Author : AMMEY LAYLERH Category : Complete Novels
suka sake haɗewa wuri guda, John ya sake kallonta ba tare da yayi ƙoƙarin ɓoye abin da ke zuciyarsa ba yace.
“Tell me…” ya ce da idonsa a kanta.
“Is it true?” Yasmine ta kasa magana saboda ta riga da ta san gaskiya ɗaya ce. Idan ta ce eh zuciyarta za ta iya fashewa, haka kuma idan tace a’a ɗin ma hakan take duk. Ga kuma iyayenta dake ƙasa suna kallon juna cikin tashin hankali…suna fahimtar cewa wannan ba kawai magana ta aure ba ce, yaƙi
ne amma na soyayya, addini, iko… da kuma makoma. Ita kuwa Yasmine ta makale ne a stairs din saboda gajeren wandon dake jikinsa babu riga se iyaka vest army green me ruwan wandon. Wanda shi shaf yama mance da cewan sune a jikinsa ɗin kuma har yanzun bema farganba, Kafin Kowa ya sake yunkurin cewa komai sega shigowar
Deepika kamar wacce aka jefo. Kai tsaye ta isa ga John din tana riko hannunsa ta fara dan jijjiga jikinsa tana faɗin. “John!, Joseph… tell me this is a lie.” ta furta cikin rawar murya. Amma idan kujerun dake parlourn sun motsa shima ya motsa, sema Idonsa dake kan Yasmine, wacce haka kawai taji wani abu ya tsaya mata game da yadda Deepika ta shige jikinsa, duk da yanda take ƙoƙarin ganin ta riƙe hawayenta amma seda suka ciko idon ta, wacce tayi saurin kawar da kanta, daidai da lokacin da JOHN ke janye deepika daga jikinsa yana kallonta da ɓacin rai yace.
“It’s not a lie.”
Wanda ya saka Deepika ta yi wata yar dariya mai ɗaci. “So it’s true…” ta ce tana girgiza kai.“After everything, after our families… after the agreement…”
Ta sake matsowa kusa da shi sosai.
“You chose her?”
Wani irin juyi John yayi tare da kamo kafadunta ya jijjiga tare yace.
“I didn’t choose you either.”
Kalmar da Deepika taji ciwon ta fiye da duk abin da ya faɗa a daren jiya. Taja baya kamar wacce aka mara.
“What…?”
Ambassador Kabeer ya ɗaga hannu.
“This is getting out of control.”
Madame Victoria tare da her family nasu da suka jima tsaye duk sun yi shiru suna kallon komai kamar mai film, Wannan ba rikici ba ne a gare ta tsari ne da zai iya rushewar da take da cikakken tabbacin babu gyara.
A hankali Yasmine ta ɗago kai ta kalle shi tare da furta.
“John… please stop.” ta ce cikin hikima
“I don’t want anyone hurt because of me.” John ya fara taka wa zuwa inda take. “You think you are the problem?” ya tambaya ta girgiza masa kai.
“I am.”
Shima ya girgiza mata kan nan yace.
“No.”
Sai ya ɗaga hannunsa a hankali kamar yana nuna mata gaskiya. “You are the only honest thing in all this mess.”
Da sauri Mecheal ya matsa baya kaɗan, yana jin kamar yana kallon wani abu ne da ya fi karfin sa. Deepika ta share hawayenta tana kallonsa.
“This is humiliation.” ta ce cikin fushi.
“I will not be part of this circus.”
daga haka ta juya zata tafi amma Madame Victoria ta katse ta ta hanyar furta
“Stop.”
Kowa dake parlourn ya juya se a sannan suke sanin da tsaiwar su a wurin...kafin a natse Madame Victoria ta ƙara so cikin parlourn tana me furta.
“No one is leaving until this is settled.”
Ambassador Kabeer ya kalle ta.
“Settled? Our children are breaking apart in front of us.” wani duba ta masa tare da girgiza kanta tace.
“This is not about emotions.”Ta nuna John. “It is about structure. Power. Future.” sai ta kalli Yasmine tace.
“And unfortunately… she does not fit that future.”
Yasmine ta ji kalmar kamar wuka aka caka mata a kirji. John ya matso kusa da ita a natse kafin ya furta.
