Advertisements
Chapter 14 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   14 / 31

39K to 42K   out of 91.1K words

Lokacin da suka koma gida goma saura don haka anan parlourn ya zube yana sauƙe wata ijiyan zuciya me ƙarfi. Babu jimawa ya miƙe ya shige bedroom nashi, da sauri Mecheal ya rufa masa baya ya bishi ya jere masa dangin su cake ɗin da suka shigo dasu. Kana ya ware masa wasu a dinning da coffee ɗin da ya saka aka haɗa masa tun kan su iso anan parlourn. Sanye ya fito da wata irin singlet ɗin da se a Indian film ake ganinta fara tas. Ahankali yakai zaune saman wata kujera mai tsananin laushi kaman gado. Gefensa laptop nashi ce saman cinyarsa ya buɗe zai yi wani aiki ne a cikinta, yanda ya maida hankali kan laptop ɗin kaɗai ya isa sanar maka da cewar kowanne aiki yake yi to kuwa me muhimmanci ne. Gefen sa ga wani ƙaramin glass table ɗin da aka ɗora masa coffee nashi cikin mug mai kyau sai zuba uban tururi yake, se wayoyinsa da suke zube gefe guda. Yana aikin nasa sama sama yana kai hannunsa ya tura cikin coily hair nashi, wacce gaba ɗaya ya gama wargaje ta saboda da yawan kai hannun da yake ya hargitseta. Jin kansa na shirin fara ɗaukar chaji ne ya saka shi kai hannunsa ya dauka mug ɗin ya fara sipping a hankali. Tsaye ya miƙe daidai da kammaluwar aikin nasa ya nufa sama. Se dai ko taku ɗaya be yi ba ƙiran waya ya shigo masa wanda ya sashi wani daƙune farar kyakkyawar fuskarsa me kyau, wacce dole ta saka shi komawa zaunen da yake yananyin fuskarsa dake ɗauke da ƴar guntuwar damuwar na sake riƙedewa lokaci guda zuwa wani irin deadly expression ɗin ka ganshi a lokacin babu abinda zai hana ka tsorata. Tsaye kawai ya miƙe hannunsa yana barin ma laptop ɗin anan hannunsa cikin aljihunsa ya nufi carridor wayar manne a kunnensa. Kafin se a lokacin yake bama wanda suke wayar da furta. “And what?....” yayi maganar da wata irin deadly voice nashi. Daga ta can ɓangaren me ƙirar kuwa aka ci gaba da kwantar masa da hankali akan amren Deepika ɗin da indai bai so babu me ɗaura masa. Se a lokacin yake sakin wata bahaguwar ajiyan zuciyar daya saka me wayar ɗan lumshe idon jin ya dawo cikin haytacinsa. Kana aka sake ce dashi. Shiru kawai John yayi yana ci gaba da sakin ijiyan zuciya. Cike da son sake bashi tabbacin babu me masa auren dolen mahaifin daya kasance na Deepikan ne wato Goush David ke kwantar ma da John ɗin hankali.
“OK. finally My boy ina son ka cire damuwan komai a ranka, kaje yanzu ka kwanta ka hutu dan nasan ka sam baka iya ɗaukan abu da zafi ba, I will call you tomorrow Alright?, I love you PAPA'S BOY” Kai kawai John ɗin ya gyaɗa masa kamar yana a gabansa ne ko yana kallonsa yace.

“Alright Dad ,I love you more " daga haka ya yanke wayar yana jin kamar an yaye masa wata gimgimemiyar dutse ne a tsakiyan ƙirjinsa....



Ɗan jujjuya kanta take yi cikin baccin nata, gaba ɗaya gumi ta gama jiƙe gaban goshinta tsaf. Cikin baccin take sake ɗan jujjuya kanta kafin tayi saurin ware masa manyan idonta masu ƙarfi a kansa, tare da buge hannunsa dake kan fuskanta yana shafawa a hankali kafin a ɗan fusace tace.

“What are you doing?”

