Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
furta. “Take care of yourself, Joseph….Remember not every journey is like the others.”
“I know, Papa…”
John ɗin ya faɗi wani ɗan worried
smile na kufcewa daga kyakkyawar fuskar san tare da furta.
“I’ll be back.”
“You better come back safe. Jesus protect you.”
Daga suka yanke wayar daidai lokacin da ya isa compound na gidan, tun kan ya ƙarasa ƙarasowa Mecheal yay hanzarin buɗe masa lafiyayyar wata mota ƙirar Black Rolls-Royce Phantom. Kai tsaye ya shiga bayan ya bashi umarnin Airport ze kashi, cikin tafiyan da basu 10 minutes ba suka isa airport na _Murtala Muhammed International Airport_ (MMIA) kasancewar tsakaninsu babu wani nisa. Motar na gama daidai parking nata Mecheal yay hanzarin fitowa yana zagayowa cikin ladabi ya buɗe masa ƙofar baya.
Ƙafafunsa dake sanye cikin classic shoe se famar walƙiya suke ya fara zirowa, kafin ya fito gaba ɗayansa cikin kayan pilot ɗinsa masu tsafta, hularsa na riƙe a hannunsa ɗaya mara bandage, fuskar nan tasa mai ɗauke da wani ɓoyayyen damuwa amma idanuwansa cike da wani irin iko. Ahankali wata sassanyan iska ta daki fuskarsa kaɗan wanda ya saka shi ɗaga kansa ya kalli sararin samaniya, tamkar me karantar yanayin samaniya. Gefe guda kuma mutane nata
zirga-zirgansu… amma mafi hankalinsu tun farkon bayyanuwar lafiyayyar motar suka dakata hankulansu yana fara karkata wuri guda sakamakon fara takun da yake yi cikin nauyin zuciya dana ƙirji, Cak wata Matashiyar budurwa ta tsaya a inda take, har jakar dake riƙe a hannunta na ƙoƙarin zubewa, gefe guda ma ga wasu maza dake magana amma suka daina maganan suma idanunsu akan John ɗin, domin kuwa wani irin baiwar kyau da zubi da tsarin halitta UBANGIJI ya masa. Wani yaro ne ya kamo hannun
mahaifiyarsa tare da furta. “Mom…who is he?” sake riƙe hannun yaron nata da kyau tayi tana cewa “I don't know him...” daga haka suka wuce.... Gaba ɗaya mutane naci gaba da kallon yadda yake tafiya, ba gaggawa, ba jinkiri haka ba garaje. Wasu daga cikin ma’aikatan airport ɗin ne suka kalli juna kafin cikin wata irin girmamawa ɗaya daga cikinsu cikin muryan raɗa ya ce
“That’s him… the one they called.” Sarai ya jisu amma bai ko tsaya ba bare kallan inda suke, zuciyarsa naci gaba da bugu yana jin kamar wata inuwa na bin bayansa. Kai tsaye John ya shige cikin hall ɗin da ake fara son ganinsa, Sanyin AC mai sanyi da ƙamshi na tashi wanda suka haɗe suka sake fidda ainihin tsafta da tsarin hall ɗin, kafin cikin muryan kururuwar ƙarar announcements ya fara tashi a sama sama na isowar _JOSEPH Mr JEF DEEFER PATRIARCH _ “Attention please… final boarding call“ nan bayan yayi wasu ƴan ƙananun rubuce rubuce ya sake fitowa wani guy na bin bayansa, ma’aikata naci gaba da gaishe shi cikin girmamawa. Su kuma dama already sauran crew ɗin jirgin sun riga sun gama daidai komai kawai jiran isowansa suke.
“Captain… we’ve been expecting you.”
Ya ɗaga kai kaɗan, kafin cikin nutsuwa ya furta.
“Let’s move.”
