Advertisements
Chapter 9 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   9 / 31

24K to 27K   out of 91.1K words

na tambayarta yau ma yawon ta sake fita ko?...

“Maamah ni ban fita yawo ba Aysher kawai na raka mall...” tayi maganar bakinta a sama tana kara sa hayewarta saman. Kanta kawai Hajiya Khadija ta jijjiga tana ci gaba da ma Yasmine ɗin fatan kintsuwa anan gaba. Tun da kuma ta shige ɓangaren nata babu wanda ya sake ganinta har dare, koda aka fito dinner Ambassador Kabeer ke tambayan Ina Baby?, Husna take sanar dashi ai tun yamma data kulle kanta a ɗaki bata sake fitowa ba, nan ya rufe Maamah da azababben faɗan duk ranar data kashe masa Ambasaja wllh daga ranar zamansu ya ƙare. Wani irin shiru kawai Hajiya Khadija tayi, takaici da dana sanin auren mijin nata take yi. Ya yake son tayi a matsayinta uwa jigo ga rayuwar ƴaƴanta?, shi kenan ita bata da ƴancin yima yaranta faɗa musamman ma dai Yasmine ɗin da take kamar ransa. Tashi kawai a wurin tayi cike da ɓacin ran da yake kokarin kai ta kasa ba tun yau ba.

Kai tsaye ɓangaren Yasmine ɗin ya isa da kansa. A lokacin tana zaune da wasu guntayen kaya a jikinta. Tayi zurfi sosai cikin tunanin wancan ƙaton arnen taji anyi wani irin knocking a ƙofar. Wata after dress brown ta janyo TA ɗora saman guntayen kayan taje gaban ƙofar taki buɗewa tana tambayar waye?. Gyaran muryan mahaifin nata da taji ne ya saka ta saurin budewa ta faɗa jikinsa tana sakar masa kukan data jima tana riƙewa se yazo, ɗan bubbuga bayanta ya shiga yana bata baki. “Kiyi hakuri Ambasajo in dai akan fita ne zan sa miki 1 billion a account naki kije shopping ki sai duk abinda kike so...” da haka ya samu fushi da kukan nata ya sauƙa suka fito zuwa dining ɗin, kanta a dage a sama ta zauna duk a tunaninta Maamah ɗin nata na wurin, har se da ta lura bata nan kana ta ɗan saki ranta. Husna da taga take takenta se ta kyale ta ƙarshe ma ta bar musu wurin, bayan sun kammala dinner ɗin har ɓangaren nata ya sake raka ta. Har ze fice ta kirayi sunan shi daya saka shi tsayawa cak. Ahankali ta dawo ta setin da yake tsayen tace. “Mukullin motar ka zaka bani, dan na fara gajiya da tawa, kamar ma ina son a sanja min ita ta gama isa na...” Murmushi yayi dama car key ɗin jikinsa ya bata fita bayan ya kashe mata hasken ɗakin ya bar mata ƙadan irin dum ɗin nan. Be jima da fita ba sega alert ɗin One billion ɗin daya mata alkawari. Wani uban ihu ta buga tana direwa a saman gado don ita kaf duniya tana son ganin Daddyn ya mata kyautar kuɗi irin haka, duk da kasancewar itama tana da wasu irin kuɗin masu nauyi cikin account nata.

