Advertisements
Chapter 29 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   29 / 31

84K to 87K   out of 91.1K words

Nan take Ummien ta tsaya cak,
ƙirjinta yayi wani irin bugawa sai dai ta ɓoye komai a fuskar ta, sai ma cikin natsuwar data bata amsa.

“Saboda wataƙila ƙaddararki tana gabatowa ne....” Kalmar ta sake jefa JANNEERH cikin wani irin yanayin daya sakata lumshe idanunta tana jin wani sanyi da zafi a lokaci guda.


A Can waje kuwa… Mama Rukayya da Mama Bilkisu dake zaune suna ci gaba da gyaran zogalensu ne Mama Bilkisu wato Anty Amarya ce ta taɓe baki tace.
“Ni wallahi yarinyar nan tana bani tsoro ma.” Mama Rukayya data kalle ta tare da gyara zamanta tana sake tattare bakin zaninta tace.

“Tsoro kuma?”

Ta matso kusa da ita tana rage murya sosai tace. “Kinga yadda MALAM yake ɗaukakarta kamar wata waliyyiya?”
Tsaki ɗayar tayi tana furta, “To ba dole ya ji da ita ba, kar fa ki manta itace mikullin arzikinsa” cike da isgilanci suka saka dariya Mama Bilkisu tace.
“Ni dai har yanzu ban yarda babu wani abu a tattare da ita ba. In banda haka wacce irin budurwa ce shekaru suna tafiya amma babu namijin da ya isa ya tsaya a gabanta?”

“Kin manta da ɗan Alhaji Bashir ne?”

Mama Bilkisu ce ta ɗan rage murya sosai tace.

“Ehhhh fa to shi ma daga karshe ai cewa yayi ba ita Hafsa ɗin yake nufi ba, Hafsan gidan Uba tela yake nufi”

“Yo in ma dai ita ɗin ce ai gashinan maganar gaba ɗaya ta mutu, tun da har yau babu wanda yace yasan abinda ya faru bayan hakan...” Wani irin shiru ne ya ratsa tsakaninsu. Kafin Mama Rukayya ta ce. “Ni dai bana son yarinyar nan. Saboda yadda take kallon mutum da idanunta kamar tana karanta zuciyarsa… nifa wani sa'in wallahi haka kawai sai naji jikina yayi sanyi ma...”
A dai-dai lokacin ne kuma JANNEERH ke fitowa daga ɗakin Ummie ɗauke da hijabinta da littafi a hannunta zata nufi bedroom guda da Baffanta ya ware mata ita ka dai. Da sallama cike da girmamawa ta sake wuce su amma kamar kullum… ba wanda ya amsa mata da kyau. Har ta kai bakin ƙofar bedroom nata kamar abin kirki Aunty Amarya ta kira sunanta.

“Hafsat…”

Ta tsaya cikin nutsuwa tana amsawa da.
“Na’am Anty…” Mama Bilkisu ta kalleta sama da ƙasa kafin ta mele baki tace.
“Yaushe zaki daina fakewa da karatu da wa’azi ne wai don ALLAH ki nemi mijin aure ne?” Wani irin shiru tayi tamkar wanda ruwan sama ya cinye kafin ta sauke idanunta ƙasa cikin ladabi tace.
“ALLAH ne mafi sanin lokacin komai Mama…” Mama Rukayya ce ta bushe da dariya tare da amshewa da cewa.
“To ai idan kika ci gaba da jiran irin haka kina fakewa da ALLAH ne bai kawo ba zakici gama da zama haka har tsufa.” Kalmar ta shiga zuciyar JANNEERH kamar an caka mata allura sai dai ta haɗiye komai. Domin tasan idan ta tsaya kare kanta…Rashin kunya ne don a hankali tace. “ALLAH ya kyauta…” har ta juya zata wuce amma
muryan Mama Rukayya ta sake katse mata lissafi.

“Ko kuma dai akwai wanda zuciyarki take jira ne?”

Cak haka jannerh ta tsaya ba tare da ta shirya ba… zuciyarta tayi wani irin bugawa don ji tayi kamar an ambaci wani abu da take ɓoyewa daga kanta ita kanta. Sai dai kafin ta iya magana…
Ummie ta fito daga ɗaki. Idanunta cike da izza da hikima ta kalli matan gidan nan take suka yi tif tace.