Daga nan suka fara takawa zuwa ainihin inda jirgin ke fake, hanya suka bashi bayan sun buɗe masa ƙofar zuwa runway, Jirgin yana tsaye babba suna isa matakala ta sauko… a wani kalan hankali ya fara takawa zuwa matakalan ɗaya bayan ɗaya. Har zuwa lokacin zuciyarsa na ɗan bugawa kaɗan da kaɗan, dan kawai mafarkin da yayi ne ke dawo masa yana yawo a ransa… a tausashe sautin takun sawunsa ke amsawa a cikin dogon corridor na airport ɗin cikin nutsuwa… ga wani kalan ɗan banzan kyawun da uniform ɗinsa na pilot suka ƙara masa,me tafe da wani irin ƙima da kwarjini wanda da ace a musulmi aka yi shi to kuwa da tabbas anyi jajirtaccen akan addininsa, se dai fuskar nan a wani irin ɗaure take sakamakon abu mai nauyin da yake jin kamar ya tokare masa ƙirji da zuciyarsa. A ƙofar shiga restricted area ya tsaya ƙofar ta buɗe a hankali da kanta John ya shige ciki, hasken waje ya bar bayansa, ya shiga wani yanayi mai sanyi da tsari inda komai ke nan bisa ƙa’ida da kuma tsari, sauran crew ɗin jirgin suna tsaitsayekowa cikin uniform nashi mai tsabta.fuskokinsu ɗauke da girmamawa suna daidaita tsayuwarsu lokaci gudan da suka hangowa tahiwarsa, Chief Flight Attendant ɗin data kasance mace ta ɗan matsa gaba, zuciyarta na bugawa da sauri amma kuma tana riƙe kanta ta furta.
“Captain Joseph… ur welcome, sir.”
Muryanta ta faɗi da ladabi me wani irin nauyi,suma sauran crew suka mara masa baya suna furta.
“Good evening, Captain!.”
Daidai lokacin da yake kawowa inda suke, ja yayi ya ɗan tsaya Lafiyayyun Idanunsa na bin kan kowa ɗaya bayan ɗaya, tamkar yana nazarin su ko kuma yana neman wani abu a cikin su. kafin ya wani ɗan ɗage kai sama kaɗan kawai tare da furta
“eveninig.”
Kalma guda ce amma kuma ta wadatar dasu, wani co-pilot ne ya matsa kusa
matashi ne amma ana ganin kwarewa a tare da shi tare da ambatar.
“Sir… mun shirya komai. Flight plan ya riga ya kammala, amma weather… stable for now.”
“...for now?”
John ya maimaita a hankali, yana kallon sa kai tsaye. Co-pilot ɗin ya haɗiye wani yawu kaɗan tare da gyada kansa yana me furta.
“Eh sir… akwai ɗan turbulence a hanyar Atlantic… amma under control.”
Ɗan lumshe ido kawai John yayi.
_Atlantic…_
Tabbas kalmar ta daki zuciyarsa kamar ƙarar ƙaho, har besan lokacin da ya faɗa wani tunanin daban ba.
“Are U okay Captain?”
muryar Chief Attendant ɗin ta dawo da shi daga ɗan tunanin daya cilla, kafin ya buɗe idonsa a hankali. Juyawa kawai yayi ya fara tafiya zuwa cockpit ɗin bayan ya furta.
“Let’s move.”
Kowa ya bi umarni ba tare da ɓata lokaci ba, wata flight attendant ce ta
raɗa ma abokiyarta.
"There’s something about him today…"
Wani murmushi kawai ɗayar tayi cikin sanyi tare da amsa mata da.
"Yeah… like he’s not alone."
A ƙofar cockpit ɗin John ya tsaya.
kai tsaye lokacin da yake bayyana a gaban cockpit ɗin. Wani haske mai laushi ya cika cockpit tare da fuskansa…...Komai a tsari yake buttons, screens, komai na aiki kamar yadda aka saba. Gaba ɗaya baya jin zuciyarsa a daidai bata cikin tsari kawai dannewa yake, Kafin ya zauna a kujerarsa tare da daura bel ɗinsa a hankali. Idanunsa suna kallon gaban jirgin amma ba ganin runway yake ba, mafarkinsa kawai yake haskowa....
“Captain, all systems ready.”
Maganar da co-pilot ɗin ya faɗa cikin girmamawa ya dawo dashi cikin nutsuwansa, ɗan jinjina kai kawai John ɗin yayi tare da furta..
“Proceed.”
Muryansa a dake rin wacce ke bayyana No nonsense ɗin nan. A ciki kuwa... mataimakinsa (First Officer) ya riga ya zauna yana duba na’urori.
“Captain John,”
ya faɗa cikin girmamawa.
“Komai ya shirya. Weather ya ɗan canza kaɗan… amma babu matsala sosai, ba kamar baya ba....”
Ahankali John ya zauna a kujerarsa yana ɗaura belt. Idanunsa suka bi dukkan panel ɗin na’urori...