Tsaye yake a balcony ɗinsa, iska na ɗan ɗaga rigar jikinsa da kuma sumarsa.
Hannunsa riƙe da ƙaramar chocolate ɗin ta Ferrero Rocher ɗin da seda ya saka Mecheal ya nemo masa a daren, Ahankali ya juya yana zama kan doguwar kujerar hutawar dake wurin, ajje ledan chocolate ɗin yayi yana lumshe idon sa maganganunta na ɗan dawo masa ka. Sake gyaran murya a kusan karo na uku kenan Madame Victoria Osteen tayi ma yaron nata, amma duk be ji taba har seda yaji hannunta cikin gashin kansa kana ya ɗan dago a firgice. Ganin Mommah nashi ce ya saka shi wani bata fuska idonsa da suka yi wani haske sosai, ga kuma alamar ruwan daya tarun masa a ciki ya zuba mata yana kamo hannunta daga sumarsa da taci gaba da shafa masa, sake kwaɓe fuskan shi yayi a saman laɓɓansa ya furta. “Mommah” a wani irin shagwaɓen da za kayi tunanin irin befi 3 year's ɗin nan bane. Kansa ta sake shafawa tana sake jefa masa tambayar lafiyansa kuwa?, tunanin meke damunsa haka? ɗauke hannun nata ya sake yi kansa yana miƙewa tare da gyara maɓalan gaban riharsa da suka buɗe kuma kai tsaye Mommah'n nashi na shirin kai hannunta saman jikinsa, gyara maɓalan rigan yake yana soma tafiya ba tare daya ɗauka sauran chocolote in nashi ba, yake ce mata babu komai kawai yana buƙatan spece ne. Ɗan zama daga inda ya tashin tayi ta lumshe idonta kafin ta buɗe su suka sauƙa kan sauran chocolote ɗin nashi. Kai tsaye ta ɗauke chocolote ɗin tana miƙewa da ita tabar balcony ɗin. Kai tsaye saman lafiyayyen gadonsa ya faɗa hoton kyakkyawar fuskarta ta ɗazun na dawo masa, ƙiran waya ce ta shigo masa yana kallon daga inda ƙirar yake yayi sweetching wayar nashi ma baki ɗaya. Ya jima beyi barci ba se can zuwa dare kana barcin ya iya nasarar sace shi.

★…

Washegari da niya yaƙi tashi da wuri se wajajen sha daya saura, kafin ya gama shirinsa ya fito kuma har sha biyu ma ta ɗan gota,kamar jiya yau ma duk yadda family nashi suka so yin dinner tare dashi basu sama wannan damar ba, gashi kakansa Patriarch na shirin tafiya da,amma se ya ce ya fasa se John ya sama lafiya. Don su a nasu ganin wai baya da lafiya ne, yana ficewa suma kaf suka fice suka nufi couch don yi masa adda'a. Ga Papa'nsa shi kuma baya ƙasar yana India kwanansa biyu da tafiya, kuma tare da Deepika ya tafi tana son ganin gida in yaso daga baya ta dawo, kai tsaye shi kuwa John wannan Mall ɗin ya koma, amma duk iyaka bincikensa da yayi be ganta ba, don haka ya rin ga bin manyan wurare ko ALLAH ze sa ya ganta amma be ganta ba har rana ta take masa, ƙin hakura ya koma gida yayi haka yau ma ya haɗa Mecheal da gantalin zaga manyan wurare a garin Lagos, ƙarfe biyar cif na yamma zuciyarsa ta sake bashi shawarin ya sake komawa wannan shagon. Aikuwa akayi haka sedai kuma bata nan ɗin. Take yaji kamar ana tafasa ƙwaƙwalwar kansa ne da rashin ganin nata, ga Madame Victoria ta ishesu da da kashe ɗin lallai duk inda suke su dawo a wayar Mecheal don shi ƙin amsata yayi,yana tsaka da wannan zafin kan yaga tamkar gimlawar wani abu, haka yaga gimlawar kyakkyawar fuskar ta, wacce ke frowning na zallar kyau yau ma sanye da brouwn dogon hijjaba har ƙasa. Don haka da sauri ya fara zagayen ta inda yaga gimlawar nata sedai be ga kome kama da ita ba, kai tsaye ya bama masu mall ɗin umarnin a tattaro gaba ɗaya jama'ar dake cikin mall ɗin yara da manya.
Kafin ƙiftawar ido kuwa se gashi an tattaro kan jama'ar wurin suna ta fitowa. Yana tsaye hannuwansa ɗaya saman kansa yana shafa sumar kanshi, ɗayan kuma rike da ledar chocolote ta raspberry yana taunawa. Kansa a sama tallefe da ƙeyarsa fuskar nan tayi wani irin ɗinkewa ɗif alamar No nonses kenan. Haka ya fara zagaye tarin jama'ar dake Mall ɗin ƙatuwar sarkar Cross nashi na faman rito tsaƙiyan ƙirjinsa da tsaban iskanci ya ɓalle mata maɓallai wajen uku zuwa huɗu, kansa a sama amma yana fahimtar kowa se wani faman huhhura hanci sama yake, yau gashi tsohun shege. Haka ya shiga zagaye matasa mata da mazan dake wurin, yara da tsofaffi amma kuma babu ta babu alamarta, kamar wacce aka ce kalla ɓangaren damar ka yaga wata na sanye da brouwn dogon hijjaba har ƙasa tana ci gaba da ɗibar duk abinda ya mata, sosai wani irin mamaki ya kama shi, ganin ita babu abinda ya dameta ko bata san anyi taron bane, don haka a ɗan fusace ya isa gare ta amma tun kafin ya ƙarasa kuma ya tsaya cak. Sabo da bugun da yaji ƙirjinsa ya masa, wanda kai tsaye hakan kamar yana alamta masa cewar ita ne tsayen, cikin ƙarfin hali ya isa gare ta yayi amfani da ledar chocolate ɗin dake hannunsa wajen karkaɗa mata saman fuskarta, amma ko wanne motsi bata yi ba. Shi kuwa Idanuwansa ne suka fara yawo ko ina a jikinta tun daga sama har ƙasa, kamar zakin daya fito domin farauta. Cikin ransa yake furta _Wannan alamar ta wuce wasa a gare ni..._ Sak idanun John su kayi akanta,duk da baya ne ta bashi tsaye ɓangare guda na mall ɗin tana ci gaba da duba wasu kaya. sanye da niƙab ɗinta kamar kullum kamar ko da yaushe. “It’s her…” ya faɗa a hankali, kuma bai jira komai ba ya fara takawa zuwa dab da ita kai tsaye. Ita kuwa daga ɓangarenta duk abinda ke faruwa tana sane kuma tun lokacin data shigo ta lura dashi,har zuwa kan sanda yake zagayen
kamo tattaro masa mutanen da akayi ɗin. Ahankali ta zame nikab nata zuwa sama, kai tsaye idanunsu suka sarƙe ana juna amma nata suna cike da ɓacin ran kaiwa maƙura a ƙoƙarin fara takura rayuwarta da wannan ƙaton arnen yayi.

