Advertisements
Chapter 28 Reading DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

DUHU na DUKAN Lokacin Duniya Ta Haɗu By AMMEY LAYLERH

Author :  AMMEY LAYLERH Category :  Complete Novels

Chapter   28 / 31

81K to 84K   out of 91.1K words

da takeaway ɗin da yayo musu as breakfast. Da kyar ya iya tashinta ya lallamata su kayi, kana ya saka tayi wanka ta sake kwanciya har wajajen sallar zuhr, da zai fita masjid ya data yace tayi Sallah ya fita a gurguje ya barta gudun kada yayi let. Koda ya dawo abinda ya bashi mamaki shi ne yadda ya barta kwancen haka ya dawo ya sameta, don haka ya sake tashinta amma ta farka cike da jin haushin katse mata baccin nata take cewa ita ya kyale ta ba zata yi sallar ba. Duk yadda yaso tashi da fahimtar da ita sallah akan lokacinta kin tashin tayi, haka ya fita ya kyale ta. Yana fita babu jimawa kawayenta na Amana Sofy da Aysha suka shigo, nan suka barar da guntun lokacinsu zaune har bayan sallar asari amma kaf cikinsu abin mamaki babu wanda yayi motsi sema topic da suka sanja zuwa ta tambayarta ya daren ta na jiya ya kasance. Wani murmushi me kyau tayi tana basu labarin yadda ya wahal da ita tana dariya tana komai dake basu labarin duk abinda ya faru tun daga farko har ƙarshe. Wani irin faduwa Ibraheem dake sanyo kansa kenan yayi yana jan burki kuwa babu shiri. Har bayan magrib suna gidan se daf da Isha'a kana suka tafi, bayan sun jidi abinda ransu ke so a gidan. Washe gari ma hakan ce ta sake kasancewa bayan yasha fama da ita kan Isha'a da se da kyar tayi ta da magrib a gabansa, wanda tashin farko a sallar nata ya fahimci akwai manya manyan gyararraki. Amma se ya sake bama hakan uziri da may be ciwon jikinta ne.... Ɗan kallonta yayi lokacin da take fitowa daga bedroom zuwa parlourn da yake zaune yana karatu, ya ɗago idanu kawai ya kalleta tare da furta.

“Kin yi latti against.”

Ya faɗa cikin nutsuwa yana ci gaba da karatunsa, babu jimawa ya matso zuwa gabanta yace ta masa dori, gaban Yasmine yayi wani irin faɗuwa a ranta tana mai furta. 'Na shiga uku ni Hauwa wanne irin miji na aura haka?' don haka seta shiga matse fuska ta nemi wuri taba kwanciya kamar bata ji shi ba saman sofa, Ahankali ya ajje alqur'ani ɗin yana komawa inda take kwancen ya dago kanta yana ɗorawa saman cinyarsa daya koma sofar ya zauna, cike da murmushi saman fuskarsa yace. “Ohhh na fahimta dake ku manya ne shi yasa ba sai da alqur'ani ba?”

'Innalillah wai me nake shirin fuskanta haka ni Yasmine, nida ko sabbi seda kyar nake rutsa ta ya taso ni gaba da wani maganar dori, Sallah, Wanka akan lokaci ba kyau kwana da najasa na shiga uku na bar duniya!, ni da nake murna nayi auren yanci babu takura babu komai tun da sabon tu ba na aura amma sai gashi tafiyar tun bata kai ko ina ba na fara da fuskantar ƙalubale da barazana..... ' “Babe ka barni nayi bacci kaina ke min ciwo pls” kan ya taɓa yana fara ɗan tofa adda'ar da yake a bayyane data bama Yasmine ɗin mamaki, don ita tana jin a cikin adda'oi dai, basu fi kala biyar ba wanda ta iya, daga Innalillah wa'inna ilaihi raji'un, sai kuwa irin su Subhanallahi Hasbinallahu wani'imal wakeen, Duk dai irin wanda ake tsinta a bakunan jama'a ne suma ɗin ta tsinta, yo ina take zuwa Islamiyyar?, Islamiyyar da idan anga taje wani malamin taso cima mutumci. Ahankali ta sauƙe boyayyar ajiyar zuciyar amsar uzirin nata da yayi, amma kuma wata zuciyar na ce mata, idan yau kin tsere gobe fa, ko zuwa anjima. Ƙululu haka taji cikinta ya bada sautin da har shi seda yaji har yana dafe cikin nata. Wani gumin tashin hankali ya shigo keto mata, don haka wata zuciyar kai tsaye ta bata bad idea akan cewar, fuska zata dena bashi, bare har yayi tunanin kawo mata wargi kuma, da hakan kuwa ta yi na'am tana bama kanta kwarin gwiwwa akan hakan.