“Ku dena ɗora wa yarinya nauyin da ALLAH bai ɗora mata ba.”

Mama Bilkisu da take Amarya ce ta taɓe baki tana cewa “Mun dai faɗi gaskiya ne kawai.” Ummie ta gyara tsayuwarta tana jefa mata wani kallo tace.

“Gaskiya? Shin wai yaushe rashin aure ya zama aibi ga mace a ƙasar Nigeria ne?” aikuwa suka yi tif kamar ruwa ya cinye kana cikin nutsuwa ta ɗora da fadin. “Idan aure ne ma’aunin darajar mace…to da matan Annabawa basu fi sauran mata daraja ba.” Wani shirun suka sake yi don kaf cikinsu kowa shakkarta yake, Ummie ta kamo hannun JANNEERH tace.

“Ku bar Hafsat da ƙaddararta.”
Sai ta kalli yar tata cike da nutsuwa da jin kwarin gwiwwar tabbas MIJINTA seya kasance na daban ɗin da sai duniya tayi alfari da wannan auren bama iyaka matan gidan ba, don haka cike da jin cikakken yakini tace.

“Domin duk ranar da ALLAH zai buɗe mata ƙofa tabbas kowa sai ya san cewa jinkiri ba yana nufin rashin dacewa bane.” fuuuuu haka taja hannun ƴar suka wuce.

★KABUGA JAN BULO★

Wani irin shiru ne ya mamaye parlourn gidan gaba ɗaya, sai ƙarar pages ɗin Alƙur’anin dake hannun IBRAHEEM da yake juyawa a hankali.

YASMINE kuwa kwance take saman kujera tana scrolling wayarta hankali kwance kamar babu wata damuwa a rayuwarta. Tun bayan maganar jiya…
IBRAHEEM ya shiga wani irin yanayi na zurfin tunani, bawai saboda ya tsani YASMINE ba…A’ahhh har yanzu yana sonta sai dai a karon farko ya fara fahimtar cewar soyayya ita kaɗai ba ta wadatar da aure. Mutum biyu na iya son junansu amma zuciyoyinsu su kasance a duniyoyi daban kamar yadda ya kasance a gare su. A hankali ya ɗago idanunsa daga karatun da yake yi ya kalleta.

“YAS-MINE…”

Ta amsa ba tare da ta ɗago ba da.
“Hmmm?” wani ɗan murmushi kawai yayi kafin yace “Zan iya tambayarki abu ɗaya?” guntun tsuki tayi tace.

“Kamar ya ya?”

“Kin taɓa jin tsoron ALLAH kuwa bare kuma kiyi tunanin haduwarsa dake?”

Cike da fusata ta mike tsaye tana me furta.

“Wai me yasa duk wata magana taka sai ta koma addini ne?” Cikin natsuwa yace “Saboda rayuwata gaba ɗaya addini ne.” Kallonsa take tana wani jijjiga kai kamar ƙadan garuwa kafin tace. “To ni kuma rayuwata ba haka take ba.” Kalmar ta tsaya masa a zuciya sai dai bai fusata ba. Sai ma a hankali ya rufe Alƙur’anin hannunsa yana kallonta sosai yace. “Kin san me yake bani tsoro dan gane dake Yasmine?” gira ɗaya ta da ge masa alamar really?. Kansa ya jinjina mata yana me furta.

“Ba rashin sallarki ba ne, ba kuma halayenki ba…Abin da yake bani tsoro shi ne yadda baki jin akwai matsala a cikin abin da kike aikatawar.”YASMINE ta ɗan ƙame karo na farko maganar tasa ta shiga zuciyarta kaɗan. Amma son zuciya ya hana ta nuna hakan, cikin rashin damuwa tace.

“Ni dai don ALLAH ka barni na huta haka nan…” ta juya zata shiga bedroom nata, amma muryarsa ta sake dakatar da ita. “YASMINE.” ya sake ƙiran sunanta, ta tsaya ba tare da ta juyo ba.
A hankali yace. “Na rantse da ALLAH idan har baki gyara tsakaninki da UBANGIJINKI BA, wata rana zaki shiga cikin duhun da babu fitarsa.”