“Not again…”

Ta furta a hankali kafin ta juya zata ci gaba da sayayyarta. Ganin tana ƙoƙarin sake ɓace masa ne ya saka shi furta kalmar.

“Hey!”

Haka muryarsa ta dakatar da ita ta tsaya cak. Kafin ahankali ta juyo idanunta cik da haushi...

“Ban gaya maka ka dena bina haka nan ba?” ta faɗa kai tsaye. Wanda ya saka
John tsayawa a gabanta, ba tare da tsoro ko nadama ba ya furta.

“I told you… I was looking for you.”

ya mayar mata cikin natsuwa, wata ƴar
dariya kaɗan tayi mai cike da raini tace.

“Looking for me? For what exactly?”

“To finish what you started…”

Shi ma katse ta yana sake matsowa daf da ita a hankali. Take fuskanta ya sauya ta ce.

“Excuse me?”

Ta faɗa da ƙarfin daya saka
Mutane suka fara kallonsu.

“Ka na nufin me?” ta sake faɗa da tsawa, bai ja baya ba sema sake tallafe kansa da yayi, kafin ya zuba mata maraitattun mayun idonsa murya a wani kalan hankali yace...

“Ina nufin… you slapped me… and left.”

yace da wata irin murya so calmly wani
ɗan murmushi na bayyana a gefen bakinsa. “That’s not how it ends.”
Wannan karon kam da ihu Yasmine tace...

