Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
zuwa inda suke zama tare da Almaz. A nan kuwa ya sami Almaz din na zaune tana kallon ruwan beach din kamar yadda ta saba.
“Kin riga ni yau,”
John ya faɗa yana zama tare da zube kafafunsa cikin ruwan.
Ta yi murmushi kawai tace “good morning” da morning kawai ya amsa ta kafin cikin kamar alamar gan ɗoki yace
“Ta yi min reply.”
Almaz ta juya kai kaɗan tana dan waro ido tace “Me ta ce?” John ya ɗan yi shiru kafin ya amsa da. “Ta ce tana sona… amma dole na musulunta.” Almaz ta sauke wani numfashi a hankali kafin
cikin nutsuwa tace.
“Tambayar ba ita ce me take so ba…”
Ta ɗan karkata kai, tana kallon shi sosai.
“Tambayar ita ce kai me kake so?”
John ya yi shiru domin ji yayi wannan tambayar… ta fi komai wahala a gare shi.
“Ban sani ba…”
Ya furta a hankali, Ahankali
Almaz ta ɗan yi murmushi tare da dubansa tace. “To mu fara daga nan.”
Tare da miƙewa tsaye tace
“Zo mu je wani wuri.”
TA fadi suna mikewa ya rufa mata baya babu musu suka ɗauki hanya zuwa wani wuri kusa da gefen beach din. wani ƙaramin wuri ne mai natsuwa ba hayaniyar kowa hasali ma wurin ba mutane da yawa. Wani tsohon mutum suka gani zaune kan buzu na farar fata.
Almaz ta gaishe shi da girmamawa, shima John da ya lura da yadda take girmama shi. Se ɗan kalle ta da ido alamar “Waye shi?” da idon ta masa alama da. “Mutum ne da yake da hikima,” ta mayar masa da amsar cikin sauƙi kana suka zauna kusa da shi.
Tsohon ya kalli John, idanunsa cike da natsuwa da kuma wani kyakkyawan murmushi idonsa tsabar fari har na fitar da wani haske haske.
“Ka zo neman amsar ka ne? Ko kuwa kazo akan kaddarorin da zasu bibiyi rayuwarkane akan, DUHU na DUKAN duhu din da kake gaf da afkawa… ?”
Ya furta kai tsaye.
Shi kuwa John kallon wannan dattijon mutumin yake, yana son ya tuna ina da ina yasan fuskar nan?, a kuma ina ne ƙarshen ganinsa da fuskar?, amma se yaji kamar an mantar dashi komai kamar an toshe basirar da yake da da wani abu me nauyi, duk da a ɗan firgicen daya tsinci kansa na sanin ko mai zai ce masa ba se ya tsinta kansa da furta.
“Wataƙila… duka biyun.”
Tsohon ya yi wani murmushi kaɗan irin na tsoffi masu cike da hikima yace.
“Idan kana neman gaskiya… to ka saurari zuciyarka. Amma ka tabbata ba tsoro bane ke magana.”
Kalmomin suka dirarma John a zuciya.
★..
Washe gari da yamma bayan rabuwarsa da Almaz ya koma masaukinsa amma ya ringa jin zuciyarsa kamar ana masa kida ne akan yana son samun abu me nutsuwa fiye da wannan. Ga wani irin shiru mai zurfin daya ratsa ɗakin nasa, irin shirun nan da ke cike da tunani fiye da hayaniya. Ahankali ya shiga cikin chart nashi da Yasmine suna nan.
Kalmar _You know what I said_ na yawo a kansa kamar ƙarar da ba ta daina ba, jin hakan ma ba nutsuwar da yake son samu zai yi ba seya shiga contact nashi yana lalubar No na almaz cewa yay mata su hadu inda suka saba haduwa, daga haka ya datse kiran yana fitowa, sedai ganin almaz din zaune yaso ya bashi ɗan mamaki matuka, wanda har ya gaza ɓoye wa yake tambayarta wai ta ya ta riga shi bayan yasan irin tazarar dake tsakaninsu?, murmushi me kyau tayi tana ce dashi ai dama tana gab da wurin ne. Kawar da hakan yayi ta hanyar kiran sunanta da yayi.
“Almaz,”
Ya kira sunan kai tsayen daya saka Almaz din dubansa tana me furta.
“Me ya faru?”
