Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
da tace da ita zasu haɗe. Don duk iskancinta tana tsoron mamy'n nasu. Sum sum take tafiyar har ta kai gaban daddy'n, zaunar da ita yayi gefensa yana tura mata duka kayayyakin dake jere a gabansa. "Eat it ambasajo na" Murmushi ta masa tana gyaɗa kanta wanda babu ko band. "Ina ɗankwalin ki Hau'wa?" Haka ta tsinkayi muryan Mummy nata wacce tayi maganar da ɗan ƙarfi, tura ɗan ƙaramin bakinta gaba tayi, domin idan da sunan da yasmine ta tsani taji an ƙirata dashi to shi ne Hau'wa. Har ƙara ƙara yasmine ɗin ma amma ita a son samunta kowa ma ya dinga ƙiranta da ambasajo ɗin da mahaifinta ke ƙiranta dashi. "Ba magana na ke miki bane yasmine?" Ta sake wulla mata tambayar a karo na biyu. "Ambasajo ɗin Daddy'n ta maza tashi kije ki samo ko hula ne, Mummy naki bata son a zauna lafiya kinji". Kanta ta ɗaga mishi tana tashi tana tashi,"yawwa that's my girl" babu jimawa kuwa se gata ta dawod da Baby shijjab jikinta. _*HAUWA KABEER USMAN MAINA*_ kenan da akafi sani da suna _YASMINE HUTU_ ƙyaƙyƙyawar budurwa ce mai kimanin shekaru ashirin da biyu a duniya. Wacce ta kasance ɗiya da farko a wurin mahaifinta Ambassador kabeer Usman Maina, Mahaifinta sananne ne da kowa kusan duka duniyar ta sanshi kasancewar matakin ambassador ɗin daya riƙe.Bayan haka babban ɗan kasuwa ne kuma mamallakin duk wani company'n dake tashe a zagayen Lagos da ketarenta. Yasmine yarinya ce da batajin magana sammm, amma ga wanda be santa ba kai tsaye ze mata kallon nutsatstsiyar yarinya ne, Se dai sammm ba haka take ba. Wanda badan mahaifiyarta dake tsaye a kanta ba da tuni rayuwarta ta jima da taɓarɓarewa, domin kuwa mahaifin shike wuce mata gaba a duk wani rashin ji da kirki nata, Idan mahaifiyarta ta tilasta mata zuwa islamiyya setayi tafiyarta manyan club's ko park. Se ta dedeci loƙacin tashi yayi kana ta nufo gida. kullum zaka kalleta idan zata tafi cikin shigar kayan islamiyya, wanda hakan yasa wasu ke mata kallon kamila kuma natsassiyar mace. gata masifaffiyar gaske ce lamba ɗaya ta bugawa a jarida. Ƴar gata ce shalele kuma ƴar shagwaɓa a gidansu, Musamman ma ga mahaifinta ambasador kabeer maina. Gatan data samu da rayuwar da take a cikin ta seta tashi tamkar renon turai,Inda ta samu zurfafa kanta harta samu wadataccen ilimin boko, sedai na addinin kuwa ko oho amma fa idan ka taɓa ta akan addinin ta bata barin ko ta kwana, wacce zaka ɗauka cewar ita ɗin irin wannan shahararrun yaran nan ce masu haddar Alqur'ani izu sittin a kansu, sedai ko rabin izu bata da. Karatunta kuwa gaba ɗaya a ƙasar ƙetare ta yisa, idan ka cire Nursery school datai a Nigeria kawai. Sam bata son harkar talauci ko haɗa hulɗa da mutanen da suka kasance talakawa, wannan dalilin nema yasa sammm ta tsani islamiyyar da Mahaifiyata ta saka ta. A cewar ta haɗa wurin zama tare da su harma da shaƙar numfashin juna kan iya taɓa ta itama, wai wataran ta zama irinsu kodai ta auri talakan, Wannan dabi'a tata yana taɓa mahaifiyarta kwarai da gaske. Abu ɗaya ne ALLAH ya taimaketa da nisantata da shi duk da rayuwar turai data tashi a ciki, shi ne kasancewa da namiji. Sedai takanyi irin su sking love haka don tace wannan kamm babu laifi, amma fa ba Inji AMMEY LAYLERH ba 🤗 🤣 ato. Inji yasmine lol 😄😍........