Tace ranta a wani irin mugun ɓace ta fesar da numfashi tana kallonsa, Wani lumshe mata lumsassun idanunsa yayi da wani irin emotion kan fuskar sa yace mata. “I'm sorry Babe na kawo miki abincin ne naga kin yi aiki kin gaji ne. Gashi kuma bakici komai ba tun ɗazun se famar kaiwa da komowa kike kar yunwa ya cin yi min cikin Baby...” A fusace ta miƙe tsaye tana kallonsa kallo irin na fusatara nan tace.

“To ina ruwan ka da ciki na?, cikin ka ko nawa?.... ehhhh nace cikinka kane ko nawa?....”

Komai daga nan bai sake ce mata ba saima miƙewa tsayen da yayi hannuwansa zube cikin aljihun bakin wandonsa. Bata lokacin da idonta ya fada kan faffaɗan ƙirjinsa da bai ƙarasa ɓalle botiran rigar jikinsa ba sai wani munafikin ƙwara ɗaya daya saƙala daga tsakiya. Wanda hakan shi ya bama gaba ɗaya surar jikinsa bayyanuwa gaba ɗaya... Ga wani irin ƙamshi me daɗin daya bar mata shi just like heaven. Don haka bata san lokacin data shagala a kallon nasa ba, musamman ma daya juya baya bayan nan, se dai kuma ko yaya aka yi se tsintar idonsa karaf tayi a cikin nasa ya kamata tana kallonsa, amma mutuniyar se tayi saurin composing ɗin kanta ta hanyar tamke fuskarta. Wani lalataccen Murmushin daya kusa kwarar da ita yayi kawai ya juya ya fice bayan ya mata wata shegiyan alaman da bata san ko me take nufi ba, ita kuma ta bishi da kallo tana jin haushin kanta da kanta, but don't blame me. Ita tasan dan bakuga abinda ta gani bane, he's perfection out of perfection. A wani kalan haukace ta farka daga nannauyar barcin daya ɗauke ta babu jimawa tana furta noooooo.....“Wllh ƙarya ne sharri ne!, sharri kawai yake son min ko kullu min wani sharrin, wllh bana son ka me zan yi da kafiri arne wanda baya Sallah....” gaba ɗaya ta gama haɗa zuba wanda ya saka Mamynta da Daddy'nta dake tsaye a kanta mata sannu, wanda ita sema a lokacin take dawowa kamar hayyacinta ne. Don haka ta sake matse fuska ta shiga muzuran gaske tana daga hanci sama. “Ambasaja lafiya kuwa?, me ke damunki?, wa ye kafirin?, waye arnen?, wani ne yake bibiyar min rayuwarki ne da bana da labari?...” gaba ɗaya a rikice Daddy'nta ke jefa mata tambayoyin yana zama gefenta yana mata sannu da share mata zufa. “ALLAH yasa ba aljannu kike je garin kwashe kwashenki kika kwaso mana ba Yasmine. Ubangiji ya ALLAH ya ƙarasa shirya ki.....” Mahaifiyarta ta faɗa wanda ya saka Daddy'n saurin kallanta yana cewa. “Ke wai Khadijah me yasa har abada bakinki baya faɗar alkhairi ne akan ambasajo?, wllh da ba'a gabana kika haife Yasmine ba da nace sanja ta akai ba kece asalin mahaifiyarta ba....” wani jimmm tayi kawai tayi kana ta saka kanta tana ficewa barin parlourn zuwa bedroom nata, don dama a parlourn take har baccin bayan la'asar ɗin ya kwashe ta. Wayoyinta kawai ta kwasa tana yin sama tana jin wata fusata da son ganinsa ta buga masa mugun gargaɗi me ƙarfi a kanta, tun da har abin nasa ya fara wuce bibiyarta iyaka a zahiri har cikin barcin nata ma ba zai ƙyale taba...