“Ina so… ki kai ni wani wuri.”
Ya fada yana ɗan lumshe idonsa.
“Wani wuri?”
Ta sake maimaitawa da alamar tambaya. Kansa ya gyada mata alamar tabbaci yana me furta.
“Inda zan samu nutsuwa… inda zan fahimci abubuwa sosai.”
Almaz ta ɗan kalle shi na ɗan lokaci kamar tana tantance gaskiyar sa ne, kafin ta miƙe tsaye.
“To mu je.”
Ba wani wurin shakatawa suka nufa ba wannan karon. Gari suka shiga sosai
suka wuce hayaniya, suka shiga wani wuri mai sauƙi… mai tsarki bakin wani
Masallaci. John ya tsaya daga bakin ƙofar ya yi shiru. Yana kallon mutanen dake shiga suna fita, wasu suna sallah, wasu suna zaune cikin nutsuwa. Bai taɓa shiga irin wannan wuri da irin wannan yanayi ba. Idonsa ya ɗan sauya yanayi jikin sa ya fara kamar alamar rawa saboda wata irin muryan dake tashi wacce da alama kuma wani recording ne na karatu aka kunna, wacce take fita da wata irin murya me sanyi da nutsuwa kuma ta mace.
“Ba dole bane ka shiga,”
Almaz ta faɗa a hankali ganin yadda yanayinsa ya koma. Kansa ya girgiza yana jin wani irin abu na ratsa ilahirin jikinsa gaba ɗayan da bai san ko menene ba.
“A’a… ina so.”
Ya fada a hankali ya taka ƙafa ɗaya… sai na biyu ya shiga. Tun daga harabar masallacin komai ya bambanta da irin kowanne wuri, ba hayaniya ba sautin kida ba komai, se iyaka muryan dake sake karade ilahirin harabar masjid ɗin. Sai ma wata irin natsuwar da ko a hasashe ba zai taɓa iya bayyana ta ba yaji na shigar sa. Ahankali ya kai zaune saman tattausan carpet ɗin dake malale daga ƙofar masallacin, Wani abu yaji kamar ya tsaya cak a kwanyar kansa,daidai sanda aka dakatar da wannan karatun me cike da nutsuwa cak. yayin da kiran salla ya mamaye gurin gaba daya. Yadda yayi shiru haka duniyar ke kamar tayi shirun tare da JAMA'AR dake cikinta, kowa yana sauraren kiran sallar dake tashi cikin wata kwantaciyyar muryar dake saukar da wani irin nutsuwar da haske ya mamayi musulmin gurin, Ko shi da yake ba musulmin ba wani irin nutsuwa yaji na shigar sa. Yana sauraren yadda wani da babu jimawa ya zauna gefen sa ƙasa ƙasa yana karanta addu'ar bayan kammala sauraren kiran sallah,baka jin abinda yake fadi tar amma kadan kadan muryarsa tana motsawar da ahankali yake maimaita kalmar.
“Allahumma rabba
hadhihid-da‘watit-tammah, was-salatil-qa’imah, ati Muhammadan al-wasilata wal-fadilah, wab‘athhu maqaman mahmudan alladhi wa‘adtah, innaka la tukhliful mi‘ad.”
Tun da ya fara karanto adda'ar John ya lumshe idanuwansa a hankali. Haka kawai ba tare da yasan ma'anar kalaman ba amma haka yaji zuciyarsa ta karɓesu kafin kunnuwansa su gama jin su. Ga wani irin sanyin da yaji ya ratsa jikin sa. Hatta da bugun numfashinsa sai da ya ɗan tsaya na wasu sakanni, sai yaji kamar hayaniyar cikin zuciyarsa tana raguwa a hankali… kamar ana cire masa wani dutse mai nauyi daga ƙirji. Bai san dalilin da yasa idanunsa suka cika da ruwa ba, shi kansa bai san yadda akayi zuciyarsa ke amsar sautin ba, domin rayuwarsa bai taɓa jin wani abu da ya shiga masa rai irin haka ba, shi ba waƙa ba, ba kuma
kalaman soyayya ba, haka zalika ba
sermon ɗin cocinsu ba. Wannan daban ɗin daban ne, wani abu ne mai nauyi amma kuma mai salama. Ya juya a hankali yana kallon mutumin dake zaune gefensa da tasbaha a hannunsa, yana ci gaba da ambaton addu’ar cikin ƙasƙantar da kai . John ya haɗiye wani yawu a karon farko cikin rayuwarsa ya ji zuciyarsa tana tambayarsa tambayar da bai taɓa bari ya fito fili ba.