Kalmar ta sata jin wani irin faɗuwa a zuciya ta danne komai ta shige ɗaki tana buga ƙofar. IBRAHEEM ya lumshe idanunsa yana sauƙe wata irin ajiyar zuciya mai zafi tare da ambatar
“Ya ALLAH…” cikin sanyin murya da kuma tausasa kalamai ya ce.

“Ka taimakeni akan abin da zuciyata ta kasa gyarawa…”
★

*AUJARA JIGAWA*

Ahankali guntun yayyafin da aka gama tsala ruwa ke sauƙa saman kwanukan gidajen bayan ALLAH. JANNEERH zaune take kan sallayarta bayan idar da nafila Idanunta a rufe hannunta kuma riƙe da carbi. Gaba daya yau ɗin jin
zuciyarta take ba cikin nutsuwar data saba samu ba ce. A kuma karo na farkon data kasa fahimtar dalilin bugawar zuciyar nata, Wanda take jin kamar akwai wani muhimmin abun dake kokarin gabatowa cikin tata rayuwar ne. Wani abu mai nauyi, wani abu da zai sauya mata komai. A hankali ta buɗe idanunta wanda taji hawaye sun gangaro mata, kirjinta ta dafe tana mai furta.

“Ya ALLAH!!!...Meye wannan da zuciyata ke ji ne?…ji nake kamar akwai wani baƙin ciki da yake nemar hanya zuwa gareni…” Sai kuma tayi saurin girgiza kanta kamar wata karamar yarinya tace.

“Ko kuma…wani mutumin da ban san shi ba?” Nan take ta tuna da mafarkin da ta yi jiya. Wani namiji cikin duhu
fuskarsa bata fito sosai ba amma zuciyarta na kuka saboda shi. Da sauri ta mike tsaye kamar mai gudun tunani.
Ta ɗauki Alƙur’aninta tana son ta karanta domin ta samu nutsuwa, ta buɗe idanu a hankali ta kalli rubutun Alƙur’anin, ta fara karantawa amma ba ta kai ko aya uku ba sai ta dakata.
Ta sauke Alƙur’anin a gefe ta dafe kanta ta sauƙe numfashi mai nauyi, tana mikewa ta fara zagaya ɗakin. Daga yanda take zagaye dakin ko bata budi baki tace maka komai ba zaka fahimci cewa akwai abinda ke damunta, amma ita kanta ba ta iya fassara abinda take ji ɗin ba. A natse ta kalli window ɗin ɗakinta da iska ke motsa labule.

Hannayenta ta zira ta cikin window ɗin ta ɗora kanta saman ƙarfen windown, ta jima jingine a haka kafin ta juya ta
koma ta zauna a kan gadon.

Alƙur’aninta ta sake buɗewa ta fara
karantawa cikin nutsuwa, wannan karon kam ta yi ƙoƙari sosai ta ci gaba, har ta kai wani lokaci tana karantawa ba tare da tsayawa ba. Amma duk da haka zuciyarta bata mata sanyin da take son mata ba, maganganun su Mama Bilkisu ne kawai ke famar mata amsa kuwwa. Alqur'anin ta ajje a gefen gado.
Ta zauna shiru na ɗan lokaci, kawai tayi shirun dake dauke da wata damuwa boyayya a fuskarta. A natse ta miƙe ta isa gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta na ɗan lokaci. Tana son ganin ta inda take da wata tawaya ko aibu, saidai kuma babu wani abu da ya bambanta a fuskarta, amma ita tana jin kamar wani abu ya canza a cikin zuciyarta. Ahankali ta janye idanu daga kan madubin ta koma gefen gadon tana sake zama tana tunanin rayuwar gidansu.

