gaba. Amma kuma yau taji abinda ya girgiza duniyarta, Husna ba ƴar gidan Daddy'n ta bace?, to yar gidan waye?, ita dai tana da wayon da tasan lokacin da Mamyn ke ɗauke da cikin Husna ɗin, kuma tana da wayon da Mamyn nata ta haihu to ta yaya Husna ɗin ta zama ba yar gidan Daddy'n nasu ba, kai ina wannan ma bame iyuwa bane makaran kunnuwanta ne suka jiyo mata ba daidai ba, amma kuma kalmar takardar sakin da Mamyn tayi niyar faɗin ne ya kusan tashin kiyamarta. Da Wannan tunanin taci gaba da gangarowa har Husna data riga kowa isa ta tare ta ta faɗo saman jikinta, daidai da lokacin da Mamyn ke isowa a fusace ta janye Husna daga jikin yasmine kafin ta juya ta kalli Daddy'n tace. "Alhamdulillah ko yanzu naga irin tarbiyar da ka ba Yasmine tayi rana, tun gashi nan ta kamu ta ƙaunar ARNE!!!....." Cak Daddy yaji zuciyarsa ta tsaya na ɗan wani lokaci numfashin sa ya kusan sarƙe maƙoshinsa. Itama a ɓangaren Yasmine ɗin Cak ta dakata ɗin, why Mamynta tasan da maganar?, tuno shashncin da tayi a daren jiyan ya saka ƙirjinta bugawa, fuskarta daga gefen idonta ya fashe, da gefen bakinta amma duk da se da ta yunƙura ta mike amma babu shiri ta koma zaune, sakamakon azabar da taji daga ƙafafunta alamar taji rauni sosai, da rarrafe ta isa ga Mahaifiyar nata cikin muryan kuka tace. "Mamy don ALLAH ki gafarceni ki yafe min..." A fusace ta janye ƙafarta tana ɗauke fuskarta da wani irin marin da kowa seda ya rumtse ido yana kuma riƙe fuska. Fuuuu taja hannun Yasmine zuwa sama don ɗaukar hijjabarta, tana nufar saman Daddy'n da jikinsa ke wani shegen rawa yayi saurin mara mata baya tana shigewa ya kulleta ta baya. Yin duniya tayi ƙofar ta buɗe taki a fusace ta nufi ɗaukar wayarta sedai tana tunowa da ashe ta barta a parlourn, zama tayi gefen gadonta tana jin kamar ta fasa ihu. Gaba ɗaya daga can ɓangaren Daddy ya haɗa uwar zufa se famar kaiwa da komo yake hannunsa goye a bayansa, gaba ɗaya yana jin be taɓa shiga tashin hankali makamancin haka ba tun da uwarsa ta haife sa. Shi kuma Yaya Omer shi ne ya tafi da yasmine asibiti. Gaba ɗaya se gidan ya koma wani irin shiru hatta masu aikin gidan duk sun shiga taytayinsu saboda halin da gidan ke a ciki. Da haka Daddy'n ya lallaɓa ya ma fi ce a gidan zuciyarsa na sake ɗaukar ɗumi. Koda suka dawo daga asibitin sashen Mamyn duk suka nufa dama kuma sun san a rufen yake, cikin tausasa murya Omer yayi ta bata baki akan ta ƙara hakuri akan wanda take kan yi, sai Ubangiji ya bata ladan ibada, kuma ta dena ma Yasmine ɗin kuka ko zuciya ta ɗebe ta ta mata bakin da ba iyaka ita kaɗai ba suma se sun shiga uku. Cikin fusata daga bedroom ɗin da take tace. "Na jima ban yi mata bakin ba dan ubanka kai ma Omer mara zuciyar nan, kuma wllh ka sani daga yau na haramta maka maganar aure tsakaninka da wannan mara tarbiyyar, tun da Annabi Sallallahu alaihi Wasallama da kansa yace muwa ƴaƴan mu zaɓen uwaye na gari,to ni kai na da nake matsayin mahaifiyar yasmine na shaida cewar bata gari bace..." Kanta take jujjuyawa daga inda take zube fuska manne da bandage Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un take son ganin ta kama tayi ta maimaitawa amma kuma harshenta ya mata nauyi....