"Ambasajo ku matso mu fara dinner, kamar Omer yana nan ma ko?" Yayi maganar da alaman tambaya. Husna ce ta ɗaga kanta ita kuwa yasmine ko motsi batayi ba, duk kuwa da cewar Omer ɗin dan ita yazo.tana ƙoƙarin buɗe kyakykyawan foodplask ɗin dake gabanta, sega Omer ɗin nan ma yana sauƙowa daga saman bene mai ɗan jiki kaɗan haka fari tas da shi. Wanda fuskarsa ke ƙawace da kwantatciyar saje da gemu mai ɗan tsawo, yana da manyan maganai kamar bull ga dogon hanci, wanda kallo ɗaya zaka masa ka kalla irin tsantsar kamar dake tsakanin sa da matar da suke kira da Mummy. A natse ya ƙara sa saukowa daga zuwa downstairs ɗin yana zama. Tare da furta. "Good evening Daddy", "Good evening Omer how was your night?" Cewar Daddy ɗin Mummy na tura masa plate ɗin dake ɗauke da abinci. Husna ce ta fara gaida shi, yayin da yasmine ta sha kunu, domin ita yanzu tunda Mummy nata ta fara sako zancen aure tsakaninta da Yaya Omer ɗin ta dena sakar masa fuska. "Hala yasmine da dukkan alamu bata ga Omer ba ko?" Mummy ta faɗi cikin gatse. Fuskarta ta ɓata ita fa wllh shi yasa sammmm bata son zama kusa da Mummy'n, duk wasu hanyar kusheta seta fito mata dasu, da kuma diagata gaban ko su waye. Ranta a ɓace ba tare data kalle shi ba ta ce dashi. "Ya Omer good evening da "how was your night?" Ya amsata yana ɗan sakar mata murmushin sa me kyau. _I don't like her_ ta faɗi a zuciyarta tana murguɗa masa baki, wanda hakan da tayi ya sanya Omer ɗin kallonta yana waro idanunsa sosai yana kallonta speechless. "Baby yadai? Nafa kina murguɗa min baki" Ya faɗi yana sake waro idanunsa akanta. "Malam wai ina ruwanka da nine ka fiye takura min fa Aha! Kana takura rayuwana."
"Ya takura rahuwar taki yasmine!, Me ya sa ke samm baki da kirki ne idiot kawai" Mummy'n ta ta faɗi a fusace tana miƙewa tayo kanta. Wanda ya sa ta kwasa a mugun guju tana ce dashi zasu haɗu ne. Ta haye samanta tana sauƙe ijiyan zuciya, a gaban mirror taja ta tsaya tare da zare band tare da ribbon ɗin kanta, tana tsurama kanta Ido slowly ta tura hannayen ta cikin gashin kanta, ko me ta tuna kuma se ta wani daki kan nata kaɗan. Tana me furta "Ohhhh ALLAH!!!" A bayyane sakamakon gilmawar kyakykyawar face nashi data gani a cikin zuciyarta. Daidai kuma lokacin ne aka fara yayyafi, kafin a tsuge da ruwan saman sosai, yanayin yayi wani irin daɗin gaske, ga wata irin ni'imtacciyar iska wadacciyar da ta ga gauraye ko ina dake cikin garin. A daidai kuma wannan lokacin John ke zaune cikin motarsa yayi Parking nata a wani bakin masjid. Tin yana saka ran za'a dauke ruwan har ya cire. Don kuwa yaga abin bana ƙare bane, se yaji duk zaman motar ya gama gundirarsa. Don haka a natse a kuma wani irin Hankali ya fito daga cikin motar. Wata brander ya hango babu kowa a wurin, se yaji kamar hankalinsa ya ɗan nutsu da daya zauna a wurin. Umbrella ɗin dake bayan motar ya miƙa hannunsa yana ɗauka, kai tsaye yana yin wajen....
