Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
komai.” Ya ɗora hannu a ƙirjinsa kana ya sake cewa. “Amma idan kuka sarrafa shi, ko hadari mafi muni ba zai karya ku ba.” daga nan suka dawo zuwa ainihin inda suke cike da alfahari da jarumta, suna sake yabama John da sake bashi wani irin girman da idan ka gani zai baka mamaki, don wannan ɗin duk cikin shirin sane shi ya shirya hakan. Nan yaci gaba da basu horo me kyau inda tun daga wannan rana, ba kawai Daniel ba… dukkan su sun canza...
♡
Haka al'amurra suka ci gaba da wakana tare da shuɗewa tuni suka sake samun wata sabuwar kwarewar da babu dar ko shakkar tuƙin cikin kowanne irin muni ko haɗarin wuri. Sun san duk wasu matakan kariyar da zasu bama jiragensu cikin aminci, misali kamar irin suna cikin tuƙin nan wani yaki ya tashi irin na ƙasa da ƙasar nan to zasu iya kuɓutar da jirginsu ba tare da an ɓaro shi daga sama ba kamar yadda ake ɓaro wasu ba. Alhamdulillah kafin ka ce sega ƙasar Ethiopia ta sake bama John wani irin girma da ƙarin matsayin da ba iyaka piloting bane, zai iya zama special pilot ga ko wacce ƙasa idan yaso, wanda dama kuma akwai ƙasa shen da suke harinsa ba kaɗan ba....
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
_Dont forget to vote, follow and comments_
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 11
Paid book
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
_Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t
Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci?
To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta
♡♡♡♡
ꨄ Duk yammacin duniya tun da yazo ƙasar a cikin Hawassa yake ƙarasa darensa, Hawassa shima duk a cikin hotel ɗin ne se dai ɓangaren ruwa ne kawai, amma irin pool pool ɗin nan kashi yafi ɗari. Ga shi kaɗai zaka ruwan na walƙiya kamar madubi tana haskaka kasan ƙarƙashin ruwan, ga gaba ɗaya wurin cike yake da wata irin natsuwa da ƙamshi irin na wuraren hutawa haka. Inda ko wanne pool yake kewaye da kujerun shakatawa da bishiyoyi masu mugun kyau da tsaruwa. Kamar kullum yau ma ahankali John ya fito sanye da light short da t-shirt mai laushi, yana tafiya a natse amma cikin ransa fal yake da tunani da kuma kewan tsiwan ta, masifanta da yadda take sarrafa cikul ɗin bakinta tana wani motsa shi idan tana masa jaraban, wanda hakan shi ne abu na farkon daya fara motsa duk wani abu a kanta, shi ne wannan yanayin da fuskanta ke shiga, idonunta kuma su wani janye irin mutum yana tsaka da masifan nan. Wanda duk yau ɗin haka ya tashi gaba ɗaya da so da ƙaunar ganin nata in yaso ko marin ne ta sake bashi, ko masifan ne ta masa yana son ganin ta da kuma ɗaukar duk wani hukuncin da zata ci gaba da bashi indai zai ci gaba da ganin koda fuskan tane. Haka zuciyarsa ke cike da tunanin da har ma bai lura da cewan ya isa bakin pool ɗin ba. Wanda se a sannan ya ankare yana jan wata kyakkyawar blue nd white chiar ya zauna yana fuskantar ruwan. A hankali ya sauke ƙafafunsa cikin ruwan inda kai tsaye wani sanyi mai daɗi ya ratsa jikinsa.
Wanda dole ya saka shi lumshe ido na ɗan lokaci. Iskar da ke tashi daga bakin Hawassa Lake ɗin na kaɗawa a hankali, tana motsa gashin kansa. Ana jin ƙarar tsuntsaye daga nesa, da kuma dariyar wasu mutanen daga ta gefen pool ɗin alaman suna cikin nishaɗi. Amma shi… ya kasance cikin duniyarsa.
