Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
ma nuna masa alamun yabi motar, take kuwa taxi ɗin ta rufa musu baya Idanun John na manne a gaban motar nasu don karta ɓace musu, ga zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri.
“Wannan karon… ba zan sake rasa ki ba My Unknown beloved,” ya faɗa a ransa.
Bayan wasu mintuna motar su Yasmine ta shiga wani hadaddiyar anguwa mai me shegen kyau da natsuwa, in da ma she basa da wata tazara ta a zo a gani tsakaninsu. Ahankali yaga motar ta tsaya a gaban wani gida mai kyau.
John ya umarci direban ya tsaya daga nesa shi ma, ahankali ya fito daga motar
yana kallon yadda Yasmine ta fito, tana taimakawa mahaifinta. Tana wata irin dariya…irin dariyar da bai taɓa ganinta tana yi masa ba. Wani abu me kama da kwanciyar hankali yaji yana kamasa na ganin gidan nasu kawai, daga nan ya saka mai taxi ɗin fita a anguwan ya faɗa masa anguwansu ya kai shi, duk da kasancewar su estate ɗin nasu taxi baya taɓa shiga, amma kuma ganin John ne ya saka su barinsa har bakin mension nasu. Kuɗin da ba ma canjin naija bane Ya bashi, wanda idan ya sanja yana iya zame masa 100k, don haka ya tafi da murnan sa yana binsa da fatan alkhairi a cikin rayuwarsa. Tun kafin ya isa ga ƙofar gidan nasu ya soma jin sautin kiɗa mai ƙarfi da ihu na tashi daga cikin gidan. Nan take yanayin fuskarsa ta sauya zuwa na ɓacin rai, idanuwansa kuwa har wani ƙanƙancewa suke cikin tsananin ɓacin rai. Wato gidan bayan baya nan ma kura ta mutu ai wasa suka mayar dashi, bayan sun san babu abinda yafi tsana fiye da wannan sokon kiɗe kiɗen da rawo rawo zuwa party birthday wanda ko jelly sedai ta saci hanya, ji yayi gaba ɗaya suna nemar ɓata masa ɗan sauran farin cikin daya samu. Kai tsaye ba tare da ɓata lokaci ba ya taka zuwa ƙofar ya buɗe da ƙarfi. Har da wata kalan sassarfa yake haɗawa, duk ma'aikacin daya gansa se kuga ya riƙe baki alamar yau da bala'i kenan. A lokacin da yake isa ainihin babban parlourn gidan abin da ya gani ne ya saka shi tsaya cak. Jelly ce tsakiyar maza da mata freind nata, tana rawa da juyi hannunta riƙe da kwalbar wine tana kwankwada wanda kallo ɗaya zaka mata kasan cewar tana cikin farin ciki sosai, tun daga yanayin yadda take tikar rawar ta cikin manyan yara maza da matan da suka cika ko’ina, wasu na rawa, wasu na dariya, wasu ma har suna riƙe da drinks. Kiɗa na tashi kamar gidan ba na iyali ba ne. Kowannensu cikin shigar shegun kaya irin nasu na Christian. Take yaji wani irin zafi na taso masa tun daga zuciyarsa. “JELLY!!!” ya daka mata tsawa a wani irin haukacen daya saka jelly yin wata irin katantanwa ta kusa hantsilawa, kafin cak ƙiɗan ya tsaya dariya ta mutu. Kowa ya juya yana kallonsa cike da tsoro don duk wasu sun san dokar John ɗin musamman ma wanda suke da kusanci sosai da Jelly ɗin,ita kuwa jelly da jikinta ke se a lokacin ta ɗago kanta tana satar kallonsa don ba ta yi tsammanin zuwansa ko kaɗan ba bare ganinsa.
