Advertisements
Chapter 19 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   19 / 31

54K to 57K   out of 91.1K words

wrapper ɗinta.
“Deepika called me today.” jin sunan ne ya sa JOHN lumshe idanunsa a hankali kamar wanda kansa ya fara sara.

“Mother not tonight…”

“Oh yes tonight!”

Ta faɗa da ƙarfi wanda ya saka John toshe kunnuwa sa ya juya yana son barin wajen amma muryarta ta sake tsaida shi. “Look at me when I’m talking to you!” Fuskarsa babu walwala ko kaɗan ya juyo, wanda ya saka Mother ɗin matsowa kusa da shi sosai.

“Me yake faruwa da kai ne?”

Ta tambaya tana kallon idanunsa kai tsaye. “Tun da ka dawo daga Ethiopian ka sauya gaba ɗaya.” ta sake fadi da harshen turanci. Komai be ce mata ba taci gaba da fadin. “Deepika is the perfect woman for you.” ta faɗi duk da tana dannar zuciyar ta, don gani take da John din nata yayi aure mace zata mallake mata shi gaba ɗaya, shi yasa take tsoron yayi auren tun farko.
Wata ƴar dariya mara sauti yayi, a ransa yake ayyana da ace Mother ɗinsa ta san yadda sunan Yasmine kawai ke iya rikita duk wani tunani nasa. To da ba zata sake cewa Deepika perfect ba.

Kai tsaye kuma maganar ta ta sake sauƙa tsakiyan kansa.

“An tsara komai game da aurenku already.” Ta ci gaba da magana. “Families, companies, future… komai!”
Sai yanzu ya ɗan ɗaga idanunsa ya kalleta. “And what if I don’t want it?”
Wani irin shiru ne ya ratsa parlour ɗin.
Mother ɗinsa ta ɗan zaro ido.

“What?”

Ya ƙarasa kusa da ita, tare da gyara tsaiwansa gabanta yana wani karkata kai irin na rikakkkun shegun nan yace.

“I said… what if I don’t want to marry her?”

Fuskar Mother ɗinsa ta sauya gaba ɗaya.

“Is there another woman?”

Tambayar ta fito kai tsaye, wanda ya saka JOHN ɗauke kansa gefe guda alamar ko a jikinsa. Wannan kaɗai ya isa ya bata cikakkiyar amsar ta akan shi akan auren. A hankali Mother ɗinsa ta ja baya tana kallonsa cikin rashin yarda.

“Oh Jesus…”

Ta furta a hankali tana ɗan riƙe kanta kafin ta furta.

“Who is she?”

Se da ya sauke wani numfashi.

“It’s complicated.” wata dariya tayi cikin takaici. “No. Don’t give me that nonsense.” Ta nuna shi da yatsa. “You are going to marry Deepika and that is final!” Wanda nan take fuskarsa ta ɗan ɗauki zafi. “For once in my life can I choose something for myself?!” wani irin kafe shi da ido Madame Victoria din tayi cike da mugun mamakinsa.

“You sound insane.”

“Maybe I am.”

Ya furta ba tare da tunanin komai ba
Saboda gaskiyar ita ce…Tun haɗuwarsa da Yasmine komai nasa ya daina tafiya yadda ya saba. Madame Victoria ta ɗan
girgiza kai cikin takaici. “This is why love is dangerous.” Wani murmushi mai ciwo yayi.

“No Mother…”

Ya faɗi yana ɗan lumshe idanunsa.
“It’s dangerous when it’s real.” Kai tsaye daga haka ya juya ya hau upstairs ya bar ta tsaye wurin tana binsa da kallon mamaki da tashin hankali. Domin a karon farko ta ga ɗanta yana yaƙar abin da ko kuɗi ko iko ba zasu iya kashewa ba. Da wannan tashin hankalin ta nufi hanyar fita, kai tsaye da niyya tace Mecheal ya kai ta gida dake da kanta tayo driving ɗin.


Fuskarta cike da tsantsar tashin hankali take kallon Mecheal din dake mata bayanin yadda Boss din ke gwagwarmaya a tituna a sabo da yarinyar kawai. “Ka tabbatar min…”
ta faɗa cikin murya mai dauke da tsantsar ɓacin rai. “Who is the girl?”

