Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
dawo dashi cikin tunaninsa, kafin a dake ya furta.
“yeah.”
Ya amsa yana jan numfashi mai nauyi,
“When is departure?” “In a few hours. Transportation will pick you up.” daga nan call ɗin ya katse, duk da haka John be motsa ba, bai kuma yi komai ba,sai iskan dake ci gaba da kaɗawa, kafin ya samu ahankali ya juya a hankali, ya sake shiga cikin Hilton Miami Airport Blue Lagoon…Matakansa sun fi na da ɗan nauyi yanzu, ba kamar wanda zai huta ba… Amma kamar wanda ake tura shi zuwa wani abu da bai gama fahimta ba, haka Lift ta ɗauke shi zuwa sama…
Reflection ɗinsa ya sake bayyana amma yanzu, ya bambanta yana jin ba kawai gajiya ba ce…Dole akwai wani abu mai zuwa koda ya isa masaukin nasa tsayawa kawai yayi a tsakiyar ɗakin.
Ya kalli gadon da bai iya bacci a kai ba daren jiya, box nashi kawai ya ɗauka ya fara shiryawa cikin nutsuwa amma cikin fushin da fuskansa bata bayyana shi ka tsaye ba, don baya son tafiyar amma amma ya sani dole ce, a haka da wannan tunane tunanen ya samu ya rufe box nashin bayan ya shirya cikin shigarsa ta pilot. key card na room ɗin ya dauke yana nufar ƙofan fitan, amma se da ya ɗan tsaya a bakin ƙofa na ɗan lokacu, kafin ya lumshe idonsa da sauƙe wani numfashi mara sautu ko kaɗan kana ya buɗe ƙofar. Ya fara tafiya Jacket ɗinsa na'a hannunsa.
Yana dap da isa compound na hotel ɗin wani sabon kiran ya sake shigo masa, kamar ba zai daga ba amma kuma dole ya amsa, kai tsaye shi da kansa ya furta ...
“Captain John. Is calling”
Muryarsa a takaice ta faɗa hakan,
“Captain…” muryar airline ɗin ta dawo, amma wannan karon akwai ɗan canji.
“We have a situation.” wanda ya saka
John ɗan faɗa fuska kaɗan ba da yawa ba, “Go on.” Sai wani ɗan shiru ya bayyana, “Your return flight has been delayed till tomorrow morning.” aka faɗi kai tsaye daga cikin wayan da ya saka John yin shiru ganin ana son sake caja masa kai ya ce.
“Delayed?”
“Yes, Captain. Technical inspection and clearance issues. We cannot proceed today.” Hannunsa ya saka yana matse wayar da ƙarfi, Idonsa na ɗan rufewa har na ɗan lokaci, kawai yana jin kamar son ruga shi kawai suke, tamkar wanda aka tilasta masa yin maganar yace. “fine.” a takaice call in na katsewa daga nan, kai tsaye ya koma room nashi, yana yasar da box nashi saman kujera da ɗan ƙarfi, Yana kai hannunsa ya rufe fuskarsa tare da furta kalmar....
“Damn it…”
A bayyane kai tsaye kayan jikinsa ya sanja bana aikin ba wannan karon
ya saka simple shirt da jeans…
Kamar wanda yake ƙoƙarin zama mutum na al’ada ba wannan pilot ɗin ba ya sake ɗaukar key card nashi ya fita daga ɗakin. Yanayin ya ɗan sake sanjawa ba kamar ɗazun ba har zuwa lokacin kuma zuciyarsa ba ta gama warwarewa ba. A bakin hanya ya tsaya sai ga wani taxi nan, ya ɗaga hannu masa hannu Motar ta tsaya a gabansa.
“Where to, sir?” me motar ya tambaye shi, ɗan shiru John ya yi na alamar tunani don bai ma san inda ya nufa ba, sai kawai yace...
“Just… drive.”