Sannu a hankali sabbin halayen data fara masa suka fara fitowa fili. Kamar su magana mai ɗauke da rashin ladabi idan ya mata gyaran wani kuskure haka. Daga ya mata zata ta be baki tace.
“Ka daina min wannan preaching ɗin, don ni ba irin matan da za ka canza ba ce, in ma banda haka kai yaushe ma ka shiga cikin muslumcin?” Shi kuma kai tsaye yake bata amsa da.

“Ba zan canza ki ta karfi ba yas-mine kawai Ina nuna miki hanyar da na ga itace me ɓillewa a gareki.” ita kuma sai tace.

“Ka ga dai! Wannan ne matsalar ka! Kana ganin kai ka fi kowa!”

Ahankali ya kawo numfashi yana ayyana tabbas anbar tarbiyya da rashin tsarin rayuwar da aka bari a baya.

Washegari da safe ma kin Sallah tayi, da yayi mata magana sai ta juya masa baya kafin cike da raini ɗauke a fuskar ta ce.

“Again yau ma dai lecture ɗin?”

A natse IBRAHEEM ya girgiza mata kansa yana nuna mata kusa da inda yake zaune shima yace.

“Zauna.”

Ta zauna din kuwa tana huhhura hanci tana kuma harararsa, cike da nutsuwa sosai yace.

“Yasmine… ba zan dinga faɗa miki kina dauka ba? And kina ganin wannan rayuwar a hakan zamu ɗore kuwa? Ki sani ita fa rayuwar kanta ba an gina mata ita bane don muyi yadda muka so kawai, ubangiji yana da nashi nufin na bauta masa da cike dokokin da duk ya gindayamana”.

Amma maimakon Yasmine ta rusuna sema wani murmushi da tayi tare da cewa.

“Ni haka na taso ban san takura ba, shi yasa na taso bama wani cikakken shiri da Mamy saboda exactly yacce ka fara nuna takurarka a kaina haka take min, So ina ganin indai kana son mu zauna lafiya ka dakatar da duk ababuwan da ka fara a kaina na nuna takurawa, Sallah kuma time to time idan naga nayi balance free na kan daure koda biyu zuwa uku ce nayi a rana, ita dai asba inayi dama, na kan yi magrib sabo da sauƙinta, so wani bin ma na kan daure nayi zuhr, Isha'a da la'asari ce ban fiye son yi ba gaskiya....” Ai tun da ta fara maganar Ibraheem yayi wani irin ƙamewa cike da wani shegen tashin hankali yake kallonta, shi da yake tunanin ya sama hasken da zata ci gaba da haskaka rayuwarsa ashe ba tare daya sani ba ita ɗin.... *DUHU NA DUKAN DUHU* Ce a cikin rayuwarsa gaba ɗaya?. A wannan lokacin ne IBRAHEEM ya fara fahimtar abu guda shi ne cewar, ba rayuwar aure mai sauƙi ya shiga ba… kawai ya shiga aikin gyara zuciya ne da kuma rayuwa wanda ba karfi hakan ke buƙata ba illa hakuri, addu’a, da kuma hikima. A wani irin hankali yaja idanunsa yana lumshe su, tare da furta kalmar.

“Ya ALLAH!… ka bani hikima kafin in rasa komai a cikin wannan tafiyar ta.
*DUHU NA DUKAN DUHU* TSAKANIN NIDA YAS-MINE....”

*AMMEY LAYLERH ✍️ *

08104493215







*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 28

Paid book

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.


Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

♡♡♡♡

ꨄ Washegari tun da safe IBRAHEEM ya shiga wani irin yanayi na tunani.
Maganganun YASMINE ne kawai ke ta yawo cikin kansa kamar ana maimaita masa su. “Ni haka na taso…ba zan iya wannan takurar ba…” daya tuna maganganun se yaji wani abu me kama da rauni na wani irin kama zuciyarsa sosai. Don haka gaba ɗaya yake a wani irin so silent gaba ɗaya yinin ranar. Koda yaje masallaci shiru kawai yayi bayan idar da salla, hannunsa riƙe da Alƙur’ani amma zuciyarsa cike da wani irin nauyi. Sheikh Albani ne ya shigo ya zauna kusa da shi cikin nutsuwa yana me ambatar sunan shi. “IBRAHEEM…”
A hankali ya ɗaga idanunsa ya kalli Sheikh ɗin. “Na lura da gaba ɗaya kwanakin da suka rufa ma na bikin nan naku baya gaba ɗaya hankalinka ba'a
kwance yake ba.” Shiru kawai yayi kafin daga bisani ya sauke ajiyar zuciya.
“Na shiga tsoron abinda ke gaban ne Sheikh…” Cikin hikima Sheikh Albani ya ɗan murmusa yana mai furta “Ka san me yasa ALLAH ya haɗa ka da ita?”
Kai ya girgiza alamar a’a. “Shekaru da yawa wata ƙaddara ta jingine maka wani keɓantaccen kadarar da kowa ya gaza mallaka... IBRAHEEM ya gyada kai a hankali don bai da abin cewar daya wuce gyada kai din.

“To wataƙila… ita ce jarabawarka ta farkon da zata sadaka da ainihin Hasken da nake hangowa tattare da kai, wani irin sirrin haske ne da ba kowa ne zai iya hangosa ba, amma kaci gaba da godiya ga ALLAH nesanka ce ke shirin matsowa kusa nan ba da jimawa ba..”
Sosai maganganun suka ratsa Ibraheem kasamcewar da turanci ne yayi maganar. Kai tsaye daga nan bayan ya dauki karatun ya dawo gida, sedai tun kafin ya gama isowa compound ya soma jin karar kiɗa!, kiɗan da yafi komai tsanarsa kaf duniyar. YASMINE kuwa dake tare da ƙawayenta da kusan kullum suna hanyar gidan ne suke ci gaba da shan music nasu suna dariya har Aysha na ɗan motsawa daga zaunen da take, domin dama can yafi Sofy rashin ji don ita babu inda bata fantamawa. Sai dai a badinin hakan a cikin zuciyar Yasmine wani irin tsoro da rashin nutsuwar dawowar gidan a koda yaushe take, domin a karo na farko a rayuwarta ta haɗu da namijin da baya tsoronta, baya bin son zuciyarta, kuma baya gajiya da jan ta zuwa ga ALLAH.


*JIGAWA*

A can JIGAWA kuwa JANNEERH ce zaune bayan gama gabatar da tafsir na matan data gama, wanda suke cakuɗe da yara da kuma manyan matasan yan mata da masu aure da take gabatarwa duk Alhamis kasancewar Alhamis ɗin babu karatu. Wata ƙaramar yarinya ce ta matso kusa da ita tana murmushi tace. “Malama… kin taɓa yin waiting ɗin mutum da baki taɓa gani ba?”Tambayar data saka JANNEERH tsayawa cak, zuciyarta tayi wani irin bugawa. Kafin
ahankali ta kalli yarinyar cikin muryan da bata gama fita ba tace.

“Eh…”

Sai ta nunama yarinyar setin ƙirjinta a hankali tace.

“Saboda wani lokacin… zuciya tana gane wanda ƙaddara ta rubuta mata tun kafin idanu su taɓa ganinsa…”

★...