“Muslim Hijjab…” Wani irin tsalle zuciyarta tayi Idanunta suka buɗe sosai, shekaru wasu shekaru da suka jima da shudewa na ɗan gitta kanta “WHAT?!” Ta faɗi da ƙarfi tare da furta.

“Impossible…”

Ta faɗa tana ɗan girgiza kanta. Muslim!?, Ita John ze jayoma abin kunya da tozarci kuma?, dama yan uwanta da dangin ubansa na cewa tsoron sa take ji, to kuwa lallai idan ta bari maganar nan ta fita cikin dangi ba tare da tayi maganin matsalar ba akwai damuwa babba ma kuwa.

“No ba ma zan taɓa barin hakan ya faru ba…” Tayi maganar da kallon Mecheal sosai tace. “Idan har wannan maganar ya fita cikin dangi, zan muzanta, Ina son yin wani abu…”
Sai ta lumshe idanunta da har sun yi ja....

“Zan kawar da ita.” Ta faɗi tana fidda wani sautin huci, kafin cikin sake hangulowa tace.

"Lallai duka bayanan yarinyar nake da ɓukata, tun daga Ranar haihuwarta har zuwa matakin da take a yanzun, And ƴar gidan uban waye ita? " ɗan zaro ido Mecheal yayi tare da furta. "Madame itama wannan girl ɗin Family nata nada wani irin power sosai a cikin garin nan...” wani kallon sa tayi cikin mugun ɓacin rai tace. “Waye ubanta a kaf garin Lagos shi ma nasa aci nashi uban harda uwarsa zan saka a haɗa min...” “Ɗiyar Ambassador Kabeer Usman Maina ce” Wani shegen lalataccen murmushi mara ɗan sautu Madame Victoria ɗin tayi, kafin ta dube shi da wani irin kallo da Idanuwanta da har na fidda wani kalan bala'i balain jin mugun zafin maganar da Mecheal ɗin ya kawo mata. Wani shegen munafikin numfashi a wahale ta fesar tare da furta...
"Kana manta cewar gaba ɗaya Lagos din a hannunmu take ne?, mune nan masu juya al'amuran ciki da wajen Lagos din, dan haka ka ringa gyara wasu kalaman naka Mecheal right and understanding?" Daga haka tace ya fice mata a mota don ta fasa yayi driving din nata ma, tana kuma sake jaddamasa cewan lallai a goben take da buƙatar sabbin bayanai dan ga ne da yarinyar.

♡

*Yasmine*
Tun da taja motar kusan hankalinta ke a rabe, ɗaya naga tukin ɗaya kuma naga John data gama kashewa da muggwan maganganun ta masu zafi. Don haka hankalinta yake kamar ba'a jikinta ba, wanda har bata san wata motar na bayan nata ba da suke kamar kusan a tare ma, hannunta ɗaya na saman sitiyarin motar ɗayan kuma ta ɗan riƙe kanta a hankali tare da ɗan lumshe fararen idanunta masu kaifi bayan tayi parking car nata. Har bata san lokacin da dayar motar ta faka ba har na cikinta na fitowa se jin saukar maganarsa tayi a kanta.

"YASMINE" Ya kira sunanta a hankali cikin muryarsa mai cike da nutsuwa, wanda jin saukar muryan nata yasa ta buɗe idanunta din da take jin sun mata nauyi ta kalle shi. Yana tsaye daga wajen wurin iska na kada gashinsa me kyau da sheki Ya Omer ne, Ya Omer ɗin da yake mata wani irin mahaukacin So bana hankalin da zai iya dauka ba. Amma tun tuni ta rasa abinda yasa taji kawai be mata a mijin da zata iya aura ba, ga kuma yanzu data kamu da tsananin ƙaunar ARNE. Wani abu me kama da abinda aka rasa ta furta tana buɗe motar ta fito, hannunta rike da wayar ta m gaba ɗaya duk tayi laushi.
"Barka da zuwa Ya Omer!, I'm sorry ban jika ba, and yau wata gajiyar da ban san taba nake jin na kwaso..." kansa ya gyada mata yana rufa mata baya don tuni har ta wuce zuwa cikin gidan. Mamynta tana kitchen Dad nata kuma be dawo ba, se iyaka Husna dake watching channel zaune a parlourn. Hannu kawai ta iya cirama Husna ɗin bayan ta bata side hug ta haye sama, ita kuma Husna na murnan taran Yayan nata da girmama kamar koda yaushe.