Gaba ɗaya dai yau yinin gidan babu daɗi. Cikinsu kuwa har da yasmine dake dake zaune daga bakin bedroom ɗin mahaifiyar nata itama anan ta wuni, Daddy se yamma ya dawo gidan ko abinci se da Ya Omer yayi da gaske ta samu taci. Ta jikin window'n ɗakin ya leƙa shima ya dinga bata baki yana sake bata hakuri da Husna wacce tayi ta ma Mamyn roƙon ta faɗa mata wacece ita amma ta daka mata tsawa tace ta sake mata wannan tambayar seta ɗauke shashar fuskarta da mari, jikin window'n ta matso tace "DADDY don girman ALLAH ka gaya min wacece ni Mamy taƙi min magana har yanzun..." Shima tsawar ya daka mata yace ta masa shiru haka nan. Sema wayarsa daya miƙa mata yace ta miƙawa Mamyn, kin amsa tayi dake a handsfree yasa wayar ya saka na cikin wayar daka tsawa yana cewa. "Khadijah way me yasa wani sa'in kike da baƙar zuciyane?,akan ɗan abin da be taka kara ya karya ba har ki buɗi baki kice mijinki ya sake ki ashe baki da hankali?, to wllh ko da wasa na sake jin zance irin haka zaki ga hukuncin da zan miki kuma ki jirayeni ina nan shigowa Lagos ɗin ma ɗan ubanki, tun ni kaina nasan idan wannan baƙar zuciyar taki irin ta kafiran farko akan riƙe ra'ayi idan ta motsa kowa baya ganin da kyau..." Cikin muryan kuka ta katse ƙanwar mahaifiyar da a yanzun ita ce matsayin mahaifiya a gare ta ce... "Addaya kimin uzuri amma Wllh ba laifi na bane, Khabeer ya gama ƙure iyaka hakuri nane akan Yasmine,kin kuwa san girman saɓon daya saka na aikata?, mugun son kansa ne ya sa yau baki na harya suɓuta gaban yara na furta ce masa Husna ba ƴar sa bace..." Daga can cikin wayar aka kwafe da cewa. "Kuma se me dama ai ba yar tashi bace, dan tun farko ƙin kine, shi yasa nace kina da baƙar zuciya wllh Khadijah da tun farkon kin bayyana ma Husna ɗin ba kune iyayenta ba ai da duk hakan bata faru ba, kuma ke da a wannan zamanin ma uban wa yace miki ana irin wannan karar da zaki riƙe ɗa har ya koma ga ALLAH ba zai san ba ku kaka haife shi ba ai zamanin ya sanja, dama nasan dole ranar hakan zata zo, wacce ke da bakinki ba sai wani ya matsa ki ba za ki bama FATEMEERH amsarta...." Ƙit ta datse wayar daga haka wacce ta jima ta faɗuwa saman gado sabo da subcewar da tayi daga hannun Husna ɗin, amma tsananin ƙarfin hali dana zuciyar da Husna ɗin ke da be sa yarda ta sume ba amma ta sake shiga mugun shock ɗin jin Mamyn ma ba tata bace, to ita wace?, wa ce ce ita?.... A sace Daddy ya buɗe ɗakin ya shigo ya buɗe baki ze mata magana ya saka ta daga masa hannu alamar bata buƙata don haka salin alin ya ɗauka wayarsa ya fice tun da yana da tabbacin babu inda ta isa ta fita yanzun.... Aka ce wai me hali baya taɓa fasawa kai tsaye bedroom na Yasmine ya wuce yaje ya sake lallashinta kana ya wuce samansa don watsa ruwa.