Wata irin nutsuwa ce ta mamaye harabar gidan MALAM MUHAMMAD ALIYU BAITA bayan dawowar JANNEERH daga tafsirin mata. Kamar kullum cikin kamala da nutsuwa take tafiya, hannunta riƙe da littattafanta yayin da babban hijabinta ke jan ƙasa kaɗan. Duk wanda ya ganta sai ya tsaya ya bita da kallo, ba wai saboda kyau kaɗai ba… A’a. Saboda akwai wani irin natsuwa da kwarjinin dake tattare da ita da ke saka mutum jin kamar yana kallon mutumiyar da ba ta cika shiga cikin hayaniyar duniya ba. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin gidan.
“Assalamu alaikum…” Sai dai kamar kullum…shiru ne ya amsa mata daga ɓangaren matan mahaifinta. Mama Rukayya ce ta fara kallonta da wani irin rainin wayo kafin ta ja tsaki ƙasa ƙasa ta amsa da. “Wa alaikis salam…” ta karasa amsawa a yatsine. Mama Bilkisu kuma ta ɗan kalli hijabin JANNEERH tana murmushin gefen baki tare da furta.
“ALLAH ya ƙara mana malamai…” ta faɗa tana kallon yar ƴar uwar cin mushenta suka saka dariyar dake cike da ma'ana. JANNEERH ta sunkuyar da kanta kawai kamar bata ji komai ba, amma duk da haka basu kyale taba musamman ma ganin babu wilgin ummieh a wurin, inda tana kokarin wucewa ne Mama Bilkisu ta sake cewa.
“To wai ni Rukayya… har yanzu kamar babu wani motsi fa da nake ji haka ne?”
Sai suka sake saka dariyar dai kusan tare, kafin Mama Rukayya ta cafe da.
“Ko dai aljanune ke tsoratar da mazajen?” cewar Mama Rukayya.
Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar JANNEERH, duka kalaman sukan zuciyarta kai tsaye cikin tsakiyar kirjinta, amma duk da haka…
ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba.
Domin ta saba tun tana yarinya take rayuwa cikin irin wadannan ire iren kalaman.

'Yarinyar nan ta cika tsarki da yawa…'

'Kamar ba mace ba…'

'Wa zai aure ta?'

'Kowa tsoronta yake…'

Wadannan kalaman sun zama kamar iska a rayuwarta. Sai dai duk lokacin da aka furta su… zuciyarta na zubar da jini ne a ɓoye. Adda'a tayi A hankali tana ci gaba da tafiya zuwa ɗakin Ummien ta.
Tana isa ga mahaifiyar nata taji
kamar wanda aka cirewa nauyi a kirjinsa haka ta sauƙe ajiyar zuciya.
Ummie na zaune kan sallaya tana Jan carbi. Tun daga kallon farko ta fahimci wani abu ya sake faruwa ke nan, duk da dai da ababuwan matan uban nata yayi sauƙi yanzu ne suka dawo dashi sabo tsakankanin ƴan satikan nan.

“Hafsat…”

Mahaifiyar nata ta kira sunanta cikin taushin murya. JANNEERH ta zauna kusa da ita tana kokarin ɓoye damuwarta ta amsa da. “Na’am Ummie…” Sai dai tun daga yanayin yadda maganar ke rawa ummien ta fahimci wani abu. Murmushi Ummien tayi tana shafa gefen fuskar ta tare da cewa. “Sun sake magana ko?” Idanun JANNEERH ne suka cika da hawaye nan take, kafin ta girgiza kai da sauri tana mai bata amsa da.

“A’a Ummie…”

Sai dai muryarta ta tona ta a wannan karon ɗin ma, don haka Ummien ta ja ta jikinta a hankali kamar ƙaramar yarinya ba ƴar shekaru ɗai ɗai har ashirin da bakwai bace gabanta.

“Ki dena ɓoye wa zuciyarki ciwo Hafsat…” Ta faɗi wanda ya saka
hawayen JANNEERH suka zubo da take ta kokarin makalewa.

“Ummie… shin ni akwai wata matsala a tare dani ne ban sani ba?”
Tambayar ta fito da wata irin rawar murya. Kafin cikin rawar murya ta ɗora da cewa. “Me yasa duk inda na shiga sai a dinga kallona kamar ni ba cikakkiyar mace ba ce saboda ban yi aure ba, ko ina da wani nakasu ko tawayar halittar da ni bana iya ganewa kai na Umm?”
Wani irin runtse ido na ɗan lokaci ummien tayi saboda tausayin yar tata.
Cikin nutsuwa tace. “Ki saurare ni da kyau Hafsat…” Ta ɗago fuskarta ta share mata hawaye. “Ba kowanne jinkiri bane rashin dacewa.” tayi maganar tana kamo hannuwanta cikin nata taci gaba da fadin. “Wani lokacin ALLAH yana ɓoye maka alkhairi ne har sai lokacin da zuciyarka zata iya ɗaukarsa.” se ta ɗan fesar da wani numfashin azaba bawai don bata jin ciwon hakan ba, amma haka ta ci gaba da mata magana cikin hikima.

“Kin san me yasa mutane suke magana?”

Kanta jannerh ta girgiza mata alamar A ahhh.

“Saboda basu san me ALLAH ya tanadar miki gaba ba.” Sai ta ɗan murmusa kaɗan kafin ta ɗora da cewa.