Tana isa bedroom nata ta zube a gefen ƙofar kamar wata yarinyar da aka watsar. Wani kuka ta fashe dashi mara sauti sabo da ji tayi in ba kukan ta fasa ba hankalinta bazai taɓa kwanciya ba. Kukan take da nufin duk abinda ke sukar zuciyarta zai janye, amma maimakon sauƙi da afwar da take nema sema jin da take kamar ana ƙara zafin zuciyarta ne. "Na shi ga uku Ƙaunar ARNE nake da gaske jama'a...." Ta faɗi tana sake cusa kanta tsakanin cinyoyinta, wanda ya saka jikin
Husna data shigo ɗakin a hankali soma dan rawa. Don ganin Yasmine ɗin haka…Da sauri ta rufe bakinta da hannunta. “Aunty Yasmine…” Se kuma ta karoso da gudu ta zauna kusa da ita.

“Me ya faru? Me ya faru haka da zafi?”

Da kyar ta iya ɗago kanta idanunta sunyi ja har fuskartama abinka da fara. Kwantowa jikin Husna ɗin tayi, don tanajin hakan shi ne kadai abinda zai iya bata salama a dai halin da take a ciki. "Son ARNE CHRISTIAN na kamu dashi Husna, Wllh da gaske ji nake kamar in ba aure shi mutuwa ma zan yi I love her³" Tayi ta nanata kalmar lover her ɗin. Dan bubbuga bayan ta Husnan ta shiga, don ba ta san abin da za ta ce mata ba saboda ta san akwai irin raunin da baya buƙatar magani. Haka kuma tasan awai irin SOYAYYAR da idan ka bari… tana kashe ka.


Tunda ya shige bedroom nashi yayi rub da ciki saman gadon sa ya lumshe ido, kalmar. “Ka tafi John…Ka tafi ka nemo kanka… kafin ka nemo ni. Domin idan ka nemo ni yanzu… za ka rasa kanka.” kalmar ce kawai ke masa amsa kuwwa, kamar kuma wanda aka zabura ya mike zaune, tare da fiddo wayarsa ya buɗe search engine. Hannuwansa na rawa yayin da ya rubuta.

*“What is Islam?”*

Kowanne layi da ya karanta… yana buga zuciyarsa kamar gudumar ne.
_Submission to the will of God._
_Peace through obedience._
_There is no god but God._

Wani rufe idanunsa yayi karo na farko cikin rayuwarsa… ya ji kamar yana tsirara. Kamar dukiyar da yake da ita, iko da yake da shi, suna… komai ya zama kamar ƙura a idonsa.

“Submission…” ya sake maimaita kalmar.

A duk rayuwarsa bai taɓa miƙa wuya ga kowa ba shi ne wanda ake miƙa wa wuya. Amma yanzu… wani ya ce masa akwai wanda ya fi shi ƙarfi. Wanda ba a gani… amma komai yana ƙarƙashinsa.

Take zuciyarsa ta shiga rarrabewa cike da rudewa...