“Copy that…”
ya amsa a hankali kafin wani shiru ya ratsa cockpit na ɗan lokaci, wanda hakan ya saka John ɗan lumshe ido
hoton Yasmine na faɗo masa…
“Captain?”
mataimakin ya sake ƙirar sunan shi da dolen dole ya saka John buɗe idonsa da sauri.
“I'm fine. Let’s proceed.”
Daga nan Engine suka fara ƙara, Cockpit ya cika da hasken buttons masu walƙiya.
“Ready for pushback.”
“Pushback approved.”
Jirgin ya fara motsi a hankali, kafin cikin wucewar wasu ƴan mintuna,
John ya ɗaga hannunsa ya kunna PA system nashi, Muryarsa ta cika cikin jirgin cikin sautun nutsuwa,iko da bada kamar umarnin kai tsaye ya ce...
“Ladies and gentlemen, this is your Captain speaking…Welcome onboard. We’ll be departing shortly. Please fasten your seatbelts.”
Tuni fasinjoji suka fara nutsuwa da jin muryarsa. wasu suna waya, wasu suna kallon waje, Crew kuma suna motsi cikin kwarewa… amma wasu daga cikinsu suna jin wani sanyi da ba su iya bayyana ba...
Cockpit…
“tashi checklist complete, sir.”
John ya ɗan gyara hularsa ya kalli runway ta gaba, yana kallar dogon layi mai haske da ke kaiwa cikin sararin sama shawagi.
“Let’s go.”
ƙafafun jirgi suka fara motsi hasken runway yana walƙiya a gefunan
Co-pilot. “Speed building…” Runway…
“Cleared for takeoff.” John ya matsa lever ɗin gaba wacce ta saka Injin jirgin ya yi ƙara mai ƙarfi, da haka Jirgin ya shiga runway…
“Speed?”
“Checked.”
“Rotate.”
John ya ɗaga hancin jirgin a hankali zuwa sama ya fara ƙoƙarin landing na tashi, gajimare suna karɓar jirgin cikin sanyi. Co-pilot ya kalli screens...
“Sir… slight turbulence unexpected.” wata nutsuwa John yayi yana kallar yadda gajimare masu duhu ke taruwa a nesa kamar suna jiransa, a hankali ya furta.
“Something is wrong…”
Daga jirgin ya fara keta sararin samaniya, mutanen dake ƙasa suna kallon yadda yake ratsa sararin sama… daidai setin zuciyarsa ya danne a bayyane ya furta....
“So I miss you… more than you will ever know, Yes, I am still struggling to let go.
This is a process I need to go through… so for now, I’m ok with missing you..
I WILL Really miss you too my Trouble....”
_Hummmmm!!! Tirƙashi. Masu karatu wai ya take ne???.😲. Mi kuke tunani dangane da littafin DUHU na DUKAN duhu ne?, shin ma wanene Wannan Joseph ɗin kansa? Sannan wacece yasmine daya laƙa ba mata sunan Trouble?, shin ku a ganinku yaya zata kasance mana ne kamm? Minene zai faru kuma?..._
*Amsar waɗanan tambayoyin duk suna a Littafin DUHU na DUKAN duhu!! da ke cikin ɗaya daga cikin lates Amazon stories na wannan year's ɗin IN SHA ALLAHU....*
_Nie dai AMMEY LAYLERH nace Wllh karku bari ayi tafiyar nan babuku, dan wannan littafin fa da zafinsa yake tafe uyhmmmm, wanda ya rasa shi yaso domin na tabbatar muku tafiyar wannan littafin ko???, to ta dabance MASOYAN AMANAR AMMEY LAYLERH😋🤗🤗😀😀......_
_ku sani cewar Wasu duhun...
suna farawa da kuskure ne... Yayin da wasu duhun ke farawa da rashin sani...._
_Wanda suke farawa da kuskuren ku sani daga ƙarshe... rayuwar tana lalace musu ne, to shin akwai bukatar ci gaba da bin littafin DUHU na DUKAN duhu kenan ko???...._
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 4
Paid book
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
_Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_
*Tabbas maganan hausawa dai dai ne da suke cewa Shimfiɗar fuska tafi Shimfiɗar tabarma, da haka nake so na mika tarin godiyana ga mutane na
musamman zuwa ga Yotawanmu, ALLAH ya ƙara mana tarin basira, ɗaukaka,tarin nasarori... Tarin godiya na sosai ga Ayshacool.....*
ꨄ Idanunsa yaja yana lumshe su, tare da crossing hannuwansa ta bayan kansa yayi shiru na wani ɗan lokaci, a hankali fuskarta ya sake bayyana a zuciyarsa, yadda ta dalla masa marin nan, har besan lokacin da ya wani buɗe idanunta masu cike da wani irin ɓoyayyen abu.