Numfashinta ne taji yana ƙoƙarin tsayawa ahankali kuma jikinta ya fara rawa, kafin cikin rawar muryan ta ɗan soma ja baya tana me ambatar sunan shi cikin ƙinƙinar da bata taɓa sanin cewar tana da ita ba. “J… John…” ta furta tana sake ja da baya har tana lafewa a jikin ƙawayenta, inda suma kowa ya lura da canjin yanayin nata, ga John ɗin da ko sake motsawa bai yi ba.
Sai ma wani irin mugun kallon da yake jefa musu na tsananin gargaɗi.
“What is going on here?”
ya faɗa a ɗan tsawace cikin turanci mai nauyi. Ba wanda ya iya amsawa sai wani farin guy ɗin matashi daya motsa kaɗan kai da ganinsu kaga irin marasa jin nan kangararru kuma, wani ɗan munafikin murmushi ya saki yana cewa. “Hey bro, it’s just a” ai tun kafin ya ƙarasa abinda yayi niyar faɗin John ɗin yayi wani irin katse shi cikin tsawa kawai yace.. “Get. Out Everybody .” Makut kuwa ya haɗiye maganar nashi don ganin yadda John ɗin ya dawo lokaci guda kamar wani fusataccen zaki. Nan take tashin hankalin ganinsa hakan ya mamaye wajen. Kafin ɗaya bayan ɗaya suka fara zarar jiki suna ficewa ba tare da jayayyar komai ba.
Wasu ma kuwa harda haɗawa da tuntuɓe saboda gaggawa. Jelly ta rage tsaye ita kaɗai… jikinta na rawa sosai.
Ta kasa kallon idonsa cikin muryan tashin hankali ta ce. “I’m… I’m..sorry…” ta faɗa da ƙyar. Kafin a hankali ya fara takawa zuwa gare ta cikin kaushin murya ya sake ce da ita. “You disobeyed me.” ya faɗa da tsawar daya saka jelly ta ƙara sunkuyar da kanta ƙasa kawai wasu ruwan hawaye na sake cika mata
Ido. “I said no parties.” ya ƙara faɗi.
“I know…” muryarta na rawa ta faɗi tana sake cewa. “I’m sorry Joseph…”
Wani shiru ne ya ɗan ratsa parlourn yama gaza cewa da ita komai kuma, daidai nan sega saƙƙowar takun sawaye nan daga saman benen, wanda jin shiru babu kida da iface ifacen ihun sune ya saka su fitowar suma kowa da nashi kwalbar giyar a hannu, haka suka fito Madame Victoria na tambayar. “Baby, what's going on? I heard your music stop.” aikuwa itama cak maganar nata ya tsaya cak ɗin lokacin da idonta suka sauƙa kan John. Tsit gaba ɗaya parlourn ya ɗauka wani irin yanayi na sauya gidan bama iyaka parlourn ba, kafin cikin muryan mamaki da kuma tsoro Papa ya furta. “John…?” ya ambata a hankali cike da mamakin ganinsa daya haɗe da wani irin tsoro. Domin kuwa babu wanda ya san zai dawo hasalin zuwar bazata ne kawai ya musu.
Madame Victoria dake tsaye a gefe ce ta ɗan haɗiye wani yawu, kana ta yi kundunbalar furta. “You’re back…” ta faɗa a hankali. Amma babu wanda ya kuskura ya matsa kusa da shi.
John ya juya ya kallesu a hankali.
“Yes.” ya amsa gajere. Sautin muryarsa kaɗai ya isa ya sa nutsuwa ta koma tsoro. Idanuwansa suka sake komawa kan Jelly ya ce. “Clean this mess.” ya faɗa kai tsaye. Ta sani baya da buƙatar maimaita magana don haka Jelly ta gyaɗa masa kai da sauri, jikinta har yanzu na rawa. Mommah ce ta yi ƙoƙarin danne tsoronta tace “John, maybe we should” tun kafin tace komai ɗin ya ɗaga mata hannu kaɗan alamar tayi shiru kawai, don a dai yanayin da yake a ciki baya buƙatan kowa yace masa komai. Papa ne ya sauke wata numfashi a hankali me ɗumi yana sake ɓoye kwalban giyarsa a bayansa ba tare daya sake yunƙurin magana ba. Haka kowa ya ƙame su ka kuma yi shiru, ganin shirun yayi yawa ne ya saka Papa ɗan gyara tsayuwarsa tare da cewa.