“Me yasa wannan addinin yake taɓa zuciyata haka…?”
Kuma abin da ya fi tsoratar da shi shi ne… Ya ji kamar yana son sake jin addu’ar.
Yana nan zauna a gefe har aka shiga sallar, yana kallon yadda mutane ke yin Sallah gwiwoyinsu na taɓa ƙasa cike da nutsuwa, fuskokinsu kuma cike da tawali’u, ahankali yaji zuciyarsa ta fara sauya wa ba saboda Yasmine ba, ba
saboda wani ya tilasta masa ba, sai don
saboda abin da yake gani da abin da yake ji a zuciyarsa.
“Me yasa nake jin haka…?”
Ya sake tambayar kansa, Idanunsa naci gaba da cika da ruwa. Har aka idar da salla kana ya fito suka sake nemar guri kusa da masallacin suka zauna.
John ya yi shiru na ɗan lokaci kafin
ya kalli Almaz. “Idan na yanke shawara…” Tayi saurin katse shi cikin nutsuwa kamar ta san abinda ke ransa dama can.
“Kada ka yi saboda Yasmine.”
Ya yi ɗan murmushi kaɗan tare da gyada mata kai.
“Na sani.”
Sai ya ɗan tsaya yana jin kamar yana shirin taryar wani gungumemen yaki ne irin na ƙasa da ƙasar nan, kafin ya ɗora da cewa.
“Zan yi saboda ni.”
Almaz ta yi murmushi irin wanda ke nuna farin ciki na gaskiya tace.
“To yanzu ka fara fahimta.”
Suka tashi suka soma tafiya domin komawa masauki. Yaso taka mata kamar koda yaushe amma tace ta gode. Yana komawa ya zauna saman sofa tare da ɗaukan wayar sa ya buɗe chat ɗin Yasmine. Amma wannan karon ba tare da shakka ba ya rubuta mata.
“I’m not there yet… but I’m searching. Not for you… for me.”
Ya danna send yana jingina bayansa zuciyarsa na mata beating. Ahankali ya Mike ya na nufar gaban doorwindow ya
jingina kansa da gilashin na windows din, idanunsa a buɗe amma zuciyarsa ta nutse cikin zurfin tunani.
“Thinking about thinking…”
Ya furta a hankali kafin ya yi dariya kaɗan ba dariyar farin ciki ba, amma ta fahimtar kansa.
“Na shiga wani irin zagayen tunani ne…”
Ya ƙara faɗa a ransa yana tunanin Yasmine amma ba kamar da ba, ba da zafi kawai ba, sai da tambaya, yana tunanin Almaz amma ba da ruɗani ba sai da godiya. Yana tunanin kansa amma wannan shi ne mafi nauyi.
“Me nake so da gaske?” ya tambayi kansa. Yana komawa gefen gado da tarin tunaninnika wata zuciyar na ce masa.
“Ka tafi wurinta.”
Wani ɓangaren kuma na ce masa.
“Ka tsaya ka gane kanka.”
Idonsa ga rufe da ƙarfi. “Why is my mind like this?” ya furta yana sake komawa duniyar tuninin, ba wai tunani ne matsala ba sai yadda yake gudu daga tunanin. Ahankali ya sake tashi tsaye a wurin yana sake komawa bakin window. Ya ɗora hannu a kirji.
“Thinking about thinking…” ya maimaita a hankali, wannan karon cikin nutsuwa, sai ya ƙara da cewa.
“Maybe I don’t need all the answers tonight.”
Ya jingina kansa da taga, idonsa a buɗe, zuciyarsa a hankali tana samun wata natsuwar yanke shawarin da yake kokarin yi. A kuma karon farko cikin kwanaki da damar da tunaninsa bai yi masa nauyi ba, cike da jin kwarin zuciya ya kwanta a ransa.
★..
Washegari bayan wannan daren mai cike da tunani, John ya tashi da wani sabon yanke shawara a zuciyarsa.