“YOU MUST BE CRAZY!” ta faɗa da ƙarfi kafin ya dawo daga duniyar ihun data masa ya sake jin sauƙar mari me ƙarfin gaske saman fuskarsa, wanda ya saka Mecheal saurin rintse idonsa tare da jama'ar Mall ɗin da har yanzun suke tsaitsaye. Komai bai ji ba dangane da marin data masa sema kawai ɗan karkata kansa gefe da yayi yana sake bata fuskan,yana sake mai da kallonsa ga kyakkyawar fuskarta ba tare da fushi ko wani abu ba. Sai ma wani irin murmushin daya zagaye fara tas ɗin fuskar shi, nuna shi ta shiga yi da yatsa tana huci tace...

“I warned you!”

Ta sake faɗa a tsawace, taci gaba da nuna shi.

“Na gaya maka ka dena bina!”

Wannan karon murmushin daya mata harb sai daya ɗara laɓɓansa,ya sauka kaɗan zuwa saman fuskarsa. Bai kuma ce komai da ita ba yaci gaba da bin ta da idonsa, yana ci gaba da bin ta da irin wannan tausassan murmushin, wanda ya saka Yasmine taji wani abu ya tsaya cak a kwanyarta. Kafin ahankali ya ce.

“Next time…”

Se kuma ya ɗan dakata alamar yana son samun hutu daga bugun da zuciyarsa ke masa kafin ya sake cewa.

“I won’t let you go.”

Sai kuma idanunsa suka rage kaifin hasken da suke ɗauke dashi a da, suna ɗan yi duhu kaɗan.

“This time… you’re mine....”

Wani shegen kallo ta masa kafin ta juya zata bar wurin, ya riƙo hannunta yana binta da wani kallo ƙasa ƙasa, sake watsa masa manyan fararen idonta tayi ta kalla hannunta ta kalla nashi daya riƙe natan, ta buɗe baki kenan zata yi wata maganar ya rigata ta hanyar furta...


“ Da nayi sakacin barin ki tafi ba tare da sanin ainihin suna ko inda kike zaune ba!, Amma wannan karon ba zan bari ki gudu ba...” wani kalan fusge hannunta a nashin tayi ta juya cikin ɓacin rai ta bar wurin yana take mata baya. Mecheal ne yayi saurin take masa baya yana cewa.


“ Easy Boss… are you okay?”

Ya tambaya cikin damuwa, da hannu kawai John ya dakatar dashi Idanunsa har yanzu suna kallon inda ta bi yana zame hannunsa cikin na Mecheal daya riƙo bayan ya ce.

“I like her more now.”

Wanda ya saka Mecheal ya tsaya cak a bayyane yana me furta..

“Lallai Boss ya shiga uku…”

★...
Saurin zaro wayarsa yayi ya dokama Madame Victoria ƙira, cikin ring farko ana biyun ta ɗauka. Tun kafin yayi magana tace “Mecheal ina yarona?...”
“Madam…” ya faɗa cikin girmamawa kafin ya dora da faɗin.
“Na ƙira ne in sanar dake… Akwai wata yarinya!, Ohh wannan Hausa gal ɗin Boss yana ci gaba da bibiyarta sosai.” wani ihu daga ɓangaren Madame Victoria ta yi tana cewa.

“Wa...ce...ce...wacce yarinya?” tana ma mancewa da batun Hausa gal ɗin John ɗin.. wani yawu Mecheal ya haɗiye da ƙarfi wanda ya kusan kwarar da shi yace...
“Ban san sunanta ba… amma tana sanye da hijab… Hausa girl narh.”
Cak numfashin Madame Victoria ya kusa yanke wa tuno da yarinyar...
“Hausa… girl?” ta maimaita sunan da taji ya mata wani irin nauyi a cikin zuciyarta, take ta fara ganin kamar duhu duhu daga cikin idanunta. Kafin kamar a zabure ta ce..
“Keep watching him, duk inda zai je… duk wanda zai gani… ina son sanin komai.” “Y-Yes, Madam…” Mecheal ya amsa kamar a ɗan rarrabe yana kashe wayar. Daga can ɓangaren Madame Victoria kuwa tana sauƙe wayar taji kamar wani abu me zafi aka zuba mata a cikin idanu da kirjinta. Wata kafuwar zabura tayi fuskarta cike da wani irin yanayi me matuƙar haɗari tayi wani ɓangare daban a cikin ɓangaren nata zuciyarta na wani irin mahaukacin tafasa.

