Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
zuciyar Yasmine.
Amma ta ƙi nuna hakan sema kallarta da tayi tace. “Toh ki gaya masa ya dena bibiyana dama wanda zan ba saƙon nake nema, amma fine tun da na hadu da gyatumarsa, nasan ke zaki fi kowa bashi gargadi me kyau!,.” ta mayar mata da maganar cikin tsauri. Wanda jin wannan maganganun ya saka Madame Victoria ta ɗan yi murmushi mai haɗari.
“Zan iya… amma ba haka nake so ba.”
Ta ɗan karkata kai tare ka kafe ta da ido tace. “Ina so ne… ke da kanki ki ɓace daga rayuwarsa.” Wani shegen haushi ne ya tuke Yasmine “So?” ta ɗan fesar da numfashi tace. “Ko me zai iya faruwa idan ban fita a rayuwan nasa ba?”
Madame Victoria ta kalleta kai tsaye tace. “Everything.” Madame Victoria din ta faɗi tana medai eye glasses nata. Ta juya daga haka zata shiga motar ta.
“HEY!”
Haka ta tsinkayi muryan John mai ƙarfi ta katse mata shiga motar. Kusan a tare Madame din da Yasmine suka juya suna kallon John dake tsaye idanunsa cike da wani abu me kama da wuta. Zuciyarsa na wani irin bugawa da ƙarfi ya kalla
mahaifiyarsa, kana ya kalla Yasmine.
“Mom… what are you doing here?” ya tambaya cike da fusata. Madame Victoria ta ɗan yi murmushi kamar ba komai me cike da munafunci tace.
“I should be asking you that.”Amma bai bi ta kanta ba kai tsaye ya matsa kusa da Yasmine yana me tambayan....
“Are you okay kuwa?” ya tambaya cikin damuwa. Amma Yasmine ta gaza kowacce irin maganama, domin wannan shine karo na farko da ta ga wani irin damuwa a idanunsa saboda Ita. Amma duk da haka bata nuna komai ba se ma cikin fusatar da tayi cikin ɗan ihu tace.
“I don’t need your help.”
Ta juya zata tafi John ya ɗan riko tsintsiyar hannunta wanda ya saka Yasmine tsaiwa cak. Ta juyo cikin ɓacin rai. “Let go of me!” Amma bai sake ta ba.
“Not until you tell me what she said to you.” Madame Victoria dake tsaye tana kallon wannan scene ɗin tuni idanunta har sun fara canza wa. Wannan ba abin wasa bane kuma, Ahankali Yasmine ta kalli hannunsa da ke riƙe da nata…
sai kuma ta ɗago ta kalleshi cike da tsauri tace. “Your mother is crazy.” Cak kusan gaba ɗayansu suka tsaya don da turanci ne tayi maganar, don haka baka jin komai sai bugun zuciyoyinsu da suke bugawa a kirjinsu. John ya ɗan matse hannunta bada yawa ba kafin ya zube mata mayun idanunsa a kanta ya furta.
“Don’t talk about her like that.”
Wannan karon muryarsa ta sauya.
Yasmine ta ƙara fusata sosai fiye da baya “Then tell her to stay away from me!” daga haka ta fizge hannunta da ƙarfi ƙaran saukar mari ya biyo baya ji kake tasss³, mari har uku a jere. Cikin fusata tace. “Ba na ce ma kada ka sake yarda ko hijjabana hannunka ya sake yunkurin taɓawa ba?, to ina son ka sani cewar indai a haka kake tunanin zaka gina SOYAYYARKA gareni Ina son ka sani ƙa ra sa ruguza komai hakan keyi Right and understanding?.....” Wani irin shiru ne ya kame wurin na ɗan lokaci, John dake kame tamkar gunkin da aka sassaka haka yake kallonta ya kasa kowanne irin motsi. Sema ci gaban da yayi da kallonta tana fidda wani huci kamar wata za kanya. “Ka fita daga rayuwata.” ta sake faɗa da ƙarfi kafin ta juya ta tafi ba tare da waiwaya ba.