Rayuwar gidansu data kasance wata irin rayuwa ce mai cike da san zuciya, sabanin shekarun baya da gidan yake cike da wata irin tsafta da girmama juna. Saboda tsarin zaman gidan abun burgewa ne ga kowa,har dama mutanen anguwa lokacin da Unmeinta ke tare da Uwar gidan Baffan nasu Mama Sakina. Mace me hakuri, kara kawaici, a lokacin tana babbar yarta mace Sadiya, se kuma namijin dake bi mata Salisu. Sedai zaman nasu be wani ci nisan wuta ba ALLAH ya amshi ran Mama sakina, Bayan rasuwarta ne Baffan ya sake auro Mama Rukayya kafin Aunty Amarya. Amma banda yanzun da zaman gidan yake kusan a hargitse, wanda ɗan wannan wancan be isa hukunta wa ba, ga shegiyar hassada da munafuncin tsiya komai na tsegumine. Su kuwa a da tun daga kan yanayin soyayya kulawar da suke gwadawa juna idan ka shiga gidan baka isa cewa kishiya da kishiya bane, ga yaran nasu suma kowa na kaunar kowa babu kawo munafuncin uwar wane ta dake ni,duk lokacin bata da wani cikakken wayo sai Yayarta Aunty Binta. Su kuma matan gidan nasu na yanzu abinda ya sake sakasu tsana da jin haushin ummien saboda kawai Mijin nasu karara yafi son ta akan akansu, kodan kasancewarta gwana wajen tsaftar jiki da kuma ta gida da yaranta, bata yarda da daukar kowanne irin wargi daga sauran matan. Amma kuma tana hakuri sosai akan yaranta, bata fiye magana akan su ba, dama kuma yaran nata uku ne kawai, daga Aunty Binta sai Yaya Jafar, sai kuma ita da take auta, duk da bayan ita tayi haihu amma dan ma be zo da rai ba. Wannan abu shi ya saka bakar kiyayya a tsakanin matan nasu har suka hade mata kai se dai bata damu babu ruwanta rayuwarta kawai take yi, tun tana da tabbacin Mijinta na so da ƙaunarta.

Ahankali ta kawo gauruwar ajiyan zuciya tana saukewa lokacin da karar wayarta ke katse mata lissafi, ganin sunan Aunty Binta ne ya saka fuskarta faɗaɗa da murmushi me kyau, mayar da kiran da har ya riga ya katse tayi, kai tsaye Aunty Binta ɗin ta taryeta da cewan...

"Me kike yi ne haka da tun dazun nake ta kiranki ina son ki hada ni da ummieh amma baki amsa ba?...”

Bata iya karya ba, ba kuma ta iya launa zance don kare kai ba, don haka kai tsaye tace. “Na ɗan tafi wani tunani ne Aunty narh ta kai na....”

“Hmmmm!, wato dai ba zaki dena cusama ranki tunanin ban za ba ko HAFSAT?”

Ɗan murmushi kawai tayi tana katse maganar da bara in mika mata wayar, daga haka ta yanke don ta san korafin yayar nata ba karewa zai ba inta fara zubo shi. A tsakar gida ta ganta tana ɗurin humrorin da take hadawa da kanta har dasu turaren wuta ne, Kabbasa ce, madarar turaren zalla duk dai wani abu daya danganci kayan ƙamshi babu abinda bata sayarwa. Tana amsar wayar Aunty Binta din ta ɗora da fadin.

“Haba Ummie wai me yasa wani lokacin Hafsa ta fiye taurin kai ne uymmm?, ba zaki saka ta dena banza yen tunannika akan wasu can mutanen da ba gama sanin kansu su kayi ba bare kuma ubangijinsu”

“To Sarkin korafin kin gama ko kuma da saura?, dama shi ne maganar da kika kira ki gaya min?”

Ɗan rusunar da murya tayi tana kuma gaida ta cike da girmamawa tana cewa tayi hakuri dama wata makwafciyar tace Maman Meemah take son hadin humra na dubu talatin. Ɗakinta ta shige da wayar ita kuma Hafsa ta zauna tana ci gaba da duddura humra ɗin, ummien na gama shige wa ɗakin nata Su mama Rukayya suka wani ja tsaki ƙasa ƙasa suna furta aikin banza. Kallo basu ishi Hafsa ba taci gaba da zuba Humrarta, babu jimawa ma sai ga ummien ta fito ta amshi zuba humra ɗin don lokacin zuwan ta Islamiyya yana daf.