“No… I mean, we didn’t expect you”
Da wani kallo kawai John ya bishi bai ce komai ba, amma kallon kawai da yake binsu dashi ya isa sanar musu komai,
Mademe Victoria ta kau da idonta da sauri a kan sa, ta ɗan matsa kusa da Papa'n kamar tana ɓoye wani tashin hankali. Jelly ta ɗan ɗago kai… tana kallon iyayensu, ta lura da suma yadda tsoron John ya bayyana saman fuskarsu suma, Kuma ba wai kawai tsoro ba ne ta sani harda giyar daya kamasu suna sha, musamman ma Madame Victoria ta ita kwata kwata ya hanata sha. Ahankali John yaci gaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya. Idanuwansa har sun ɗan yi zurfi.
“Is there something I should know?” ya tambaya a hankali. Babu wanda ya amsa, sai ɗan wani murmushin dolen da Papa yayi yana samu ya ɓoye kwalbar nashi cikin wani ɗan dub daya samu yana furta. “No. Nothing.” ya faɗa da sauri fiye da kima wanda ya saka Madame Victoria saurin gyaɗa masa kai tana cewa “Yes… nothing at all.”
Amma kuma muryarta ta ci amanarta wajen bayyana ƙin bata damar bayyana gaskiyar. John ya ɗan matsa gaba kaɗan ya musu wani kallon daya saka dukansu zuciyarsu bugawa da sauri...
“You’re lying.” ya faɗa kai tsaye, nan take Madame Victoria ta haɗiye wani yawu. Komai be sake ce musu ba ya juya ya nufi sama, ƙafafunsa na takawa a hankali… amma kowanne taku na ɗauke da wani irin nauyin da iayayensa suka haifar masa. Suna tabbatarwa da cewar ya gama hayewa sama Madame Victoria ta saki wani numfashi da ƙarfi.
“Oh jesus…” ta faɗa a hankali Papa kam rufe ido yayi na ɗan lokaci.“John he’s back…” ya fadi a bayyanen daya saka jelly sake kallon iyayen nasu kamar a ɗan firgice tace “Me kuke ɓoye masa ne bayan party…?” ta tambaya a hankali.
Amma babu wanda ya amsata. John dake tsaye saman bene yana kallon su daga sama bayan ya ji kamar shirunsu ya yi yawa ya saka shi dawowa. Saurin riƙo hannun Papa Victoria tayi tana sauƙe wata ijiyan zuciya tace....
“We can’t hide it anymore…” ta faɗa cike da kamar tsoro amma Papa ya girgiza mata yace “Not now… not like this.” Jelly ta sake kallarsu da mamaki tace. “Hide what?” Madame Victoria
ta kalli ƙofar sama ta rage murya sosai tace. “His marriage…” wanda ya saka jelly buɗe ido sosai da sauri ta sake maimaita kalmar “Marriage for what?!”
“To Deepika…” Papa ya faɗi wanda kai tsaye se cikin kunnuwan John dake tsaye har zuwa lokacin daga sama...
Take Idanuwansa suka canza a bayyane ya maimaita “Deepika…?” Wani irin shegen murmushi na kwace masa.
“So… this is what you’ve been hiding from me na yheeee.”
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 13
Paid book
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
_Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t
Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci?