*BY AMMEY LAYLERH ✍️


08104493215






*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 19

Paid book

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡

Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215


*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

♡♡♡♡

ꨄ Shiru kawai John yayi a tsakiyar gadonsa, idonsa na kan wayar amma zuciyarsa ba ta nan. Kalmar “Submission to the will of God” na ta juyawa a kansa kamar ana maimaita masa ta daga sama. “Submit…” ya sake furta kalmar a hankali. Wani irin murmushi mai cike da ruɗani ne yaso kwace masa. In banda abu ma ta ya za'a ce wani abu guda ɗaya ne za'a ware shi za'a bautama a masa biyayya ?, shi da ake masa biyayyar, shi da kowa ke tsoron kuskura ya ce masa a’a… yanzu shi ake cewa akwai wani da dole a masa biyayya?. Ahankali kuma ya sauke wayar daga hannunsa tare da dan lumshe idonsa ya koma yana jingina da jikin gadon. “Who exactly are you… Yasmine?” ya furta kamar tana gabansa.
Amma a lokaci guda, hoton Yasmine din ya sake bayyana a zuciyarsa, kukan ta, yadda muryarta ke rawa idan ta kira sunan ARNE CHRISTIAN, da kuma yadda ta kalli tsakiyar cikin idonsa tace.
“Na zaɓi addinina akanka.” Wani zafi yaji kamar ze tsaga masa kirji, ya tashi tsaye da sauri kamar wanda ake tunzurawa tunani mai nauyi. Ya fara yawo a cikin ɗakin, hannunsa sarke a kirjjnsa. “No… this is not normal.” ya faɗa da ƙarfi. Amma duk yadda yake ƙoƙarin karyata abinda yake ji… zuciyarsa na ƙara tabbatar masa da akasin haka. Haka jonh ya kusan raba
daren yana searching dangane da kalmar Islam, da kyar ya iya barin kansa runtsawa wajen uku da rabi na daren ranar. Basu sake haduwa ba da YASMINE har tsawon 5 day's, ga Dad ɗin India yazo mahaifin Deepika wacce yau kwananta biyu a gidan John din amma ko kallo bata ishe shi ba.
♡
Madame Victoria tana zaune a ɗakinta da yake kamar na sirrin ta wanda yake ɗauke da duhu kaɗan, labarin Mecheal ya jefa mata tashin hankali fiye da yadda ta zata. “Muslim… Hijab…” ta sake maimaita sunan cikin ƙiyayya, waɗan su ababuwa da suka shude na kokarin faso brain nata su fito,
Ta mike tsaye ta soma zagaye dakin a hankali kamar mai lissafin wani abu. Ta jima tana juya abinda zuciyarta ke kudirta mata kafin t ɗauki wayarta a hankali ta fara kira. Ana amsa kiran abinda ta fara bada umarni dashi shine.
“Get me everything about Ambassador Kabeer Usman Maina’s daughter. Everything.” Daga haka ta katse kiran tana fitar da numfashi mai nauyi.
“Idan aka bari har John ya yi kuskuren nan…” ta yi shiru na ɗan lokaci.
“Ba zai zama John nawa ba kuma.”
♡
A gidansu Yasmine kuwa…
Ta kwanta a kan gadon ta, idonta a buɗe amma zuciyarta a rufe da nauyi. Husna ta bar ɗakin bayan ta tabbatar Yasmine ta yi bacci ko da kuwa na karya ne tayi. Wayarta na gefenta, amma ba ta da ƙarfin ɗauke wa. “Ya Omer…” ta furta a hankali. Amma sai hoton John ya shiga tsakanin tunaninta ba tare da izini ba, ta rufe idonta da sauri tana me furta.
“No… no no no…” ta fara girgiza kai.
“Ya isa.” ta sake faɗa tana ta shi zaune cikin sauri tana riƙe kanta dake mata barazana da fashewa.

“Why am I thinking about him?”

Sai ga hawaye sharrr suka zubo mata.
Domin gaskiya ita ma ta sani da wannan ɗin kamar wani gagarumin yaki ne tsakanin karya da kuma gaskiya.

Karfe biyar saura John ya sake buɗe laptop ɗin sa. Ya fara karanta game da Islam fiye da da. Kowanne layi yana ƙara masa tambayoyi, ba amsoshi ba.
Sai ya tsaya a wani abu:
“A Muslim, God is closer to you than your jugular vein.” Ya ɗaga kai a hankali. “Closer than my life?” ya maimaita. Wani abu ya tsinke a cikin zuciyarsa, a wannan lokacin kamar ya ji muryar Yasmine a nesa. “Ba zan iya sauya addini ba…” Sai ya tashi tsaye da sauri. “Then why do I feel like I’m the one about to change?” ya furta cikin tashin hankali. Wani bugun ƙofa ya katse shi. “Boss…” Haka ya tsinkayi muryar Mecheal daga waje. John ya tsaya cak, kafin ya bashi izinin shigowa ta hanyar furta.

“Come in.”