Driver ya kalle shi a mirror ɗin gaba, amma bai tambaya ba motar ta
fara tafiya bayan ya shiga, ahankali motar ta fara ratsa titunan Miami…
Garin yana da kyau sosai musamman
bishiyoyin da suke kusan kewa da garin, gashi sun fara hango ruwan teku daga nesa, ga dogwayen gine-gine masu kyau da tsari, shiru kawai yayi kallon komai ne tamkar be taɓa zuwan ƙasar ba, A ahhh sedan wannan ɗin jin sa yakai daban da sauran, ahankali motar nasu ke ci gaba da tafiya har suka wuce kusa da South Beach… Ga teku nan nata famar walƙiya, Mutane na yawo a wurin, wasu na dariya, wasu na hutawa ne kawai, shi ma se yaji yana son kasancewa ɗaya daga cikin mutanen don haka bar besan lokacin da bakinsa ya furta...
“Stop ita....”
Dan waiwayowa driver ɗin yayi alamar gaskata wa tare da sake tambayar.
“You wanna stop here, sir?”
Sake kallar wajen John ya yi ahankali tare da sake furta
“…Yeah.”
Daga nan ya sauƙa a motan kai tsaye ƙafafunsa na nitsewa cikin yashi me laushi, Iskar tekun kuma ta taho da ƙarfi ta bugi fuskar sa. Nan ya fara takawa zuwa gaba a hankali, ya tsaya yana kallon ruwan. Ruwan yana motsi a hankali, amma yana da ƙarfi a ƙasa kamar yanda yake jin zuciyarsa, hannuwansa duka biyun na cikin aljihunsa ya lumshe idonsa ahankali yana shaƙar ƙamshin ruwan, baka jin komai a wurin se iska da ƙarar tekun.
Sai ya buɗe idonsa a hankali, wanda yaji sun ɗan yi masa sanyi kaɗan, amma kuma ba cikakkiyar nutsuwa ba ce, yana jin kamar yayi missing wani abu me muhimmanci a cikin rayuwarsa tun daga lokacin da ya haɗu da ita... tamkar kuma dama wanda tunanin ke jiran ya fado masa kalmarta ta.
_Koda yake alamu sun gama nuna cewar Musulunci ma kai baka da!...._ Ɗan runtse idonsa yayi, amma har yanzun be dena jiyo ci gaban kalmar nata ba. _Don da dukkan alamu arziƙinsa ma baka samu ba, bare kuma har aje ga sanin daraja ɗan Adam..._ Se yaji kansa kuma na ɗan fara jujjuya yawa, kalmar musuluncin kawai nemar tarwatsa kansa yake, _Amma duk da haka Kai mutum ne wadda ko acikin Christian ɗin ma kai baka da daraja daga kallonka na tabbata haka, duk iskancin da irinku masu addininku suke dashi basa taɓa wulaƙanta ɗan Adam irin haka...._ Hannunsa ya zare daka toshewar da yama kunnuwan yana fara jujjuya a wurin, kafin ya fara tafiya a bakin rairayin… kamar wanda ke nemar wani abu amma bai san ko menene shi ba, kafin a hankali ya cira kansa ya kalli sararin sama, yana jin wani abu me zafi na kama zuciyarsa,
_To dan ma kaji Wllh² baka buge banza ba!, tun da kai baka da cikakken imani da kuma tausayi, to kuwa wllh se na nuna maka hasalin yadda ake mutum ta mace da kuma darajantata!...._
Kalmarta ta gaba ta sake dakar kansa, jikinsa ya ɗan fara masa rawa nan take, ga hasken ranar daya soma dakarsa a hankali, wata kara yayi yana me furta.
“Ohhh jesus”
Ya furta yana samar wata ƙarƙashin bishiya ya kwanta a ƙarƙashin lemar wurin, kusa da wani ɗan farin dattijon dake zaune saman darduma da Alqur'ani a wurin yana karatu cike da wata irin natsuwa, kuma dattijon da ganinsa ɗan 9j ne ma, wata irin nutsuwa John yaji yana sama da jiyo sautun karatun Alqur'anin, take wani daddaɗan bacci yayi awon gaba dashi, baccin daya jima be sama irin saba da jimawa, shi kuwa wannan Dattijon a natse ya sauƙe idonsa kan John ɗin da tun farkon bayyanuwarsa akan idon sane, da ihun da yayi da kuma jujjuya kan daya ringa yi duk a kan idon sane, haka kawai yaji ƙaunar son yaron, da kuma son rabauta shi daga cikin wannan ƙazamin addinin nasa, don kallo ɗaya ya masa yasan cewar ba musulmi bane, kuma ba yau bane karonsa na farkon daya taɓa haduwa da John ɗin ba, a natse ya ƙarasa har inda yake ya kama kan John tare da soma furta....