“Mutane suna ganin wanda yayi saurin aure shine mai dace…” ta sake fesar da wani numfashin me cike da bacin rai.

“To wa yace haka?”

Kafin a wani irin hankali ta ɗaga haɓarta jannerh ɗin kaɗan tana kallon cikin idanuwanta da suke cike da rauni tace.

“Wasu auren nasu jarabawa ne. Wasu kuma jinkirin nasu rahama ne.”

Kalmar ta shiga zuciyar JANNEERH sosai, sai dai har yanzu tana jin wani irin ciwo a kasan ranta. Cikin sanyin murya tace. “Amma Ummie… ni ma ina son a SONI !, INA SON naji wani yace yana SONA ...” Murya ta karye amma haka taci ga da faɗin “Ina son na kasance a ɗakin MIJINA nima…Ina son wani ya kalle ni nima kamar sauran mata ya ce ni ce natsuwarsa…”

Wani irin tausayinta ne ya sake kame zuciyar Mahaifiyar nata. Ta rungumeta sosai tana shafa bayan ta cike da bata kwarin gwiwa tace. “Kuma zai zo IN SHA ALLAHU HAFSAT…” ta lumshe idon ta tana ɗauke kwallar data cika idon ta tace.

“Na rantse miki da ALLAH zai zo. Saboda mutumin da zai zo cikin rayuwarki ba zai zo saboda kyanki ba ne, ba kuma zai zo saboda sunanki ba ne… Zai zo ne saboda ƙaddara ta gama rubuta sunanki cikin zuciyarsa tun kafin ku haɗu…” A lokaci guda wani irin bugawar zuciya JANNEERH taji.
Kamar akwai wani abu da ke kokarin tasowa daga cikin kirjinta, wani suna, wata fuska… amma duk ta kasa gani.
Sai kawai ta dafe ƙirjinta da sauri har
Ummie ta kalleta da damuwa.

“Hafsat?”

A hankali JANNEERH ta lumshe idanunta. Sannan ta furta cikin muryar da bata gama fita sosai ba tace.

“Ummie…Kullum zuciyata na jin kamar akwai wani mutum da yake kirana…”

Ta ɗago idanunta masu cike da ruɗani ta ɗora ta faɗi

“Amma ban san ko waye shi ba…”

*AMMEY LAYLERH ✍️ *

08104493215






*◦༺DUHU na DUKAN duhu°࿐*
_Royalty versus love_

~Maryam Naseer Mirrah~

*AMMEY LAYLERH ✍️*

Page 29

Paid book

𝙔𝙊𝙐𝙉𝙂 𝙏𝘼𝙇𝙀𝙉𝙏𝙀𝘿 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎.


Duk mai buƙatan karanta book na *DUHU na DUKAN duhu* yamin magana ta WhatsApp da wannan phone number ɗin 08104493215

*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ*

♡♡♡♡

ꨄ Wani irin kallo Ummie ta tsaya yiwa JANNEERH ɗin…Kallo mai cike da zurfin tunani da kuma wani irin tsoro na uwa.
Domin ba wannan ne karo na farko da Hafsat ke furta irin waɗannan kalaman ba.Tun shekarunta na ƙuruciya akwai wasu mafarkai da take yawan yin su.
Mafarkai masu cike da duhu… hawaye… da wani mutumin da bata iya ganin fuskarsa gaba ɗaya, sabo da yana a cikin tsakiyar wani irin DUHU ne da ko tafin hannu ba'a iya gani. Sai dai duk lokacin da zata farka zuciyarta cike take da wani irin raɗaɗin kewa. Kewar da take jin kamar ta rasa wani ɓangare na rayuwarta ne. Ummie ta ɗan shafa kanta cikin lallashi kafin tace.

“Ki dena tsoratar da zuciyarki da tunanin da baki da tabbacin sa Hafsat…” ta sake janyo ta jikinta kamar yar shekara biyu. “Wasu lokutan zuciya tana jin abubuwan da basu faru ba tukuna…” JANNEERH ta sauke ajiyar zuciya. “To amma Ummie…” Ta ɗago idanunta masu cike da ruɗani.
“Me yasa duk lokacin da nake yin addu’a…sai naji kamar ina roƙon ALLAH ya kare min wani mutum ne daban?”

28 / 31