Madame Victoria ta ɗan yi murmushi a hankali…amma a zuciyarta wuta ce na marin da aka ma dan nata me kama da tozarci. Amma kuma a wani bangaren dadi take ji ta san ko babu komai dole ya hakura da Hausa gul din nan dolen dole, a cikin zuciyarta tace. “Toh… haka ne kenan…” ta furta a hankali tana jin wani abu me kama da samun sassauci.
John kuwa…ya ɗaga kai a hankali yana kallon sama idanunsa sun canza gaba daya. “I won’t stop…” ya faɗa a hankali.
“Not now.” ya faɗi yana kaima iska naushi kafin ya nufa motarsa Mecheal na bata wuta wanda dama ganin Madame Victoria din ne ya sa bai fito ba, don shi ya nuna mata Yasmine ɗin ya kawo ta har wurin aikin nata a jiya.
★
Daddyn India ne da kansa yaje ya dawo John din gida, inda Madame Victoria tayi gum da bakinta taki sanarma kowa labarin abinda idanunta suka gane mata, amma Papa’nsa yasan da maganar Muslim girl ɗin da John din ke so, sedai baya da labarin abinda ke faruwa daga iyaka haka nan. Ga mugun sanya idon da aka masa kamar wani ragon da ake son tirkewa, Ba a daɗe ba gidan ya fara sauyawa gaba daya, bada
hayaniya ba, ba da faɗa kai tsaye ba. Don Daddyn India ma da dawo ba sosai ya fiye fitowa babban parlor ba sun fi gane kowa yana nasa bangaren. Gefe guda uwar Amarya Deepika wato Lady Rebecca, ita kanta wata macece da kamar ma taso tafi Madame Victoria jiji da kai, sedai tasu tazo ɗaya sosai amma kowa na hassada tsakaninsu da ci gaban da wani ya samu. Ahankali ya sauko jin gidan babu hayaniyar komai yau din, a dining ya tarar da iyayen nasa, a natse ya zauna a dining table ɗin, iyaka papansa ne se kuma Madame Victoria se Jelly me bi mishi kenan. Suna dinner nasu a natse babu wanda ke magana cikinsu saboda ganin yau din su kadai ne ya saka Madame ba Papan labarin abinda ya faru ranar. Madame Victoria ce fara ɗaga kai a hankali ta kalleshi
“Joseph…”
Ta kira sunansa cikin nutsuwa.
Ya ɗago ba tare daya kalla inda take ba ya furta.
“Yes, Mom.”
Ta ɗan yi shiru na daƙiƙa ɗaya kamar tana nazarin fuskarsa, cikin son danne komai dake son taso mata tace.
“Ka canza.”
Kai tsaye wani shirun ya sake ratsa wurin kafin ya saki murmushin da yaba kowa mamaki yace.
“People change.”
Tare da ɗan ɗaga gira ɗaya yana ɗaukar glas cup yakai bakinsa.
“Not like this.”
Papa’nsa ya ɗan kalleshi daga gefe.
“Your mother is right.”
Cak John ya tsaye tare da ɗan daure fuska. “Me kuke nufi?” Madame Victoria ta ɗora hannu a tebur a hankali cike da muryan bada umarni tace.
“Muna son ka daina fita kamar da!, ka daina mu’amala da mutanenka kaf koma waye, ka daina duk ababuwan da ka saba.” Se ta dan dakata tare da motsawa ƙadan taci gaba da fadin.
“Saboda muna son killace daga annobar dake kokarin riskoka kamar shekarun baya.”
“Stop bringing up things nobody asked you about.”
Papa ya dan faɗa cikin tsawa don bai son kowa nasu ma yasan da wannan shudadden labarin, kafin Papa’n ya ɗan haɗe gira ya kalli John din yace.
“Don’t what?”
“Don’t bring her into this.”
Madame Victoria ta ɗan yi murmushi…
amma ba na farin ciki ba tana kallon Papa din daya furta.
“Toh kenan gaskiya ne.” ya faɗa yana tsaida idonsa akan John.
“Wace ce ita?” Papa’n ya sake jefa masa tambayar kai tsaye.
Shiru John yayi yaki ya musu magana ba don bai san abin da zai ce ba, sai don saboda kawai ba zai faɗa din ba, in yaso wacce ta kawo zancen inta matsu ta faɗa, kamar kuwa Madame Victoria tasan abinda ke ransa kenan ta riga shi yin maganar ta hanyar furta.