“Captain John? Are you there?!”
Muryan co-pilot nashi ta katse shi yana buɗe idonsa tare da furta.
“I’m on my way.”
Ya furta yana ɗora hannunsa kan controls, amma haka kawai yake jin wani sanyi na ratsa jinin jikinsa, Co-pilot ɗin sa ne ya kalle shi tare da sake jefa masa tambayar.
“Sir, everything okay?”
Ɗan Lumshe masa idanunsa yayi da wani ƙaramin murmushin da bai gama fitowa gaba ɗaya ba. “Yeah… let’s fly.”
_Shin kai babu zuciya a ƙirjinka ne hala!?...._ yaji kalmomin sun wani daki cikin kansa, _kokuwa kana tunani da zuciyar naka ne bada ƙwaƙwalwa ba?...._ ya sake rumtse idonsa yana kuma toshe kunnuwan nasa, amma duk da haka hakan be saka kalmar ta na gaba sake bugar cikin kwakwalwarsa.
_Amma kaikam duk ahalunka babu masu imani !, kuma bakusan menene daraja da muhimmancin ƴa mace ba?_
Haka muryarta ta sake shiga kunnensa, wanda hakan har yasa be san lokacin daya saka hannunsa da ƙarfi yana danne controls na jirgin ba, “Sir?” co-pilot yay gaggawar masa magana wanda yasa John haɗiye yawu wani abu yana me furta. “I’m fine.”
Wanda a baɗini kuma ba hakan bane, gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya tare da shi, mafarkinsa ne ya sake kutsowa cikin tunaninsa, tuni idonsa suka wani irin rine suka yi jaaa sosai,
sai ya ji kamar yana sake shiga cikin wani duhu ne da bai taɓa fuskanta ba. gefe guda kuma ga Jirgin dake shawagi a sararin sama cikin nutsuwa, komai na tafiya yadda ya kamata.
A can cikin cockpit ɗin kuwa hasken na’urori naci gaba da walƙiya a hankali green, amber, da ɗan ja duk suna nuna cikakken aikin da suke kai bisa tsarin da aka gana seta su, shi kuma yana zaune a kujerarsa, hannayensa a kan controls cikin ƙwarewarsa wacce har ta saka duniya ta sanshi a matsayin shahararren pilot number ɗayan da suke ji dashi a duk faɗin Nigeria bama iyaka Lagos ba... “Altitude steady.”
Ya faɗa a hankali idanunsa na kan dashboard. Co-pilot ya amsa da girmamawa shima yana me furta. “Confirmed, sir.” ɗan baya John yaja tare da ɗan matsa wani lever…
ya gyara heading… ya duba instruments ɗaya bayan ɗaya, komai dai naci gaba da tafiya daidai. Haka jirgin yaci gaba da keta sararin samaniya cikin daren daya fara rufe sararin samaniyar… a cikin idonsa yake hango wani kalan duhu, duhu mai ɗauke da kauri tamkar ana zuba shi da hannu, amma hakan besa ya girgiza ko jin komai ba Jirgin yaci gaba da shawaginsa a cikin gajimare masu nauyi, shi kuwa Captain John ya zauna cikin nutsuwarsa, idanuwansa suna manne da instrument panel, wani haske mai launin kore da ja yana haskaka fuskarsa yana ƙara masa wani irin kwarjini mai ban tsoro.
“Altitude stable… speed normal…” in ji First Officer ɗin cikin ɗan sanyi murya, wanda tun kan ya kai ga rufe bakinsa ƙarar ƙararrawa ta cika cockpit na
Jirgin yana girgiza da ƙarfi, kamar wanda jirgin ya bugi wani abu ya daga waje. “Captain! Turbulence is increasing!” tabbas wannan ba gizon fuskanta yake gani ba, jirginsu ne ke ƙoƙarin shiga cikin matsala, wanda hakan ya saka John matse handle ɗin da ƙarfi. Idanunsa na canzawa zuwa wani mataki na daban, “Stay with me…” ya faɗa a hankali kamar yana magana da jirgin kansa. Autopilot ya kashe da kansa, jirgin ya shiga sanar musu da WARNIN warning system failure. Take hankalin First Officer ya fara tashi cikin tsananin ruɗewa yake furta... “Sir… we’re losing control fa...!”