Kwana uku gidan ya kwashe baya cikin yanayi me daɗi ana huɗun kuma se ga zuwan Addaya gidan, wacce tun usili Mamyn ce ta saka mata sunan Addayar, dake haka kowa yake ƙiranta Adda a lokacin harda mahaifiyarta kafin ALLAH ya mata rasuwa, to shi ne itama kuma se ta daddage tace mata Addaya, wai tana nufin Addata. Shi ne Addaya ɗin. Zuwan nan nata kuwa shi ya kawo ƙarshen komai, ta zaunar dasu gaba ɗaya har da Omer ɗin da tace ya tattara kayansa yau ɗin nan in sha ALLAHU zasu wuce Kano. Kasancewar hasalinsu yan can ne har Daddy'n,wanda shi kasuwanci da yawon siyasa ne ya dawo dashi nan Lagos ɗin zaman gaba ɗaya..... Hannun Husna dana Mamyn na cikin nata bayan ta huta dake zuwan wuri tayi, kuma ƙarfe biyar In sha ALLAHU zasu ɗauki hanya. Duk da Mamyn ta so ta tsaya tayi ko kwanaki uku ne amma tace lalalala bada ita ba. Cikin taushi da kwantar da murya take tausar zuciyar Mamyn da Husna har dama Omer bayan ta kawo bayanan ban hakuri dana kamar sake ta'aziya gare su ta fara da cewa.... "UBANGIJI yaji kan Fatimatul zahra, yasa halinta nagari ya bita, ya kuma sa aljannatul firdausi ita ce makomarta." Da Ameen duk suka amsa harda Husna da duk take jinta ba daidai ba. Cikin sanyi shiga basu labarin Fatima babbar ƴar ta da kusan tare suka taso ita da Khadijan (Mamy). Komai nasu a rayuwa iri ɗaya ne har ALLAH ya karbi ran yayarta Haj Fatima da itama Addaya ɗin tata fatimar sunan yayar nata ne ta saka mata, tashin hankali matuƙa sun shiga a wancan lokacin koma dai tace ta shiga akan mutuwar yayar nata, daga nan se riƙon Khadijan (Mamy) ya dawo hannunta da ƙarfin tsiya, don da dangin mahaifin Khadijah ɗin sun ce su ba zasu bayar da ƴar ɗan uwansu itama ta dage har dai suka haƙura suka bar mata. Don haka Fatimah da Khadijah suka taso a taro kamar yan biyu, dama kuma kusan komai nasu iri ɗaya ne ko lokacin da mahaifiyarta take raye, don haka komansu seya sake zama ɗaya. Har ta aurar dasu rana ɗaya. Sedai da wuri Fatima ta sama ciki saɓanin Khadijah, sedai har Fatima ta haifi ɗan ta namiji Omar Khadijah babu labarin ciki, wacce ita sam bata ma wani damu a ganinta tun da ƴar uwarta ta haifa musu ai shinenan. Seda Omer yayi 7 year's itama ALLAH be sake bata wata haihuwar ba, kwatsam kuma sega Khadijah da ciki wacce suka koma Lagos last year's. Faɗin irin zallar murnar ma da suke ciki a wancan lokacin to kamar ɓata baki ne ma su a wurinsu, a ɓangaren mijin ta kuwa cab babban hauka ne kawai be buga ba, amma yayi ɗan ƙaramin kam, don wannan cikin jin sa yake fiye da duk wani hasashen me tunani, wani abun mamaki kuma kuma shi da Fatima ba'a san wanda yafi wani ƙaunar cikin nan ba, don kusan kullum tana hanyar Lagos dake itama sun koma Abuja da mijinta. Haka har ALLAH ya sauki Khadijah lafiya wanda ta haihu gaban ƴar uwarta Fatima dake nurses ce itane ta amshi haihuwarta, se dai abu na farko ko nace saɓanin farko daya fara ratsa farin cikin haihuwar Khadijah shi ne Mijinta, don tazo masa da tsohuwar maganar da kusan suka yi alkawari tun kafin aure cewar duk randa ALLAH ya