“Don’t talk about her like that.”
Ya faɗa da ƙarfin da wannan shi ne karo na farko da muryarsa ta nuna fushi sosai a wurin. Madame Victoria ta kalle shi cike da zafi tace. “Then what do you suggest?”John ya yi shiru na ɗan lokaci kafin kamar wacce aka fusgi maganar daga bakin sa yace.
“I cancel everything.”
Kowa yaja ya tsaya cak, Deepika ta ɗago kanta cike da tsoro. Ambassador ya ce cikin mamaki. “You can’t just cancel arranged marriage like it’s a meeting.”
John ya juya masa kai alamar tabbaci kafin yace. “I just did.” saurin katse shi Yasmine tayi tana girgiza kanta tace.
“No… John… don’t.”
Amma John ya riga ya yanke hukuncin da babu wanda ya isa tilasta shi.
“Enough.” ya ce. “Enough control. Enough arrangements. Enough forcing lives.” Sai ya matso kusa da Yasmine ya wani kalle ta yace.
“I choose my life now.”
Ya furta kalmar ne amma muryarsa na ɗauke da wani irin ciwo da ya kasa ɓoyewa.
Wani shiru mai nauyi ya sake kame ilahirin wurin.
Deepika ta fashe da kuka ta fita a guje daga falon. Ambassador Kabeer ya koma ya zauna a kujera cikin gajiyawa.
Madame Victoria kuwa wani murmushi tayi me ɗaci tare da furta. “You think this is freedom?” ta tambaya John din daya kalle ta yana me bata amsa da
“Yes.”
Idonta har ya fara ganin biyu biyu ta isa gabansa ta jijjigasa da kyau tace.
“Then you will learn the price of it.”
TA ɗan juya. “Because I will not allow this disgrace to continue.” Yasmine ta ɗaga kai cikin halin ko in kula tace...
“What are you going to do?” ta tambaya.
Madame Victoria ta kalleta kai tsaye tace. “Protect my son.” Wanda kalmar ta ma Yasmine nauyi sosai kamar wacce tafi kama da barazana ce.
A waje kuwa tuni ƙofofin sada zumunta sun riga sun cika da labari, kowa na ta fira da hotuna da kalaman da ke yawo kamar wutar daji. Wanda bama a san wanda ya fitar da maganar ba, kuma maganar nasu ɗaya ce kawai ke yawo shi ne. “Engagement officially broken!Ambassador’s daughter na cikin wani babban scandal da ya girgiza zukata!.
Uwar John ta yi barazanar daukar mataki mai tsauri!” Gaba ɗaya tun daga kan shafukan Instagram zuwa X (Twitter), mutane na ta jefa ra’ayoyi, wasu na tausayi, wasu na zargi, wasu kuma na ƙara tayar da kura. Kofar gidan kuwa ta cika da motoci, ‘yan jarida, da masu son ganin abin da zai biyo baya. Daga can cikin gidan kuwa wani irin tashin hankali ne ya mamaye parlourn bayan fitan Deepika. Kowa na wurin ji yake kamar iska ma ta sauya masa yanayin shakar da yake da. Kowa a cikinsu maganganun da JOHN ya furta ɗazu sun tsaya a zuciyar kowa kamar ƙarar fashewar wani abu mai girma.
Madame Victoria dake tsaye cak tun ɗazu awurin, idanunta akan ƙofar da Deepika ta fita, duk da nutsuwar da take ƙoƙarin nunawa amma ta gagara saboda zuciyarta a dagule take fiye da yadda kowa zai iya zato. Hannunta ta matse sosai har farcen yatsunta suka kusa soke tafin hannunta. Ambassador Kabeer dake zaune murza goshinsa kawai yake yi cikin gajiyawa. Domin ko a shekarunsa a siyasa bai taɓa tunanin wata magana ta soyayya za ta kai wannan matakin ba. Mamy ma gaba ɗaya ta rasa abin cewa, idanun ta ne kawai akan Yasmine wacce ke tsaye kamar mutum-mutumi, zuciyarta na wani irin bugawa da ƙarfi kamar zata faso ƙirjinta ta fito. Sai JOHN ya ɗan ja numfashi a hankali. Ya kalli kowa ɗaya bayan ɗaya ba tare da ya sake cewa komai ba. Fuskar nan tasa babu alamun wasa ko sassauci ko kaɗan. Kafin daga bisani ya juya ya fara tafiya zuwa ƙofar fita. “John…” Madame Victoria ta kira sunansa cikin murya mai nauyi.