*Around 5:00pm*
♡
Ahankali slowly ya shiga buɗe blue eyes nashi wanda suke ɗauke da barci, kai da ganin idon nasa zaka san cewar idon nasa barcin be gama ishar shi ba, yanayin seya sanya idon nasa ya ƙara kyau dan yanayin se yayi yanayi na daba, wani kalan saurin miƙewa a zabure yayi tuno da wani kalan hargitsetstsen mafarkin da yayi akanta. Wani kalan duka yaji ƙirjin sa ya masa lokaci guda, wadda yasa yaji barcin ya watstsake masa, miƙewa yayi zaune a tsakiyar makeken gadon nasa yana dafe da saitin faffaɗar kirjin sa, "What happiens?, Meke shirin faruwa da rayuwana? " dan bai taɓa jin makaman cin wannan bugun zuciya ba a tattare da shi, shiru ya ɗan yi na ɗan lokacin kafin ya yaye bargon jikin sa a hankali ya zuro zara zaran kyawawan fararen kafafunsa zuwa ƙasan bed ɗin kana ya miƙe yana nufar toilet. Wanka yayo yana fitowa jikin sa na ɗigar ruwa ya shirya kansa cikin wani haɗaɗen jeans mai kyau da tsada launin baki da high neck sleeve shirt launin ash, hakan ya bayyanar da kakkafar suran ƙirjin sa, faffaɗar kirjin nan nasa abuɗe take sosai cikan damatsan hannun sa yasa faffaɗar kirjin nasa ta kara buɗe wa sosai, ba karamin kyau kayan suka masa ba, kamar dan shi akayi su se hular pcap ɗin daya sanya, bayan ya ɗaure dark black curly hair nashi inda gashin ya sakko harta ƙasar ƙeyarsa. Kai tsaye yana fitowa zuwa garden na shi, yayi kyau over ita ma hulan ta masa kyau sosai, fuskar nan a ɗaure take tamau don mafarkin da yayi sosai ya sake taɓa zuciyar sa, don haka na yau ma tafi na kullun matse wa, jikin sa sai tashin fitinannen kamshi yake, hannunsa na ɗaure da diamond watch me shegen kyau, kyawawan kafafun sa na sanye cikin Hermes Birkenstock sandal wadda a kalla kuɗin sa ya kai $56000, kasan cewar takalmin launin baƙi ne sai yayiwa farar ƙafar sa bala'in kyau bana wasa ba, a natse yake takunsa irin na manyan jaruman na, ko baka gan shi ba kaji sahun takun sa kasan cikkaken namiji ne mai jini a jika kuma lafiyayye kakkarfa ke tinkaro ka. Zaune ya kai kan wata Linder exclusive chair fara. Tare da janyo laptop nashi yana fara wasu ayyuka ta cikin ta. Cikin kwanciyar hankali yake danna laptop amma fa da an jima kaɗan zaka kalla yana famar cizan lallausan laɓɓansa, ga lips nashi har ya ƙara yin jawur kamar yasa lipstick saboda ciza sun da yake famar yi a kai a kai, duk wannan latsa laplop da yake hankalin sa na can duniyar tunanin me wannan mafarkin da yayi yake nufi?, dan shi har yanzu yaƙi bama ko wacce ƙofa kome mafarkin nasa yake nufi, duk lokacin kuma daya tuna mafarkin sai yaji zuciyar sa ta buga, Tamkar walƙiya haka yaga gilmawar fararen mayun idanunta, zaro nashi idon waje yayi yana tunanin wai meke shirin faruwa da shi ne haka?, "Oh Jesus help" ya furta a bayyane yana kaima iska naushi tare da furzar da abin da ya to kare ƙirjinsa. Tsaye ya miƙe ya shiga kaiwa da komawa zuciyar sa na daɗa ɗaukar ɗumi....
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
𝐂𝐎𝐌𝐌𝐄𝐍𝐓𝐈𝐍𝐆 𝐀𝐍𝐃 𝐒𝐇𝐀𝐑𝐈𝐍𝐆
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 3
Paid book
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
_Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_
```Mommah Narh!, Oum narh, Masoyiya ta Ashanty love, tare da ƙaunata Nainerh kd, tare da Ta Ƙarfen (Rabi'atu Fulani),Aysher Na Lado, Aunty Sayyada narh,ku sani haƙiƙa bana da baƙin da zan iya buɗewa wajen furta kalmomin tarin ƙaunar da kuke min, kawai abinda zance Rabb yabar ƙauna ta har gaban abada abadan abada....```
ꨄ Shigowar ƙira ta hanyar vebratin Vibrating ring doorbell sound ɗin da wayan shi ya soma ne ya sanya shi dakatawa cak, ɗakin ya ɗau wani shiru… se ƙaram vibrating na wayar kawai, amma zuciyar John na bugawa,
numfashinsa kuma na fita da sauri da sauri idanunsa jajir, jikinsa na rawa kamar wanda aka zubar da shi cikin sanyi.