Mecheal ya shiga cikin girmamawa, amma fuskarsa cike da damuwa.
“Madame Victoria… ta fara bincike sosai.” John ya kalle shi cike da madaukakin mamaki. “Bincike akan me?” Mecheal ya yi shiru na ɗan lokaci kafin ya ce. “On Yasmine.”
Idanunsa da yake dauke da bacci ya dan ja yana lumshe wa kamin ya ce.
“Tell her…” ya fara magana a hankali.
Sai ya dakata. Wani irin zafi ya hau masa zuciya. “Tell her… not to touch her.” Mecheal ya ɗaga kai cikin mamaki.
“Boss… you sound like you’re falling.”
John ya kalle shi da idonsa da suke cike da nauyin bacci yace. “No.” kafin yaja numfashi yana mikewa tare da furta.
“I’m already in it.” Ya faɗa toilet Mecheal ya fita. Kwana biyu bayan haka…Karfe shida cif da cif Yasmine ta fito daga wurin aikinta da se yau ɗin take dawowa ma, ta fito ke nan tana gyara likab nata ta nufi wurin motar ta taji an furta kalmar....

“Ke…”

Da wata murya mai kaushi mai ɗauke da iko haka taji an kira daga bayanta.
Cak! Kuwa ta tsaya zuciyarta na bugawa. Kafin ta juya a hankali tayi tozali da wata mata tsaye a gabanta…
Cikin kaya masu tsada da kamshi mai ƙarfi. Idanunta cike da wani irin ƙarfi da iko me tafe da girman kai. Kafin ta tako a hankali bodyguard biyu na take mata, kallo ɗaya ta mata ta tabbatar da cewar ba musulma bace, tun daga yanayin kananun shigar dake jikinta dan wata rigace a jikinta wacce da ƙadan ta wuce gwiwwarta. Cikin izza ta isa ga Yasmine ɗin tana tsayawa a gabanta cikin kaushin murya tace.
“Ni ce nake nemanki…” matar ta faɗa a nutse amma kuma cike da cikakken iko mai kama da Umarni, Yasmine ta ɗan haɗe gira dan in jiji da kai da girman kai ne ai gidansa tazo. “Ni kuma ban san ki ba.” Matar ta ɗan yi murmushi me kama dana mugunta ko dai wani abu tace. “Amma kin san ɗana.” ta faɗi tana ƙare mata kallon sama da ƙasa don taga me yaja hankalin Yaron ta da har akanta ya gaya mata maganganun daya ga dama irin na daren jiya?. Cak! Yasmine ta dakata kalmar ɗana ta daki zuciyarta da gaske. “Ɗanki…?” ta maimaita kalmar, Matar ta ɗan matsa kusa da ita.

“Joseph.”

Nan take Yasmine ta gane har fuskarta na sanja yanayinta tace. “Toh?” ta faɗa da ɗan tsauri. Matar ta sauƙe tabarau ɗinta a hankali faffadar fuskarta na bayyana ta nuna kanta da yatsa tace.

“I am his mother.”

Matar faɗi tana sake kallar Yasmine daga sama har ƙasa, daidai da lokacin da wata iska me ƙarfi ta dage nikab ɗin Yasmine. Wanda matar taga kamar walkiya ce ta gimla mata, amma dake gwanace wajen shanye ko wanne irin tracks bata karaya ba sema matsawa data sake yi ta nuna ta da yatsa tace.
“Ki nisance shi.” Ta faɗi kai tsaye ba
tare da ɓoye ɓoyen komai ba. Wanda hakan ya ɗan ba Yasmine dariya har ta dan dara din mai sanyi, ta dan kada hannunta a fuskar matar babu tsoron komai tace. “Hi excuse me?” sedai kafin tace komai Matar ta rigata ta hanyar cewa. “Ki ji ni da kyau… duk abin da kike tunanin kina yi da ɗana…ki dakata haka nan.” wanda ya saka Yasmine gimtse fuskarta tana haɗe rai sosai tace.
“Ni ban neman ɗanki ba.” Matar ta ɗan ɗaga gira. “Amma shi yana nemanki.”
Shiru ne ya ɗan ratsa wurin, wannan karon kalmar ta shiga

19 / 31