“Allahumma ihdi JOHN waftah ƙalbahu lil-Islam. Allahumma ihdihina siratal mustaƙim....Allahumma a’iz al-Islam bihi....” _Ma’ana yana nufin ALLAH ka shiryar da John ka bude zuciyarsa zuwa ga Musulunci... Ya ALLAH ka shiryar da shi hanya madaidaiciya.... Ya Allah ka karfafa Musulunci ta wurinsa...._
Kafin ya rufe da...
“Allahumma a‘izzal-Islāma bi-aḥabbi
hādhaynir-rajulayni ilayka... Ya ALLAH!, ka shiryar da wannan bawan naka, ka kuma buɗe zuciyarsa ga hasken ka, ka faɗaɗa kirjinsa ga imaninka, ka fitar da shi daga duhu zuwa haske, Ya Ubangijin talikai.... Ya ALLAH!, shi bawanka ne, Kai ka fi sanin halinsa, ka ji tausayinsa, ka gafarta masa, ka sanya shi cikin bayinka na ƙwarai. Ya ALLAH!, kada ka bar zuciyarsa ta ƙaƙƙarfu, kada ka bar shi ga kansa ko da kiftawar ido ne, ka shiryar da shi zuwa hanya madaidaiciya....” ya masa adda'an cikin nutsuwa mai girma da murya mai sanyi. Daga nan iska ta tsaya,duk wani sautin dake tashi a wurin ya rauraya,
kamar duniya ta saurari addu’ar,
Shi kuwa John tamkar wanda aka farkar a cikin baccin haka yaji sautin kalaman wannan dattijon da ke riƙe da saman kansa har zuwa lokacin. Ga wani kalan abu da ya fara ji daban, shi ba tsoro ba haka shi ba fushi ba, saima wani irin natsuwan da bai taɓa ji ba ne a caf rayuwarsa na kamasa, ahankali cike da nutsuwa mutum ya yunƙura da nufin miƙewa amma kuma John ya riƙo hannunsa, har lokacin kalmomin adda'ar nan da ya masa na ci gaba da ratsa zuciyarsa. Don haka mutumin yaja da baya kaɗan yana kallon John ɗin da shima shi yake kalla cike da nutsuwa, yana jin kamar wannan ba shi ne karon farko daya taɓa ganin fuskar ba....
“Me… ka yi min…?”
Muryan John ya ratsa cikin kunnuwan dattijon, ahankali ya kalla John ɗin cike da wata kalan nutsuwa da haiba ya ce.
“Ban yi maka komai ba…sai kawai roƙon Ubangijin mu da nai kan ya seta ka akan hanya madaidaiciya, wacce zata tseratar da kai ranar gobe kiyama... Ina son wannan rana ta zama ranar farkon haske a gare ka…..a cikin DUHU na DUKAN duhu!!!......” John ya saki hannun mutumin ya koma ya sake kwanciya baccin ya sake tafiya da shi me cike da wata kalan salama da nutsuwa, se wajajen uku ya farka, hakan ma iska me ƙarfin da aka fara kaɗawa ne, da kuma ruwan da aka soma yi sama sama, yana tashi yaga gorar ruwa har biyu a gabansa ya bude ya shanye na farkon, na biyun kuma ya ɗauke yana tafiya da ita cikin ruwan dake ƙara ɗan ƙarfi, fesss yaji zuciyarsa tayi akan zuwansa wurin da yazo cikin wani irin ƙuncin da duhun zuciya, kai tsaye masaukinsa ya wuce, yana shiga ya zare Jiƙaƙkun kayan jikinsa da suka jiƙe sosai kana ya fito yaci abinci ya sake kwanciya, Washegari gari...
Misalin goman safe ya shiga buɗe idonsa a hankali, ba' a firgice kamar jiya ba, bayan haka ga wata cikakkiyar nutsuwa yana jin tana bin ilahirin gangar jikinsa, zaune kawai yayi yana kallar Pop na room ɗin, yanajin kamar yayi loosing wani muhimmin abun da be gudanar ba a cikin safiyar, da yake jin kamar nauyin hakan na neman dannar zuciyarsa, wayar aka kira ake sanar dashi Flight nasu is ready...