“Why am I even here…?” ya furta a hankali cikin turanci kamar yana magana da kansa. Tunanin duk abin da ya faru ya fara dawo masa kai, yadda aka tilasta masa tafiya zuwa Ethiopia, yadda ya so ya ƙi amma aka matsa masa. Ba shi ne ma zai tuƙa jirgin ba, amma aka ce dole sai saboda zai bada horo ne, shi yasa yayi zuciya da ƴan gidan nasu baki ɗaya, yaƙi yin waya da kowa tun da yazo, wanda se suna suka yi tattaki suna zuwar masa har karo biyu, ganinsa cikin nutsuwa kamar babu alamar komai tattare dashi ya saka su farin cikin da har suke jin kamar zasu iya sallamawa ƙasar shi yaci gaba da mata aikin kawai. Ahankali yaja wani numfashi Kafin ya buɗe ido, ya kalli ruwan pool ɗin da ke motsi a hankali saboda ƙafafunsa dake ciki. Ta cikin ruwan ya ga hoton kansa yana motsi amma ba irin John ɗin da ya sani ba ne, A ahhh wannan John ɗin ya gaji,
wannan John ɗin ya rikice komai na nemar kwace masa kafin daren jiya zuwa wayewar yau. A hankali ya ɗago da kansa ya kalli sararin sama mai shuɗi. Yana tsaka da wannan tunanin wata murya ta katse masa tunanin nasa ta hanyar furta....
“Nice view, right?”
Wanda dole ya saka shi juyawa a hankali ya na kallar kyakkyawar matashiyar budurwan dake tsaye a bayan sa, sanye da farin riga mai sauƙi, gashinta gaba ɗaya zube a kafaɗunta da iska ke kada shi. Idanunta suna cika da natsuwa sosai. Ahankali John ɗin ya ɗan gyara zamansa sedai fuskar nan babu alamun rahama ko annuri ya ce. “Yeah… it is.” a natse ta zo ta zauna a kusa da shi, amma ba kusa sosai ba. Ta sauke nata ƙafafun cikin ruwan itama wani shiru ya ratsa wurin, kafin ta katse shirin ta hanyar ce wa. “Sometimes… people come here to forget things.”
John ya ɗan motsa kaɗan cikin sautin da bai fita da kowacce kalan sauti ko hayaniya yace. “And sometimes… they come here because they have no choice.” sai ta juya ta kalle shi sosai, kamar tana son fahimtar abin da ke zuciyarsa. “Which one are you?” Ya yi shiru na ɗan lokaci komai be ce da ita ba. Kafin ya kalla ruwan a hankali ya ce... “I don’t even know anymore…”
Ahankali iskar dake kaɗawa taci gaba da kaɗawan da ya saka ruwan pool ɗin ya motsa shima, ga uwa uba hasken ranar dake haskawa yana faɗuwa a kan Hawassa Lake ɗin, yana ƙara masa kyau kamar wani zane. Ahankali zuciyar John ta fara jin kamar wani sabon labari ne yake shirin farawa shima, labarin da bai san inda zai kai shi ba.Iskar mara ƙarfi ta sake kadawa a gefen swimming pool ɗin, tana motsa ruwan a hankali. John ya ɗan sunkuyar da kai, kamar yana tattara kalmomin da zai faɗa. Wanda ya saka budurwar ta kalle shi da nutsuwa, sannan ta yi murmushi kaɗan ba tare da damuwar komai ba tace. “Sunana Almaz,” ta faɗa a hankali. John ya ɗaga kai ya kalle ta kafin a wani irin hankali ya ce da ita “John.” se shiru ya sake ɗaukan wurin amma wannan karon ba irin na farko ba ne ya ɗan fi sauƙi. Almaz ta ɗan karkata kai kai tsaye ta jefa masa tambayar, “Kana da wanda kake tunani ko kewa ko?”don tashin farko a kallonsa ta karanci hakan, wanda ya saka John ɗan motsa bakinsa kaɗan, se ya sama kansa da murmusawa don yau ɗaya ze fara firan yasmine da wata. Ahankali ya yaci gaba da motsa ƙafafunsa cikin ruwan kamar komai ba zai ce mata ba don ita har ta fidda rai ma kana kamar daga sama taji yace... “Eh… akwai wata. Sunanta Yasmine.” Da jin sunan, Almaz ta ɗan yi shiru, amma ba da wani irin kishi ko damuwa ba. Sai dai wani irin fahimta da ta bayyana a fuskar ta.
“Ka na sonta sosai?” John ya kalli ruwan pool ɗin, ƙafafunsa suna motsa shi a hankali kafin yace. “Fiye da yadda zan iya bayyanama duniya…” wani kallo me tattare da zallar fahimta ta masa, kana ta sake cilla masa tambayar. “Are a Muslim yasmine ba?” Cak ya dakata domin kuwa kalmar Muslim ɗin wani irin duka tama ƙirjinsa. Wanda dole ya saka shi yin wani irin shiru kamar ruwa ya cinye.Almaz ta ja numfashi a hankali tana kallon nesa inda Hawassa Lake ke haskawa. Kafin cikin nutsuwan da muryanta ke da yaji tashin maganarta tana cewa. “Wani lokacin rayuwa tana kawo mana mutane biyu ne cikin duniyarmu, ɗaya da zuciyarmu ke so… ɗaya kuma da rayuwa ke ba mu don ta koya mana wani abu.” se ta dakata cak wanda ya saka john ɗaga kai ya kalle ta sosai kafin shi ma ya jefa mata tambayar...“Ke wa ce ce?” gyara zamanta Almaz da wata ƴar siririyan dariya kaɗan mai cike da natsuwa ta ce.