bata haihuwa indai macece yarta ta farko Fatima ce, a lokacin seya amsa ya kuma yi na'am da zancen har bayan aure takan tuna masa, amma kuma bayan haihuwar tazo masa da waccen maganar yace be san zance ba shi sunan uwarsa da bata jima da rasuwa ba ze saka wato Hauwa'u. Wannan abu shi ne matsala ta farkon da ta saka seda ni da kaina nayi tattaki tun daga garin kano har nan Lagos kamar rana irin haka bana mancewa. Na zo na rarrashi Khadijah tare da ƴar uwarta data nuna mata ba komai gaba seta saka ta In ALLAH yaso, yarinya ta amsa sunan Hauwa'u da ake ƙiranta Yasmine, tun daga haihuwar Yasmine gaba ɗaya hankalin Khabeer ya koma kan Yasmine. Sedai wata sabuwa tun Yasmine na yarinya idan tayi ba daidai ba irin na yara uwarta bata isa tsawatar mata se uban yahau sababi, itama data gane idan tayi abu ko baya nan daya shi go seta harhada cikin gwarancinsu na yara ta faɗa masa. Haka dai har ta girma kusan da shekaru sega Fatima da Khadijah na ɗauke da ciki. faɗin irin sabuwar murnan da muka tsinci kanmu gaba ɗaya bata baki ne, zuwa lokacin kuma Omer nada Shekaru sha biyu. Yayin da yasmine keda huɗu kawai a duniya, wannan karon kam dole Fatima ta matsawa mijinta Aminu suka dawo Lagos da zama sabo da samun damar ganin ƴar uwarta a koda yaushe, kusan a anguwa ɗaya. Rana ɗaya ciwon naƙuda ya kamasu sedai Khadijah tafi Fatima jin jiki, don haka Khadijah cikin mawuyacin hali take barma Fatima sallahun idan ta mutu ta sakama yar da zata haifa suna Fatima, ma'ana sunanta kenan, inda ashe ba haka abin yake kowa na nashi ne shi kuma ALLAH na nashi. Khadijah se ta riga Fatima haihuwa sedai dama abinda ta haifa be zo da rai ba, tsiransu babu nisa Fatima ta haihu sedai tana haihuwar kuma jikinta ya rikice jini ya ɓalle mata, babu jimawa tace ga garinku nan.... Innalillahi wa'inna ilaihir ³ mutuwar Fatima ba ƙarami tashin hankalinmu tayi ba, inda shi kuma mijin nata dake dama shi almajiranci ne ya kawo shi Kano ɗan asalin Jigawa ne ya tafi ɗauko ɗaya daga cikin danginsu Ubangiji shi ma ya amshi ransa, wanda shi ne ƙarasa rikicewar jikin Fatima jin ALLAH ya ɗauki ran mijinta, a lokacin da ake isa da Babyn da Fatima ta haifa tana canyara kuka irin nasu na jarirai wurin Khadijah. Kifeta kawai a ƙirjinki tayi tana fasa wani kukan da itama ya kusan wucewa da ita, se da tayi 3 day's bata san inda kanta yake ba. Mu kuma can muna can cike da tashin hankalin rashin sanin takamaiman dangin mijin Fatima, gashi kaf cikinmu babu wanda yasan inda taka maiman dangin nasa yake a Jigawa,inda a lokacin mijina yayi ta fafutar bi gari gari a Jigawa sedai be gano dangin mijin Fatima ba, a dawowarsa shi ma yayi accident ALLAH ya ɗauke nawa mijin nima tashin hankali iyaka tashin hankali mun tsinci kanmu a wannan lokacin. Farfaɗowar Khadijah take jin mutuwar Abbansu Abdullahi ta sake komawa doguwar sunar da saida ta sake ninka one week. Itama har mun gana fidda rai da ita, a lokacin Omer shi yayi ta aikin kula da jaririyar da ko takamaiman suna bata da, duk da dai uwarta Khadijah ta ƙirata da