“Problematic Girl” ya furta a hankali murya cike da rauni, sakamakon hotonta daya sake gitta fuskansa. Wani kalan rumtse idonsa yayi kafin da ƙarfi ya ɗaga hannunsa ya bugi madubin da ke gabansa... Take madubin ya tarwatse ya zama gutsuttsura, jini ya fara fita daga hannunsa… amma bai ji zafi ba.
Abinda yake ji kawai…. Idanunsa sunyi jaaa sosai gefe guda kuma ga gutsattsarin madubin daya fashe nan suna walƙiya a ƙasa, suna nuna fuskar John.... fuskar da duniya ta sani a matsayin kwararren matukin jirgin sama, amma yau ita ce a rikice haka.
Numfashinsa na fita a hankali, amma zuciyarsa kamar zata fashe.
“A dream? No… this isn’t a dream.?” ya furta murya ƙasa ƙasa sosai, wannan ba mafarki bane kawa, wani abu ne da yake neman karya shi daga ciki. Yana tsaka da wannan tunanin har besan lokacin aka sake kiran shi ba a karo na biyu ba, shigowar ƙira na ukun ne ya katse masa tunaninsa, yana sake lumshe ido ya nufa wayar nashi ya ɗauka a hankali, ahankali raunin daya jima hannunsa ke zubar da jini, Screen ɗin ya haska.. _CAPTAIN JOHN – PRIORITY LINE_ Idanunsa ne suka ɗan sauya colour,wannan ba kawai ƙira bane na kowa da kowa ba, ƙira ne me muhimmancin da duk abinda yake yi da zarar ƙiran ya shigo se iya katse ko uban maye kuwa.. kai tsaye answering call in yayi...
“Captain John speaking.”
Muryar da ta amsa masa cike take da girmamawa.
“Sir… we need you!. Urgent deployment. International flight. No one else can handle this route like you.”
Wani kalan shiru yayi sai numfashinsa kawai dake ɗan fita kamar a wahalce, yana kuma furzar da wata iska me zafi daga cikin bakinsa, ya jima da sanin cewa shi ne mafi kyau. Shi ne kuma wanda ake nema idan komai ya tsananta, shi ne… wanda sama ta yarda da shi. Se dai tunanin da yake a yanzun shi ne cewar anya ze iya?, domin zuciyarsa tana can a wajen yasmine.
“Sir?”
Aka sake ƙiran sunansa wanda ya saka shi lumshe ido, yana jin kalmar mafarkin tana dawo masa amma yana danne hakan. Se ma buɗe rinannun idonsa a hankali da yayi. “Prepare the aircraft…” ya faɗa da murya mai sanyi.
“Captain John is coming.” Ya katse wayar amma bai motsa ba, A karon farko yana jin wani tsoron tuƙa jirgin cikin rayuwarsa, ba wai tsoron jirgi yake ji ba, A ahhh se tsoron zuciyarsa kawai da yake ji dangane da lamarin da take nemar jefa shi, cikin danne duk wani abinda ke taso masa ya miƙe a natse da ƙyar ya faɗa toilet, bayan yayi dressing ya tsaya gaban madubi.