7:10pm ta fita da motar ta ta ringa zaga garin nemar inda zata gansa. Amma ALLAH be sa sun gamu ba haka ta koma gida. Washe gari da wuri ta fita zuwa Islamiyyar da take zuwa. Wacce se ta kwashe sama da One Months ba'a leka taba, ko ta leka ɗin kuma babu malamin da take kalla da rahama bare zaman aji, idan kuwa kaga taje to wata tijarar ta shirya ma wani daga cikin malaman makarantar, wanda su kansu duk lokacin da suka ganta a cikin tashin hankali suke tsintar kansu. Domin kuwa sun san ba alkhairi bane ya kawo ta se wata tsiyar ko lokacin sanja wani malamin ce tayi. Suna daidaita shiga islamiyya ɗin ta gan shi tsaye jingine da jikin mota, wannan bita zai zai ɗin nasa na gaban motar da alamar gyara musu yake tsayawa ne tayi. Wani uban birki taja tana takawa har zuwa inda suke dama akwai ruwan roba me sanyin dake hannunta tana zuwa kawai ba tare da tunanin komai ba ta juye masa a fuska. Babu zato ko tsammani se jin sauƙar ruwan sanyi jikinsa yayi, wanda ya saka shi wani irin zabura sedai haɗuwar idonsu a kan junane ya saka shi wani irin ƙamewar ban mamaki, domin kuwa exactly jinginen nan da yake irin mafarkin sak yake yi. Mamakin be sake kashe shi ba har se da yaji ta fara magana cikin zallar fusata.

“Me na ma ka????...., Malam na ce me na ma ka? haka da zafi da har kake bibiyan rayuwana irin haka?. Bayan hakan ma duk ba zaka ƙyale ni se ka bini har cikin bacci na kana min hauka Where are doin?, wa ne ne kai?... Idan ma wani abu ne a cikin ranka game da yasmine to ina son kayi gaggawar cire komai ye, domin kuwa akwai wani irin banbanci me girman tazarar da ba zaka iya kamo ni ba...Kai bama kawai bambanci bane…wani layi ne da ba kowa ke iya tsallakawa ba.” Cak John ya tsaya yana kallon bakin dake rufe shi da bala'i da masifan da cikin kwanakin da basu wuce 5to6 days ba yaje ya koyi Hausa a sabo da ita kawai. Sedai komai a maganar nata be fahimta ba sakamakon guma guman Hausa ne wannan take yi masa. “What if I can?” ya tambaya a hankali wanda ya saka yasmine jan wani numfashi ta fesar ta ce. “Saboda ni ba abokiyar wasar ka bace...” Sai kuma ta wani ɗan karkatan da kanta gefe taci gaba da faɗin.
“I’m not playing. Again Mr No Name
Ni ina rayuwa ne da abin da na yi imani da shi.” Sai ta ɗora hannunta saman ƙirjinta tace. “Kuma shi wannan abun daya faru bisa kuskure ina son ka manta dashi a cikin memory naka in ma shi ke sake taɓa kan ka shaidan kuma ya buga maka ganga, to ka sani niba irin sauran Christian watsatstsun ƴan matayenku bane, ina da addini!, ina da daraja daga yau karka kuma kuskuren leƙa cikin rayuwata ba.” Cak John ya tsaya a karo na farko ya kasa magana.

“ Bayan wannan abin kuma idan har a cikin zuciyarka da abinda kake shirin aikata min...” Se kuma ta dakata cak kana ta nuna shi da yatsarta manuniya ta ce...

“…Toh kuwa ka shirya rasa abubuwa da yawa daga cikin rayuwarka.” wanda ya saka John wani jan idonsa su tafi luuuu kamar zasu lumshe amma be lumshe ba. Wani kalan bugawa tsakiyar ƙirjinta yayi da ya saka ta ja baya kaɗan ta sake nuna shi da hannunta ta ce. “Na...tsa....ni....duk me takura rayuwa na ka san wannan....” wani buɗe idonsa a kanta yayi "And I love marh?....” wani rumtse idonta tayi ta toshe kunnuwanta tace. “Kada ma kace zaka fara....ka da ma ka ce kana sona mr No Name…”
Wanda ya saka John fesar da wani abu me nauyi daga cikin ƙirjinsa tun kafin yayi shirin furta wata kalmar ta riga shi ta hanyar furta.. “Because loving me…is not easy.” fuuuuuuu daga haka ta juya ta barshi a daskare....