“Hausa girl ce.”
Cak Papa’n ya ɗan ja da baya kadan akan kujerar da yake.
“Hausa…?”
Ya fada cike da tashin hankali domin shi duk labarin da take bashi ai bata taba ce masa ga yaren gul ɗin ba.
“Joseph…”
Ya faɗa cikin mugun bacin ran da baya John mamaki.
“Ka san abin da kake shirin aikatawa kuwa?” wani dage girarnsa John din yayi tare da dage kafadunsa yace.
“I do.”
“Then stop it.”
Papa’nsa ya faɗa yana mikewa tsaye
“Ba za ka sake jawo mana irin wancan matsalar ba.” John dake kallon Papan da mugun mamaki yace.
“What problem?” ya tambaya cikin son sanin ko ma mi suke shirin ɓoye masa din daya danganta rayuwarsa ta bayan. Papa’nsa ya ɗan buga tebur da hannu. “Everything! Difference in culture… religion… background!” John ya miƙe tsaye a hankali har kujarar daya tashi a kai na ɗan ƙara kaɗan, cike da son ya fusata iyayen ya musu wani kallo ya dage kafada daya...
“This is my life.”
Ya faɗa cike da isar daya saka Madame Victoria miƙewa ita ma tace. “Mu kuma ai mu muka haife ka. Wanda ya saka John kallonta kai tsaye yace.
“And that means I don’t get to choose?” Yayi maganar da alamar tambayar daya saka su yin shiru. Iyaka wannan tambayar ta tsaya a iska. Madame Victoria ta matso kusa da shi ta taɓa kirjinsa tace. “Zaka zaɓa…” ta faɗa.
“Amma ka zaɓa da hankali.”
Ta ɗan tsaya kaɗan sai taci gaba da cewa. “Domin wasu zaɓukan… ba sa dawowa baya.” Hanyar samansa ya dauka yana sake ce wa dasu.
“This is my life.”
_Hhhhhhhh tabbas nie AMMEY LAYLERH ✍️ nace wllh duk wanda ya bari akayi tafiyar nan ba tare dashi ba, to kuwa tabbas anci da rabon sa ne.
_Saboda a labarin kansa bamu fara komai ba, duk wata sauran kulla kulla da cakwakiya tana can a gaba, inda muka kusa kammala free pages.... _
_Kana na baku wata ƴar satar..... Amma dai bari nayi gummm da baki na masu hasashe da zurfin tunani tuni zasu fara hango gaskiyar cewar Yasmine ba ita ce hasalin S tamu ba🤸😎😍🤣😂😜 Hhhhhh ALLAH dai yasa masu karatun na ganewa _
*BY AMMEY LAYLERH ✍️
08104493215
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 20
Paid book
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
♡♡♡♡
ꨄ Gaba ɗaya da kallon tashin hankali suka bishi harda jelly. Lady Rebecca ita kuma da sawo kanta kenan ta tsaya cak ɗin tana daskare da mutuwar tsaye, wani shegen baƙin cikin bata san kome ne farkon labarin ba na kamata, da Kyar ta iya danne abinda take ji ta kara so parlor din tana shimfida murmushin yaudara ta maza kamar bata ji komai ba, suma sai suka yi saurin gyara yanayin nasu tana zaman daya bama Papa damar barin wurin kai tsaye, hannu lady Rebecca sukayi da Madema Victoria kana suka zauna, Lady Rebecca din tana faɗa mata dinner tazo yau Chicken wings and BBQ ribs Emo ya musu se juice na Cranberry juice. Ita kuma wannan duk bata fiye son su ba, saboda bata son tayi jiki sosai, shi kuma naman alade jiki da kitsen jiki yake sawa ya saukarwa da mutum tumbi da teɓa. Ta kuwa ci sa'a su nan mutanenta aka yi, Beef steak, Roast chicken, se lemu na Lemonade, Eggs (omelette, boiled, scrambled) Bread, pastries da cakes duka su sukayi. Kaɗan kaɗan suke taɓa ƴar fira har rana ta gota, kana ta koma nata bangaren cike da tunanin san sanin abinda ke faruwa. Tun da Lady Rebecca ta bar sashen itama Madame Victoria ta wuce nata bangaren, ita kuma jelly ta wuce school gidan ya koma wani irin shiru, Yayi tsit tamkar ba a cikin sa ake rayuwa ba. Kowa yana nasa ɓangaren, amma duk da haka wani irin nauyin da ba a gani yana yawo cikin ko ina na gidan.