Ba gudu ba haka za bada rikicewa ba sai dai tafiya don fahimta. Ya shirya jakarsa cikin nutsuwa, ya kalli ɗakin da ya zauna tsawon kwanaki a Hotel ɗin, sannan ya fitar da wani numfashi mai zurfi. “Time to move…” ya furta a hankali.... A filin jirgin sama kuwa baka jin kai sai sautin tashi da saukar jirage na cika iska. John yana tsaye yana jiran jirgin sa idonsa cike da tunani amma zuciyarsa tana da wani sabon natsuwa.
Yasmine bai sake rubuta sake rubuta mata komai ba tun saƙon ƙarshe.
Almaz kuwa ta masa saƙon ban kwana me tattare da fatan alkhairi, wacce ita ce ma ta saka shi a hanyar ita da mahaifinta suka bashi address na inda ya nufa a kasar Saudia. “Ka je ka gano kanka. Kada ka ji tsoro.” Bakuna biyun suka hade baki zuciyoyi da idaniyarsu cike da fata da kuma burin da bai san ko na minene ba...
Ahankali ya sake jingina kansa da kujerar jirgin da babu jimawa ya tashi idonsa a rufe, Yana jin yadda jirgin ke ci gaba da ratsa sararin samaniya.
Bayan wasu sa’o’i jirgin daya taso daga kasar Ethiopia ya sauka a kasar Saudi Arabia. Ƙasar dake ɗauke da natsuwa da kuma tsari. A natse ya biyo sawun passenger's na jirgin zuwa filin jirgin, wata iIska mai dadi ta masa maraba a filin jirgi, Kamala Ilmaha da natsuwa suka bambanta da abin da ya saba gani.
John ya tsaya na ɗan lokaci a ƙofar fita yana kallon mutane suna tafiya cikin natsuwa, wasu cikin sutura masu alamar addinin Musulunci, wasu cikin girmamawa da shiru. Zuciyarsa ta ɗan yi nauyi amma ba tsoro mafaka ba.
Sai dai nuna jajircewa da bada kwarin Gwiwwar da yake jin cewa yana shiga wani sabon babi ne na rayuwa. A birnin Riyadh John ya fara wata sabuwar rayuwa, ba tare da hanzari ko garage ba. Sai dai kallo, sauraro, da koyo.
Yana ganin yadda mutane ke rayuwa cikin tsari da ibada. Yana ganin masallatai masu haske da nutsuwa.
Yana jin wani abu a zuciyarsa yana ci gana da motsawa ba tilas ba, sai dai tambaya. “Is this what I’ve been missing… or just what I’m learning?”
Tun da yazo babu da wanda yayi waya ko chart, don haka yau da yake karasa cika kwanki uku cif ya ɗauki wayarsa ba tare daya buɗe chat ɗin Yasmine ba.
Bai kuma nemi Almaz ba ya buɗe sabon note ya rubuta.
“I'm not becoming someone else. I'm trying to meet myself.”
Daga haka ya rufe wayar yana kallon gajimaren da sukama sama ƙawanya ta hanyar ado. Iskar yammacin ranar naci gaba da kadawa me ɗauke da wani irin shiru mai nauyi amma mai kyau. Washe gari ya shirya kansa cikin wasu yard masu taushi milk ya dauki cap zuwa inda zuciyarsa keta azalzalarsa akan yayi yaje. Rana ce mai haske ga
iska mai ɗan sanyi tana ratsawa a cikin harabar wajen, tana motsa ganyaye a hankali suka nufi babban masjid dake ƙasar. Ahankali ya fito daga cikin motar
Idanunsa na kallon wajen da bai saba da shi ba. Duk da baya son hayaniya, ba kuma ya son ya fiye ganin taron mutane, shi yasa ko da can ma ya tsani zuwa club ko party haka. Amma yau ya zo ne saboda wani abu da bai san dalilinsa ba. Kamar wani abu na tura shi haka yaja ya ɗan tsaye tare da shakar wani ni'imantaccen numfashi ya soma tafiya ahankali, kafin ya ɗaga kansa a natse yana kallon Babban Masallacin dake tsaye a gabansa....