“Let’s get this over with…” kawai ya faɗi ƙasa ƙasa yana shigewa bathroom, fuskansa kawai ya wanke da ruwan sanyi ya tsaya yana kallar kansa a cikin mirrorn dakin, sai yaga Fuskar sa ta fi jiya nutsuwa kaɗan, a natse ya shirya kansa cikakken uniform ɗinsa.
White shirt mai tsabta sai Epaulets a kafaɗansa, Jacket ɗinsa riƙe a hannunsa ɗaya ahankali ya fara taka ƙafafunsa har zuwa Corridor ɗin da ya yi shiru kamar jiya, Ya shiga lift ƙofar ta rufe,
Reflection ɗinsa ya bayyana. collar ɗinsa kaɗan ya gyara Kamar yana ƙoƙarin saka mask, har ya sauƙa a Ground floor. Reception ɗin Hilton Miami Airport Blue Lagoon ya fara cika da mutane sosai, mutane nata zirga zirga da dangoginsu.
“Good morning, Captain.”
Wannan ma'aikaciyar ta jiya ta sake gaida shi, wannan karon kam kai tsaye ya amsa mata da “Morning.” yana ɗan jinjina kansa. Kai tsaye Motar da aka tanadar masa tana jiransa, don haka yana fita compound na hotel ɗin driver ya buɗe masa motar, yana me furta...
“Airport, sir.”
John ya shiga ba tare da magana ba, kana shima ya shige ya soma driving John suka bar harabar hotel ɗin a baya.
Titunan Miami suna cike da motsin safiyar ranar. cikin ƙanƙanin lokaci se ga gine-ginen airport suka fara bayyana a nesa kaɗan dasu, haka har suka iso dab jirage suna ta sauka da tashi abinsu, Motar ne ta tsaya driver ɗin ya ɗan saci kallonsa don ba ƙaramin cika ido bane da John ɗin, kafin ya iya furta....
“We’re here, Captain.”
yayi maganar yana buɗe ma John ƙofar motar ya fito, wata sassanyan iska ta bugi fuskar sa ya ɗaga kai a hankali ya kalla samaniya kafin ya dawo da kallonsa ga filin jirgin, Miami International Airport na wani ɗan lokaci…kafin ya soma tafiya yana jin kamar ƙafafunsa sun yi masa nauyi.
Direcly cikin Miami International Airport ya wuce, inda wurin ke cike da motsin crew lounge ɗin su, wasu na shan coffee. Wasu na duba schedules,
wasu kuma na dariya a hankali,yayin da wasu ke sabgoginsu, kai da ganinsu komai na tafiya musu yacce suke so, ahankali ya shigo cikin wurin, nan take
idanu da dama suka ɗan karkata zuwa gare shi. Ba wai don saboda sabon abu ba ne a gare shi, A ahhh sai don saboda yadda ya shigo ɗin,tafiyarsa a hankali amma cike da nauyi, Fuskarsa a tsaye babu walwala sosai kuma ba a ɗaure take can ba....
“Captain John!”
Ɗaya daga cikin cabin crew Mary ta taso da murmushinta tana me furta.
“Good morning, sir!” Ta zo kusa da shi cikin girmamawa shi kuwa John kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kansa itama yana amsa mata da. “Morning.” ɗin kawai cikin murya mai sanyi, ba tsauri amma ba kamar yadda ya saba ba. Ganin hakan suma sauran crew ɗin suka zo kusa suna miƙa tasu gaisuwar.
“Morning, Captain!”
“Glad you made it, sir.”
Kowa na ƙoƙarin nuna girmamawa da annuri ɗauke saman fuskokinsu, ɗaya daga cikin crew ɗin da ba nasu bane radawa na kusa dashi... “he looks different.” ƙasa ƙasa shima ɗayan ya furta... “Yeah… like he didn’t sleep.” daga haka yayi gum da bakinsa kamar an ɗinke da zare, shi kuwa John ajje jakarsa a gefe ɗaya yayi, tare da cire
safar hannunsa a hankali, Idonsa yana sake zagaya wajen sosai tamkar me nemar wani abu, First Officer (mataimakinsa) ya matso kusa tare da ambatar “Captain.” cikin muryan nutsuwa ya sake cewa. “Everything okay?” Idonsa kawai John ya ɗan lumshe kana ya ce “we fly today.”