John yana tsaye jikin glass window na ɗakinsa, hannunsa cikin aljihu, idanunsa akan hasken birnin da ke kyalli daga sama. Amma ba komai yake gani ba face fuskar Yasmine lokacin da ta mare shi. Tasss³… Har sau uku tamkar yanzu abin ke sake sauka a kunnensa. Ya ɗan runtse idanunsa tare da sauke numfashi a hankali.
“She hates me…”
Ya furta da wata murya mai cike da ruɗani. Amma zuciyarsa ta ƙi yarda.
“No…”
Ya fada yana girgiza kansa kaɗan
“She’s fighting me.”
Wani ƙaramin murmushi marar daɗi ya suɓuce masa. Bai taɓa tunanin akwai ranar da wata mace za ta mare shi ba… har kusan karo na uku kenan… sannan shi kuma ya tsaya ba tare da ya fusata ba. Yadda take riƙe da shi kamar numfashinta, wani irin bugun zuciya ya doki kirjinsa lokacin da ya tuna yadda ta ce: “Na zaɓi addinina akanka.”
Ya juya da sauri kamar wanda wani abu ya tokare masa ƙirji. Hannunsa ya dafe kansa. “Why is this getting into my head?!” Ya furta da ƙarfi sai kuma ya tsaya cak… Domin a karon farko a rayuwarsa… ya ji tsoron kansa.
Tsoron cewa wata rana zai iya rasa komai saboda yarinyar nan.
A can ɓangaren Madame Victoria kuwa…Tana zaune cikin duhu tana kallon video ɗin CCTV da aka turo mata.
Video ɗin marin Yasmine. Sau ɗaya. Sau biyu. Sau uku, shiru ta yi tana kallo har video ɗin ya ƙare. Sai kuma ta ɗan murmusa. “Interesting…” Ta furta tana ɗaga wine glass ɗinta. “Yarinyar tana da zuciya.” Ahankali kuma murmushin nata ya ɗauke. Idanunta suka canza launi zuwa wani irin baƙin duhu.
“But she touched what belongs to me.”
Ta ajiye glass ɗin a hankali.
“John…” Ta furta sunansa kamar mai mallaka. “Ka fara manta ko kai ɗin waye.” Sai ta ɗauki waya ta kira wani number. Ana ɗagawa ta ce cikin muryan bada umarni tace. “I want the girl watched everywhere she goes.”
Ta ɗan dakata. “And if she tries getting close to my son again…” Kafin a hankali
murmushinta ya dawo. “Break her completely.”
♡
Yasmine kuwa… Tun da ta dawo gida take jin kamar zuciyarta na cin kanta.
Ta cire nikab ɗinta a hankali ta zauna gefen gado. Hannunta har yanzu na rawa. Domin duk da tsanar da take ƙoƙarin nunawa… Lokacin da John ya riƙe hannunta taji wani abu. Wani abun ɗin da ya tsorata ta, saurin dafe kanta tayi tana furta. “Astaghfirullah…”
Hawayen da take ƙoƙarin dannewa suka silalo mata. “Ya Allah…” Ta sake furtawa cikin rauni. “Kada ka jarabceni da abin da zuciyata ba za ta iya ɗauka ba…” Sai kuma ta tuna yadda ya kalle ta bayan marin. Ba fushi bane cikin idanunsa, ba kuma ƙiyayya bace, wani irin ciwo ne mai zurfi, mai kuma karya zuciya. Nan take ta mike tsaye cikin tashin hankali tare da furta.
“No!”
Ta faɗa tana girgiza kanta da ɗan ƙarfi.
“Ba zan tausaya masa ba.” Amma kuma zuciyarta ta kasa bin umarninta ta karfi.
Domin duk sanda ta rufe ido shi kawai take gani, yadda ya tsaya yana kallonta kamar wanda aka cire masa rai.
♡
Washegari…Tun karfe tara na safe.
Dining hall ɗin gidan ya cika da manyan mutane cikin nutsuwa mai nauyi.