“Ni? Ba zan zama matsala a rayuwarka ba, John.” se kuma ta sake yin shiru kana tace. “Zan iya zama ƙawa kawai.” Wani shiru yayi kamar me tunani ko nazarin wani abu kana ya miƙa mata hannu kawai. Almaz ta kalli hannun da John ya mika mata na ɗan lokaci, kana ta girgiza masa kai tana murmushi alaman ba zata kama ba tare da furta.
“A friend sounds good kawai.” A wannan lokacin, wani abu ya sauya.
Ba soyayya ba, haka ba rikici ba, sai dai wani irin sabuwar fahimta ta abota mai tsaftar data shiga tsakaninsu. Daga nan suka zama good friend ita da John, wanda mafi akasari anan suke yawan haɗuwa, abu na farko daya fara jan hankalin John ga yasmine yadda take kunna wani abu a cikin wayarta me kama da waka, amma kuma yasan ba waƙar ba ce duk da kasancewar ba da Yaren da yake ji bane, amma yasan ba waƙar bane. Haka zai ga ta lumshe idonta tana bin sautin abin cike da wata irin nutsuwa da bin harrufan ɗaya bayan ɗaya, se dai be taɓa gigin tanka mata ko mata shishshigi ba duk da abin na birgesa, don har so yake tazo don yanzun ta kai ta kawo idan bata zo ba tsintar kansa yake cikin ƙuncin daya rasa gane masa, kamar yanzun daya da yake a zaunen da tsammanin ko zai ganta, ga wayarta baya shiga kwata kwata yau tsayin 3 day's kenan rabon daya saka ta cikin idonsa...
Ahankali ya ɗago kansa yana fesar da wani numfashi me zafi, ya kwashe sama da 50 minutes zaunen da yake, fararen zaratan sawayensa zube cikin swimming pool ɗin. Amma babu ita babu dalilinta. Ahankali yaci gaba da karkaɗa ƙafafunsa cikin ruwan, bayan 40 minutes ɗin aƙalla ya sake kwashe sama da 30 minutes ɗin data rufama 40 ɗin baya awurin yana jiran yaga ta inda zata ɓullo amma babu ta babu alamar nata. Wani irin shiru kawai yayi yana sake jingina bayansa da kujerarn hutawan dake wurin. Ahankali iskar dake kaɗawa take sake shiga cikin jikinsa da shafar fuskarsa kamar tana son kwantar masa da hankali.... Hannunsa ɗaya na riƙe da glass na juice ɗin da be jima da ɗauka ba, ɗayan kuma ya jingina a gefen kujerar. Ahankali yake ta ƙoƙarin ya danni kansa a kan wani irin fushin da yake jin na taso masa,amma duk da yana ƙoƙarin dannewar hakan be hana har fuskarsa fidda yanayin ba. Gaba ɗaya yaji wurin ya haɗa masa wani irin shegen yanayi be cike da cunkushewar zuciya, duk kuwa da yanayin dake bayyana tsantsarn nutsuwar da ƙaton beach ɗin ke bashi amma banda yau ɗin nan kam, buɗe idonsa yayi yana ɗan taune jajayen lips nashi tare da dafe saman goshinsa.Yanda ya dafe goshin nasa kaɗai ya isa baka tabbacin ka fahimci cewar kanne ke masa ciwon,
musamman idan kai duba da yadda
ya dafe kan da tafin hannunsa. sake lumshe tsumammun idanunsa yayi yayin kamar wani abu na nemar hanyar kassara rayuwarsa ne gaba ɗaya, ahankali cikin daure ciwon da kan ke masa ya sake taune lips nashi da ɗan ƙarfi tare da nutsa hannuwansa cikin tulin sumar dake kwance luff luff saman kan.ya shiga chakudawa da duka hannuwansa kafin a wahalce ya miƙe yana tangaɗi tamkar ɗan maye yana nufar hanyar komawa lodge nashi.