To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta
♡♡♡♡
ꨄ Gaba ɗaya kusan a tare suka ɗaga kansu zuwa ga inda suka jiyo sautin maganar John ɗin. Kafin a hankali cikin nutsuwa ya ke sauƙowa daga benen, but at the same time cikin kuzari da taku irin na cikakkun mazaje, that confident masculine stride of a man da ya san worth ɗinsa. ƙarasa saukowansa cikin parlourn ba ƙaramin rikita iyayen nasa yayi ba, sai dai a nashi ɓangaren ba tare da ya ko kalli sashen da suke tsaye cirko cirko ba yayi wucewar sa ya buɗe ƙofar babban palourn ya sake ficewa kamar bai gansu ba ko bai san da su a palourn ba, da idanu duk suka bisa kowa da irin abinda ya ke saƙawa a zuciyarsa ga baki ɗayansu sun girgiza da irin kwantaccen ɓacin ran da suka hango daga fuskar John ɗin. Kai tsaye Mecheal na ganinsa yay hanzarin nufar wata rantsatstsiyar mota ya buɗe masa don dama zaman jiran hakan yake yasan doke se ya dawo,direct motar tasa ya nufa mai matuƙar kyau da tsada ya buɗe masa ya shiga sannan ya maida murfin ya rufe tare da sauƙe wata gajeriyar ajiyar zuciya, tun da dai be tanka kowa ba. John kuwa a nashi ɓangaren ƙatoton mikin da yazo ya dannesa masa ƙirji
ne ya sa ko buɗe bakin bai son yi bare har yayi magana, wanda kai tsaye har zuwa lokacin wata irin kwantacciyar ɓacin rai ne zagaye da fuskar nashi. Sa'ar sa ma ɗaya p-carp ɗin da ke kansa ya rufe rabin fuskar nasa da kuma shade ɗin idanunsa, sannan ga nose mask ɗin da ya sa ya toshe hancinsa da bakinsa, wanda ko samun damar cire su bai yi ba bayan ɓacin ran da suka shaƙa masa shi ne suka sake guma masa wani ta hanyar tsomo da auren ifritin wannan yarinyar cikin rayuwarsa.
A hankali Mecheal ɗin yama motar key kasancewar ya san Boss ɗin nasa idan yana a irin wannan yanayin baya son gudu sosai can a mota, kafin su ƙaraso harabar har mai gadi ya wangale masa gate ɗin, take ya cilla motar titi nasu saman titi suka fara tafiyar da baifi ta 30 minutes ba suka isa wani kayataccen gida. Hong ɗaya kawai yayi get man ɗin dake kula da gidan yay hanzarin zuwa ya buɗe masa ƙofar, kana ya cinna hancin motar nasa ciki. Parking yayi koda yayi ya jima kafin ya fito har lokacin da fushin sosai a cikin fuskarsa...
Direcly ya wuce zuwa ainihin babban cikin gidan dake a gyare sosai tamkar macece a ciki, kai tsaye wani lafiyayyen bedroom ya nufa har zuwa lokacin ji yake kamar zuciyarsa zata iya faso ƙirjinsa ta fito fili kowa ya ganta. Dama haka yake duk lokacin da yake cikin tension irin haka dawowa yake nan ɗin yayi zamansa har se zuwa lokacin daya sauƙa dan kansa. Ko ta kan abincin da Mecheal ya kawo masa be yi ba bare ma tunanin zai ci. Zuwa lokacin kuma tuni har 8:00 na dare ya gota ma, don haka ƙarƙashin shower kawai ya wuce da kayan jikinsa yana son samun sassauci daga zafin dake neman illata rayuwarsa gaba ɗaya. Ya jima sosai ƙarƙashin shower ɗin kafin ya zubar da Jiƙaƙkun kayan jikinsan anan cikin bayin ya fito, dake yana da uban kaya anan ɗin don yana yawan zama sosai a gidan,wanda nasa ne idan yaso har kamar kusan ma dawowa yake da zama gaba ɗaya. Sanin ainihin halinsa da baƙar zuciyarsa idan ta motsa ya saka Mecheal zama ya kwana a gadroom. Washe gari har sha biyu be fito ba zuwa ƙarfe biyu sega su Madame