Amma ko juyowa bai yi ba sema ta kun san da yaci gaba da yi ba. Yasmine ta ɗan matsa gaba kamar zata bi bayansa amma ƙafafunta suka kasa motsi. Tana jin kamar wani abu a zuciyarta ya hana ta kiransa, ko kafin kowannensu a cikinsu ƙarar hayaniyar mutane daga waje ta fara shiga cikin gidan.
Tun kafin security su samu damar tarwatsa su, reporters suka cika harabar gidan gaba ɗaya da cameras da microphones. JOHN na fitowa flashes suka fara haskawa tamkar walkiyar aradu. “Mr. John! Is the engagement truly cancelled?!. Are you in love with Ambassador’s daughter?!. Did you reject Deepika officially?!, Is there crisis in your family?!” Wani ɗan tsayawa yayi a saman stairs ɗin entrance ɗin gidan. Idanunsa cike da wani irin baƙin yanayi mai firgitarwa. Gaba ɗaya wajen yayi tsit na ɗan lokaci saboda yadda kallonsa kaɗai ya isa ya saka tsoro a zukatan mutane. Sai ɗaya daga cikin reporters ɗin ya sake ɗan matsowa kusa da microphone ɗinsa. “Sir, people are saying you disgraced your family tonight” Cikin wani irin sauri JOHN ya fizgi microphone ɗin daga hannunsa ya jefar gefe da ƙarfi har ya buga ƙasa ya tarwatse. Kafin ya matsa kusa da mutumin sosai cikin sanyin murya mai ɗauke da fushi yace. “Next person that blocks my path…” Yay maganar na daƙiƙa biyu kafin ya tsaya yana kallon kowannensu ɗaya bayan ɗaya.
“…will regret it.”
Babu wanda ya sake motsi a cikinsu se numfashin mutanen dake fita kamar suna tsoron yi. Daga haka JOHN ya wuce kai tsaye zuwa motarsa ya shiga. Da ƙarfi ya fisgi motar daga harabar gidan ya bar wajen cikin wani irin tashin hankali da hayaniyar cameras.
Wani lumshe ido Yasmine tayi a hankali bayan jin ƙarar tafiyar motarsa. Wani irin faɗuwar gaba taji wanda ita kanta ta kasa gane dalilin sa. Madame Victoria ta juya cikin fushi tana kallon sauran family ɗin ta. “This is exactly what I warned all of you about.” Ta furta maganar cikin matsanancin ɓacin rai kafin ta ɗauki jakarta ta fita ita ma ba tare da ta sake kallon kowa ba. Gaba ɗaya sauran sauran wuni da daren ranar babu wanda ya yi su cikin kwanciyar hankali. Washegari tun da sassafe gidan nasu JOHN ya shiga cikin wani sabon tashin hankalin. Servants na zirga-zirga cikin tsoro yayin da Madame Victoria ke saukowa parlour da sauri cikin doguwar rigarta ta alfarma.
“Where is John?”
Ta sake tambayarsu cikin tsananin fushi, domin gaba ɗaya an rasa shi har gidansa da yake yawan zuwa idan ransa na a bace amma baya can. Shugaban securities na gidan ne ya haɗiye wani yawu da kyar kafin yace.
“Ma’am… he didn’t come home last night.”
Sake tsuke Madame Victoria tayi tana me ambatar.
“What?”
Cikin rawar murya ɗaya daga cikin guards yace.
“His cars are gone too.”
Wani irin shiru ne ya ratsa parlourn.
A karo na farko wani mummunan tsoron ya sake shiga zuciyar Madame Victoria na gaske. Da sauri ta juya tana ɗaukar wayarta ta saka ƙiran number na John amma switched off, Haka ta ringa jera masa kira amma har zuwa lokacin amsar daya suke bata wato switched off. Ta ɗaga wayar kenan za tayi jifa da ita sai wayar ta ɗan yi vibration. _Unknown number_ ta gani alamar boyayyar numba ce da ba'a son a santa, kamar ba zata daga din ma amma se wata zuciyar ta bata kwarin gwiwwar dagawar.