“Ba zan bari wata mace ta karɓe min ɗana ba…” Ta sake faɗa da karfi
Idanunta naci gaba da rikiɗewa ta sake ce “Not this time.”

John kuwa ko kafin ya isa har ta sake ɓacema ganinsa, duk kuwa da yacce yayi ta zaga harabar wurin, wani ƙaramin ihu yayi ya daki ginin dake gabansa wanda ya saka take hannunsa fashewa jini ya fara zuba, goshinsa ya sake bugawa ya sake daga hannu da niyar fasa glass na motarsu Mecheal yayi hanzarin kamo hannun yana furta...

“Easy...Easy Boss, Relax Pls...”

Rinannun idonsa ya ɗago yana watsawa Mecheal ɗin daya saka shi ja baya da sauri, daidai da lokacin da kakansa Patriarch da Madame Victoria taje ta sanarmawa suka iso wurin suka kamashi yana ihu yana komai suka zira cikin mota suka tafi dashi gida....


*BY AMMEY LAYLERH ✍️*

08104493215




*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 9
Paid book

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.


Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215


*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

_Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t

Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci?
To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta

♡♡♡♡

ꨄ Tun da shige ɓangarensa yau ɗin ma kamar jiya babu wanda ya sake jin koda motsin sane, ga likita sun riga da sun kirawo da zai duba goshi da hannunsa.
Haka daren ranar yazo ya riskesu tamkar masu zaman makoki sun jere a gaban bedroom nashi. Shi kuwa a nashi ɓangaren koda ya shige saman sofa ya zube a ruf da ciki, sam be damu da jinin da hannunsa ke zubarwa ba, duk kuma uban bugun da suke yana jin su yayi kunnen uwar shegu dasu, daga ƙarshe ma parlourn ya bari ya shigewansa bedroom nashi... Ko nutsatsestsiyar dinner babu wanda ya samu yayi a cikinsu kowa hankalinsa a tashe da ciwon da John ɗin yaji, a daren ranar haka Papa da ko rabin abinda ya kaishi India be biya biyo jirgi, don sun gama rikita shi da cewan John ba shi da lafiya sosai. Shi kuma a duniya baya taɓa iya haɗa kowa da ƙaunar yaron nasa, don jinsa yake kamar shi ne ransa gaba ɗaya. Take wani mayataccen mayen zazzaɓi ya kama Madame Victoria don kaf duniyar ita har Papa ɗin ma gani take ta fishi ƙaunar John ɗin. Duk kin ta da Deepika haka tana ji tana gani dole se ita ce ta ringa kula da ita don jelly bata nan tana wurin wani birthday ɗin freind nata Solomon. Har zuwa dare can sosai gaza runtsawa tayi har se da Deepika ta taimaka mata da adda'a bayan ta ɗauko bibble nasu. Abincin kuwa da ita ma bata ci ba kenan,don cewa tayi idan taci ai kamar taci amanar John ne, tun da shi yana can rai a hannun ALLAH. Yana tsaye gaban mirrornsa fitowansa a wanka kenan ɗaure da fari tas ɗin towel a ƙugunsa, ahankali ya kalla kansa ta cikin mirror ɗin,kafin ya sake dawo da kallon masa kan hannunsa dake naɗe da bandage ɗin da shine ya saka gashi a disheveled, amma idonsa kamar yana neman abu ne da ya ɓace tun da daɗewa hannunsa yakai saman goshinsa yana me furta...

“Crazy…”

Amma baga yasmine yake nufi ba wa shi kansa yake nufi. Ƙirar wayar daya shigo masa ne ya saka shi kallar inda wayar yake,sunan Mecheal daya gani kawai ya bashi tabbacin Mommah nashi ce. Kamar ba zai ɗau wayar ba se kuma ya ɗauka. Jin a daga wayar kai tsaye ya saka Mecheal saurin cewa.



“Boss!, please

9 / 31