*JOHN*

Tin da abun nan ya faru gaba ɗaya jikinsa ya rikice wanda da kyar Mecheal ya lallaɓashi suka koma gidan daya koma, ko da dare kasa bacci yayi duk inda ya juya ita kawai yake kalla tana masa masifa da bala'inta. Don haka ya tashi zaune daram ya zabga uban tagumi shi kaɗai a cikin zuciyarsa yake tambayar kansa. _Menene matsalan?, da ga kuma ita take?, shin to kodai shi ne matsalan?.... Wani numfashi zazzafa ya fesar kai tsaye tare da ɗaukan wayarsa ya doka ƙiran Mecheal. Yana jin anyi answering call ɗin kai tsaye yace. “Mecheal.” daga ta can ɓangaren Mecheal ɗin kamar wanda yake gabansa ya wani sara masa da faɗin..
“Yes, Boss.”

“Find me a place…” ya faɗa yana ɗan dakatawa kana ya sake ce. “…where I can learn.” wani jimmm Mecheal yayi tare da tafiya duniyar tunani har seda gyaran muryan John ya tayar dashi kana ya ce. “Learn what, sir?” Mecheal
ɗin ya tambaya, wanda ya saka John rufe idanuwansa na ɗan lokaci kawai ya ce... “Her world.” ƙit daga haka ya datse ƙirar yana jifa da wayar da take ta fashe tayi rugu rugu....

*BY AMMEY LAYLERH ✍️*


08104493215





*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 14

Paid book

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.


Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215


*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

_Ya ALLAH! ka sa abin da zan rubuta ya zama mai anfani ga mutane, kuma ya zama sadaka a gare ni ranar gobe kiyama, ka kuma tsarkake ni daga kuskure, ka sa kalamaina su shiga zukata cikin sauƙi Ameen ya nabiyyun rahamati_

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/I0is8GOll5V7h8rhwnyat4?mode=gi_t

Kin dade kina neman inda zaki samu kaya masu kyau da inganci?
To nesa tazo kusa ki matso kiga abubuwan da muke siyarwa cikin sauki da rahusa Muna aika kayanmu ko ina afadin kasar nan da kewayenta Muna siyar da Laces masu kyau da inganci Atamfofi masu quality Bags and shoes masu kyau Luxury Abayas Embroidery atamfa da materials Duka fa akan farashi mai kama dana kyauta

♡♡♡♡

ꨄWayar da yay jifa da ita ta watse ba ƙaramin razana Mecheal tayi ba, duk da cewa bai ji ƙarar ba amma ya san halin Boss ɗinsa. A hankali ya sauke numfashi yana kallon wayar hannunsa kamar yana kallon matsalar da zai warware.
“Her world…” ya maimaita a hankali.
A wannan daren kuwa, John bai sake kwanciya ba. Ya zauna a gefen gadonsa, idanunsa buɗe, amma zuciyarsa a wani wuri daban. Kalaman Yasmine na ta yawo a kansa kamar ana sake kunnawa.
"Because loving me… is not easy." Wani lumshe idonsa yayi a bayyane yana me furta. “Then I’ll make it easy…” kawai ya furta a hankali.ꨄ Ko washegari da safe da yasmine ta tashi ta John ta tashi cikin ranta,wani irin abu me kama da farat ɗaya take ji a kansa sosai. Wani irin motsi take jin kamar ana motsa wani abu daga cikin zuciyarta.uwa uba kuma kwana mafarkin John da tayi, se dai mafarkin nata me cike da sarƙaƙiya da rikita ƙwanya. Gaba ɗaya basirarta ta toshe ta rasa ma ta yacce zata ma mafarkin nata dalla dalla ta wargaje bare kuma in ta wargaje ɗin ma ta sama damar sake haɗe shi cif wuri guda. Mafarkin ba ƙaramin girgiza tunaninta yayi ba, gaba ɗaya ji tayi kanta ya cunkushe ya cushe mata da wasu hargitsatstsun ababuwan da bata san
ko su miye su ba ɗin ba. Wani lumshe idonta tayi daga kwancen da take gaba ɗaya rabin jikinta na saman gadon yayinda ƙafafunta suke a zube a ƙasa tana jijjigasu cike da zafi da rashin sanin mafita. Wani saurin zabura tayi sakamakon fuskar John data wulga mata tana buɗe idonta duka. “Na shiga uku” ta furta tana ɗora hannu a ƙirjinta.
“Me ke shirin faruwa dani ne haka?” ta sake tambayar kanta cike da tashin hankalin abinda ke shirin kamata akan wannan arnen. Mutumin da a koda yaushe take cike da jin haushinsa, amma yau ace zuciyarta zata mata haka?, Shin me yasa zuciyarta zata ci amanarta irin haka ta ƙaunaci mutumin da bai dace ba.? Husna data kwashe sama da 15 minutes a kanta tana mata magana ne ta ɗan girgiza ta da kyau tana tambayar... “Yaya Yasmine lafiya kuwa? Tun ɗazun inata ta miki magana Daddy ya na son ganinki amma kamar kin tafi wata duniyar tunani ce ta daban…” wannan maganar ta Husna
da girgiza tan da tayi shi ya dawo da ita hayyacinta.