“Mr. John left Nigeria early this morning.”
Numfashinta ne ya tsaya cak tana kokarin silalewa kasa aka sake furta.
“Destination to Ethiopia.”
Wani irin ɗif taji ƙofofin kunnuwanta sun mata, kafin wayar ta sulale daga hannunta tana fadowa ƙasa ta tarwatse amma jelly da isowarta kenan tayi saurin cafe ta.
*Ethiopia*.
Ƙaton private jet ne ya sauka a cikin nutsuwar sanyin safiyar ta Addis Ababa. Bayan mintuna kaɗan saiga fitowar JOHN daga cikin jet ɗin sanye cikin baƙar jacket da glasses, fuskarsa ɗauke da wani irin yanayi mai wahalar karantawa. Iskar Ethiopia mai sanyi ta bugi fuskarsa a hankali yayin da ya tsaya cak na ɗan lokaci yana kallon sararin garin. Kafin ya furzar da wata iska me zafi ya yi oder Cap. A can wani luxury penthouse dake tsakiyar birnin JOHN ya kama, kai tsaye bayan sun isa ya bashi credit irin na kasar kana ya wuce daga shi kayan jikinsa, don babu abinda ya dauka nashi a gidan. Bacci me rai da lafiya ya yi har bayan sallan zuhr kana ya fito sanye da kayan shan iska, Ya nufi bakin glass window yana kallon yadda garin ke kayace ta ko ta ina, hannayensa zube cikin aljihun wandonsa, amma zuciyarsa cike take da wani irin tunaninta.
*Yasmine*
A hankali ta sauke wayarta daga hannunta bayan ta gama kallon hotonta tare da na JOHN sun mamaye social media gaba ɗaya. Wani irin nauyin abu ne ya tsaya mata a ƙirji, musamman ganin yadda mutane ke ta magana akanta kamar ita ce silar rugujewar komai. Gashi dama abinda ya fara farkan da ita tun safe take receiving calls daga manyan mutane, investors, relatives…Friends kowa na neman jin gaskiyar abinda ke faruwa, wani dafe kanta tayi tare da furta.
“This is becoming a disaster…”
Ta furta cikin fushi tana jefa ipad ɗinta saman table Husna tayi saurin taro ta.
*BY AMMEY LAYLERH ✍️ *
08104493215
*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_
~Maryam Naseer Mirrah~
*AMMEY LAYLERH ✍️*
Page 23
Paid book
𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.
♡
Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*
♡♡♡♡
*Ethiopia*
ꨄ Bayan John ya gama warwarewa abu na farko daya fara shi ne neman ƙawarsa Almaz, ita ke zuwa ta debe masa kewa suyi yawonsu tare tana sake nuna masa wuraren daban daban , shi kuma yana faɗa mata abubuwan da ke damun sa. Amma duk da dariyar da yake yi… zuciyarsa tana tare da Yasmine har zuwa lokacin. Wata rana da yamma suna zaune a cikin beach na hotel ɗin bayan sun dawo daga wuraren da suna ziyarta Almaz ta dube shi ƙadan, tana kallon yanda ya sake haske yayi fawai akan ranar daya zo. Cike da hikima tace “Kana son komawa wurinta, ko?”
John bai ɓoye mata komai ba a wannan karon kai tsaye ya ce mata.
“Eh.” se kuma ya ɗan furzar da iska daga bakinsa tare da shafo keyarsa yace. “Ta ce ba za ta aure ni ba sai na musulunta.” Almaz ta kalle shi, amma ba tare da mamaki ba tace.
“Shi ya sa kake a rikice?”
John ya gyada mata kyai kawai yace.
“Ba kawai hakan bane amma ina jin kamar zan rasa kaina ne idan na yi wani abu da ba daga zuciyata yake ba.”
Almaz ta ɗan yi murmushi me kyau cike da wannan hikimar nata tace.
“To kada ka yi komai saboda wani.”