_To fa jama'a AMMEY LAYLERH me john ke shirin yi ne?_
_Ikon ALLAH me yadda yaso to bari mu taro page na gaba kuma jama'a...._
*BY AMMEY LAYLERH ✍️
08104493215
#MUSLIMS
#JANNEERH
AMMEYLAYLERH
#JOHN +IBRAHIMUL KHALEEL
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 23
Paid book
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
♡♡♡♡
ꨄ Ahankali John ya sake ɗaga kansa yana kallon Babban Masallacin dake gabansa. Wani irin haske ne ya mamaye harabar gurin, fararen ƙoyaye na kyalli ƙarƙashin hasken rana yayin da iska mai ɗan sanyi ke ratsawa tana ɗauke da sassanyar ƙamshin turare da tsabtar wajen. Wasu mutanen na ta shiga suna fita cikin nutsuwa bada hayaniya, ba kuma ture-ture ba, komai na gurin na ɗauke da wani irin salama da zuciyarsa ke kasa fahimta. Ya haɗiye wani yawu a hankali kafin ya taka mataki na farko zuwa cikin harabar masallacin, wanda duk taku ɗaya da zai yi yana jin kamar yana taka wa ne da bugun zuciyarsa.
“Why do I feel like I’ve been here before…?”
Ya furta ƙasa-ƙasa ahankali ya ƙarasa shiga. Kai tsaye da sautin karatun Al-Qur’ani ya fara cin karo wanda ya karade kunnuwansa, wannan karon ba recording ba. Murya ce ta gaske, murya mai sanyi, mai zurfi mai ratsawa kai tsaye har cikin zuciya. John ya tsaya cak jikinsa na ɗan ɗaukar wani irin rawa.
Da Idonsa ya bi inda yake jin sautin na tashi har ya hango wani Dattijo zaune daga can gefe cikin fararen kaya masu sauƙi. Al-Qur’ani ne a gabansa yana karantawa cikin nutsuwa kamar wanda babu komai a duniya face shi da kalaman ALLAH. Kusa da Dattijon wasu mutane ne zaune suna sauraro, John bai san dalilin da yasa ƙafafunsa suka soma kai shi wajen mutumin ba, duk da rawan da ƙafafu sa keyi amma haka yake jin kamar ana jansa ne zuwa ga Dattijon. Cikin kamar tafiyan sassarfa ya ƙarasa kusa da dattijon, kamar yasan da zuwan John ɗin Dattijon ya ɗago kansa a hankali, inda kai tsaye Idanunsu suka hadu da juna. Wani irin
faduwa john yaji gabansa yayi saboda haduwar idanun mutumin da nasa.
Cike da wata irin nutsuwar cike da wani irin haske, wannan Dattijon ya yi murmushi kaɗan.
“Lokacin har ya ƙara so kenan?.”
Wanda wannan tambayar da yayi ya saka John tsayawa cak yana kallonsa.
“Ka… ka san ni?”
Mutumin bai amsa kai tsaye ba sai ma rufe Al-Qur’anin da yayi a hankali yana nuna masa wajen zama kusa da shi.
“Zauna, ya Jikina.”
Bai san dalilin da yasa ya bi umarnin mutumin ba ya kuwa zauna din, sun jima a zaunen har na wasu daƙiƙu babu wanda ya yi magana. Sai sautin iska da kuma sassanyar karatun wani yaro daga can gefe dake tashi, kafin daga
bisani Dattijon ya dubi JOHN.
“Ka daɗe kana ta gudu.”
Yayi maganar daya saka John ya ɗan haɗe gira yana furta. “Daga me?”
“Daga kanka.” Kalmomin suka bugi zuciyarsa kai tsaye. Ya sauke numfashi yana shafa fuskarsa tare da furta.
“I don’t understand what’s happening to me…”Ya furta cikin raunanniyar muryan daya saka Dattijon ɗan sakin murmushi kaɗan. “Ba dole ka gane komai yanzu ba.” Yayi maganar tare da ɗan matsa kusa da John ya cilla masa tambayar data saka John saurin dagowa yana kallonsa. “Ka faɗamin… Lokacin da ka ambaci ‘YA ALLAH’ a karon farko… Me ka ji?” Nan take jikin John ya ɗan yi sanyi take yana tuna daren nan, yadda zuciyarsa ta sami nutsuwa ya kuma yi bacci cikin salama da kwanciyar hankali. Idonsa ya sauƙe ƙasa tare da bashi amsa da.
“…Peace.”
Ya amsa da ƙyar, Dattijon ya gyada kai a hankali yana