Victoria nan sun biyo sahunsa ita da Papa, don suna ta ƙirar wayarsa amma baya ɗauka daga ƙarshe ma seya kashe gaba ɗaya duka wayoyin nasa. Kuma har lokacin bai fito ba, har kusan karɓe huɗu na yamma suka zauna zaman gadin fitowar nasa bayan ya sha magiyar ya buɗe musu amma in ginin wurin yayi motsi to kuwa shima John ɗin yayi. Huɗu da rabi suka tattara nasu ya nasu suka mension nasu abin mamaki kuma suna tafiya da kamar 30 minutes ya fito shirye tsaf cikin shigar wasu riga da wando Calvin Klein underwear. Kansa da p-carp ya fito kai tsaye wurin parking car na gidan ya nufa, Mecheal na ganinsa ya miƙe da sauri ya buɗe masa ya shiga suka fita. Duk da dai yau yaso zuwa gidan su yasmine amma baya mood ɗin da zai iya fuskantarta don haka kawai wani store market yace ya sauƙe shi, yana son yayi sayayya don gaba ɗaya babu ababuwa da yawa na ci. Tsaf suka kammala sayayyar duk abinda yake so don ya rantse a wannan karon ze musu yajin da yake jin be taɓa musu irin saba kaf rayuwarsa. Mecheal ne ya wuce da kayayyakin zuwa cikin mota shi kuma yana tsaye yana duba wayarsa da wani saƙo ya faɗo masa. Kamar ance daga kanka ya ganta cikin hijjaba dogo har ƙasa fuskanta ƙawace da murmushi me kyau tana tafe tana ɗago hannu alamar sallama sune yi da wata ko wani, har ta isa inda tayi parking car nata bata dena daga hannunba, ɗayan kuma riƙe da keda bame girma ba. Tana ƙoƙarin buɗe motar ta ta shiga taji kamar tsaiwan mutum a bayanta, a hankali ta ɗan juyo ido biyun da suka yi ne ya saka ta haɗe kyakkyawar flluskarta nan take cike da fushi. John kuwa kallonta kawai yake
Idanunsa a kanta ko kyaftawa ba yayi.
“I like you, nd I Miss U My unknown beloved…” ya faɗa a hankali wanda ya saka bakinta rufewa ruf daga Ƴar ƙaramar haukar da taso manna masa. Domin kuwa ba ƙara mun duka kalmar ta mata ba a cikin zuciyarta. Amma kuma se ta dake saima wata ƴar dariyar rainin hankalin da ta yi ta nuna shi da yatsanta manuniya ta ce. “You made a mistake…” ta faɗa a hankali kafin ta sake nuna shi da yatsan taci gaba da cewa “Kayi kuskuren fahimta.”
Kaɗan ya matsa gabanta hannuwansa duka biyun zube cikin aljihunsa yace.
“I’m serious.”
Ɗaga hannu tayi ta dakatar da shi ta hanyar furta.
“Don’t.”
Sai kuma ta ɗan matsa kusa da shi kaɗan… idanunta har sun sauya zuwa na fushin kai tsaye tace.
“Who Are you?, kai ɗin wanene? How dare you talk about my life?, menene haɗin ka da rayuwana?.What do you want?,why did you bring me here?, leave me I can't... ka fice daga cikin rayuwana idan ma kwai wani lalataccen buri kake dashi a kaina to ina son ka sani Nie *HAUWA KABEER USMAN MAINA* nafi ƙarfin ka!, domin kuwa ba kanwar lasarka bace, idan ba dan wani tunani daban kazo to ka sani cewar wannan yasmine ɗin dake tsaye gabanka ba irin sauran marasa ɗa'ar nan bace irin ta Addininku na christian. Domin Addinina da naka… sun yi nisa da tazarar dake tsakaninsu tamkar tazarar dake tsakanin ƙasa da sama ne, don haka ka fita a cikin rayuwana gaba ɗaya, in ba haka ba wllh³ zaka yi nadamar sanina a cikin rayuwarka ok?....” daga nan ta shige cikin motar ta fuuuu ta jata da mugun gudu tana barin wurin. Wani huci me zafi ya fesar kana ya kaima iska naushi ya shige tasu motar suma suka tafi.