Ta ɗan tsaya kaɗan sannan ta ƙara da cewa.
“Idan zaka canza… ka canza saboda ka yarda. Ba saboda soyayya ba, se dan saboda kai da kuma ALLAH.”
Kalmomin da suka shiga zuciyar John kenan, ya ɗan ware hannayensa yana kuma jan idonsa kamar zai lumshe amma bai lumshe ɗin ba. Sema kamar a karon farkon da bai ji kamar yana gudu daga wannan gaskiyar ba. Komai be sake ce mata daga haka ba ya mike, itama ta mike suka jera suka fara tafiya ya kama hanyar bedroom nashi ita kuma ta kama barin fita daga hotel ɗin, don wanna karon ya canza Hotel ne. Yana shigewa ɗakina ya kwanta akan doguwar sofa tare da zaro tsadaddar wayarsa ya shiga chat, number Yasmine ya shiga tare da ɗan tsayawa na wani lokaci kamar me na zartar wani abu.
Kafin yayi kundunbalar rubuta mata,
_I miss you… but I need to find myself first._ Ya danna send yana sake lafewa luf cikin sofa ɗin hadi da lumshe ido.
Yana a kwancen har zuwa lokacin da daren ya dan fara nisa, amma hasken fitilun hotel dake haskawa ba zai sa ka gane cewar ma daren bane, idanunsa lumshe yana amsar bugun da zuciyarsa ke masa cike da nauyi. Kamar kuma daga sama yaji wayarsa ta yi ƙara.
Zuciyarsa ta bugo da ƙarfin daya saka shi saurin buɗe ido, hannunsa na ɗan rawa ya buɗe saƙon.
_I miss you too… but you know what I said._
Ɗan lumshe ido John yayi a hankali yana jin yadda kalmomin ke shigar sa suna ratsa zuciyarsa kai tsaye. Saboda wannan shi ne karo na farkon data taɓa furta masa kalma matankwacin wannan, wayar ya sake kalla yana sake bin saƙon ya karanta. Sai ya ajjiye wayar a hankali, ya tashi ya nufi taga. Iskar dake kadawa daga wajen ta bugi fuskarsa har tana motsa bishiyoyi cikin hasken fitilun da suke nan kamar rana.
“Ohh Jes…” se kuma yaji harshensa ya sarke numfashinsa na rikewa, saboda kalmar Jesus ɗin kawai da yayi niyar ambata baya. Wani shiru ne ya biyo bayan hakan, yana komawa ya jingina da bangon windows ɗin zuciyarsa na bugawa sosai. Shin soyayya ce kawai ke jan shi? Ko kuwa akwai wani abu mafi girman da yake kiransa?... Hannuwansa duka biyun ya saka yana rufe fuskarsa ya koma da baya da baya yana komawa inda ya baro. A fisge yana me furta kalmar.
“YA ALLAH!!!?... "
Kalmar data taho masa da wani irin kwanciyar hankalin da yaji tun da yake be taɓa samun kalar saba. “YA ALLAH?!!” Ya sake ambata nan take wani nannauyar baccin da yaji a da kamar ba zai iya ba ya ɗauke sa, ko washegari da yake tashi se yaji komai kamar a mafarki ne suka faru. Kuma ba komai ne ma ya tashe saba illa ƙiran sallar subhi da masallacin Hotel ɗin ya ƙira. Ahankali yaji wani nauyi na taho masa, nauyin da yake jin ya hausa kuma kamar yana da danganta da kiran sallar da aka ƙira, duk yadda yaso daya koma ya kwanta abin faskara yayi, ƙiran sallar ne kawai ke masa amsa kuwwa cikin kunnuwansa. A hankali ya ziro fararen kafafunsa yana mikewa ya shige bayi yayo wanko ya fito, koda fito din ma kasa zama yay, haka kawai zuciyarsa ke jan sa zuwa ga kiran Sallah ɗin, don haka ya fito harabar Hotel ɗin har wurin masallacin ya zaune daga gefe. A kan idonsa mutane suka fara shiga masallacin aka tayar da Sallah aka idar duk yana zaune. Wafi yawan duk wanda zai wuce se ya kalla John kan yayi gaba, daga nan ya wuce