Cikin sassarfa ya kutsa kansa cikin lafiyayyar lodge ɗin yana kama hanyar bedroom nashi. Cikin bala'in zafin zuciya ya nufi part 0122 yana haɗe baki ɗaya abubuwansa wuri guda yana jin dole a yau se ya bar ƙasar Ethiopia ɗin tun da bata ubansa bace. A irin wannan masifaffan yanayin da yake ciki ya ci gaba da shirya kayansa kamar ma a hargitse. Kafin kace me cikin ƙankanin loƙaci har ya buƙaci barin ƙasar duk kuwa da cewar sai nan da 10 days zai tafi, amma baki ɗaya yaji gida kawai yake da buƙatar komawa domin sammm zuciyarsa ba zata ci gaba da ƙuntata irin haka ba, wanda a zahiri da za'a iya buɗe zuciyarsa da kuwa tabbas kun girgiza da ganin abubuwan dake ɗan ƙare a cikin ta. A loƙacin 4:00pm na yamma ne, amma haka yasa dole aka barshi yabi jirgin da zai tashi aka keta hazo dashi yau ma a matsayin passinger's yana barin kasar baki ɗaya....
6:15pm na magrib jirginsu ya sauka a airport ɗin Nigeria dake lagos. Inda filin jirgin yake cike da hayaniyar mutanen da wasu sun zo ɗaukar iyaye ne wasu yayye wasu mataye wasu ya'ya. Haka mutane keta famar shiga da fita wasu na runguma da ƴan uwansu, wasu kuma na hawaye na farin ciki. John ya sauko daga jirgin, gajiya na bayyane a fuskarsa bayan duguwar tafiya daga Ethiopia. Hannunsa riƙe da jakarsa, amma zuciyarsa ba ta kan tafiyar ba… tana kan abu guda...Yasmine....Almaz. lokacin da sunan yasmine ɗin ke ratsa zuciyarsa ji yayi kamar wutar da ba ta taɓa mutuwa ba ce take ƙoƙarin ruruwa. Kansa ya ɗan girgiza jin kamar bugun zuciyar ba daga iyaka ambatar sunan nata kawai ba ne, kamar dole tana cikin airport ɗin ne, don duk lokacin da zai ganta irin wannan bugun zuciyarsa ke masa.... Tamkar wanda aka ce waywaya gajiyayyun Idanunsa suka sauka kanta tana tsaye ta bada baya kaɗan amma kuma ana ganin fuskarta, tana sanye da hijabi fari mai tsafta, idanunta zube tana kallon masu fitowa tamkar tana jiran wani. Da wani irin ƙarfi zuciyar John ta buga har besan lokacin da bakinsa ya ambata sunar.
“Yasmine…” ya furta a hankali kamar yana tsoron aikata wani mugun kuskure ne.....
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
_Dont forget to vote, follow and comments_
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 12
Paid book
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
_Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t
Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci?
To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta
♡♡♡♡
ꨄ Cak ta dakata da alama taji sadda ya haɗa sautukan fitan sunayen nata, don haka ta ɗago kanta a hankali ta masa wani ɗan kallon fishaa da slowly eyes nata kafin ta janye, batare da tayi ko irin alamun nuna ta san shin nan ba tayi gaba abinta daidai Daddy'nta ke ƙarasowa ta rumgumoshi cike da missing na kewar shin da tayi wajen One months. Ko da ta sake ɗagowa
Idanuwansu ne suka sake sarƙewa wanda yanayin fuskarta ya sauya nan take daga farin cikin da take a ciki zuwa tsauri. Shi kuwa kai tsaye ya tuna mari na farko, mari na biyu, kamo muggwan kalaman da take faɗa masa duk lokacin da zasu haɗu da suka fi masa mari zafi.
Ahankali ya taka ƙafafunsa da nufin isa inda take, amma kafin ya isa ta sake rungume Daddy'n nata cike da tsananin farin ciki ta ce. “Daddy!, I miss you so much” ɗan bubbuga bayanta ya shiga yi cikin kulawa da SO me ƙarfi sosai ya ke cewa. “I miss you more than I thought ambasaja shalalen Daddy'nta I miss you...” daga nan ta kama hannunsa suka nufi motar da ita kawai tazo ɗaukarsa, don ma babu wanda ya san da zuwan nashi se ita kaɗai, John da bai motsa ba na ɗan lokaci ne zuciyarsa tayi saurin ankarar dashi akan cewa kada ta sake ɓace maka. Ai kuwa da wani kalan sauri ya ɗauki jakarsa ya bi su a hankali daga nesa. Ba ya son su gane
amma ba zai sake barinta ta ɓace masa haka kamar kullum ba, suna fita daga filin jirgi suka shiga mota. John ya tsaya cak... “Damn…” ya furta kamar a ɗan fusace sai ya hango taxi, ya ɗaga hannu da sauri. “Follow that car,” ya faɗa da gaggawa bayan ya shiga, driver ya kalleshi da mamaki, amma ya tada motar John