“Ba komai…”

Ta furta da ƙyar tana ƙoƙarin boye halin da take ciki don bata san Husna ɗin ta fuskanta komai ɗin. Ɗan matsowa kusa da ita Husna tayi idonta cike da damuwa tace.
“Aunty Yasmine, wannan ba kamar ba komai bane. Nifa wani lokacin kina bani tsoro wllh…” kanta ta juyar gefe
tana gujema kallon Husna ɗin tace.
“Na ce miki ba komai Husna enough mana kije zan zo yanzun” ta faɗa da ƙarfin da sai dai Husna ta ɗan tsaya tana kallonta kamar zata sake wata maganar amma daga ƙarshe ta juya ta fita kawai... Tana fita Yasmine ta saki wani numfashi mai nauyi, hannunta har yanzu manne a ƙirjinta. _Duk abinda ke faruwa dani… ba na fahimtarsa._ ita kaɗai ta faɗi cikin zuciyarta tana miƙewa tsaye a hankali, amma ƙafafunta na ɗan soma mata rawa kamar ba nata ba. jingina ta ɗan yi da jikin gadon na ɗan lokaci kafin ta nufi madubi. Idonta kai tsaye ya sauka akan madubin ya sauka a kan fuskar kanta…Amma ba fuskar da ta saba gani ba ce jiki, cikin abinda be wuce seconds ta hangi fuskar John a cikin madubin daya saka ta fasa ihu tana me furta.

“Ahh!”

Ta ja baya da sauri, zuciyarta na bugawa da ƙarfi kamar zata fasa rufin fata bakwai ɗin dake ƙirjinta ta fito.
“Me hakan ke nufi…?” ta furta da muryar da ke rawa. Jin motsin kamar za'a shigo ne ya sakata saurin faɗawa toilet ta rufe kawai tana fasa kuka bayan ta saki shower yanda ko waye ta shigo ba zai ji sautin tashin kukan nata ba. “Baby ambasa ki na ina ne haka?” Daddy'nta daya shigo da kansa don jin shirun yayi yawa shi ne ya biyo bayanta, daidai kuma lokacin da take fitowa jikinta gaba ɗaya da laimar ruwa tana murmushin yaƙe tace. “Daddy ina zuwa fa wanka ne nayi...” fita yayi don bata damar shiryawa, kayan jikinta ta zare ta saka wasu marasa nauyi ta fesa tura. Daga haka ta nufo ƙasa ta sauƙo sedai ganin Mamynta a dining ɗin be mata daɗi Ba. Su kuwa a nasu ɓangaren tun kamin ta iso wannan shegen ƙamshin nata tuni harya gama sanar musu cewar zuciyar Daddy'n ce tafe, daga gefen Daddynta ta zauna tana wani bata fuska da kumbure kumburen ba kawai. plate ɗin dake ɗauke da donut,pizza taja zuwa gabanta ta ɗauka tana ɗora shi kan cinyarta gefenta ga kwalin picanto ɗin data fito dashi zata ci... Kai tsaye metres sarvice ɗin dake aikin shirya kitchen ta kwalama ƙira tana bata umarnin kawo mata fruits masu kyau daga fridge. Babu jimawa kuwa se gata hannunta riƙe da plate da yankakkun fruits ɗin a ciki masu sanyin kuma kamar yacce ta buƙata,

14 / 31