Lady Rebecca na gefen Daddy'n India data fito dashi zuwa babban parlourn, tana sanye cikin shiga ta alfarma. Sai Madame Victoria dake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya tana sipping coffee ɗinta cikin Isa. Sai John da sakkowarsa kenan daga saman stairs. Yaja ya tsaya ba tare daya kalla kowa ba, domin yau ne karo na farkon da ya sauko breakfast ba tare da ya gaishe da kowa ɗin ba. Ya ja kujera ya zauna shiru kawai. Daddy'n India ne ya ɗan kalle shi tare da ƙiran sunanshi.
“John.”
Bai ɗago kan ba see kawai amsawa da yayi da.
“Hmm.”
Madame Victoria ta aje cup ɗinta a hankali. “Where were you last night?” shiru yayi ya kiyin magana.
“John, I’m talking to you.”
Sai ya ɗago idanunsa a kanta.
Cold. Heavy. Tired.
“Don’t start.”
Tsit kowa a wurin ya yi kamar wanda ruwa ya cinye. Lady Rebecca ta ɗan ɗaga gira ɗaya cikin mamaki. Madame Victoria kuwa ta ƙanƙance idanunta.
“Excuse me?” Sai John ya ɗan matsa gaba. “For the first time in my life, Mom…” Ya haɗe idanunsa da nata.
“I need you to stay out of my business.”
Wani irin shiru ne ya sauka akan dining hall ɗin. Saboda babu wanda ya taɓa yi wa Madame Victoria magana haka.
Koda Daddy'n India sai da ya ɗago kai.
Amma John bai tsaya ba. “Don’t go near her again.” Ya furta a hankali amma da nauyin da ya girgiza zuciya.Madame Victoria ta yi wani murmushi mai cike, Murmushin da baya nuna farin ciki ko kaɗan.
“Oh…”
Ta furta tana gyara dan gyara zaman ta cike da isa. “So the Muslim girl has finally destroyed your senses.”
John ya matse face nashi sosai fiye da farko fitowarsa.
“She didn’t destroy anything.”
Daga haka ya miƙe tsaye tsam ahankali.
“She made me realize how empty this life is.”
Kusan sarkewa numfashin Madame Victoria yayi a karon farko na ganin cewa tabbas da gasken gaske ɗanta yana fara kubuce mata da kwarai.
ꨄ Tun bayan maganar da John yayi a dining hall gidan ya sake sauyawa ba
wai an fara faɗa kai tsaye bane ba… a’a.
Amma komai ya sauya hatta da iskar
gidan ma ta koma mai nauyi. Kowa na kallon John kamar wani baƙo da ba su taɓa gani ba, duk da dai dama in ya tashi cin mutuncinsa ya kan shuka musu tafi haka ma, So amma abinda yasa wannan ɗin yafi musu ciwo shi ne akan Hausa girl ne. Shi kansa Daddy India ya fara lura da yanda JOHN din ke canzawa a hankali. Canjin da ba kuɗi bane ya jawo hakan ba. Ba kuma mace kawai ba. Wani abu ne mai zurfi… wanda yake fara shiga ransa. John ya daina yawan zama da mutane. Hatta fav piloting nashi ya jima da jingine shi a gefe, se dai a waje babu wanda yasan ainihin abinda ke faruwa. Saboda duk dare… idan duniya ta yi bacci… John na cikin duhun ɗakinsa shi kaɗai da laptop. Islamic lectures. Qur’an recitations. Videos akan rayuwar Annabi ﷺ. Tambayoyi akan Allah. Tambayoyi akan rayuwa. Kuma duk sanda ya gama sauraro…Sai yaji kamar zuciyarsa na narkewa. Sannu a hankali
wani abu ya fara rushewa a cikinsa.
A ɓangaren Madame Victoria kuwa…
Ranar da aka kawo mata rahoton cewa John ya soke babban dinner meeting saboda yana cikin ɗaki yana kallon Islamic documentary… Ɗan ƙaramin babban hauka ne kawai bata buga ba a gidan, amma dai kam tayi ƙarami tare da dukan glass tana furta.
“What nonsense!!”
Ta faɗa cikin tsananin fusata tana kallon Mecheal dake