ɗan kallonshi first Officer nashi yayi yana jinjina kai yace. “Yeah… we do.”
shi kansa ya fahimci cewan wannan Captain ɗin na yau ba na jiya bane,
Mary ce ta sake magana cike da ladab ta sake cewa, “Sir, briefing in 10 minutes.” kansa kawai ya jinjina mata yana cewa. “I’ll be there.” tare da ɗaukar box nashi ya fara tafiya zuwa briefing room. Crew ɗin da suke tsaye suka biyo shi da idanu kawai, duk cikinsu kuma babu wanda ya sake furta uffan har zuwa lokacin, sai zuwa can ahankali yace. “Something’s off.” yaci gaba da tafiya sauran crew naci gaba da mara masa baya kowannensu shirye cikin uniform ɗinsa a tsaf… lokacin da suke isa ƙofar briefing room ɗin,suka tsaya yakai hannunsa a natse kan handle, A hankali ya buɗe ƙofar cockpit na jirgin, kai tsaye switchet, screens… controls komai na a shirye, Kafin ahankali John ya zauna a kujerarsa yana daidaita belt ɗinsa…hannunsa ya taɓa controls na ɗan lokaci, First Officer ya zauna a gefensa yana ambatar.
“Pre-flight checklist, Captain?” A hankali John ke kallon gabansa, yana kallar yadda screens ke nuna masa komai normal daidai, A tausashe ya ce.
“Go ahead.”
Ya faɗa a hankali Checklist ta fara.
“Battery?”
“On.”
“Fuel?”
“Checked.”
“Instruments?”
Sai…John ya tsaya Idonsa na maƙale akan screen, cike da kwarewa yake gudanar da komai, gefensa, co-pilot yana shirye. “Let’s make this a smooth one… Lagos awaits.”
“Copy that, Captain. All systems checked. We’re good to go.”
“Tower, this is Flight JX-217, ready for departure Lagos.” “Flight JX-217, cleared for takeoff. Runway 27. Safe flight to Lagos.”John ya ɗan murmusa yana kama controls da ƙarfi amma cikin Jirgin ya tare da furta “Thrust set.”
Engines suka fara karar tashi suna cika iska. Ahankali jirgin ya fara landing na tashi a sannu a sannu John ya ɗaga hancin jirgin a hankali… ya tashi daga ƙasa zuwa sama, “Positive climb.” co-pilot ya fadi. “Gear up.” John ya amsa, Jirgin na hawa sama cikin nutsuwa, yana barin ƙasar United States a baya. A hankali John ya daidaita jirgin akan hanyarsa na zuwa Nigeria, John naci gaba da kallon gabansa, “Long journey ahead… but we’ll get them there safe.” Fasinjoji kuwa baki ɗayansu suna cikin kwanciyar hankali, wasu suna barci, wasu suna kallon sama ta taga wasu na ɗan zarya zuwa cin abincin ne toilet ne,sauran ma'aikata naci gaba da kula dasu har suka kawo Ƙasar NIGERIA...
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 6
Paid book
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
_Ya ALLAH, ka buɗe min ƙofofin hikima, ka bani basira da fasaha mai amfani. Ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_
ꨄ Bayan doguwar tafiya a cikin sararin samaniya, jirgin JX-217 yana ci gaba da sauka a hankali yana kusantar Lagos.
A cikin cockpit, Captain John yana zaune cikin cikakken nutsuwa, hannunsa a kan controls, Ahankali Co-pilot nashi yace. “Captain, we’re approaching Lagos airspace.” a tsanake John ya furta. “Alright… let’s bring her down nice and smooth.” ga sadarwa ta ƙasar Lagos ɗin na kururuwar furta...
“Lagos Tower, this is Flight JX-217, requesting permission to land.”
Lagos Tower....“Flight JX-217, you are cleared to land. Runway 18L. Wind calm. Welcome.”Ƙaramin murmushi John yayi wanda ya bayyana har a kan fuskarsa. “Copy that… cleared to land.” a hankali Jirgin ya soma sauƙa a hankali, yana ratsa gajimare masu laushi, hasken birnin Lagos