sunan ƴar uwarta Fatima, se bamu gama yanke sunan ba kuma kuma sake tsintar kanmu cikin wata sabuwar duniyar da mutuwar ta sake kawo mu. Dan haka kaf cikin dangina dana mijina babu wanda yasan hasalin waye mahaifiyar jaririyar dake raye, don haka muma dake a lokacin muna tsaka da tashin hankali na rashi yasa babu wanda na tara da wannan zancen, har Khadijah ta farfaɗo tace ita yar ta bata mutu ba dama can ALLAH yayi Fatima itace yarta. Banda mijinta se ni se kuma Omer babu wanda yasan ba Khadijah bace hasalin Mahaifiyar Fatima ba, wacce take kiranta da Husna, bayan lafawar komai har an ɗan ɗebi shekaru ma samu Khadijah da maganar ya kamata ko yaya ne Husna tasan labarinta amma Khadijah tayi kicin kicin harda kukan wai kawai so nake na nuna mata iyakarta akan Husna ni kuwa jin wannan magana yasa naja baki na nayi kitsim amma ni dama a raina nasan a wannan zamanin dai dole ko shi mijin wata ran se ya saka ka faɗi ɗan dake hannunka ba naka bane da bakinka gashi kuma yau ALLAH ya kawo mu ranan, bayan tazarar shekaru ɗai ɗai har shekaru goma sha takwas...
Da wani irin kuka da rarrafe Husna ta rarrafa gafan Mamyn tana sake rungumeta ta shige jikinta tana fasa wani kukan daya saka kowa kwallar tsananin tausayinta zubo masa harda Yasmine duk kuwa irin yacce take da ƙarfi zuciya. Cikin kukan take faɗin. "Wllh har zuwa gaban abada kene mahaifiyana Mamy ki gafarceni ki gafarceni idan na taɓa miki wani abu ba daidai ba, wllah tun da na taso ko daga ɓangaren Daddy'n Addaya ban taɓa fahimtar wani abu da ba daidai ba, na rantse da ALLAH duk iya kwakwkwafin mutum be isa gano waɗan nan bayin ALLAH ba sune hasalin iyayen da suka yi sanadiyar kawo ni duniyar ba, domin sune suka bani rayuwar, suka kuma bani tarbiyya me kyau, kuma ni ko abinda Daddy kema Aunty Yasmine wllh wani bin tausayi ne suke bani, wanda nasan hakan shi ne jarabawarsa, kuma nasan da yawa daga jikin family iren waɗan nan ababuwan kan faruwa don me zan fitar da wani tunani na daban a cikin rai na, wllh kunyi min komai Mamy Daddy kuma In sha ALLAHU kune zakuci gaba da amsa sunan iyayena,kuma kamar yadda maganar nan babu inda ta fita In sha ALLAHU ta zaunu kenan kawai abu ɗaya ne nasan naji daɗin sa ko babu komai zan yima mahaifiya na da mahaifina harma da Abba Abdallah adda'a...." Se kuma kukan da take yi yaci ƙarfin ta Ya Omer karonsa na farko yaja ƴar uwarsa jiki ya rungume sosai a jikinsa yana ɗan bubbuga bayanta yana ɗauke kwalla. Daga nan Addaya ta sake musu nasiha harda Daddy'n da gaba ɗaya jikinsa ya gama sanyi da yasmine wacce take jin In sha ALLAHU itama zata ƙaunaci ƴar uwarta kwatankwacin yadda iyayensu suke ƙaunar junansu, wanda dama tana masifar ƙaunarta kawai dai wani sanin kamar suna mata shishshigi a cikin rayuwarta ne ya saka take nesantasu cikin rayuwarta... Da haka Addaya ta fara shirin tafiya wacce dai taki yarda ta kwana ɗin har da Omer ɗin kuma suka tafi......
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 16
Paid book
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.