Wani kalan fusga jirgin yayi ya fara ƙoƙarin karkata kansa gefen da ba nan suka nufa fa, ganin wannan babban hadarin dake nemar ruskar mutanen dake cikin jirgin suka fara kururuwan ihu, gaba ɗaya tsoro ya gama mamaye kowannensu masu ƙarfin imanin cikin sune kawai ke adda'a daga cikin musulmanmu kenan. Amma shi kam John ko kaɗan bai firgita ba, sai wani numfashi da yaja a hankali, yana saka
hannunsa ya kama throttle, ɗayan kuma yana sarrafa yoke. Jin har lokacin ihun passinger's bai dena ratsa tsakiyan kan sa bane ya sake shi furta....
“Listen to me,” ya faɗa da murya mai ƙarfi a kuma tsawacen daya sakasu dole haɗiye komai. “we are not going down.” se kuma wata walƙiya ta sake bugawa
jirgin ya nutse ƙasa kaɗan...
“PULL UP! PULL UP!” Ƙarar system na ƙara tsananta, John ya ɗaga jirgin da ƙarfi har wasu daga cikin jijiyoyin jikinsa suna fitowa waje, idanunsa sun ƙone da determination. “Come on… come on…” ya sake furtawa a dake yana
juya jirgin cikin dabara, ya fice daga tsakiyar gajimaren daya shigar masa hanya, A hankali ahankali kuma girgizan da jirgin yake ya fara raguwa. Wanda ya saka First Officer nashi zaro ido woje, duk da kasancewar ba yau bane karon farkon daya saba ceto rayuka daga cikin hadarin jirgin, kai tsaye tare da furta... “Sir… you did it.”
John dai bai ce komai ba, se ɗan murmusawan da yayi kaɗan tare da furta. “Not yet. Keep watching.” ci gaba da kula da daidai na'urorin yayi zuciyarsa na masa wani irin bugun daya gaza kane ko na miye. A cikin cockpit, ƙarar alarm ta dawo fiye da farko ma.Wannan karon kuma _ENGINE FAILURE_ ne, a ɗan rikice First Officer duba inda John yake kai tsaye tare da furta. “Captain… engine one is down!” nan take Jirgin ya sake karkata har kamar wannan karon ma ya fi muni akan ɗazun, tuni passinger's suka sake ɗaukan wani sabon ihun wasu suna kuka, wasu suna kiran sunayen ALLAH kamar ɗazun. Ahankali John ya sake ɗaga kansa kaɗan yana me furta musu. “Declare emergency,” ya faɗa cikin taushi amma da iko. “Mayday, Mayday, this is Flight 271… we have engine failure, requesting immediate landing clearance…” Sai wata murya daga control tower ta amsa mai cike da damuwa ta hanyar furta. “Flight 271… nearest runway is unstable due to storm. Visibility almost zero…” a tsorace
First Officer ya kalli John yace. “Sir… we might not make it…” kafin shiru na ɗan lokaci ya gitta kawai se John ya ɗan yi wani murmushi kaɗan irin murmushin da ke ɓoye wani abu mai girma, ahankali ya furta. “Then we create our own way.” daga haka ya kama controls ɗin da ƙarfi. Sedai Jirgin yana saukowa da sauri, iska na dukan shi kamar za ta tarwatsa shi..._ALTITUDE LOW
TERRAIN! TERRAIN!...._
“Pull up, Captain!!” “A’ahh No!…” John ya faɗa a hankali. “not yet…”Wata walƙiya ce ta haskaka filin samaniya tana bayyana na ɗan lokaci, sannan ya ɓace.. “NOW!” Da ƙarfi ya daidaita jirgin
ya juya shi cikin dabara da zallar kwarewansa wajen iya sarrafa jirgin.
*Florida...... Miami International Airport...*
A can cikin babban control tower na Miami International Airport kuwa, hasken fitilu ne kawai suke kyalli, allunan radar suna ta haskawa da motsi ba kakkautawa, sai kuma ƙarar ƙararrawa mai tsanani