A hankali ya gyara farar rigarsa mai tsabta, ya ja hannun rigar ya daidaita cuff nata sannan ya ɗora epaulets ɗin zinariya a kafaɗunsa masu ɗauke da layuka huɗu masu walƙiya. Alamar dake nuni da iriyar kwarewar da yake da da kuma babban matsayin da yake takawa a sararin samaniya duk da kasancewarsa ba musulmi ba. A natse ya ɗauki tea shima baƙi ya ɗaura shi da nutsuwa. Idanunsa suna kallon kansa cikin madubin amma zuciyarsa kamar tana wani wuri daban, sanin cewar tuƙin dare ne zeyi gashi kuma ƙasar daya nufa me sanyi ce ya saka shi ɗaura
jaket ɗinsa dark blue akan shigar ma'aikatan dake jikinsa, yana sake daidaita komai ya yi fitting kamar an ƙera shi ne domin shi kaɗai dama, p-carp nashi ya ɗora a kans. sannan ya ɗan sunkuyar da kansa kaɗan yana kallar yadda cikakken kamanninsa na iko, na izza na wanda duniya ke girmamawa... A natse ya soma takowa zuwa entrance ɗin fita daga parlourn nasa zuwa na gidan gaba ɗaya, yana tafiyan ne kuma takalman sa baƙi masu sheƙi suna bada umarnin saƙƙowarsa.
“John…”
Haka yaji murya Mahaifiyarsa da wasu lokutan yakan ƙirata da Mother ko Marh ta daki kunnuwansa, don haka cak ya tsaya a hankali tare da juyowa,
A nan ya hango Madame Victoria tsaye daga jikin ƙafar benenta cikin kayan alfarma, idonta cike da wani abu mai wuyar a fassara shi kai tsaye… wanda yafi kama da tsantsar ƙauna kai tsaye ta sake jefa masa kalmar...
“Where are you going tonight?”
ta jefa masa tambayar a hankali amma muryarta na ɗauke da nauyi, wani daƙune farar fuskansa yayi yay kaɗan…
“I was brought to Florida by an urgent job”
Wani yanka zuciyarta tayi tana faɗuwa tare da takawa kusa da shi idanunta na sauka kan epaulets ɗin sa...
“Captain…” ta faɗa a hankali kamar tana ƙoƙarin gwada kalmar ne, tare da ɗago da kanta ta kalle shi kai tsaye bayan ta iso har inda yake tsayen.
“Amma wasu hanyoyin ba kowanne ne ya kamaci ace ka bi ba, John!, saboda ban gama yarda dasu ba...”
Kai tsaye kalmar Mother ta tsaya masa a zuciya, domin kusan ya gama haddar waɗan nan kalmomin kamar tana nufin wani abu ne daban. Amma koma dai miye shi yanzun baya da lokacin ɓatama lokaci lokacinsa, peack ta bashi a goshi tare da sake nanata masa kalmarta irin ta ɗazun sakk dai, wanda ya saka John matse hannunsa a hankali.
“Me kike nufi, Mother?”
Wani kalan shiru Madame Victoria tayi kafin ta juya baya, ba tare da ta ba shi amsa ba ta furta... “Ka yi hattara da abin da nake yawan maka tuni Love bye....” ta faɗa tana barin entrance ɗin da yake gaba ɗaya kamar wata walƙiya. Tsaiwa kawai a wurin John yayi zuciyarsa na bugawa da ƙarfi. Kalmar “Ba kowanne hanya ba…” na sake dawowa cikin kansa, lumshe idanunsa na ɗan lokaci yayi numfashinsa na fita a hankali.
wayarsa ta sake ƙara wanda ya yanke masa tunaninsa... Yana answering call in aka sake furta...
“Captain John… we need you NOW.
Emergency flight to Florida No delays pls.” take komai nashi ya dawo yaji kamar ana ingiza jinin jikinsa duk wata damuwarsa na ɓacewa zuwa ƙwarewar da duniya ta gama sanin shi da ita.
“Copy that,” ya faɗa a natse yana juyawa ya nufi hanyar ficewa kawai tare da ƙoƙarin saka ƙiran Paah nashi. Wayar na fara ring Papa nashi ya amsa da....
“Hello, John?”
A hankali yace, “Paah!, I’ve been called in… it’s urgent.” kafin ya ɗan ja numfashi ya sake furta. “I’m leaving for Florida… right now.” daga inda paah nashi yake ya wani karkatan da kansa tare da furta, “Florida? Right now?” tamkar John na a gabansa ya gyaɗa masa kai yana kuma ci gaba da tafiyan ya ce... “Yes… there’s no delay. I’m the only one they can assign to this route.” wani ɗan numfashi Papa'n nashi ya fesar tare da