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215

*AMMEY LAYLERH ✍️ *

08104493215






*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 30

Last free page's

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡

Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

♡♡♡♡

ꨄ Wani irin shiru ne ya mamaye parlourn gidan gaba ɗaya… Shirun da idan mutum ya zauna a ciki na ɗan lokaci zai fara jin kamar zuciyarsa na nutsewa cikin wani irin duhu ne.
IBRAHEEM zaune yake saman dardumar parlourn. Alƙur’ani a buɗe gabansa… amma yau karatun ma baya shiga zuciyarsa kamar da, tun bayan maganar da yayi da Yasmine, wani irin tsoro ne ya shiga ratsa shi, tsoron makomar rayuwarsa, tsoron auren da yake rushewa a hankali… alhalin har yanzu zuciyarsa na son matar nan.
A hankali ya ɗaga idanunsa ya kalli bedroom ɗinta babu motsinta. Babu dariyarta, babu sautin wayarta. Sai dai duk da hakan jin zuciyarsa yake bata samun nutsuwa. A hankali ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya mai zafi.“Ya ALLAH…” “Ka nuna min gaskiya ko da zata karya zuciyata ne…” ya furta a bayyane yana kwantar da kansa jikin kujerar.
★
A Can cikin bedroom kuwa Yasmine ce zaune gaban mirror tana share tears ɗin mascara ɗin data ɓata. Fuskar nan tata cike take taf da takaici da wani irin ɓacin rai. “Wai duk saboda addini…” Saboda addini mutum zai dinga takura rayuwarsa haka?” Ta furta tana ɗan cije lips ɗinta sai kuma ta tuna yadda ya kalleta ɗazun. Wani irin kallo mai cike da tausayi amma kuma mai karya zuciya ne, kallo irin wanda mutum yake yiwa wanda yake son cetowa daga hallaka. Da sauri ta girgiza kanta tana mai furta. “No! I can’t live this kind of life…” Ta furta da turanci cikin rawar murya. Sai dai duk yadda take son ƙaryata zuciyar ta amma maganar IBRAHEEM taƙi fita a ranta.

“Wata rana zaki shiga cikin duhun da babu fitarsa…”

Ibraheem har lokacin yana zaune saman sofa yaji ƙarar horn ta tsaya a harabar gidan. Don haka ya ɗago kansa a hankali tare da yunkurawa ya leka, gabansa ne ya faɗi saboda ganin motar PAPA ɗinsa. Da sauri ya mike tsaye daidai da lokacin da ƙofar parlourn ɗin ke buɗe.Papa ne sai Mom daga bayansa wacce duk ta fice hayyacinta. Wacce kai tsaye Idanunta suka sauka akan IBRAHEEM. Nan take hawaye wasu ruwan hawaye suka cika cikin idanun nata tana mai ambatar.

“Oh my Jesus help… John…”

Kalmar ta fito daga bakinta kai tsaye wanda take fuskar Ibraheem ta sauya
sai dai bai ce komai ba. PAPA ne ya ƙaraso kusa da shi yana kallonsa sama da ƙasa. “You look tired…” Ibraheem ya sauke idanunsa ƙasa cike da wata irin girmamawa irin ta iyaye yace.

“I’m fine Papa.”

“Fine?” Papa ya ɗan bushe da dariya mai ciwo yana nanata kalmar.

“You abandoned everything for this life… and now look at you.”

Shiru kawai Ibraheem yayi Mommah kuma na matsowa kusa da shi tana riƙe hannunsa, cikin rawar murya take furta kalmar.

“John… please come back home.”

Da sauri ya ɗago idanunsa da suka surka da wani abu me karfi ya ɗan ja baya yana dan girgiza kansa, kafin ya ce. “Mother.... My name is Ibraheem! Ibrahimul khaleel” Wani shiru ne ya ratsa wajen Mommah ta wani lumshe idanunta cikin rauni tana mai furta.
“I know…But you’re still my son.”
Nan take zuciyarsa tayi wani irin bugawa. PAPA kuwa juyawa yayi yana kallon parlourn ɗin gaba ɗaya. Simple, ba wata rayuwar alfarma, ba wata rayuwar da ya taso a cikinta ba ta asalin jin dadi da hutu, babu aikinsa da ada din yafi ƙauna sama da komai. Ahankali ya dawo da kallon sa kan ɗan nasa cikin son ya kure shi yace.

“Is this really the life you want?”

A hankali Ibraheem gyada kansa yana amsawa da. “Yes Papa! Even with the pain?” Shiru Papan yayi kafin ya matso kusa da shi sosai yace cikin sanyi kuma wannan karonm

“Come back to the mansion Ibrahim.”
Numfashin Ibraheem ya tsaya. PAPA ya ɗora da magana cikin nutsuwa.
“You can still be a Muslim. You can pray!, You can worship your God.”
Sai ya ɗan dakata kafin yaci da

29 / 31